Showing 3001 words to 6000 words out of 180087 words

Chapter 2 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

ɗan hasken da kan leko ta window dake can sama karami na hasken rana ko wutar lantarki. Ta matuƙar zama wujiga-wujiga da fita a hayyacinta dalilin ƙin cin abincin da ake kawo mata sau ɗaya a kowane yini, sai madara. Tun a ranar farko ta gama fahimtar akwai babban ƙuli da ya kamata ta fara fahimta kafin zuwan wannan lokacin. Zuwa yanzu ta gama fahimtar su Miran Jasim sunyi amfani da ita ne, sunyi amfani da ita duk da itama da wannan ƙudirin a ranta. Sai dai kuma cika baki ne kawai, ta fahimci a hakanne a randa ƙaddarar dake tafiya da rayuwarta ta yanzu ta tabbata. Dole ta kira hakan da ƙaddara, dan inba ƙaddara ba babu ta yanda zata iya cutar da waninta mai bautar ALLAH da hanunta. Ƙwarai da gaske tanajin zafi, matuƙar zafi na rasa ƴan uwanta guda biyu a dalilin auren Shahan-shan. Hakan kuma shine ya zama sanadin komai na jin kangarewar zuciya da ƙudirin da babu tabbacin iya aiwatar da shi. Komai ya nema canja mata a lokacin da tai tozali da fuskarsa, bata san dalili ba ta dingajin kamar shi bazai iya kasancewa mai cutarwa ba, ta dinga jin dole akwai abinda yake ɓoye da ya kamata ta sani, sai dai a lokacin data gama shirinta tsaf akan hakan ƙaddara ta sake sauyata, komai ya nema rushewa a zuciyarta batare da riƙe wata makama mai ƙwaƙwarar hujja ba ta yanke hukunci ga wanda bata da wata hujja ko shaida akansa, wanda maimakon ya bada umarnin ɗaukar mataki a kanta ya nuna mata hanyar kuɓuta ta hanyar bata umarnin zubar da madarar da bata san yanda akai takaita gareshi ba. Amma kash, da alama ƙoƙarinsa na kubtar da ita bai tabbata ba. Dan gashi maƙiyansu da alamu suka nuna shirinsu bana yau bane sun gama cin nasara, nasara biyu a lokaci ɗaya, kaudashi da kaudata itama batare da ta san mi taci burin son sani ba. Sai ma sake tsunduma a duhuwa tayi. Dole ta kira gaɓar da suna duhuwa, dan tanada tambayoyi masu ɗunbin yawa akan kanta ma. Mafi girma a ciki sune taya Ajmaal ya zama Shahan-shan? Wake halaka matansa idan har ya kasance ba shi bane? Miyasa bai iya cewa komai bayan shine keda hakkin cewar? Da gaske ta rasa iyayensu suma da ɗan uwanta tilo daya rage kokuwa duk cikin shirin su Miran Arshaan ne?.... Shi kansa Sir Fawzan tana da bukatar sanin wani abu a kansa. Sai dai ta yaya? Ta wace hanya? Duk yanzu bata sani ba. Zafafan hawayen da a kwana ukun nan bata taɓa gwada sharewa ba suka sake zubowa masu zafi. Ta lumshe raunanan idanunta murmushi mai ciwo na suɓuce mata. Fuskarsa take kallo a kan allon zuciyarta a lokacin da yake sakar mata murmushin da har abada bazai taɓa zama mai gogewa ba a tarihinta. Siririyar dariya da tafin dake shiga kunnenta a bazata ya saka ɓacewar murmushin kan fuskar tata da buɗe lumsassun idanun nata lokaci guda..
        Kanta ne ya sara da ƙarfi, da sauri ta maida su ta rumtse sakamakon hasken daya ratsasu mai kaifi, yau kwananta uku tana a cikin duhu, dolene karfin idanunta ya samu rauni a lokacin da aka samar da haske cikinsu. Duk yanda taso sake buɗewa ta kasa, dan har cikin kwakwalwarta taji shigar kaifin hasken na bazata. Ta cije lips a hankali tana mai ƙoƙarin ganin ta riƙe hawayenta da son danne tasirin raɗaɗin dariyar izgilancin da bata san daga wanda take fita ba. Sai dai zuciyarta na bata Miran Jasim ko Miran Arshaan ne. Bata da ƙarfin tashi daga kwancen da take, dan haka tai jarumtar sake buɗe idanun nata sannu a hankali a karo na biyu, zuciyarta na ambaton (Hasbinallahu wani'imal wakil). Da ƙyar ta iya tsaidasu akan Miran Jasim dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya bisa kujerar da basai tayi wani tunani ba da ita aka shigo masa. Raɗaɗi idanun ke mata, gasu a kumbure jajur amma haka tai jarumtar cigaba da tsaidasu a kansa harya gaji dan kansa daga dariyar yay shiru..
        _“Zawgatu al-ibn! (Daughter in-law) proud of you. Kin zama ta daban a cikin dubun da bazan so na manta ba. Duk da nima dai nasan ban cancanci ki manta ni ba ta sauƙi, na san na cancanci zama abin alfaharinki a yanzu. Cikin sauƙi na cika miki burinki, gaskiya na cancanci karɓar tukuyci na musamman. Koda yake kwantar da hankalinki bama sai kin bani komai ba, zamanki anan ma babban tukuyci ne. Zan sake faɗa “Ina al'fahari da ke”. Yay wata ƴar dariya mai ƙona zuciya dake shiga har ƙarƙashin zuciyar Iffah, amma kasancewar ta jarumar gaske mai ƙarfin zuciya sai batako motsa ba, raunanan idanunta kuma har lokacin suna a kansa duk da raɗaɗin azabar shigar haske dake ratsasu har yanzu. Dan kansa ya tsagaita da dariyar tare da gyara zamansa yana binta da wani shegen kallon ƙurulla har yana lasar lips ɗinsa kaɗan.
      “Bana son ki kalleni da irin kallon da nake da yaƙinin shine a allon zuciyarki Zawgatu al-ibn!. Ina son ki dai fahimci ni ɗin mutum ne mai son kansa, zan kuma iya kauda koda yatsan hannuna ne in har zai iya zame min cikas domin samun cikar burina”. Yay wata ƴar dariya a zahiri, a can ƙasan ransa kam kallon da Iffahr ke masa ko ƙiftawa babu yay masa tsaye a kan allon zuciya, amma kasancewar sa gwani sai ya shanye babu alamun hakan a kan fuskarsa. Sai ma miƙewa yay cike da kasaita, a gabanta yaje ya tsugunna tare da kai hannunsa fari sol zai shafa fuskarta. Cikin wata irin zabura da ƙarfin da Iffah bata san yay ragowa a jikinta ba taja da baya tana watsa masa wani mummunan kallo har hucinta na bayyana akan hancinta. Murmushin gefen baki yay da lumshe idanu, sai kuma ya janye hannun nasa cikin ɗage kafaɗa da son basarwa. Idanun ya sake lumshewa da buɗewa a kanta yana shu'umin murmushin dake sukar zuciyar Iffah matuƙa. “Hakan ma ya burgeni Zawgatu al-ibn”.
     Harara ta watsa masa kai kace idanun zasu faɗo, cikin kaushin muryar da ke fita da ƙyar ta fara magana a karo na farko cike da gargaɗi. “Kai fagalalle ka rubuta ka ajiye, a duk ranar da koda ɗan yatsan ka yay kuskuran taɓa jikina ni Fhareedah bint Zayyan na maka alƙawarin karyasa, karaya irin wadda har kabar duniya tabonta bazai goge a idanunka da zuciyarka ba. Iffah babban goro ce sai magogin ƙarfe”.
       Tabbas maganarta ta matuƙar sukarsa, ta kuma zauna daram bisa zuciyarsa tamkar rubutu akan dutse, amma a zahiri sai ya murmusa harda lasar lips a karo na biyu. “Immm bazance kinyi ƙarya ba kam, nima shaida ne ke ɗin babban goro ce, kuma tabbas sai ni magogin ƙarfe. Ina miki albishir daga yau ki fara takaba da irga kwanakin zamowarki babban goro ta magogin ƙarfe ni Shahan-shan na ƙasar ruman Tajwar Jasim ibn Abdul-majeed Aliy! Nayi alkawarin sai na maidake karuwar da zata zama a ƙololuwar abin kwatance a duniya duka bama ƙasar ruman kawai ba. Daga yanzu kisa a ranki ƙaddararki ta fara a hannuna hhhh!!!”.
       “hhahhaha!!!”.
   Itama Iffah ta fara dariyar kamar yanda yake yi, sai dai tata cike da ƙarfin haline kawai. Tsagaitawa yayi da tasa yana kallonta cike da mamakin da yake ƙoƙarin dannewa, sai dai kuma fuskarsa na ƙoƙarin fallasa shi. Ganin bata da alamar tsagaita dariyar tata ya miƙe cikin zafin rai....
      “Alfahari da ƙaddara akan Fareedah rauni ne ai Aam! Dan ƙaddarar itace hasken fitilar nasarar Iffah. Ƙyaƙyƙyawan mafarki Uncle”. Ta ƙare maganar da cigaba da dariyar da tafi ta farko saka ƙuna a zuciya.
     Miran Jasim dake tsaye cak shi bai fitaba shi bai dawo ba yay wani irin cizar lips, sai kuma ya fice cikin zafin nama dan har ƙarƙashin ruhinsa dariyar Iffah ke shigarsa.. Sai da ta daina jin takun sawunsa gaba ɗaya da kulleta da aka sakeyi sannan ta tsagaita itama, a maimakon dariyar sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Ta tabbatar duk abinda Miran Jasim ya faɗa zai aikata mafiyinsa, sai dai ba tana kuka bane akan kanta, tana kuka ne a maimakon talakawan ƙasarta da Tajwar Eshaan bin Haysam Abdul-majeed. Tana kuka ne akan tsananin buƙatar son sanin zahirinsa da baɗininsa da su Miran Jasim suka zaburar da ita. Sai dai tasan guri ya ƙure, ƙurewa irin ta numfashi da ƙarewar rayuwa. Koda ace shi ya rayu ita bazata rayu ba, koda ace wasun sa na buƙatar ta rayu ita bata buƙatar rayuwar a halin yanzu.........✍️


      (ALLAH sarki Iffah 😭🙏).


   
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (03)



......Kamar yanada Malikat Haseenat ta faɗa an sake tsaurara tsaro a ɗakin da Iffah take, bana dakaru kawai ba harda tarin jami'an tsaron da Shahan-shan kawai suke bama tsaro tako ina yayinda ta kasance cikin masu iya bibiyar komai kai tsaye. Shi kansa abincin da ake kai mata a yanzu ya kasance na musamman dake samun saka ido, dan a rana ta biyar da yunwa ta nema mata illa sai dai likita ya shiga ya dubata. Dan dole ta koma cin abincin sai dai bata wuce lauma uku ko kurɓa uku na madara take ta ajiyewa..



....A ɓangaren masu faɗa ajin masarauta ana ta cigaba da tattara bayanan da suka kamata ta hanyar bincike. Sai dai tsaiko na farko da aka fara samu shine rasa cctv footage na sashen Tajwar Eshaan da ga asubahin randa al'amarin zai faru har zuwa lokacin isar su Daneen Ammarah da su Miran Jasim sashen. Sai wayar Iffah da itama aka nema ƙasa da sama aka rasa da lap-top ɗinta. Wannan al'amari ma ya kawo ka-ce-na-ce bana wasa ba har takai jami'an tsaro cafke mai kula da ɗakin tsaron aka garƙame. Amma kuma juyin duniya yace bai san yanda akai ba. Hakama hadiman sashen Iffah kaf ɗinsu an tattare, suma kuma sun rantse sun kuma basu san yanda akai wayar Iffah da lap-top ɗin sukai ɓatan dabo ba. Ba kuma suga wani ya shigo sashen ba. Waɗan nan abubuwa na rashin makamar tabbatar da Iffah akan laifin da kowa keda yaƙinin ta aikata ya kawo rabuwar kai da rikici babban akan mata hukunci. Yayinda su Miran Jasim suka sha jinin jikinsu, dan haka suka zama ɓangaren masu nuna kawai a kashe Iffahn. Ɗayan sashen kuma da suka haɗa da zuri'ar Sayeed Khairul-Bashar suka bore akan bincike na har sai an tabbatar a kuma ji dalilinta dan in ma har ta aikata to dole akwai saka hannun wasu a masarautar.

Rikici ne bana wasa ba, dan har takai anyi wani zaman a karo na biyu amma sam babu masalaha daga kowane ɓangare. Ɓangaren kuma dake ganin kashe Iffahn shi yafi sauƙi sune ɓangare mafi ƙarfi dan da yawansu na jikin Tajwar Eshaan ɗin ne. Malikat Haseenat ce kawai ke nuna a dai cigaba da bincike kar a aikata aikin dana sani. Hakama Daneen Ammarah sam zuciyarta taƙi aminta Iffah zata aikata bisa raɗin kanta, idan ma har ita ta aikata ɗin kenan tunda har yanzu babu wata shaida dake nuna itace ɗin ta bashi madarar dan bayan ita suma masu dafa masa abinci da amintacen hadiminsa duk suna a rufe. Ƙulle-ƙullen su Miran Arshaan ne yasa dukan zargin yafi ƙarfi akan Iffah. A yanzu haka kuma sunyi kane-kane wajen sake rura al'amarin da nuna ɗaukar zafi fiye da kowa musamman Miran Jasim daya kasance mai riƙe da masarautar har zuwa samun lafiyar Tajwar Eshaan da ake fata...



★★.... ★.....



Har cikar kwanakin mako babu wani cikakken masalaha akan al'amarin, sai ma ɗaukar zafi da kowane ɓangare suka sake yi. Iffah kuma taƙi taɓuwa bisa jajircewar Malikat Haseenat na sai fa anyi bincike. Wannan kafiya ta saka Miran Jasim da Miran Arshaan kasa zaune da tsaye. Barbushi kuma ya tabbatar musu in har fa Malikat Haseenat na numfashi bazasu taɓa samun yanda suke so cikin sauƙi ba. Dan haka ya basu zaɓi biyu. Kodai su gaggauta kasheta da hanunsu, ko kuma suyi ƙoƙarin tunzura Malikat Bushirat dayin amfani da ita kamar yanda sukayi da Iffah ta kawar musu da ita. Hankalinsu ya tashi, dan kashe Malikat Haseenat abu ne ba ƙarami ba musamman a wannan gaɓar da take taka wata rawa mai banbanci da tasu duk da tafisu kusanci da Tajwar Eshaan. Duk yanda suka tattauna da aunawa sun gafa wannan hanyar mai wahala ce a gare su, dan haka suka zaɓi nufar sashen Malikat Bushirat ɗin domin fuskantar ta kai tsaye. Fatansu zaman ya zame musu jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, dan tunda aka fara rikicin nan Malikat Bushirat taƙi tofa komai ma, ta tattare hankalinta kacokan akan ganin lafiyar Tajwar Eshaan da aka hana kowa gani a masarautar sai ita da Malikat Haseenat har zuwa yau da ake cika kwanaki tara da faruwar komai.......



★... MALIKAT BUSHIRAT ★...



Yanda take magana cikin fitar ɗacin sauti tana kaikawo a fusace zai tabbatar maka ranta a ɓace yake ƙololuwa. Malikat Bushirat kenan da tun faruwar al'amarin nan babu wanda zaice yaji bakinta duk wannan sa toka sa ƙatsin da akeyi. A yanzu babban burinta bai wuce samun lafiyar tilon ɗan nata ba, batun hukunta wadda ta zama sanadin komai wato Iffah kuwa duk faɗi tashin da ake komai tana sane, sai dai bata shirya saka baki ba a yanzu acewarta akwai lokaci. A tsahon kwanakin nan dukkan wani motsin masarautar ruman a cikin kunenta yake fiye da masu kai kawon. Hauhawa da bunƙasar ɓacin ranta na yanzu kam yana da alaƙa ne da tattaunawar ta da su Miran Jasim, zaman nasu kuma kacokan ya alaƙantu ne ga hana hukunta Iffah da Malikat Haseenat tayi kai tsaye har sai anyi binciken da ta sharɗanta.

Irin wannan fusatar ga Malikat Bushirat shine fatansu, dan haka suka dubi juna cikin son danne murmushin kan fuskokinsu. Zama suka gyara tare da sake buɗe sabon shafin abinda suka faro. Miran Arshaan ya sake marairaice fuska mai cike da tsantsar damuwa yana mai duban Malikat Bushirat..

“... Ni a ganina ɓacin rai ko damuwa bashi ne zai zame mana mafita ba. Mu zauna mu tattauna yanda abinda ya dace kafin lokaci ya ƙure. Ban san miyasa Mammah ta ɗauka al'amarin nan da rashin muhimmanci ba. A yanda nake ji a zuciyata da tuni labarin wata akeyi ba yarinyar nan ba. Dan banga dalilin da zaisa ace wai sai anyi bincike za'ai mata hukunci bayan komai data aikata a bayyane yake, wannan tamkar muna nuna rashin muhimmancin ran yaronmu ne ma ai.....”

“Gaskiya kam Arshaan Akhi”. Miran Jasim ya tari numfashinsa da sauri, cikin nuna ɓacin rai shima ya cigaba da faɗin, “Ni kaina komai na kasa fahimta musamman akan ra'ayin Mammah. Sai nake ganin bata damu bane? Ko kuwa tafi son yarinyar sama da gudan jininta? Inba hakaba minene na waɗan nan sharaɗin marasa tushe? Bayan komai a bayyane yake. To gashi tace sai anyi bincike, amma dai-dai da cctv footage an nema an rasa tabbacin komai shiri ne. Inada yaƙinin komai sai dai yarinyar nan ta shirya kafin ta shigo masarautar nan. Dan binciken mu ya nuna ta aurensa ne dama domin ɗaukar fansar ƴan uwanta guda biyu, shiyyasa ta kwantar da kai ta shiga jikinsu musamman Mammah da Akia Ammarah da a yanzu suke nuna goyon bayansu kan cigaba da rayuwarta sai kace sun manta matsayin wanda taso halakawa a gare su...”

Maganganunsu sake hargitsa Malikat Bushirat suke da tunzurata. Tuni jin zafin Malikat Haseenat da tsanar Daneen Ammarah ya sake bunƙasa a ranta. Dama kullum Jasrah cikin munana Daneen Ammarah ɗin take a wajenta yanzu bisa huɗubar Miran Arshaan, dan tafi kawo mata zancen duk motsinsu a masarautar fiye da kowa, musamman daya kasance ra'ayinsu ya babanta da nasu akan hukunta Iffah. Yanda take sake kumbura jira suke kawai suji tace wani abu, amma kasancewar ta mace mai bahagon hali dama fahimta ko uffan da suke so bata tofa ba, sai cika take dai tana batsewarta ita ɗaya. Duk yanda suka cigaba da fanfatan kuma batace ɗin ba har lokacin samun damar ganin Tajwar Eshaan yay a gareta, dan tunda abin ya faru suma ɗin basu samu ganinsa ba kasancewar akwai doka mai haɗe da babban tsaro akan ganin nasa ga duk wanda ya kwana ya tashi a daular ta ruman, su kansu bisa tsayawar Malikat Bushirat ɗinne da itama sau ɗaya take da hurumin ganinsa a rana zasu ganshi yau ɗin.

Duk wani motsi da shiga da fitar jama'a a ƙarƙashin saka idon masu tsaron sashen yake a yanzun. Tako ina ka waiga cctv camaras ne. Su kansu ma'aikatan cikin sanya ido suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login