Showing 174001 words to 177000 words out of 180087 words

Chapter 59 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

wayi gari da dadin rai, dan su Babiy duk sun farfado. Hakama Tajwar Eshaan kaka ya saka masa magani an kuma masa na asibiti da dorin karayar sai dai ace Alhamdullah. Itama dai Iffah an samu nasarar tsayar da jinin kuma cikin da aketama damuwar zai iya lalacewar dai yana nan. Malikat Bushirat ce dai idanun nan da kai kawai ke aiki, sai dai duk abinda za' a fada tana ji. ALLAH sarki Jasrah bata gazaba a yi mata hidima. Jama'"ar gari dama na masarautar da basu san komai akan al'amarin nata ba sunata tausayinta da gain Uwa ta tsafeta ne saboda cikar burinta. Was har addu'a suke mata na samun lafiya. Gawarawakin dangin uwa an tattaresu anyi rami acan daji an biznesu, wanda kuma suka rage tare da uwa an zubasu a kurkuku har sai ALLAH ya bama Tajwar Eshaan lafiya.

Tako ina labaran abinda ya faru a kasar ruman dinne ke yawo a duniya, wasu na caccakar Shahan- shan akan abinda akai bai dace ba suma mutanen nada yancin kansu, wasu ko na ganin hakan da akai shine dai-dai. To koma dai yaya ne yan kasar ruman sudai hakan da akai yayi musu. Dan babu wata kasa da zata so rayuwa da masu bakin kafirci irinsu uwa.Masu ganin ba'a musu dai-dai ba ma son zuciya ne kawal.

Lokacin da Iffah ta tartado taci karo da Tajwar Eshaan jikinsa ta fada kawal ta fashe da kuka. Ya rungume kayarsa yana murmushi shima idanun nasa dai sun kada. Sai da tayi mal isarta sannan ta dago, babu zato kawai yaji ta manne lips dinsu a waje guda. Idanu ya zaro itama sai ta zaro nata tare da janyewa tana dariya. Da sauri ya rikota da hanunsa mai lafiyar ya maidota jikinsa yana murmushi.

"Wannan ai mugunta ce a lasama mutum zuma a baki a gudu". Ya fada cikin rada a kunnenta. Dariya ta shigayi a hankali tana boye kanta a cikin jikinsa, da ga haka ya canja wasan a yanda yake bukatar kasancewarsa, duk da kuwa komai da yake na karfin hali ne kawai, dan sam zuciyarsa babu dadi, shi kadai yasan halin da yake ciki akan mahaifiyarsa. Amma yanata kokarin dannewa da gayama ALLAH kukansa.

Lokacin sallar azhar domin sake Kwantan da hankalin mutane ya fita sallar cikin karfin hali duk da
hanun nasa an masa dorin karaya ne. Ga yankan wukar nan da yay matukar shiga jikinsa sosai, saukin ma dal anyi maganin dafin. Bayan anyi salla an fito ya dan gana da manema labarai da yasa a tara masa. A nan yay ma al'ummar kasarsa godiva da fatan alkairi bisa kokarinsu da addu'oinsu. Ya kuma sake jaddada Iffah matsayin SARAUNIYARSU har yanzu dan bazai amshi mulki ba sai ya samu lafiya. Babu wanda yay jayayya da wannan al'amari. Sai ma Tajwar na jihohi da manyan kasar dake ta layin zuwa dubashi tako ina, tare da sauran mutanen da suka fita wannan gumurzu. Musamman yan kauyukan nan da Hadimai da wasu a jama'ar gari da suka taimaka musu anhadasu da manyan kyautuka, hakama itama SARAUNIYA Iffah ta bisu su dukansu da manyan kyaututtuka da ya sakasu a farin ciki, dan ita dukansu ta hada har matasanta.

Lokacin da don Malikat Bushirat ke gain bayanin Shahan-shan akan Iffah zata cigaba da rike matsayinsa har sai ya samu lafiya, da lokacin da ake nuna Iffah'r akan karagar mulkin Shahan-shan din randa take zartar da hukuncin kyautukan da ta bama wanda sukaje yakin a matsayin Sarauniya kuka ta dingayi, kuka mai zafi da tsananin kona zuciya. Sosai takejin radadi matuka a cikin kirjinta, ji take inama kafin zuwan wanna ranar ta mutu ta huta. Bayan tasha kukanta ta godema ALLAH ta cema Jasrah a cire mata tvn daga dakin. Jasrah har ta amsa da to Malikat Haseenat ta ce kar a cire. Dan tsaf ta fahimci manufar Malikat Bushirat din. Tana ammakin taurin zuciyar matar nan, ace duk wadan nan abubuwan daka gani basu isheka izna ta saraya ba. Ko dan data haifa ta kasa neman gafararsa ma balle su. Kai ALLAH ya rabamu da irin wanna mummunar zuciyar ta kafuran farko,

Kullum sai Tajwar Eshaan yabi ta barauniyar hanyarsa dubota. Zasuje da safe shi da Iffah da an idar da sallar asuba. Zakuma suje bayan sallar isha' i. Da ga gaisuwa da tambayarta yaya jiki bai iya kara sake cewa komai. Sai ma ita Iffah'r ce kan dan mata addu'a ta tofa mata, duk da dai kaka nata kokarin bada magani ana mata ko za'a dace. Haka zatayi ta kallon Tajwar Eshaan tana hawaye, amma shi daga kallo daya na gaisheta baya sake yarda ya kalleta har yabar dakin kansa a kasa yake.




**.




Bayan kwanaki bakwai abubuwa da yawa sun dai-data, musamman masu kananun raunuka sunji sauki sosai, sai wanda suka jigata ne sosa ke cigaba da karbar magani. Baby ma dai da yake buguwace Alhamdullah jikinsa da sauki, dan haka Tajwar Eshaan yace kawai Daneen Ammarah ta tare haka nan. Duk yanda taso zamewa sai da aka shirya wani dan kwarya-kwaryar walima data kayatar. Dan anyita ne irin ta manyan mata masu aji da ilimi. Zuwa dare aka shirya mika amarya dakinta, Iffah kuwa ta dage sai taje. Sai da aka tuna mata itafa SARAUNIYA ce a yanzu, babu yanda ta iya dole ta hakura, amma tanata ima Mamyn (Daneen Ammarah) tabarar wai shikenan ita haka kowa zai tafi ya barta. Ita an kawota gidansu ita kuma za'a maidata gidansu. Itakam data san hakane kawai kowa yay zamansa gidansu. Dariya sosai Malikat Haseenat da Daneen Waheeda keyi da drama din tasu. Dan wata shakuwace ta musamman ta sake shiga tsakanin Iffah da Mamyn (Daneen Ammarah) taja yarta jikinta sosai da sake tabbatar mata da kaunar da take mata dabance a rayuwa. Haka itama Iffah'r tana kaunar mahaifiyar tata matuka duk da bata rayu da ita ba. Sannan tana kaunar Ummu dinta da Baby. Hanash Akhi kam ai shi na musamman ne gareta da Kakanta abin alfaharinta. Kullum cikin lallabasa take shi da lyyani su dawo cikin masarautar da zama ko zata dan ji saukin kewarsu da tayi. Shi dai ya nuna bazai dawo ba. Amma Tajwar Eshaan ya ce ta kawantar da hankalinta zai dawo mata dasu, Ba karamin farin ciki tayi da hakan ba.Dan shima Babiy an gyara masa gidansu sosai dan bazai iya barinsa ba saboda gidan gonarsa.

Lokacin da za'a wuce da Daneen Ammarah sai gashi tana kuka, ta rungume Malikat Haseenat da Iffah sunata kuka. Da kyar Daneen Waheeda da Malikat Ashwaq suka rabasu aka fita da ita. Yau kuma sai dakin mijinta ban yarta.

Tarbace ta mutuntawa suka samu da ga su Ummu, kowa halayen Ummu na birgesa, dan mace ce data amsa sunanta cikakkiyar mace jaruma abin koyi da nunawa a duniya ga kowa, Yan kawo amarya basu wani jima ba suka wuce abinsu. Lokacin da ango zai shigo Ummu da kanta tayo masa rakkiya cakin amaryarsa. Zata gudu Daneen Ammarah tace saifa ta zauna sunyi hira. Babu yanda Ummu ta iya dole ta zauna. Sai dai hirar ma dai duk akan rayuwarsu ta bayace data shude. Kuruciyar Iffah da su Arfa Daneen Ammarah har kuka tayi, ta jinjinama hakuri irin na Ummu. Ta kumayi alkawarin kyautata zamansu tamkar yan wan juna har abada. Zasu zama aminan juna bawai kishiyoyi ba. Ganin dare yaja da wayo Ummu ta tattare kwanikan da sukaci abinci ta gudu. Dama shi Hanash Akhi yana can masarauta Iffah ta rikesa wai shine amintaccenta, nan ko duk wayone dan taita gain dan uwanta ne. Dan babu wani abu da yake yi sai idan sun dan shiga fada zatai wani zama mai muhimmanci da manyan masarautar ya kasance a gefenta. Hakan sai ya saka mata zaman lafiya da Tajwar Eshaan sarkin kishi, dan tana ambata maganar Hanash Akhi dinne zai kasance amintaccenta harda kyauta sumba aka bata. Wai hakan shine dai-dai.

Ummu na fita Babiy sauka yay kasa gaban Daneen Ammarah ya zabga tagumi ya wani zuba mata idanu. Murmushi tayi da jan mayafin jikinta ta rute fuska cike dajin kunyarsa. Ya lumahe idanu da budewa yana murmushin shima, Kafin ya mike tsaye ya yaye mayafin gaba daya ya kama kafadunta ya mikar da ita ya rungume abinsa. A tare suka dinga sauke ajiyar zuciya, sai kuma hawaye na tsananin kewa da tuna baya.

"ALLAH na gode maka daka maimaitamin wannan rana a rayuwata. Ka gamamin komai UBANGIJINA daka bani mafi tsadar nan a cikin mata matsayin matata"

"Ni zan godema ALLAH da samunka matsayin miji kuma uban yayana Zayyan. Tare da yar uwa jaruma Saliha irin Jumaymah. Yanda kuka sharemin hawayena, da zama silar canja labarin da ban taba tunanin zai canju daga kaddarata ba kuma ALLAH ya share naku hawayen. ALLAH ka hana shaidan shiga tsakaninmu. Nayi alkawarin in har inada rabon sake haihuwa a duniya zan malakama Jumaymah (Ummu) yayan nan har abada".

Cikin rada-rada a kunenta ya furta, "Insha ALLAHU a yau din nan zan dasa kwam Arfa da Fariha gimbiyata." cike da jin kunyar furicin nasa ta wani kankamesa da boye kanta a jikinsa. Wani irin rungumeta tsam-tsam Baby ya sakeyi shima yana dariya, tare da bata sumbata tako ina a jikinta harya sauke akan lips dinta, Jin tsaiwar na neman gagararsu ya dauke abarsa tsamm suka shige daga ciki, dama dai ga Daneen Ammarah yar dum-dum kai kace bata wuce talatin a duniya ba. Jin an rufo kofa harda murza key nayi baya dan wanna fagen na manya-manya ne ba gain kanana irimmu ba 🥱😉😂🚴







* BAYAN WATANNI SHIDA DA FARUWAR YAKI TSAKANIN SU SHAHAN-SHAN DA SU UWA



Kai kawo yaketa famanyi a cikin bedroom din nashi bakinsa dauke da addu'a. Duk ko yanda waya ta motsa sai ya daga da tsammanin su Malikat Haseenat ne. Babu abinda yafi burin ji a wannan gabar kamar ace ALLAH ya sauki Sohaa dinsa dake nakuda tun a daren jiya lafiya. Duk yanda yake da tarin ayyuka a fada ya kasa fita. Su Sayeed Fayzul-haq ma sun hakura da fitowar tasa yau tun sanda labarin nakudar Iffah'r daya iso kunensu. Sai kowa ya koma fatan saukarta lafiya.

Daga wayar da tai dai-dal da bugawar agogo karfe sha biyu dai-dai na raar litinin din ya wani irin sauke ajiyar zuciya da zama cikin kujerarsa a hankali. Murmushi ne mai sanyi ya subuce ma kyakykyawar fuskarsa. A hankali ya motsa lips dinsa ya ambaci "Alhmdullah"., Sai kuma hawaye suka dan ciko idanunsa. Shi Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ne yau ALLAH ya azurta da kyautar yayan har guda biyu mace da namiji daga jikin yar uwarsa kuma matarsa, farin cikinsa Fhareedah bint Zayyan. A take bakin ciki da kuncin dake tare da zuciyarsa a cikin watanni shidan nan yaji ya wani fada masa daga makoshi zuwa cikin ciki. Babban yatsarsa ya kai a idanun nasa a hankali ya dauke hawayen da sake furta. "Abbie an haifo maka jikoki har guda biyu a rana daya, lokaci daya da ga tilon danka. Insha ALLAHU za'a sake haifo maka wasu biyun kamar haka har sau hudu Abbie na. ALLAH ya gafarta maka, ALLAH ya yafe maka kurakuranka kai da Jaddi da ma duk zuri'ata data musulmi baki daya. Kai da Jaddi da Jaddah ne abin AL'FAHARINA ABBIE NA"……✍️


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (94)



*_MAAB LUXURY HOME._* _Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini. Ina uwar gida da Amarya, Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._


_____________________


.........Cikin ƙanƙanin lokaci zancen haihuwar Iffah ya karaɗe ƙasar ruman baki ɗaya. Tuni farin cikin kowa ya bayyana, tare da addu'oi ga waɗan nan jinjiraye da ga bakin al'umma. Yayinda Tajwar Eshaan daya matsa a kai masa su ke can rungume da kayansa tsam-tsam a jiki. Jinsa yake a yau ɗin kamar wani sabon mutum, final shima dai ya zama Abbie. Ga yaran sun ɗakko kamanninsa sosai musamman ma mace kamar an tsaga kara an karya da shi, gara namijin yafi rinjaya da Iffah shi kuma. Da kansa ya tauna dabino ya basu tare da musu huɗuba.
      Duk yanda yaso ganin Sohaa ɗin sa hakan bata yuwuba sai bayan la'asar tai barcinta ta huta sannan. Murmushi ta dingayi kanta a sinne saboda irin kallon nan na ƙasa-ƙasa da yake faman binta da shi. Duk sai taji kunya ta lulluɓeta. Har ya ƙaraso gaban gadon bata yarda ta ɗago ɗin ba sai da ya zauna a kusa da ita ya ɗago fuskar tata da kansa. Bai tsaya wata wata ba kawai ya manne lips ɗinsu waje guda. Sai da yayi yanda yake so da ita ya barta dan kansa sannan ya rungumeta yana jero mata daɗaɗan kalamai masu sanyi da ratsa zuciya da bata san yayi nisa a sani ba har irin haka. Jitai kawai idanunta sun cika da ƙwalla. Dan ita kanta bata san adadin ƙaunar da takema wannan bawan ALLAH ba zuwa yanzun. Tana jinsa daban a cikin daban a duniyarta. Shi ɗin na musamman ne a gareta fiye da yanda yake jinsa na musamman...

      Lokacin da aka kaima Malikat Bushirat da har yanzu ake nan yanda ake babu abinda ke motsi sai kai da ido Jasrah baiwar ALLAH nata wahala da ita kuka sosai ta fashe da shi. Suko yara kamar sun san inda aka kawosu suka wani dage da tsanyara kuka tsiyau-tsiyau kamar ƴaƴan magena da yau mukasha bikin sunansu (Na manta ban faɗa muku ba magena ta haihu ƴaƴa hudu kowa sai ya kawo kayan barka haihuwar fari ce babu ɗaga ƙafa😂🚴🥱) kuka sosai suka dingayi har abin ya bama kowa mamaki, ana fita da su sukai shiru kuma kamar basu ba. Koda aka maidasu anan bama Malikat Haseenat da Iffah labari murmushi kawai Iffah tai batace komai ba. Garama Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai ta tofa kaɗan.
      A can ko jikin Malikat Bushirat rikicewa yay sosai. Dan har sai da takai an kira Shahan-shan da Malikat Haseenat. Al'amarin kam yau dai bana wasa bane. Dan doctors da suka rufu a kanta ma dai sunyi iya ƙoƙarinsu amma bata bar jijjigar da ta dingayi ba, daga baya ma sai ga aman jini. Hankalin kowa ya tashi musamman Tajwar Eshaan, dan da kansa ya hau gadon ya rungumeta jikinsa ta dinga bulesa da aman jinin nan. Addu'a ya dinga tofa mata, ganin fa tafiyar mai tsaho ce Malikat Haseenat ta fara maimaita kalmar shahada ko za'a dace Malikat Bushirat ɗin ta karɓa. Hakan yasa suma sauran jama'ar dake a ɗakin suka dinga maimaitawa, Jasrah dai kuka take kamar ranta zai fita. Sai dai kuma ita rayuwa duk yanda kaso, bai zama lallai abinda kaso ɗin ya kasance a yanda kaso shi ba. Dan kuwa dai Malikat Bushirat ta koma ga UBANGIJI batare da ta iya neman gafarar koda ɗan cikinta tilo data jefa kanta a halaka domin haihuwarsa ba. Tayi mutuwa mai ban tsoro da tashin hankali, dan kuwa maimakon kalmar shahada da suka so ji daga bakinta sunan UWA ne ƙarshen ambaton ta cikin wani irin gurnani mai ƙarajin gaske daban tashin hankali. Wannan al'amari ya matuƙar kiɗima Shahan-shan. Dan jikinta na gama saki shima ya kife kansa akan fuskarta. Tsahon lokaci bai ɗago ba har sai da kowa ya fita a ɗakin Malikat Haseenat tazo tana lallashinsa. Sannan aka samu ya ɗago idanun nan nasa jazur matuƙa abin tausayi, sai dai baiyi kuka ba, ya jima yana kallon fuskar mahaifiyar tasa abubuwan data lissafa ta aikata na dawo masa tiryan-tiryan kamar yanzu take yinsu....

        Masarautar gaba ɗaya ta gama rikicewa. Dan mutuwar nan kam ta daki kowa musamman da Malikat Bushirat ta zama tamkar wata tauraruwa a zamaninta a cikin gidan. Sai dai yanda mutuwarta tayi dai-dai da mutuwar kaf mutanen nan ƴan ƙabilar uwa abin ya bama kowa mamaki. Dan kamar waɗanda aka shayar guba kawai aka samesu duk a mace su kusan goma sha uku. Dama wasu sun ɗan mummutu ɗaɗɗaya. A yanzu dai kam Uwa kawai ta rage a raye. Itama ɗin dai sai a hankali dan duk ta ƙara wani irin yamushewa na tashin hankalin faɗuwa ƙasa da tai. Wai yau itace mai zaman kurkuku a cikin masarautar ruman kuma da ranta da lafiyarta tsahon watanni shida. Ai ko'a iya haka aka tsaya ta gama kunyata a wannan duniya.

       Jasrah ce ta mata wanka tana kuka abin tausayi ita da yayarsu Badiha. Bayan an mata sutura aka fiddota Tajwar Eshaan ya jagoranci sallatarta tare da miƙata gidanta na gaskiya aka barta da halinta kuma. Dan ya rage ita da UBANGIJINTA. A yanzu kam. Wannan itace ranar da ya kama kowa ya kasance yana gudu a rayuwarsa. Dan ko kaƙi ko kaso sai tazo. Ko kai mutumin kirki ne kona banza ne ma dai sai tazo. Ko shekara dubu bisa dubu zakayi a duniyar sai tazo. Koka shirya ko baka shirya ba sai tazo. Yau dai gashi Malikat Bushirat ta tafi tafiya ta har abada. An shafeta an shafe babinta dama iyakarta kenan akan duk wani abin kirki ko ɓarna da zaka shuka a duniyar....
     Tajwar Eshaan bai samu hawayen dake riƙe da maƙoshinsa sun zubo ba sai da yaje ya rungumi ƴaƴansa da matarsa sannan. Kuka yayi sosai Iffah na tayasa. Sai da sukayi mai isarsu abin tausayi. Ranar ma har zazzaɓi yayi dole Iffah ta kwana tare da shi da ƴan yaransu da sukaci sunan Ajwaad da Ajwaa (Dan su bawani al'adar suna a sati ɗaya suke ba ba irin ƴan 9ja bane😝). An dai yankama yara raguna da shanu akai sadaka a washe gari tunda ranar mutuwar Malikat Bushirat ta hana. Gida kam ya cika maƙil, ƴan gaisuwa da taya murnar haihuwa ta ko ina ketowa suke. Su Mamy (Daneen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login