Showing 147001 words to 150000 words out of 180087 words

Chapter 50 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

mu fadi tare, sai dai ai mutuwar kasko mu dukanmu baki daya" wani irin kuka ya sarketa, wasu kalaman Iffar ne suka sake shiga dawo mata…. _(Ammie wihy inada abubuwan ban mamaki da daga labulen sirrinki sau daya kawai sai ya hana wannan idanun naki barci.....)_ wani irin naushi ta kaina mirror din akin da sake kwala kiran sunan uwa_(…..……To wai nikam wane buri ne kike son cimmawa mai alaka da makiyi a tsakaninki da shi? Kin ko san da ace yasha ganyen shayin nan ko madarar nan illar da zatama rayuwarsa sai tafi wadda zatama tawa rayuwar? Sannan ke da kanki sai kin dawo kina kuka da dana sani. Idan ma wani ke baki wadan nan abubuwan matsayin wani kariya washi ko gurbata tawa rayuwar to tabbas ki farka. Ki farka why tunkan guri ya kure miki ki rasa kofofin fita a wannan masarautar.…)_ "Har abada! Har abadan abada bazan taba faduwa kasa ba, bazan rasa komai ba a lokacin da komai ya zama nawa ba....


"Dole ki rasa! Dole kirasa!! Dole kirasa ta-kurya!!Hahahahaha!!!!". Uwa ta fada cikin karaji da amsa kuwwar mummunar muryarta alokacin da take bayyana. A kallo daya zaka fahimci itama a birkice take. Dan idanun nata sun sake jajur, fuskarta ta sake muni matuka. Da wani irin karsashin wutar bala'i Malikat Bushirat ta fiskanceta, a yau babu wani tsoro ko shakku tare da ita balle girmamawar da ta saba ga uwar. Gabanta taje ta tsaya tana mai nuna ta da yatsa.

"Sai dai mu rasa gaba dayanmu, amma ba Malikat Bushirat kawai ba. Miyasa kika yaudareni?..

"Ke kika yaudari kanki, domin a yarjejeniyar mu akwai sharadin kin auren yarinyar data fito a wannan zuri'ar musamman mai tambarin na hakika".

"Amma da umarninki ta zama matar Saiful-malik, shin bokancin naki ya fara raunine ko dama ke din mayaudariyace kamar yanda yarinyar ta fada?!!!".

"Ki iya bakinki ta-kurya!!!".

*Bazan iyaba, nace bazan iyaba uwa. Wihy why, kinji na rantse, bazanyi asarar wahalata ba. Sai dai ni da ke duk muyi mutuwar kasko".

"Kece da danki zakuyi mutuwar kasko, kuma dole ki bamu jinin Ajlaan madadin sauran ayyukanmu da baki cika ba!!".

"Har abada, har gaban abada jinin Saiful-malik yafi karfinki azzalumar mushirika. Nima da kike gani hatsabibiyar kainace uwa, dan tun kafin ke gwanace a iyawata!!"

"Kin san da iyawar taki miya hanaki iyama kanki sai da taimakona. Butulu ke wacece, har wacece ke nace ta-kurya? Har mi kike takama da shi? In ce dai Ajlaan ne ko? Kuma mune muka samar miki da shi a lokacin da kike neman samuwarsa do rufe (Wa'alaikissalam 😭ALLAH ne kadai ke badawa da hanawa a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso. To ki rubuta ki ajiye mune zamu shafe babinsa da tarihinsa, kamar yanda muka shafe na ubansa da kakansa a doron duniya.Idan kin isa, Kin cika sunanki tsagera mu zuba!!!!"

Bat uwa ta bace a akin kamar tashin guguwa. Wani irin fashewa da kuka Malikat Bushirat tai cikin ihu da fisgo duk abinda ya tare mata gaba ta dinga ratsawa da kasa. Jikinta want rin jiljigar rawa yake na masifa, da ga karshe ma kawai sai ta yanke jiki ta fadi dan jini ya balle mata sosai saboda raunikan da ta jima kanta a dalilin fashe-fashe.….✍️








🥱 Tofa anzo wajen kenan, wannan da alama fadan
cikin gidane fa. Akwai kuma babban kulli akan
haihuwar Tajwar Eshaan ma kansa 🤔. 🚴 Bari dai mu
cigaba da bin uwa da diyarta muga yaya wasan zai
kaya ne.

DAUDAR GORA
Book2
Chapter 78

.....…..Bayan idar da sallar magrib dunbin al'ummar dake cikin masarautar ruman suka shaida daurin auren Zayyan ibn Abbas Jumna. Da amaryarsa Ammarah bint Abdul-majeed Aliy Qutb, akan sadaki mai darajar gaske, inda Kaka ya zama waliyyin ango, Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ya zama waliyyin amarya. Ba mutanen daular ruman bane kawai suka girgiza, masarautar ce gaba dayanta ta girgiza da wanna al'amari na bazata. Duk da ana cikin dunbin jimami na abubuwan da suka faru a kotu yau, babu wanda yay zato ko tsammanin faruwar abinda ya farun kamar haka ba. A take sabon topic ya sake barkewa a saman wanda dama aka yini anayi har
a cikin hadimai…




**



Tun bayan sallar la'asar da suka shigo da su Kaka bata koma ba tana a sashen nasa. Dan sanda zasu fita domin gabatar da sallar magrib har zata bisu itama Malikat Haseenat ta dakatar da ita. Kasancewar sallar magrib da ake kira ita da shi babu wanda yacema dan uwansa komai. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke a bayan fitarsa sallar, sai kuma ta shiga wanka dan a karo na farko tun bayan samuwar cikinta yau ne take jin zazzabi a jikinta. Doguwar riga mara nauyi kawai ta saka ta tada salla, bayan ta idar ta zauna komai na dawo mata daki-daki kamar wani shirin film. Kuka sosai tayi fiye da wanda tayi a dazun, a haka kunnenta ya tsinkayi shelanta sake aura auren mahaifanta guda biyu da kaddara ta hada. Kuka ta sake rushewa da shi har kanta na mata ciwo batare da tasan dalilinsa ba. Shin farin ciki ne ko sabon rudani, da kyar tai sallar isha'"i ta zame akan abin sallar ta kwanta.....

Tana kwance a wajen cikin yar takurewar sanyin zazzabin da take ji ya shigo dakin da sallamar nan tasa ciki-ciki. Bata motsa ba har ya karaso gabanta, jin tsaiwarsa a kusa da ita ya sata bude idanun a hankali ta sauke kansa. Kallon juna suke kamar yau suka fara ganin kansu, kafin itama ta fara janye nata idanun ta mike a hankali. Ganin yanda take dan layi na wandda jiri ke kwasa ya sashi mika mata lallausan farin hannunsa sol mai dauke da dogayen farata. Nata ta daura a hankali cikin nasa, ya dagata gaba dayanta ta mike tsaye a gabansa. Yanda yake binta da kallo kamar sabuwar halitta ya sake raunana mata zuciya, sai kawai ta sakar masa wani shagwabebben kuka da fadawa jikinsa ta kankamesa. Bashi da zabin da ya wuce amsarta hannu biyu shima ya kara matseta a jikin nasa yana mai lumshe idanunsa dake cike da so da kaunarta. Kuka take sosai dake sake sukar zuciyarsa, sai dai baice mata uffan ba har kusan tsahon mintuna uku suna tsayen. Sai da yaji ya daina jin dumin hawayenta dake sauka masa a kan kirji ta koma sauke ajiyar zuciya sannan ya dagota. Mayafin da tai rolling ya warware, yaja hanunta a hankali ya zauna a bakin gado ita kuma ya daurata a saman cinyarsa.

"Shi kukan baya isa ne".

Ya fada a fisge fuskarta a cikin tafukan hannunsa. Fuskar ta sake kwabewa zata saki wani sabon kukan ya girgiza mata kai da fadin, "Please bana son gani kuma, kin cika shagwaba fa". Shaaa hawayen suka zubo dan ta kasa rikesu, sai kuma ta turo masa baki gaba. Murmushi yayi a zuciyarsa, tare da matso fuskarta dab da tashi ya tura yatsunsa cikin gashin kanta ya zare ribbon din data dauke gashin a tsakkiya ya shiga yamutsa mata shi yana goga mata hancinsa kan nata, lips din ta sake dan turowa, shiko ya samu damar hadesa da nashi kirif. Iya kokari yayi na ganin ya tsaya iya hakan, sai dai zuciyarsa gaba daya taki bashi hadin kai. Sai kawai ya zarce da abinda gangar jikinsa ke tsananin bukata da kwadayi, da ga haka labarin ya canja da salo mai matukar nauyi dake kara tabbatar musu yanda suka narke a so da kaunar juna mai tsananin gaske.


Dakin yay shiru sai fitar sanyin na'ura tana lafe a jikinsa cikin muryarta da ta disashe take fadin, "Komai kamar a mafarki ko? Ji nake kamar idan na farka zanga ba haka bane ba Maleek. Har yanzu gaba dayan zuciyata taki yarda da komai dari bisa dari".

Murmushi yayi mai sanyi da sake gyara mata kwanciya a jikin nasa, hannunsa kam na'a kan cikinta. Lumsassun idanunsa ya bude a kan kyakykyawar fuskarta da hatta dan kumbura saboda kukan da ta sha a yinin yau. Motsa lips dinsa yay a hankali ya furta "Rayuwar ma gaba dayanta tamkar mafarkice Niger. Yanda muke kwantawa mu tashi da wucewar gobenmu haka kwanakin kaddarar rayuwarmu ke shudewa da abubuwan da suka gabacemu. A duk abinda kikaga ya far a yau tabbataccene da tabbatar rubutun alkalamin kaddara. Wata hikimace kuma da ga hikimomin UBANGIJI. a randa na fara hacuwa dake komai ya cigaba da maimaitamn kansa tamkar mafarkina. Da ga cikin duk abinda ya faru har kina tunanin akwai abinda zai iya gagara da ga tarkar UBANGIJI?

"Murmushi ta danyi mai sanyi a karo na farko tare da dagowa tana kallon kyakykyawar fuskarsa. "UBANGIJI gagara misalin masu misali ne ai, duk abinda ya zartar haka yake babu kokwanto ko shamaki a cikinsa. Kai dabanne a cikin daban MIJINA RAYUWATA" tai maganar da dan ja masa hanci. Murmushi yayi mai Kayatarwa da dungure mata kai. Ya ce, "Ai kin fini zama daban. Mai mama biyu, yayu biyu, kakanni biyu, gida biyu, kefa hatta duniyarki biyu ce My sohaa".

Dariya ta kyalkyale da shi kamar ba yanzu ta gama rusar kuka ba. Ta kankamesa da fadin, "Idan na hada da taka duniyar ma uku garan FARIN CIKINA".

"Oh oh, yarinyar nan fa naga alamar kin fetsare". Yay maganar yana dagota. Gashin da ke a gemunsa ta kamo da yatsunta tana wasa da shi, cikin shagwabe fuska ta ce, "To ai duk karatunka ne, su Ummu ma shaidane ba haka suka baka ni ba, ni da ko kallon mutane bana iyayi cikin ido..."

"K din dai dana sani?".

Ya fada cikin katseta da dan waro idanunsa waje. Fari ta masa tana murmushi cikin dage gira sama da fadin, "Kaima ai shaidane, saliha dani aka kawo maka ga hakuri ga shiru-shiru"., Mizai yi inba dariya ba, sai da yay mai isarsa tana kallonsa cike da jin dadi sannan ya dungure mata kai. "Wai ke din nan ce mai shiru-shiru, bayan randa na fara ganinki da rashin kunyarki nai karin kummalo. Lallai an cuci masu shiru-shiru kuwa indai aka sakaku. Ke Fitinanniyar nan. Ranar fa harda fadin wai ko Shahan-shan ne sai kin sashi ya tsaya dole. Kai yarinyar nan ke abar toro ce".

Dariya ta kyakykyale da shi, sai kuma ta shiga boye fuskarta dan sai yanzu abinda tai din yake bata kunaya ma. Kanta a boyen ta ce, "Wai dan ALLAH ranar bakaji kamar kasa a tsireni ba?".

"Ke dai kika tsiremun zuciya ban shirya ba. Danni kadai nasan dauriyar da nayi ban fallasa abinda ke a raina ba tun a wajen".

Dariyarta mai tada masa tsigar jiki tayi da fadin, "Nima fa kadan birgeni a ranar, dan kamshinka ya tafi dani matuka da wadan nan fararen idanun masu kyalli kamar madara. Kawai dai ranar haushin kowa nakeji ne sai na samu na sauke akan yaranka. Wai kuwa suna ina ma?".

Murmushi kawai yayi baice komai ba, sai da ya mula da kansa sannan ya magantu. "Uhm ashe nayi babban kamu tun a ranar faro amma aka tsiwaceni tas. Ke ta dabbance yar kanwata. Su Azaan suna nan abinsu, ma'aikata ne a gidan jaridata ta AFRICAN EYE. Inda kika so zuwa ki tone mun asiri da min zigidir a bainar nasi ALLAH ya taimakeni".

"Shine ka tareni ko? Ashe dai kanajin tsorona?".

"Kai sosai ma kuwa. Mra Eshaan ko bakin nan naki da baya gajiya da magana ai yasa aji tsoronki."

Harara ta dan masa tana tura bakin, sai kuma kamar wadda aka tunatar ta ce, "Wai dama dan ALLAH gidan jaridar Africa eye naka ne?".

Kai ya gyada mata idanunsa a lumshe ya ce, "Shine burina na farko dana cika bayan kammala karatuna".

"Uhm Masha ALLAH, shiyyasa akema manyan duniya tone-tone ba ragi babu ragowa kuma komai
bai faru ba. Amma gaskiya kayi kokari. Nima wannan
shine burina"

"Ki dauka kin cikashi insha ALLAHU My Sohaa, Kina haifomin babyna makaranta zaki koma, insha ALLAHU arena bazai tauye miki cikar duka burikanki ba. Zan tsaya miki da tsayawar UBANGIJI har sai kin cika duk burin da ALLAH ya rubuto a cikin kaddarar rayuwarki na alkairi".

Wani irin rungumesa tai da fashewa da kuka. Hannu biyu ya amsheta yana murmushi. Gain kukan na gaske ne aka sauya masa salon lallashi kamar ba yanzu aka fito a komar ba. Da alama dai Iffah'r mu ta haddace karatun gwarzon nata har sun zama dai-dai,🚴









Hankalin Jasrah ba karamin tashi yay ba da yanayin data samu yar uwarta. Rasama abinda ya dace tayi tai, a rikice tai kiran number likitan Malikat Bushirat din. Cikin kankanin lokaci kuwa sai gashi. Shima hankalinsa ya tashi, dan shi abinda ma zuciyarsa ke raya masa da ban da wanda ke a hakika. Zai zauna bin ba'asi Jasrah ta katsesa da fadin, "Yanzu ba lokacin sanin miya faru bane. Ceto rayuwarta shine mafita first".

"Hakane"

Ya fada cikin gamsuwa. Da taimakonsa suka maidata saman gado, babu bata lokaci ya shiga aikinsa, ya samu nasarar tsaida jinin, tare da ceto numfashinta da tuni yabar gangar jikinta. A tare suka saki ajiyar zuciya bayan daidaiton komai. Jasrah ta dubesa cikin roko ta ce, "Doctor Please wanna al'amarin ya tsaya da ga ni sai kai dan ALLAH. Dan yana da kyau mu fara sanin abinda ya faru da ga bakinta karmu tashi hankalin mutane. Musamman ma Shahan-shan abubuwan zasu masa yawa. Ga wanna rikicin da yake ciki ga kuma wannan. Shima mutum ne kamar kowa yana bukatar sassauci".

"Gaskiya ne ranki ya dade. Insha ALLAHU baki da matsala. Dan aikina ne wannan. Ki dai kasance a kusa da ita dan zata iya farkawa a firgice kasancewar daga suma muka maidata barci, Sannan gaskiya ya kamata kusan abinda ke damunta Kinga wanna fa shine karo na biyu, zata iya samun matsala idan haka ya cigaba da faruwa. Dan yanzu haka da kyar na samu bugun zuciyarta ya daidaita, ga jininta ya hau matuka sai tana samun kulawa lafiyarta zai samu daidaiton da muke bukata".

"Insha ALLAHU Doctor za'a kiyaye".

"ALLAH ya tabbatar, zuwa safiya zan kawo magunguna ko kuma zuwa anjima kadan"

"Okay inaga ka kawo anjima din zai fi".

"Shike nan bara naje sai na dawo"….✍️


5:21 m
DAUDAR GORA
Book2
79



…..Bayan wucewar Doctor jagwaf Jasrah takai zaune idonta akan yar uwar tata. Abubuwane da yawa ke mata kaikawo, ga dunbin mamakinta da al'ajabin wai mike faruwa haka? Ko ita dake a cikin halin tashin hankalin hallayar mijinta batajin tana a rabin wannan yanayin. Amma ita da bata nema komai na rayuwa ta rasa ba tarasa mike faruwa da ita. A kwanakin nan fa har rama tayi, sannan zaka ganta jigum kamar mai tunani duk ta hargitse. Gaskiya ta fara ji a ranta lamarin ya fara zarce na kiyayyar Iffah kawai. Akwai dai abinda take boye musu da ya kamata ace sun sani, dan al'amarin ma kamar gaba- gaba yake. Jiba dai yanda ta hargitsa dakin yau gaba daya, ta fasa abubuwa masu daraja da tasan ko sanda suna yara bata bari su taba mata. Tashi tai da kanta ta gyara komai, dan kiran wata hadima ta gyara kamar yana nufin fitar zancen ne, dan hadimai da yawa dake akowane sashe zaka samu an leken asirin wasu ne. Musamman ma ita da girman ikonta yasa kowa kunnensa bude yake da son jin labarin wani al'amari ya bullo da ga gareta makamancin haka. Tana cikin gyarawar doctor ya kirata ya dawo, ajiye aikin tai taje ta amso magungunan ta daw sannan ta karasa gyara komai ya koma need.

Gabannin asuba ta farka a wani irin firgicen da yafi wanda ma Doctor ya ce zata iya tsintar kanta a ciki. Yanda jikinta ke rawa haka gadon ke rawa, ta fasa wata irin gigitacciyar kara ganin halittun da suka firgitata a cikin barcinta zahiri muraran a cikin dakin. Gaba daya sunma gadon zobe ga wani kalar kuka da sukeyi mara dadin saurare a cikin kunne., Sotake ta ambaci sunan ALLAH koda sau daya ne amma bakinta ya gagara furtawa, sai rawar da lips dinta keyi kamar yanda jikin nata ke rawa. Duk da sanyin ac dake dakin ita a jike take sharkaf da zufa kai kace wanka tayi.

"Hahahaha!!!!"

Uwa ta bayyana cikin mummunar dariyarta. Kamar koda yaushe a kan kujerar tata take cikin jajayen kayan nan. Mummunar fuskarta ta tsufa ta sake munancewa tsabar itama bata a cikin hayyacinta.Dariyar ta sake kyakyalewa da shi da fadin, "Kikace zaki ¡ya hahaha! Dama na fada miki ke karamar mara kunyace Bushirat, k! Karamar tsagerace!! Hahaha!!!!! Daga yanzu zuwa ranar cikar burina saina dandana miki azaba, kisa a ranki yanzune wasan zai fara na gaskiya. Kuma dole ne ki biya diyyar da jinin dan da mune mukai sanadin samuwarki garesa (Wa'iyazubillah🙏) da ga karshe zan tona miki asiri ta yanda jama'arki su zasu idasamin rayuwarki karamar yar iska kawai butulu. Hahahaha!!! Kuje gareta, ku sauyamun kamaninta". Ta fada cikin bada umarni ga munanan halittun nan ita kuma tana bacewa. Wata irin zabura sukai kanta, hakan yay dai-dai da bude kofar da Jasrah tayi a rikice, dan ta farka saboda kiran sallar asuba kawai ta dinga jin kamar dokuna na sukuwa a cikin masarautar, shine ta fito a zabure, amma maimakon jin da take duka masarautar ne sai taji kamar a dakin Malikat Bushirat din ne kawai, shine ta nufo nan a rikice. A take duk suka bace batare da taga komai ba, sai Malikat Bushirat da gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Sallallami ta dauka tare da haurawa gadon a rikice, bata kawo komai a ranta ba face maganar doctor da yace dama zata iya farkawa a rude, ita kuma ta koma daki ne dan taji yace zata iya kaiwa ma safiyar gobe bata farkaba saboda nauyin allurar da yay mata.

Rikota tai ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu na tausayin yar uwar tata. Zuciyarta ta fara bata kodai asiri akai mata ne wai....





**..




Itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login