Showing 168001 words to 171000 words out of 180087 words

Chapter 57 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

tsigar jiki, tuni tayi tsakkiyar masarautar ta wani irin karta takobin bisa kasa. Kamar yanda mafi yawan mutanen masarautar sukaji wanna tashin hankali haka sukaji karta takobin da Iffah tayi akan kasa da yin wani irin kara ji ta ce. Duk wanda ya shirya idan ya isa yazo gabanta. Saiko ga kusan mutum hudu sun bayyana gaban nata tsirara sai dan ganye a gaba suna wani irin huci da bulbulo da wutar tsafi ta baki, Juyi ta sake. yI, da wulwula takobin ta cake akan kasa, kafin tai wani irin zarota tai juyi bakinta na ambaton sunan ALLAH tamkar kyattawar ido sai ga kawunan shegun a kasa hudu reras. Zo kaga ihu, ga hadiman da duk suka farka saboda tsabar tashin hankalin firgitasu da wadan nan mutane sukayi, wanda sune a
daren jiya suka shigo sukai musu kisan gilla dama. Ba kowa bane kuwa face a cikin zuri 'ar su uwa. Tuni fa masarautar ta kara rikicewa, wanda ma bai farka ba sunata farkawa. Can sai ga Jasrah ta fito cikin kuka da kururuwar an dauke Malikat Bushirat. Ba kowa yasan mike faruwa akan Malikat Bushirat din ba sai su shakikanta, duk da dai dazun anga duk ahalinta sunzo gidan, sannan Malikat Haseenat ta fito ranta a bace da sashen ita da Daneen Ammarah. Dama Daneen Waheeda bataje ba dazun din dan haka maganar dai har yanzu bata fita akan tsiyatakun da Malikat Bushirat din ta fada ta aikata da bakinta ba. Kowa dai nata hasashe da son bin kwakwkwafin al'amarin. Masarautar ta rude gaba daya, ALLAH dai yasa itama Daneen Ammarah da nata kwankwaman a ka da kyar ta rike Iffah. Barci dai a wannan dare yara kanana ne da basu san komai ba a wannan masarauta suka yisa. Dan tuni shima Tajwar Eshaan ya farka. Tun a daren Iffah tai kiran kaka a waya, asubar fari kam a cikin masarautar ta masa. Ana idar da sallar asuba aka shiga meeting na gaggawa. Kaka, Iffah, sai manyan masu fada ajin masarautar irin su Sayeed Fayzul-haq da sauransu........✍️



DAUDAR GORA
Book2
90




.....Kaka ne ya fara magana rai bace. "Wadan nan mutanen yaki suka shirya dan gaske bawai wasan yara ba. Daren shekaran jiya sun zo sunyi kisan gilla jiya ma sun dawo harda daukar Malikat. Wadan nan da Fhareedatu ta sarema kawuna jiya bawai su kadai bane, guduwa sauran sukayi. Dolene a nemo mafita dan a dawowa ta uku zasu sake sabon shiri ne. Shakaran jiya sun kashe kusan mutane hamsin, yau ga kusan mutum tara fa, dan ma yau ALLAH ya fargar da da sai sun gama illarsu sun tafi kamar ta shekaran jiyan sannan za'a sani".

Sayeed Hifzur-rahaman ya ce, "Tabbas akwai matsala kam, dan da gaske suke ba wasa ba. Sai dai fa matsalar idan munce wani yunkuri zamuyi ta ina zamu kama ne?. Ku dubesu kamar ba daga jinsin mutane suke ba, ko kyawun kallo basu da. Ga su da karfin tsafin mai ban tashin hankali.....


'"Babu wanda yafi karfin UBANGIJI ai. Dan haka zamu tunkaresu gaba-da-gaba". Iffah ta fada cikin bacin rai. Duk kallon toro sukai mata, sai dai kafin wani yace komai da ga bayansu aka amsa da "Tabbas mune zamu tunkaresu kamar yanda ta fada".

A razane duk suka juya suna kallonsa. Shi din ne dai ba wani ba. Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul- majeed Aliy Qutb. A kallo daya idan kai masa bazaka sake marmarin karawa ba dan firgicin a yanda yake yau. Cikakken GWARZON BARDE abin tsoratarwa ga duk wanda zai iya kallonsa. Karasa takowa yay cikin takun nan nasa daddaya da yau ya kara zama cikin izzar damuwa da bacin rai. Ga ido ya toshe da bakin gilashi alamar yau babu koda digon sassauci. Dole kowa ya mike cike da girmamawa a garesa.Maimakon zama tsaye yay kikam idonsa akan Iffah, cikin bada umarni ya ce, "Cigaba da bayanin ki".

Kai ta jinjina masa cikin girmamawa sannan ta dubi
kaka. Shima kai ya jinjina mata dan haka ta sake fuskantarsu. "Tunkararsu itace babbar mafitarmu kamar yanda Kaka ya fada, dan tsafinsu da wani karfin maita babu abinda zai mana da karfin tasirin UBANGIJI. Dan dole ne mu shafe babinsu gaba daya in har muna son cigaba da rayuwa cikin salama.Mataki na farko a yanzu shine Taswirar jejin da ake saka ran samunsu, sannan hada manyan baradan mayaka da ga yanzu zuwa awa biyar kacal da muke da ita….

'"Amma ranki ya dade ai bamu san jejin da za' a iya riskarsu ba. "Sayeed Aashiq-Muhammad ya fada cike da girmamawa ga Iffah'r".

Kaka ne ya amshe da fadin, "Wannan bazai zama mai wahalarwa ba, dan dukkanin abinda ke zagaye da wanna kasa muna dasu a rubuce a kundin litattafan tarihinmu. Za'a iya bincikawa tunda kabilar tasau dadaddiyar kabila ce".

Itama Iffah kanta ta jinjina da fadin hakanne kam, dan nima a karance-karancen tarihi da nai a kwanaki akwai wani littafi daya tabo makamancin dabi unsu. Dan haka muna bukatar Sayeed Aynul-Hassan shima anan".


Ba'a wani bata lokaci ba wajen kiransa, sai ko gashi da tarin littafai da wasu manyan takardun taswura da ke kunshe da gaba daya kasar ta ruman da dazukanta. Kaka ya bada umarnin tattara mayakan da ake da kyakykyawan zato a kansu, dan haka Sayeed Tasadduq-Husain ya fice domin yin wanna aiki. Sayeed Aynul-Hassan mai alhakin kula da da books room na masarautar, wanda kuma yayi rubuce- rubuce da yawa hakama mahaifinsa da kakansa a take ya bada littafin da ake kyautata zaton sune a wannan tarihin, dan bayan su din akwai dazukan da wasu mutanen daba su din ba ke zama sai dai su sun banbanta da su. An aika amintaccen Tajwar Eshaan wajen Malikat Haseenat domin amso wasu taswuriri nan ma da ke a daki littatafan sirri dake ainahin dakin karatun Tajwar Abdul-majeed. Nan take su Iffah suka shiga bincike aka kuma baje manyan taswuririn a bangwayen babban dakin meeting din. Annan ne fa Tajwar Eshaan ya bama kowa mamaki, dan ashe masanin taswurane matuka. Komai da shi akayi, kusan shine ma gaba wajen bada sirrikan dazukan, kaka da Iffah na bada shawarar yanda ya kamata a shigesu a kankanin lokacin da ake da shi suma. Suma dai sauran kowanne da irin rawar da yake takawa.

Da ga can cikin masarautar Kuwa kowa ka gani hankalinsa a tashe yake, dan hadimai masu karfin hali ne kawai suka iya gudanar da ayyukansu. Wanda aka kashe kuma anata kokarin musu sutura amma na iya cikin masarautar. Wadan da Iffah ta fillema kawuna ko ace aljanunta kam suna a nan tsakkiyar masarautar rufe yara da mata dama wasu a mazan sun zagayesu sunata kallo. Yan uwan Malikat Bushirat tuni sun iso masarautar suma hankali tashe da jin cewar wai Uwa ta dauke ta. Duk da tsiyatakun data aikata, da kuma ciwon da ke jikinta sai ya zam maganar nan ta malam ba haushe da kan ce *_DAUDAR GORA CIKI KA SHATA_*

Hankali iyaye musamman mata na masarautar bai kara tashi ba sai da suka ga ana tattara matasan masarautar ga dokuna majiya karfi ana fiddowa, Sayeed Tasadduq-Husain nata waya da shugaban sojoji na kasa ana shirya motsocin yaki da jirage uku da ya bada umarni. Hakan na nufin mataki na karshe ake shirin tunkara wato yakin gaba-da gaba da matsafan mutane irin su uwa, kafirai da basa gane komai da ga tsoron ALLAH. Wasu tuni suka fara nuna basu yarda yaransu suje ba. Amma matasan samarin nan da Iffah ta dunkule akan sakasu aikin raba abubuwan azumi dana salla sun hade kawuna akan sufa babu gudu babu ja da baya zasu kare martabar masarautarsu da sarkinsu da kasarsu ne. Duk da
basu san wahala ba, bama su taba gain yaki na zahiri ba. Gain fa abinda matasan nan sukai yay matukar burge was hadiman suma suka fito da shirinsu na kasancewa a cikinsu..




Ga al'ummar gari ma ba'a barsu a baya ba. Dan tun zuwan labarin abinda ke faruwa ta hanyar matasan nan da suka yada a social media sai ga mutane nata yo gangami musamman matasa da dama jirafa suke ace kule suce cas, Dan shi matashi a duk inda ake dan shirin a mutu ko ai rai ne, shiyyasa a mafi yawan gaba ta rayuwa inhar wani rikici ya tashi sai ka samu matasa ne sukafi zama gaba-gaba akan al'amarin.


**.





Da sauri Iffah tabi bayan Tajwar Eshaan da ya fice da ga dakin meeting din, Shigowarta dai-dai da fitowarsa da ga closet dinsa rike da sulken yaki da bata taba sanin da su ba ma a masarautar. Da ga shi har kayan takema kallon mamaki. Shiko ya dauke kai kamar bai fahimci abinda take kalion ba ya hau shirinsa. Dammarar da yake kokarin daurawa ta rike jikinta na rawa. "Maleek mi kake shirin yi ne haka?!".

"Fita bama kasata kariya mana da al'ummar cikinta, ko kina nufin zan bar yayan mutane su tunkari wannan hadarin su kadai Sohaa".

'"Ba haka nake nufi ba, sai dai ka tuna mutanen nan kai ne fa abin harinsu kai tsaye a wanna gabar shiyyasa ma suka dauki Ammie, fitarka wannan yakin akwai damuwa. Kayi hakuri ka barmu mu muje".

Ido ya tsira mata na wasu mintuna, sai kuma ya saki murmushi ya cigaba da daura dammararsa. "Ai ke badake ma za'aje din ba..."

"Saboda mi?".

Ta fada cikin tsananin damuwa. Nan ma shiru kamar bazai amsa mata ba, sai da ya mula dan kansa a fisge yace, "Saboda matata kwai ce a a hannuna, tattalinta shine abu mafi girma a gareni, kuma kin manta kinada karamin ciki ne."

"Amma..

"Shini!!!!"

Yay saurin katseta ta hanyar aura yatsarsa akan bakinta idanunsa da har yanzu suke jazur a cikin nata. Kif-kif ta farayi da nata sai ga hawaye sharrr. A hankali ta daura hanunta saman nashi da ke a bakinta ta janye, hannunta biyu ta saka ta rike hannun har yanzu idanunta dake cikin nasa na zubda hawaye. "Bazan Iya barinka ka tafi kai kadai ba".

Murmushi ya sake sakar mata yana lumshe idanunsa A hankali ya ce, "Sohaa idan mun tafi gaba daya waye zai rike al'ummar kasar? Dole kece madadina anan, roko daya zan miki koda a rasa rayuwata a wanna gabar ki zama shugaba adala, karkiyi sakaci da hakkin, al'ummar wanna kasa. Kiyi gaskiya da adalci akan masu gaskiya, ki hukunta duk wanda yay kuskure akan kuskurensa. Ki zama uwa ta gari da zata bama ya ko dan da zaki haifa mana, ki tsaya akanta ko a kansa da ilimin addini dana zamani, ki cusa masa muhimmanci tsoron ALLAH da gaskiya a zuciya.....

Kuka ta wani irin fashewa da shi ta fada jikinsa.Rungumeta yay tsam-tsam shima yana sauke ajiyar zuciya. Gangi da aka fara bugawa na umarnin fitowar mayaka ya sashi janyeta a jikinsa a hankali, shirinsa ya karasa sai gashi ya fito a cikakken gwarzon barden sa. Bai bata wata damar cewa wani abu ba ya kama hanunta kawai suka fito. Tsitt kakeji masarautar tayi da mamakin ganin har da shi za'ai fitar, sai kuma hankalin iyaye da yawa ya dan kwanta, al'amarin kuma ya kayatar da kowa. Sai da ya gama kallonsu daya bayan daya duk kawunansu a kasa sannan ya nisa yana lumshe ido da budewa. A hankali ya furta,"Kuyi hakuri! Kuyi hakuri!. Kuyi hakuri da gazawata a matsayin shugaba gareku. Ina jin ciwo fiye da irin ciwon da kuke ji, duk abinda zan iya fada muku a yanzu kun riga kun sanshi. Wanda zan maimaita kawai shine koda na rasa raina a wannan yakin MATATA itace mai gadon shugabancin da ALLAH ya daura min, inada yakimin zata samar muku fiye da abinda ni na samar muku. Idan kuma inada rabon dawowa gareku akwai abubuwan fada a bakina sosai zan kuma isar da su gareku. Duk wanda nama ba dai-dai ba a wannan hukunci ya gafarceni, ina hango muku abinda ba lallai ku hangoma kanku ba. Nagode da tarin kaunar da kuka nunamin a tsahon shekarun dana dauka matsayin shugabanku".

Hawaye kowa keyi a wajen.

Ya dan murmusa yana hadiye abu mai ciwo da ya tsaya masa a makoshi. Hannun Iffah kawai ya kama ya nufi fada, gaba daya aka take musu baya, sai dai manyan ne kawai suka shiga. Can ya dagata ya ajiye akan kujerar karagar mulkin Shahan-shan. Wani irin kabbara aka dauka Iffah kuma ta fashe da kuka. Murmushi yayi tare da kaiwa gabanta ya ajiye guywarsa kasa ya tokare kafa daya kamar wanda ke shirin saka mata zoben baiko. Hanunnta ya kamo cikin nasa ya rike tare da kaiwa saitin bakinshi ya sumbata. Cikin wata irin murya mai sanyi da nutsuwar ya ce, "Kin tuna ranar da kika sanar da Ajmaal burinki na hawa wannan kujerar? To ki dauka yau ALLAH ya cika miki, ALLAH ya baki ikon sauke nauyin hakkin al'umma My Sohaa".

Gaba dayanta ta zubo kasa ta fada jikinsa suka kankame juna. Dole gaba daya kowa ya fice kawuna a kasa…


Bayan minti kamar biyar suka fito hanunsu cikin na juna, a gaban barden dokinsa dan amana suka tsaya, kamar yanda ya saba yay haniniya tare da kwafutar kasa yay wata irin girgiza. Murmushi yayi a hankali tare da daura hannunsu dake cikin a juna akan fuskar dokin. Sai ko dokin ya kara girgiza da matsawa gaban Iffah sosai. Murmushi Iffah dake hawaye tayi, ya kalleta shima murmushin har yanzu akan fuskarsa. Dayan hamunsa yasa ya goge mata hawayen sannan yay wani irin salon tsalle na bajinta ya haye saman dokin. Take suma sauran suka haye nasu dokunan aka cigaba da buga gangi. Iffah ta kallesa ta kalli Babiy ta kalla kaka ta kalli Hanash da duk suna a cikin wanna tafiya sai kawai ta fashe da kuka..........







🚴🚴🚴🚴Basai munga yakin ba kawai a tsallake ALLAH na gaji 😫

DAUDAR GORA
Book2
91


....Sun hadu ne a mahadar shiga jejin su da sojojin kasar da suka rigasu isowa kasancewar su a dokuna ne. Shine ya fara dirgowa da ga dokin nasa. A tare sojojin suka mika gaisuwar girmamawa ga Shahan. shan din nasu. Ya amsa musu da kulawa, tare da basu umarnin mikewa. Duk mikewar sukai, sannan shugaban sojojin ya iso garesa tab…. a hannunsa ya mikama Sayeed Tasadduq-Husain dake a gefensa. Amsa Sayeed Tasadduq-Husain yayi tare da matsawa kusa da Tajwar Eshaan, shi din masanine na gaske akan ilimin sanin taswura da bibiyar waje, dan haka cike da kwarewa ya fara sarrafa tablet din cikin bibiya ya saita abinda suke bukata. Tab.. din a maidama Sayeed Tasaddug-Husain yana mai dubansu gaba daya. Kowa sake nutsuwa yayi akan kafafunsa har shugaban sojojin.

Taku daya biyu yay sai kuma ya tsaya cak hannayensa goye a bayansa. "Bazai yuwu ace mun fito wannan yakin batare da an rasa ran wani ba a cikinmu, ina fatan koza'a rasa din to ya kasance ni ne!?.……." babu wanda maganarsa bata razanar ba a cikinsu. Dan sai da duk suka zabura suka kallesa.Basarwa yay tamkar bai fahimta ba ya cigaba da fadin, "Kowanne shugaba yakanyi yaki ne domin kare al'ummarsa da kasarsa. Haka ma kowace al'umma kanyi yaki ne domin kare shugabansu da kasarsu. To a wannan gabar ina son kuyi yakine domin kare kasarmu da kayinku. Karku damu da bada kariyarku gareni zan kasance a karkashin kariyar UBANGIJINA.Mutanen da zamu tunkara duk nan mun san mutane ne masu hadari, wanda kuma bai sani ba ya sani anan sunada hadari, sannan an raini zukatansu ne da daukar fansa tamkar yanda uwa ke rainon yaronta da abincin jikinta. A mu duka da muke nan akwai masu mata da iyaye da yaya, akwai masu yaya da mata kawai, akwai masu yaya kawai, akwai masu iyayen ma kawai. Mu duka mun barsu ne suna kuka, kuka, mai ciwon shiga kila wa kala a saran dawowarmu ko mun rabu kenan. Ya zama dole musa a ranmu mun barsu da wannan tabon, musa a ramu koda bazamu dawo ba to mu kasance su mun karesu da ga sharrin wadan nan mutanen ta hanyar shafe babinsu a doron kasa na har abadan abada. Dukanmu bamu taba yaki ba a zahirance, amma sanin kowane dan kasar ruman iyayensa kan horesa da iya wasan takobi tun yana kankaninsa musamman mu maza. Wanna yasa bana jin ko dar da ga gareku jarumaina. Zamu tunkaresu da karfin ikon ALLAH, da karfin zukatanmu, da karfin kwanjinmu, da karfin horaswarmu, da karfin kare
kasarmu, da karfin kare al'ummar mu da addininmu.
Ka tuna a ranka mafifici a halitta ya yaki kafirai ne da duk wadan nan karfin ikon domin mu kasance a yau din mu cikin bautar UBANGIJI babu wani mai kuntatamu. Sai dai idan har mune muka wofantar da darajar daya sama mana tun a wancan lokacin sai mu rayu a karkashin mulkin mallakar kaskastattun kafirai. Bana fatan mu kasance hakan da karfin ikon ALLAH "

A tare sukace insha ALLAHU. Murmushi yay a karo na farko tare da duban kaka da shugaban sojoji. "Mu ukun nan mune kwamandojin wannan yakin, kar'a taba kananan yara, dan zamu iya zama jagororin canja musu alkibla bayan sun dawo hanunmu. Daga basu ba kowa abin harinmu ne. A lokacin da kuke shagalta da yakarsu, ni zan tunkari shugabar tasu ne..

Duk sun amsa da girmamawa. Daga haka aka fara nufar abin hawa. Wasu a cikin sojoji sun shiga jirage, inda aka bukaci Tajwar Eshaan shiga daya da aka kawo domin shi amma ya ce shi akan doki zaije. A dai duk cikin matasan idan da mai sha'awar haka ko rashin jimirin tafiya a doki ya kasance a cikin sojojin.Wasu sunyi hakan, wasu ko suna tare da shi a dokunansu. Bayan anyi doguwar addu'a masu bibiyar hanya ta na'urori suka fara aikinsu. Masu dokuna ne a gaba, motocin yaki na sojoji a biye da su, ta sama jiragen yaki da suka rarrabu a jejin domin sanar musu motsin komai da zai iya tunkarosu a tafiyarsu su da suke kasa musamman ma nakan dokuna. Kamar yanda Tajwar Eshaan ya bada shawara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login