Showing 45001 words to 48000 words out of 180087 words
Chapter 16 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
kuwa?”.......✍️
_😂Da alama ta manta Shahan-shan, sai ka tuna mata fa🏃🏃🏃🥱._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (24)
........Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ido ta ɗan kallesa, babu shiri ta sake maidawa da sauri. Amma gudun kar yaga gazawar tata sai cewa tai, “Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Shahan-shan ɗin ƙasar ruman mana”. Ta bashi amsa tana ƙwaɓe fuska babu ko gargada a harshenta balle muryarta.. Mutuwar tsaye yay na mamaki, ya lumshe idanunsa a hankali, shi yau shi Eshaan ƙaramar yarinyar nan ke ambaton sunansa babu ko gargada a harshenta ko nuna shakkarsa balle akai ga tsoro a gabansa ido cikin ido. Abune da bai taɓa jinsa ba sai a bakin mahaifiyarsa ko kakarsa. Suma ɗin akan jima baiji sun ambata ɗin ba. (Kai wannan yarinya zata halaka shi)
“Kada fa kace nayi rashin kunya kasa a ɓatar da ni ban gama cika burina ba, tunda ai dai kai ka tambayeni ko”. Ta faɗa tana mai langaɓar da kai idanunta na ɗan cikowa da ƙwalla na shagwaɓa da katse masa tunani da muryar nan tata mai ingiza bugun zuciyarsa kamar tasan mi yake tunani.
Komai baice mata ba, duk da yanda take kallonsa a kaikaice. Ya dai ɗan matsa gabanta yana cigaba da kallon ta kawai har tsawon wasu mintuna yanda tai kamar wata ƴar baby na bashi dariya a ƙasan zuciya. Sai kuma ya janye tare da ɗan matsawa da ga jikin nata da ya matso a zahiri babu ma alamar yasan minene murmushi. Aiko sai gata tana jan ajiyar zuciya. Basarwa yay kamar baijita ba.
“Miye burin naki?”.
Kalmar ta fito da ga harshensa a ɗan fisge tamkar wanda akaima dole. Batare da ta yarda ta kallesa ba ta ce, “Suna da yawa, muhimmai a cikinsu dai yanzu duk sun shafeka”.
Wani kallo da ke nuna alamar ni ɗin yay mata. Tako ɗaga masa kanta idanunta na ɗan cikowa da hawaye tana ƙiƙƙifatasu. A raunane kamar ba ita ba ta ce, “Ina son sanin halin da Iyayena ke ciki duk da an sanar min ka halaka su. Ina son sanin wanene Ajmaal?. Ina son idasa tabbatar da masu fuska biyun daular ruman wa duniya koda ni bazan iya wanke kaina ga kowa ba”.
Yanda yake kallonta kamar wata sabuwar halitta sai ka ɗauka idanun nasa sun kafe ne a kanta. A hankali ya ɗaga kafarsa yay ɗan taku ɗaya zuwa uku, a gabanta ya dakata gab-gab kamar zai haɗe jikinsu. Sai dai kuma baiyi hakan ba ya ɗan bar tazarar da bata wuce tsahon yatsa manuniya ba. Da sauri-sauri ƙirjinta ya hau dokawa ganin ya mata runfa, dan duk da kasancewar ta mai ɗan tsayi a gabansa ba komai bace duk da shima ba wani dogo bane na bala'i can, sai dai kuma dole a kira shi da dogon. Kamar yanda yake duban cikin idanunta haka itama ta ke dubansa, sai dai nata cike suke da ƙwalla ga tsumar da jikinta keyi ta kasa janyewa. Hannunsa ya dogare jikin lafiyayyar ƙofar mai tsananin ɗaukar ido, sai hakan ya sake bashi damar rufeta ruf har tana jin shaƙar numfashi ma na neman mata wahala tsabar yanda kwarjininsa ya cika mata ko'ina, har ji take kamar ma ɗakin ya musu kaɗanne.
Rasa abin cewa ya sashi ɗaura yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau suna kallon juna, nasa ya sake lumshewa da sake buɗe wa a cikin natan cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara ya furta.
“Bayan kin cika waɗan nan sai me kuma?”.
Yanda yay maganar yana mai sake sarƙe kaifafan idanun nasa cikin nata da ke tara ƙwallar da bata san dalili ba ya sata shiga jujjuya masa kanta a hankali idanunta na sake cikowa da ƙwalla dan jin kusancin nasu take kamar wani dabaibayi da ya fi ma zamanta a kurkuku. Lips ɗinta ta motsa a hankali, cikin raɗa-raɗa muryarta na ɗan rawa ta furta, “Yi maka hukunci akan laifukanka”.
Da ƙyar ya iya haɗiye murmushin da ke ƙoƙarin yinƙuro masa. Sake matsar da fuskar tasa yay gab-gab da tata, hakan sai ya sake hauhawar bugun zuciyarta har yana iya jiyo yanda nunfashinta ke fita a sarƙe. Amma sai ya fuske abunsa ya cigaba da jujjuya nasa ƙwayoyin idon a nata cike da wani irin salon da ke neman fallasa sirrin da yake faman dannewa a ƙasan zuciyarsa.
“Bayan hukuncin da kikai min na son kasheni duk bai isa ba *_Niazmina_*?”.
Idanunta ta waro a matuƙar razane, tari mai ƙarfi ya sarƙeta, dan maganar tasa tazo mata a matuƙar bazata. Duk yanda yaso shanye dariyarsa a wannan karon hakan ya gagara har sai da lallausan murmushi ya suɓuce masa. Sai kawai ya jawota ya manna da jikinsa ya cigaba da yin abunsa dan ya kasa riƙewar..
(🥱Wato guy ɗin nan mugun ɗan latsi ne🚶🤭)
★Sosai take tarin har sai da ya janyeta suka koma bakin gado, shi dai murmushin sa kawai yake yana cigaba da shafa bayanta. Sai da ya ɗan lafa mata ya ɗauka tambulan ɗin ruwa da ke a side drawer ya tsiyaya kaɗan a ƙaramin cup. Ɗagota yay, batare da yayi magana ba ya ɗaura mata akan lips ɗinta. Da sauri ta shiga sha ƙwallar da ya cika idanunta da yay jajir na cigaba da sakkowa. Sai da ta shanye tas ya janye yana ƙara tsuke fuska kamar bashi ne ya gama murmushi ba yanzun. Ƙin yarda tai su haɗa ido, sai ma ta zame ta kwanta abunta ta juya masa baya. Shima komai bai sake ce mata ba yama miƙe.
“Dan ALLAH kada kaje zasu cutar da kai, dan sun saka abu a ƙasan kujerar zamanka”.
Shaƙaƙƙiyar muryarta da ke fita a dakushe saboda sarƙewar da tai ta sake ratsa dodon kunensa. Cak ya sake tsayawa tamkar wanda ake juyawa da remote, sai kuma ya ɗan waiwayo ya dubeta ganin abun nata serious ne. Tana a kwancen da take dai ta juyama ƙofar baya. Kallon kusan sakkani a shirin ya mata sai kuma ya juya ya cigaba da tafiyarsa batare da ya tanka ba. Idanu ta rumtse da ƙarfi jin ya fice a binsa.
Ranta a dagule cikin kamar bori-bori ta shiga kaima gadon ƙananun duka da tittirza ƙafafunta tana fadin, “Ni dai na faɗa ma gaskiya ai, duk abinda ya sameka kai ka sani mi ma ya shafe ni”.
(🥱Ato idan ya mutu bashi ya huta ba Iffah'r mu🤭🏃😜).
★Tsahon wasu mintuna bata iya ta tashi a kwancen da ya barta ba. Kokawa take da zuciyarta dake ingizata taje ta duba karfa ya fita ɗin. “In ma ya fita shi ya sani”. Ta faɗa a fili tana tura baki irin ko'a jikintan nam. Sai kuma can ƙasan zuciyarta ta ayyana mata (Idan ya mutu shikenan bazaki san gaskiyar rasa iyayenki da sanin waye Ajmaal ba fa kenan) zumbur ta miƙe kamar wadda aka tsikara, sauri-sauri ta fisgi mayafin abayarta ta yana a kai tana zira slippers. Ko sanda ta zauna a sashen bata san wannan ɗakin ba, amma ko gezau ta fito tana kalle-kalle. Da canki canka ta fito katafaren falon kamar wadda aka jeho.
Da sauri Sayeed Fayzul-haq da ke zaune a ƙasa gefen ƙafafunsa da wasu tarkace marasa ƙyan gani ya ɗago, shiko hamshaƙin ko motsi bai yi ba idanunsa na kan waya da ke hanunsa. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da ɗan galla masa hararar ƙasan ido, sai dai kuma can ƙasan zuciyarta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Dan tabbas tarkacen gaban nasu irin abubuwan da ta gani ne a mafarkinta kamar yanda kayan da ya sanya sukai dai-dai da wanda ta gani sanye jikinsa a mafarkin.
A ɗan daburce Sayeed Fayzul-haq ya sake maida kansa ya rissinar. Tunaninta ya katse cike da girmamawa ya ce, “ALLAH ya ƙarawa Zawjata-almilk lafiya da tsohon rai mai albarka. Barka da fitowa”.
Jin al'amarin tai wani gin-girin-gin ganin dattijon da shi kansa Tajwar Eshaan ɗin zai girmesa nesa ma ba kusa ba amma yana gaisheta da wani sinne kai na tsantsar girmamawa. Kai ita kam wannan mulkin mallaka na masu mulki baya burgeta. Tajwar Eshaan ɗin da har yanzu bai nuna yasan da zuwanta wajen ba ta ɗan saci kallo, sai kuma ta ɗauke a kasalance ta buɗe baki tana gaishe da Sayeed Fayzul-haq. Bawon ALLAH duk sai ya rikice, duk da kasancewarsa shaƙiƙin a zuri'ar gidan ina shi ina Zawjata-almilk ta gaidashi. Komai bata sake cewa ba ta juya ta koma hanyar da ta fito.
Da kallo ya bita ta ƙasan idon da tun ɗazun yake kallon nata dama. Harga ALLAH ta fara bashi tsoro. Dole yace tsoro, da farko ƙin ɗaukar abinda ta faɗa ɗin da muhimmanci yayi, amma sai zuciyarsa taƙi yarje masa hakan. Shine ya kira Sayeed Fayzul-haq akan a sallami shari'ar mutanen da ke jiransa sai nan da kwana biyu bisa wani uzirinsa. Cikin girmamawa Sayeed Fayzul-haq ɗin ke sanar masa ma ai ɗaya a ciki bai ƙara so ba har yanzu, dan sunama shirin tura dakaru nemosa ne kasancewar dama shine wanda ake ƙarar.
A dakatar kawai ya bada umarni ya yanke wayar. Bayan tabbatar da fitar kowa Sayeed ya sake kira ya sanar masa. Shine ya bada umarnin a duba masa kujerar zaman nasa da tace an saka abu. Sai gashi kuwa a cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Sayeed Fayzul-haq ɗin ya iso da tarkacen da aka samu ɗin, daka gani kuma kasan kayan surkulle ne.......✍️
_Tofa kowa sai yay takansa aljanancin Iffah da alama ya fara bayyana yau ɗin nan😂🏃🏃🏃🏃_
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (25)
........Kamar ko yaushe tana kishingiɗe amintacciyar hadimarta Jazaa na da ga gefenta tana yanka mata tupa. Magana take mata a hankali itako idanunta lumshe. Jazaa cikakkiyar ƴar leƙen asirinta ce a cikin gidan. Dan duk wani hadimi dake mata aiki Jazaa ya sani ba ita ba. Ita a karan kanta Jazaar ta ɗauka tsahon shekaru uku a sanda ta fara mata aiki bata isa faɗin ainahin wacece ita ba a cikin gidan. Dan takanzo mata ne da fuskoki daban-daban kafin ta bayyana mata ainahin fuskarta. Duk da kasancewar ta ba'a cikin hadiman gidan ba, kai ita bama a masarautar take ba UWA ce ta kawo mata ita ta razana a sanda ta san wacece itan. Amma har yau da suka kwashe tsahon shekaru tare bata taɓa iya ɗaga baki ta faɗama wani wacece ta-ƙurya ba, ta dai so gwada hakan sau ɗaya taci wahala dan daina ji da magana tayi baki ɗaya ta koma kurma. Sai da tai kusan shekara a haka sannan ji da maganarta ya dawo bayan tasha doguwar barazana. Duk wanda zai shaida makirci da tsantsar rashin imani irin na ta-ƙurya to lallai itace Jazaa. Kuma a hakan ma ba komai ta sani ba itama sai abinda taso ta sani kawai.
“Bincike na ƙara nisa kan hadimi Israr Uwargijiya ta. Dan a yanzu haka ma naga baƙuwar fuska a cikin rukunin hadiman da Israr ke aiki. Inaji a jikina kuma ɗan leƙen asirine aka turo daga jami'an gidan nan”.
Idanunta ta buɗe a hankali kan Jazaa. Kallo take mata mai kaifi da ya sakata sake gurfane gabanta kamar mai neman gafara. Cikin isa da kaushin harshe ta furta, “Ya jima yana mana aiki, kuma kowanne an samu nasara. Sai dai a gareni sabo da kaza bazai baya hanani yankata. Zan yanke masa hukuncin da ya dace da shi, dan dama na sanar masa in har aka samu matsala hukuncin zai zama dai-dai da irin na kowa. Bazan taɓa barin wani gaɓa da zai zame min matsala ba”.
Yawu masu kauri Jazaa ta haɗiye. Zuciyarta sai bugu take da sauri-sauri. In dai har Israr bazai tsira da ga mummunan hukuncin uwargijiyar su ba kenan itama wataran idan tai kuskure zata iya fuskantar kowane irin hukunci. Ya ALLAH wannan wace irin rayuwace ta faɗo ciki mai ban tsoro. Wai shin mi matar nan take nema a duniya bayan wanda ALLAH ya azurtata da shi tari-tari da ita kanta bata san adadinsa ba?. Tsawar data ratsa kunenta ce ta sata zabura. Mikewa tai jikinta na rawa. “A gafarceni uwargijiyata”. Ta faɗa illahirin jikinta na tsuma. Sai kuma ta fice da sauri ta ɓarauniyar hanyar da ta ke shigowa da fita in har ganawa da uwargijiyar tata ya kama.....
Ba ƙaramin tashin hankali wannan saƙo na Jazaa yazo mata da shi ba. Gaba ɗaya sai duk wani ɗan farin ciki data tashi da shi yau ta nemesa ta rasa. Tabbas dole ne hadimi Israr ya bar duniya a yau. Dan duk rintsi ita bata barin ƙurar da zata zame mata bi baya a bayanta koda kuwa ta wacece. Israr hadiminta ne na amana, ya matuƙar sanin abubuwa a kanta da in har aka kamashi duk da bai san ainahinta ba ayyukanta da yawa zasu kwaɓe. Wani irin lumshe idanu tai da mahaukacin zuƙar iska ta fesar, kafin tabar inda taken cikin sassarfa zuwa cikin bedroom ɗin ta, dan a yau dole ne tayi aikin nan da kanta.
★Duk yanda Jazaa taso haɗiye mummunan furucin Uwargijiyar tasu kan Israr ta kasa hakan, gaba ɗaya ta kasa samun nutsuwa. Ba yau ta saba jagorantar ai ma Uwargijiyar su aiki ba, idan aka samu kuskure kuma a sata da hanunnta ta shayar da mutum madarar mutuwa. Amma a wannan karon sai take ji bazata iya ba. Badan komai ba sai dan sanin irin bautar da Israr yay ga ta-ƙurya kamar yanda itama tayi koma take kanyi, duk haɗarin aiki aka sakashi sai ya zartar da shi koda zai cutu, dan kawai an samu akasi a wannan karon, akasin ma ba daga garesa bane tunda ya gudanar da umarnin data bashi sai a halakar da shi. Kai itakam zata samesa ta sanar da shi gaskiya (Ki kiyayi kanki) wata zuciya ta gargaɗe ta da sauri, tare da tuna mata wacece Ta-ƙurya idan ta manta...
Ni dai nace, “Hummm”
★★... MALIKAT BUSHIRAT ★....
Kamar ko yaushe kishingiɗe take a katafaren falon nata da ya jiƙu matuƙa da nau'i-nau'in kayan more rayuwa. Yayinda hadimai uku ne ka ɗai ke tare da ita dan yau tace bata son hayaniya duk da dama basu isa yin hayaniyar ba gareta. A kallo ɗaya zaka iya fuskantar tana cikin damuwa, duk da ita ɗin ba wai mace bace mai fara'a tun fil azal. Ba komai ke mata kaikawo a rai ba sai tattaunawarsu ta ɗazun da Jasrah. Tabbas tana buƙatar yaronta ya ƙara aure, kodan ya samu nutsuwa irin ta kowane namiji irinsa. Sannan tana son yakice Iffah da ga jikinsa, dan tunda har ta iya gwada kashe mata yaro wataran zata iya cin nasara ai. Ba'a ƙaramin damuwa take da zaman yarinyar nan tare da shi ba gudun karta maimaita abinda ta fara, kallafa babu tsoro ko shakka tattare da ita take sanar da cewar ita ta bashi madarar ya sha, ta rasa gane wai Iffah mutum ce ko aljana. Ita kama bata taɓa cin karo da yarinya mai shekarunta da babu tsoro ko shakka tattare da ita ba. Taya ma