Showing 162001 words to 165000 words out of 180087 words
Chapter 55 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
lafawar ciwon, harna samu damar zaman saurarenta. Ta ce da ni (Bushirat ke ce kika kawo kanki gareni ban gayyatoki ba, kika kuma zo min da bukatarki ta magance miki ita?) Kai na daga mata alamar hakane, taci gaba da fadin (Gadai abinda kike nema nan kin samu, da ga yau zuwa gobe sunanki ya koma *_MALIKAT BUSHIRAT ne, zaki samu girmamawa da ga kowa. Ada nayi alkawarin hana Haysam gadar sarautar kujerar Shahan-shan, dan in har bashi da magaji ko ubansu mutuwa yay bai isa hawa ba. Amma a yanzu saboda ke na janye komai, Zan hukunta Abdul-majeed da Haseena akan laifukansu su da zuri'arsu, amma ke kam kin tsira keda danki, zan baku gata zan maidaku yan lele) godiya na mata cike da jin dadi. Cigaba tai da fadin, (Sharadina na farko bayan kin haihu zan dauke mahaifarki gaba daya, dan wanna dan kwara daya ya isheki yakar kowa a masarautar nan, sannan haihuwarsa shi kadai a nufin shine kawai magajin wanna masarauta) na amince Uwa. Na bata amsa babu wani tunani ko kyakykyawan nazari. Murmushi
tayi tamun jin jina. Ta cigaba da fadin, (Sharadi na biyu bayan haihuwarsa zakiyi yankan bakaken shanu guda goma, rakuma mata da basu wuce shekara uku da haihuwa ba suma goma zaki soke. Sai bakaken karnuka) anan ne na dani diri-diri da jin karnuka, amma sai tai saurin fadin (Karki damu su wannan karnuna zaki yankasu domin kariyar duk wani cutarwa da wani zai kawoma danki ne, dan kina haihuwar magaji tofa babu mai zama haka kuma bayanki za'aita yunkurin gani ke da dan) hakane kuma uwa. Na gane mi kike nufi na amince. Na bata amsa cike da gamsuwa da bayanin ta. Nan ma tayi murmushi da cigaba da fadin (Zaki cigaba da wannan yanka ne duk bayan watanni shida, sannan zaki sadaukar da jinin macen hadima mai dauke da ciki karami bayan ya cika wata uku, idan ya kara wata wata ukun zaki sadaukar da hadimi mai sabon aure da basu wuce wata daya ba shima) nan ma nadan shiga rudani amma ta nunamin idan bana bukata zatai gaba, ai duniya babu abinda ake iya samu cikin sauki. Sannan kuma bawai tace na kashesu bane da kaina, nawa kawai shine bata sunansu, sauran aikin nata ne) nifa matsalata kawai shine a haifi magaji, na zama abar kwatance akan karfin iko fiye dana Malikat Haseenat dan haka na amince. Ta cigaba da fadin (Saradi na biyu lokacin da yake cika shekaru goma sha biyu a duniya zakiyi kokarin a hada aure tsakanin wani makaskancin talaka da wadda kukafi shakuwa a kannen Haysam idan an samu ciki aka samu kuma mai tambarin zuri'arsu a gado bayan kwana uku zamu amshe yarinyar, inma babu tambarin ma dai ahakan zamuyi, za kuma mu kauda Abdul-majeed a doron duniya Haysam ya gajesa. Haysam zaiyi mulki na tsahon shekarun girman danki, yana cika shekarun gadar mulki zaiyi murabus ya daurasa. A ranar nadin zamowarsa Shahan-shan za'a aura masa mata hudu, matan nan dukansu zasu zama sadaukarwarmu tare da Haysam, dan in har yana raye tofa zaki cigaba da zama yar kallo ne sai abinda Haseenat tace danki ma yayi zai yi.…..) Da sauri nace na amince, dan bazan taba iya cigaba da zama karkashin ikon wata ba bayan kuma dana ke mulki. Tayi murmushi a lokacin da fadin (Shiyyasa nake jinki kamar yar dana haifa a cikina ta-kurya. Zan saki ki zama mai nasara kuwa bisa nasarar kowa. Wannan yaro da zaki haifa zai cigaba da aure muna kauda matan har sai sun cika adadin da zasu zama ginshikin rike karagar mulkinsa. Da ga karshe zamu kawo masa matar aurensa da zata zama duk wani motsinta sai da umarninki ne, koda ta haifa masa magaji kece zaki cigaba da amsa suna MALIKAT. Dan hatta shi a karan kansa ko hukunci bazai iya zartarwa ga wani ba sai da umarninki. Ki kula ki nutsu kisa hankali a jikinki a duk aure-auren sa kada ya auri wata mai alaka da zuri'arsa, idan kuma har kikai hakan to komai ya lalace kenan, duk wahalarki ta tashi a banza, mu kuma bazamu taba amsar kuskure ba, in har kika
gagara cika wadan nan sharucidan namu zaki bamu
madadinsu ne da jinin abinda zaki haifa, dan shine diyyar kuskurenki. Kuma shine hukuncinki) hankalina ya matukar tashi dan duk duniya a yanzu babu abinda nafi so kamar abinda ke cikina din, a shiga rokonta da magagiya. Ta tabbatar min itafa saina kuskure mata ne zata aikata hakan, dan bijirewar Abdul- majeed ga ayyukanta bisa shishshigin matarsa yasa zatai masa hukunci da mutuwa da mutuwar dansa (Haysam) da ya fi so, zakuma ta tabbatarma Mammah ita ba komai bace a wanna masarautar shiyyasa ta hanyar yayan da take takama da su, dan haka Ammarah ce zata zama wadda za'"aima auren sati biyu ta haifi yar da muke bukata, dama ta kashe Miran Nayyar a cikin ruwan swimming pool na gidan, Waheeda kuwa dama bawani tanada zuciya mai kyau bane kanta kawal ta sani dan haka bata gabanta, Jin wanna kashe-kashen hukunci da zatai ga zuri'ar Mammah saboda abinda Sukai mata a bijirewa yasa na karajin tsoronta, dan haka na amince ga dukkanin shardanta. Ta bani magani nasha, tare da tabbatar min zata kaworin hadimar da zata kasance amintacciyata wajen gudanar da ayyukana. Dan dolene zan boye kaina tsahon rai batare da kowa yama taba kawowa kansa nice ta-kurya ba. Koda kuwa a cikin hadiran da zasu dingamun aiki ne matsayin ta-kurya, Bayan tafiyarta haihuwa ta tashi gadan-gadan, Alhamdullah na haifo yarona namiji mai kamanina dana Haysam. A hankali, abinda duk ta fada ya cigaba da tabbata, babu wata matar Haysam da ta kara koda kwatanta samun ciki, dan haka na kara sakankancewa da ita, duk kan umarninta na fara cikasu kamar yanda ta bada, kuma komai na tafiyamun babu wata damuwa har zuwa lokacin da aka dauke Eshaan daga gabana. Ta nuna bacin ranta, kamar yanda na nuna damuwata, sai dai duk wani kokarin mu babu wanda ya saurareni, da Mammah ce ma, itama daga baya ta bada goyon bayan dauke san. Duk da tafiyace ta wani shekaru naji zafinta, sai dai bana iya cika wata guda banje na dubeshi ba. Yawan zuwana yasa Abbu (Tajwar Abdul-majeed) yayi magana a lokacin, aka kuma sakamun dokar sai bayan shekara-shekara. Naci kuka a ranar amma uwa ta kwantar min da hankali akan daukar mataki da tabbatar min ba sai yana raye dokar zatai aiki ba.Lokaci yayi da Ammarah zatai aure. Da taimakon su Miran Jasim aka cika wanna aikin, bayan wucewar su Mammah Umrah. Anyi auren Ammarah an kuma samu cikar burin samun ciki. Bayan dawowarsu an kwashi rikicin da har yay sanadin kai Jasim kurkuku. Da ga baya dai komai ya lafa Ammarah ta haihu. Bayan haihuwarta abubuwa suka nema cabewa dalilin samo wani hatsabibin mutumn, sai dai duk da haka muni nasarar mallakar abinda ta haifa da kuma kauda Abbi (Shahan-shan Abdul-majeed) nafi kowa jin ciwo da shiga tashin hankalin abinda akaima Uwa a masarautar nan dan ranar ni nasan irin kukan da naci na tashin hankali. Kwatsam bayan na gama fidda rai da rasa uwa a wata raar da Haysam ke cika shekara uku da hawa karagar mulki sai ga uwa ta bayyana.Farin cikine ma da bazan iya musaltashi ba, itama har taitamun dariya, ta kuma nuna jin dadinta da yanda na damu da rashin ta, ashe tanada y an leken asiri da ke kai mata rahoton komai a shekarun nan da bata nan…✍️
DAUDAR GORA
Book2
87
…..……….Bayan dawowar uwa al'amuran mu sun cigaba da tafiya, dukan shardanta a cigaba da cikasu, dan dama ko bayan batanan ban fasa ba, dan ina tsoron abinda ta fada akan Saiful-malik ya tabbata. Dan wannan tsoron da son cimma buri ne suka jagoranceni har zuwa wannan lokaci. Ni naita zungurar Haysam akan yin murabus lokacin da Saiful- malik ke cika shekara talatin da uku a duniya, nayi hakanne kuma bisa umarnin uwa. A duk sanda nai maganar yakan yi murmushi ne kawai, amma baya cewa dani komai, Sai hakan ke cimun rai da tunanin baya son ya sauka ya daura Eshaan din ne. Ni kuma abinda nake hange adadin shekarun da Uwa ta tabbatar min zai rasa ransa a dalilin shayin da nake shayar da shi gabatowa suke, ta kuma tabbatar min infa ya mutu ba'a daura Saiful-malik a karagar mulki ba akwai rikici sosai, domin Haysam nada kanne, shekarunsu kuma sunfi zama shekarun hankali da yan kasa zasuyi jayayya da samun rabuwar kai akan magajinsa Eshaan. Na sake takura masa da tada hankalina akan hakan har takai wata rana ya furta min abinda ya girgizani. Ya ce (Bushirat basai kinyi gaggawa akan mutuwata ko rayuwata ba. Idan kaddarar mulkar kasar ruman na rubuce a littafin kaddarar Eshaan sai yayi ko ina raye ko bana raye, abinda na sani kawai ina matukar tausaya masa, ina tausaya masa yaki na cikin gida da waje. Yakin da zai masa matukar wahala musamman kasancewarki ke wa mahaifiya da kika zamto a cikin manyan makiyansa) rai bace nace ban gane ina cikin manyan makiyansa ba? Bai sake cemin komi ba, illa murmushi kawai da ya saba mun. Maganar ta zauna min a rai matuka, har ta kaini da fadama uwa. Itama naga alamar ta girgiza, dan haka take anan ta tabbatar min dole muyi motsin da Haysam fa zai bada mulkin nan sannan mu kaudashi, dan alamominsa na nuni da akwai abinda ya sani game da ni, idan kuma har mukai sakaci wahalarmu ta baya zata zama a banza. Babu wani damuwa a raina na bata goyon baya, dan saima tashin hankali da nakeji akan cewar Haysam yasan wani abu game da ni din, ina tsoron ya fadama mahaifinmu, dan wilhy zai iya tsireni ne kawai kasancewarsa mutum mai zafi da bin dokar addini. Haka akai, ta kawo abinda naita saka masa a madara yana sha har tunaninsa ya karkata a yin murabus, babu zato babu tsammani kawai ya dawo da Eshaan gida, ya kuma tabbatar da zai yi murabus ya daurasa a karagar mulkin Shahan-shan. Kalubalen dana so fuskanta shine Eshaan da kansa, dan yaso bijirewa da cewar shifa baya son mulkin nan, bai taba ma birgesa ba, yafi son rayuwar yanci, yayi abinda yake so a lokacin da yake so, a cikin tarin burukan rayuwarsa ma babu maganar mulki a ciki. Na tashi hankalina Uwa tace na kwantar, ta bani wani turare tace na basa kyauta, in har yay amfani da shi na kwana uku sai ya amince. Hakan ce kuwa ta kasance. dan satin bai shigeba sai gashi da cewar ya amince. Uwa ta kara shiga raina da jin bani da kamarta duk duniya, zata kuma iya sakani komai nayi amma banda sadaukar mata da Eshaan, dan shine abinda nafiso fiye da komai a duniya. Anyi nadin sabon Shahan- shan tare da shagalin bikin aurensa na mata hudu, ko sau daya bai tanka akan auren ba, baice bai son su ba bai kuma ce yana so ba. Ni kuma bam ma damu da tambayarsa ba tunda nasan makomarsu. Kamar yanda uwa ta fada Haysam ya shude, matan Eshaan ma daya bayan daya sun zama labari, an cigaba da auro masa was suma tarihinsu na shudewa, a haka har nazo gab da cikar burina na gama wannan sharadin. Rana tsaka, ina gab da cimma abinda na faro kwatsam yarinyar ta shigo rayuwata. Ba kai tsaye ta shigoba, dan bana jin ma ta sanni ita. Yaki ta shirya, ya ki domin yakar Eshaan saboda rasa yayunta biyu da suka shigo cikin aikina. Itama tanada tunani ne irin na sauran mutanen kasar ruman akan Saiful-malik ne ke halaka matansa. Wanna itace mafarin matsala, dan tunkan ta shigo ita nacema uwa ta kauda min ita, dan ina a gabar da zuciyata ta gama dakewa da bushewa zuwa yanzu, hatta hadiman dake mun ayyuka da sunyi kuskure mafita daya nake hangoma kaina shine kawai na kaudasu, idan na kaudasu matsalata ta kare kenan. Da nayi din sai inga ta kare kuma, dan haka nake kallon kashe duk wanda ya shiga gabana akan cikar burina kawai na kauda san Uwa ta tabbatar min babu kaddarar mutuwar yarinyar a wannan tsakanin, sai dai mu nemo wata hanyar, a cikin neman mafitar ne muka yanke zamowarta a daya da ga cikin matansa, domin a ganinmu idan ta matso gab da mu sai munfi cin nasara a kanta. Sai dai kuma al'amarin bai kasance yanda mukai hangesa ba, dan tunda ta shigo rayuwar gidan komai ya daina yiwuwa a cin sauki. Labarin farko ya canja zuwa wanda bashi muka tsara ba. Dan hatta madarar farko da nake shayar da duk Zawjata-almilk ita kin sha tai, alkyabba da turaren da nake badawa a musu wanka da shi a sako musu tun daga gidansu shima basu akai mata ba, ban hakuraba na bibiyeta da su nan ma taki yarda tai amfani da shi, duk ta inda muka bullo sai ta waske, da ga karshe ma wata rigar da mu bamu san ta ina ta fitoba ce ta sanya, daga haka ta koma sashen Mammah da zama, ita kuma ta kaita sashen Saiful-malik batare da shawarar mu ba bayan mun yanke a yanda zamu mata rakkiya zuwa can. Dan saboda na rabota da sashen Mamma da uwa bata iya zuwa yasa na bada shawarar maidata sashen Saiful-malik ta mana bincike, amma sai Mammah ta canja shirin namu gaba daya. Wannan abu ya konamin rai matuka, ya kuma zafi zuciyata na kasance a bakin ciki. Mairakon nasara komai sai sake tabarbarewa yake, da kyar muka samu cikon ayyukan mu akan Zawjata-almilk data tarar, Itako dai ta kasa tabuwa a garemu a duk ta inda muka bullo. Tun ana yakin sunkuru har komai ya fito fili da fitar da ban san mafari ba da ga gareta, yakin ya koma na kasanni na sanka......" ta rushe da kuka mai karfi. Sai da tayi mai isarta babu wanda yace mata ko kanzil sannan ta cigaba da fadin, "Babban tashin hankali na a yanzu da jagorantar dukkan karfin halin iya maida martanina ga uwa a wannan gabar da komai na tabbatar da ya lalace shine rasa Saiful-malik, ta sake tabbatar min sai sun amshi jininsa matsayin diyyar kin cika shardansu, bana son na rasashi, shine kadai ya kuka ya sarketa ta kasa cigaba. Jasrah ma kuka take iya iyawa, sauran yan uwanta kam tagumi duk sukayi kawai. Hankalin Iffah gaba daya akan Tajwar Eshaan yake, dan tunda ya dukar da kansa da kamo hanunta ya rumtse a cikin nasa har yanzu bai ko yi wani motsin kirki ba, hannun nata kuma na rumtse a nasan duk da azabar da takeji saboda yanda yake matse a cikin nasan haka ta cigaba da daurewa tana mai ambaton addu'oi da duk sukazo bakinta. Fatanta ALLAH ya saukaka masa zuciyarsa, ya bashi juriyar dauka.
Gyaran muryar kaka ne ya katse tunanin kowa. Ya nisa a hankali tare da gyara zamansa. "Lallai kinyi kuskure, kin kuma shiga rigar yaudara irin ta wadda bokaye kanyima bayin ALLAH saboda son zukatanmu da burin gina DUNIYA mai yankewa. Wannan mushirika tai tasiri da tasirin gurbataccen burinki ne da niyyarki ta shigowa wannan gida. Amma karya take bata da alaka da samuwar cikin Shugabamu da kikayi, dan dama sanda ta baki maganin kina tare da shigar cikinsa…....
Babu wanda bai zabura ba, hatta da Malikat Bushirat din kanta. Tajwar Eshaan kam sake kankame hanun Iffah yay cikin nasa tsam-tsam fiye da farko.
Kai Kaka ya jinjina musu, "Wanna maganar da nake fada muku haka take, dama akwai cikin. Koda ace babu shi ta bada taimakon magani shi wannan maganin sai dai ya magance matsalar wani ciwo da ya zama sanadin jinkirta samuwar haihuwar bawai ya samar da dan ba. To sai a wannan labarin ma akwai samuwar cikin ma kafin ta shigo cikinsa. Rashin samuwar haihuwa jarabawace ga duk wanda baiyiba, jarabawa kuma mai ciwon gaske da radadi a zuciya, bazaka fahimci haka ba sai in ka kasance daya daga ciki. Ya halatta ka nema magani da ga kowace irin cuta a rayuwa. Sai dai fa akwai matakan da ya kamata mumini yabi wajen neman magani kowane irine balle ma akan neman haihuwa. A duk lokacin da muka rasa haihuwa idanunmu kan rufe da fadi tashin neman mafita ta kowanne yanayi. Burinmu shine kawai mu haihun. Sam babu tunanin maybe ita haihuwar ba alkairi bace a tare damu, a ganinmu kawai mun rasa shine mu nemota ta kowace irin hanya. Duk da abinda UBANGIJI ya baka ya fika sanin dalilin baka shi, idan kuma ya hanaka ya fika sanin dalilin hanaka da yayi. A rayuwa babu abinda yafi karfin addu'a, sadaka, yarda da kaddara mai kyau ko sabaninta. Idan kuma har ta kama saika nema maganin ka zama sani ba a wata gabar. A neman haihuwa wajen bokaye da malaman tsibbu zakaci karo da abu hudu in har ka samu daya da kaje nema. Na farko rasa imaninka da cire yardarka ga UBANGIJI mai badawa da hanawa, dan zaka cigaba da ji a ranka shifa wanna din nan ne ya baka wannan haihuwar (Wa'iyazubillah). Na biyu zata iya yiwuwa dan aljani ma aka samar a cikin naka batare da kasan hakan ba kai tunda kai a kai kanka ai. Na uku wasu matan ko da saninsu, ko bada saninsu ba zata iya yuwuwa bokan yay mata cikin a zahirance ko kuma ta hanyar tsafe-tsafen sa batare da ita tasan hakan ta kasance ba domin shi tsafi gaskiyar mai shine. Idan kuma ALLAH yasa dama ana a kan gabar da ALLAH ya iyakance ne dama haihuwar
tata ta kusanto gareta batare data sani ba sai a samu dai-daito da bada maganin nasa haihuwar ta samu amma zuciyarta na tabbatar mata ta sametane daga wannan bokan ko malamin tsubbun……..✍️
Mu hadu in ALLAH ya kaimu Please🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴 hannuna ya gaji😂
DAUDAR GORA
Book2
88
."Kamar dai yanda ta kasance a gareki. Ita tana da buri akan wannan masarautar, sai akai sa'a ke ma kinada naki burin da kika kai kanki gareta. Ita kuma sai tai amfani da haka kika zame mata yar aiken isar da sakonta ta yanda babu wanda zai fahimci