Showing 33001 words to 36000 words out of 180087 words
Chapter 12 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
zargi bayan mu akwai masu harar rayuwar yarinyar nan kenan akwai ɗin?”.
“Ga alamun hakan ka gani. Sai ma nakega su ɗin sun fimu shiri. Sai dai abinda ke ɗauren kai su kuma miye nasu dalilin? Dan na hanga na hango a duk cikin wanda zasu iya aikata hakan burinsu zai kasance irin namu ne amma basu da hujjar yin hakan. Idan a matan mahaifinsa ne miye ribarsu tunda ba wasu ƴaƴane da su ba balle ace suna yaƙi irin namu ne? Anya kuwa ba iyalan Sayeed Khairul-Bashar bane ke son ɗaukar fansa?”.
“Idan kuma zasu ɗauki fansa sai su ɗauka akan wadda ba'ita ta musu laifin ba?. Idan har sune rayuwarsa zasu hara bata matarsa ba. Kuma ai tun farkon shigowarta masarautar nan aka fara wannan wasan. Akwai dai wata a ƙasa daya kama mu sani mu kuma san mai wannan shirin dan dalilinsa mai ƙarfi ne.”
Cikin gamsuwa Miran Jasim ke gyaɗama Miran Arshaan kai fuskarsa ɗauke da murmushi, dan koda basu suka aikata ba abinda ya farun ya musu daɗi har cikin rai yake jin farin ciki da nishaɗi..
★.....
Tunda Doctor ta gama dubata ta fice ya cigaba da tsaiwa akan ƙafafunsa lumsassun idanunsa da suka canja kala kaɗan na ɓacin rai ƙyam a kanta. Kallonta yake tamkar wata sabuwar halitta a rayuwarsa. Kallonta yake zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Kallo yake mata irin na miyasa kika zaɓi shigowa rayuwata a haka?, bayan ba haka na so ki kasance ba. Ƙanƙance idanun ya sakeyi a kanta yana mai datse lips ɗinsa da haƙori har yanajin raɗaɗin hakan a karan kansa. Sannu a hankali ya fara kai kawo a ɗakin hannayensa duk biyu goye da bayansa. Sosai a wannan gaɓar fuskarsa ta nuna matsanancin fushi. Zuciyarsa ta fara kaiwa maƙura akan abubuwan dake faruwa a masarautar, ya fara jin bazai iya cigaba da jurewa akai gaɓar da yake buƙata ba tun farko. Kalaman wasiyyar mahaifinsa ne suka shiga dawo masa ɗaya bayan ɗaya. A yanzu kam idanun ya rumtse tare da kaiwa zaune cikin kujera. Zuciyarsa na gudu da sauri-sauri. Sosai yake jin ɗaci mai sosa zuciya. Hawayene suka cika masa ido domin shima mutum ne kamar kowa, zuciyarsa irin ta kowa ce, yanajin zafi, yanajin farin ciki. Sosai yake buƙatar son jinsa a jikin wani. Mahaifiya ko mata. Sai dai yasan hakan shine abu mafi wahala a gareshi bayan abubuwa masu yawa da ALLAH ya azurtashi da su. Yanada tarin dukiya daya nema da guminsa, mahaifinsa ya bar masa tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. ALLAH ya bashi mulki, mulki mafi daraja sama da kowane shugaba da ke a ƙasar ruman. Ya azurtashi da ƙyawu irin wanda ko'a cikin ƙyawawa yasan zai zama abin kallo. Ya azurtashi da ilimi na boko dana addini da babu abinda zaice sai Alhamdullah. Sai dai ya tawaya ta ɓangaren mace, shi mutum ne mabuƙaci, ya daɗe da fahimtar hakan, amma ƙaddarorimsa sun nisanta shi da samun cikamakin waɗan nan ni'imomin da UBANGIJI ya mallaka masa. A hankali ya sauke lumsassun idanunsa kan Iffah zuciyarsa na kaikawo. (Abbie miyasa kace na kasance haka?) Ya ambata a zuciya cike da ƙunar da take masa mai raɗaɗi..
★★......
Jigum-jigum aka yini a masarautar cike da jimamin abinda ya faru. Al'amarin ya fara ɗaure zuciyar kowa a yanayin da yake da wahalar fassara. Sai dai a zahiri babu mai iya cewa komai sai ƴar ƙus-ƙus kai da abokin maganarka. Har yamma Tajwar Eshaan na tare da Iffah, duk da damunsa da na'urar ɗumama ɗakin da aka kunna saboda ita keyi haka ya cigaba da zama a ɗakin. Hatta da fada da akai zaman fadanci da tunanin zai fito yace wani abu akan abinda ya faru bai fitan ba. Sallama a ɗakin yayi ta yau. Hakan ya fara ankarar da mutanen masarautar kenan duk lokacin daya killace kansa yaƙi fita yana fushi ne ko cikin damuwa. Dan yau dai kusan kowa a haka ya fassara rashin fitowar tasa.
Su dai ke kiɗansu suna rawarsu, dan shi dai bai ce ba babu kuma alamar zai ce ɗin har yammaci. A hankali ta fara motsi dai-dai lokacin da yake zaune yana raira karatun Alkur'ani mai girma da wata irin sassanyar murya mai tsaushi da ratsa zuciyar mai saurare. A duk lokacin da ya samu kansa a irin wannan yanayi na damuwa mai ƙuna yafi buƙatar zama yayta karatun Alkur'ani sai ya samu nutsuwa. Da atshawa ta fara a jere har guda huɗu, hakan ya ankarar da shi farkawar tata. Amma tsabar ƙasaita da miskilanci baiko motsa ba ya cigaba da karatunsa har inda yaji zai tsaya dan kansa. Koda ya ajiye Alkur'anin ma bai juyo ɗin ba kai tsaye duk da atishawar da ta cigaba da jerawa a wahalce kuma a jajjere. A nutse ya miƙe babu alamar gaggawa ko garaje tattare da shi, sannu-sannu ya sauke manyan ƙyawawan fararen idanunsa kanta dai-dai ta sake yago tissue dake gefenta a bed side drawer ta toshe bakinta domin tare atshawan da ya sake taho mata. Kusan uku ta sake jerawa kafin ta ajiye tissue ɗin inda ta tara sauran cikin ƙanƙanin lokaci. Numfashi take saukewa a ɗan wahale kumburarrun idanunta na lumshewa da buɗewa.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (18)
.........A haka idanun nata suka kai garesa, zuba masa su tai a yanayin kallo na ƙasan ido, har ranta take jin bugun zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Ba yau ta fara ganinsa cikin ƙananan kaya ba idan yana sashensa a keɓe, amma sai taga yau ɗin kamar special ne. Baƙaƙen kayan sun masa ƙyau matuƙa da sake bayyana haskensa da ƙuruciyarsa kamar wani matashin saurayin da bai taɓa mallakar ko budurwa ba. Tsantsar ƙasaita da izzar mulki dake yawo a jininsa na ƙara masa wani irin kwarjini mai cika ido da barazana. A hankali ta ƙara ƙasa da kanta jin kamar yana nufota. Gareta ɗin ko ya iso fuskar nan ɗam-ɗam babu alamar yasan minene murmushi ma balle a kai ga dariya. Mug ɗin hanunsa da keta faman tururi da tashin ƙamshin haɗaɗɗen shayi na musamman ya ajiye a side drawer ɗin batare da yayi magana ba. Shayin ta ɗan kalla da sake maida kallonta gareshi cike da mamaki, dan ya ajiye baice komai ba ya bar wajen, bathroom ya shige, ta ɗan lumshe idanu batare data iya cewa komai ba. Babu abinda take buƙata sama da shayin a yanzu, dan haka ta ɗauka ta fara sha lokaci-lokaci tana atshawa ɗin a wahalce da duban hanyar bathroom ɗin. Tsahon mintuna biyar sai gashi ya fito yana faman sake tsuke face. Da sauri ta ɗauke idonta kamar bata gansaba itama, ta ajiye mug ɗin hanunta data kammala shanye shayin da ya zuba matan tana yaye duvet ɗin da take a ciki jin zufa na karyo mata tako ina a jikinta. Yunkurin sakkowa take a gadon dai-dai yana isowa gab da ita, hakan yasa ta dakata da miƙewar ta ɗan dubesa ta kauda kai. Idanu ya tsura mata kamar mai tunanin ta yanda zaice wani abu, kusan minti ɗaya ya ɗan yamutsa fuska cikin motsa lips da ƙyar yace, “ki shiga ruwa a bath....” ya haɗiye sauran a maƙoshi batare da ya ƙarasa ba. Sake ɗago ido tai ta kallesa, ganin nasa idanun a kanta sai ta tura baki kawai ta kauda fuska gefe sai kace wata ƴar yarinya.
(Taɓara) ya ayyana a zuciyarsa shima yana ɓata fuskar. Ƴan jin kanne yau a kusa, wanda dama ita su ta sani a zahiri. Bama ta taɓa kallonsa a jerin mutane masu sauƙi ba. Batare da sake cewa uffan ba kawai taji ya ɗan duƙo kanta, zabura tai baya, sai dai kafin tai wani yunƙuri ya ɗagata cak kamar wata ƴar baby. Yo akansa micece wata Iffah. Tsayayyen namiji ne fa ingarma da duban damtsen hannunsa kawai ya iya saka mai tsoro zawayi a wando. Baka gane hakan sai yana sanye da ƙananun kaya. Gaba ɗaya ta waro idanunta sai cikin nasa, da sauri taso kauda natan ya hana hakan ta hanyar sarƙesu. Sai kawai taji zafin zazzaɓinta na ƙaruwa ma...
“Ni dai ka daina kallona”.
Furucin ya fito cikin suɓutar baki tana laɓe fuska kamar zatai kuka, dan da gaske idanun nan nasa tsoro suke bata. Ta ɗan so bashi dariya, sai dai a zahirinsa babu ko alamar hakan sai ma sake tsuke face ɗin da yay bai kuma janye idanun nasa ba. Sai ma tafiya da ya farayi da ita a hankali. Rumtse nata ta samu nasarar yi da ƙarfi dan gaba ɗaya jikinta yamutsawa yake har zuciyarta na zallo a cikin ƙirji. Zabura tai da buɗe idanun nata a lokaci guda jinta cikin ruwa mai ɗumi sosai. Taja ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo Ummuna”.
Bai kulata ba ya ida ajiyeta a ruwan dake ta faman tashin ƙamshi na masifa, ga wani ɗumi mai ratsa ƙashi da ɓargo. Fuska a ƙwaɓe take duban kanta da yanda ya sakata ita da kayan gaba ɗaya cikin ruwan. Sai taji kamarma ta saki kuka kawai ta huta. Wannan wane irin kalar walaƙanci ne. Idan yace mata taje tai wanka kawai ai ya wadatar, amma yanzu gashi ya jiƙa mata kaya duka al'halin bata da yaƙinin wasu dan ta fahimci a sashensa take. Bai dai san tanai ba, dan tuni ma shi ya fice abinsa. Haka ta cire kayan a jiƙe ta ajiye a gefe, nutsa kanta ta sakeyi a ruwan tana mai lushe idanu kamshin ruwan da ɗuminsa na ratsata, ga yanda kumfar tai a sama ful-ful na wani irin ƙayatar da ita.....
★Ta jima a bayin kafin ta fito, sam batai tunanin samunsa a ɗakin ba. Dan haka ta fito kanta tsaye a zatonta ai zai fita ya bata waje tunda ya san wanka ta shiga. Sai da tazo tsakkiyar ɗakin tana ƙoƙarin sharce ruwan dake sakkowa daga jiƙaƙƙen kanta data wanke zuwa kan fuska ta tsaya turus. Da sauri ta juya bayanta kamar zata fasa ihu. ALLAH ma ya sota bathrobe ta sanyo ba towel ba. Ai da yau taji ƙarshen kunya a duniya.
Babu alamar zai motsa a zaman ƙasaitar da yay cikin haɗaɗɗiyar kujerar da yake duk da yaji fitowar tata. Sai da ya mula dan kansa ya ɗan ɗago idanunsa ya dubeta kaɗan ya kauda kai. (Bata tausayama kamata) ya ayyana a zuciyarsa yana jan sirrin tsaki a can ƙasan maƙoshi. System ɗin dake a cinyarsa ya ajiye saman ɗan coffee table ɗin gabansa ya miƙe fuska a daƙile, ta gabanta ya raɓa ya wuce kamar bai ganta ba. Jitai kamar tasa ihu dan takaicinsa, sai dai kuma ta kasa motsawa da ga tsaiwar har ya sake dawowa. A bazata yanzun ma taji tattausan hanunsa kan dogon gashinta data naɗe dan ya tsane da wuri kasancewar ta jiƙesa lungu da saƙo dan wanki ta masa mai ƙyau. Warwaresa yay sannan ya ɗaura karamin towel ɗin hanunsa baby pink a kanta ya fara tsane mata ruwan. A yanzu kam ba mamaki ne ya kashe Iffah kawai ba har da suman wucin gadi tai na ɗunbin mamakinsa. Ita Iffah, ɗiyar Babiy da Ummu ne tsaye Shahan-shan ke mata hidima, Shahan-shan fa ba wai hadimin daular ruman ba. Shahan-shan gaba ɗaya, wanda ke amsa shugaban na ƙasarta baki ɗaya, shugaban kuma al'ummar ƙasar ruman baki ɗaya. Sarkin da duniya ke shakka da tsoron nunama koda ƙasarsa yatsa. Ɗan gata da iyayensa suka haifa shi ɗaya ƙwallin ƙwal a duniya. Shi ɗin nan dai da duniya ke kallo matsayin wani babban tauraro mai girman gaske. “Kai ya ALLAH anya ba mafarki nake ba?”
(Idonki biyu) zuciyarta ta bata amsa da tabbatar da abinda takewa kokwanto. Ai kanta bai nema kwancewa ba sai da ya kama igiyar bathrobe ɗin jikinta ya kwance. A ɗan zabure ta riƙe hannunsa caraf cikin nata tana waro idanu. “Mi zakayi...?” kalmar ta fito a suɓuce daga bakinta. Wata irin dariya ce ta nema kufce masa ya danneta da ƙyar. Cikin ƙara kame fuska ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifin tsiya, hanun nata ya ture zai ƙarasa kwancewa abinsa. Sai kawai ta daka uban tsalle ta faɗa masa a jiki “Ni wlhy ba ƴar iska bace, babu fa komai a c....” ta kasa ƙarasawa tana ƙara cikuykuyesa da ƙyau.
Jikinsa rawa ya neman farayi saboda yanda ta ƙanƙamesa, tunda yake a rayuwarsa bayajin ya taɓa rungumar mace kamar haka. Gaba ɗaya abinda ya ɗauka tsahon shekaru yana dakon dannewa ya nema yunƙurowa. Ƙoƙarin janyeta yake tana sake ƙadandanesa a tunaninta so yake ya cire matan koda tsiya. (Ya arrahaman zata halakani) ya faɗa a zuciya yana mai rumtse idanunsa da masifar ƙarfi a zahiri. Cikin zafin nama ya finciketa da sauri yana ƙoƙarin riƙe rawar da jikin nasa ya fara. Cikin wata ƴar sassarfar da bata hana takunsa na ƙasaita fita a yanda yake ba ya bar wajen, a kujerar da ya tashi ya koma ya zube. Faɗi yake (shike nan ta buɗe aiki, Fitinanniyar yarinya zata halakani).
Oho Fareedatu batama san yanai ba, dan tana samu ya jayetan daga jikinsa ta kwasa da gudu sai saman katafaren gadon da aka gyara tsaf kamar ba yanzu ta sauka akansa ba. Bata da nutsuwar tunanin yanda akai aka gyara ɗin ko wanda ya gyara taja lafiyayyen duvet ɗin ta naɗe jikinta dake faman kakkarwa. Dan jinta take kamar wadda ta jonu da lantarki. Shiru ɗakin kowa yay ɗif a cikinsu. Babu ko motsin ac dan bai kunna ba saboda ita, duk da yana buƙatarsa, sai dai ya kashe na'urar ɗúmama ɗakin dake aiki tun ɗazun saboda itan. Sai da ya ɗan saita kansa kaɗan kafin ya miƙe, batare da ya dubeta ba ya nufi hanyar fita. Ƙasa-ƙasa ta bishi da kallo, ganin ya tsaya tai saurin kauda kanta. Bai juyo ba sai dai yaji a jikinsa ana kallonsa, murya a shaƙe can ƙasan maƙoshi ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ki canja wannan rigan”.
Jitai kamar ana narkama jikinta ƙanƙara, ta wani lumshe idanunta dake faman yin mar-mar, sai kuma ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya dai-dai da rufe ƙofar da yay bayan ya fice. Jitai gaba ɗaya kanta yama tushe, ta gagara tunanin komai kamar yanda take buƙata, kamar wadda aka zabura ta miƙe, idanunta ne suka sauka kan wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai ɗaukar idanu. Karasawa tai ta daga rigar, sai kuma ta ɗan waro idanu ganin b&p a ƙasa, “Kam babbar buta, duk shi ya ajiye wannan ma? OMG! Wannan Shahan-shan ɗin daular ruman ɗin ko”. Ta ƙare faɗa kamar zata fashe da kuka. Dan ji take duk ta daburce tsabar wata kunya da take ji na ratsata tamkar tana a gabansa.........✍️
_🥱🏇🏇🏇🏇Babu abun faɗa yau kam, nayi nan kar ace kuma..... To bara dai nai shiru kawai._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (19)
.......<<★★ TA-ƘURYA ★★>>
_(Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa mako huɗu. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya hahaha!!! hahaha! hhhhh!!!!)_
Zumbur ta miƙe daga ɗan barcin daya figeta, firgitattun kalaman uwa da tayi mata su a zahiri ne waccan ranar ke maimaita kansu yanzu a barcinta matsayin mafarki. Hannu takai ta yarce uban gumin da ya jiƙe mata goshi har yana zirarowa akan