Showing 99001 words to 102000 words out of 180087 words
Chapter 34 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
share hawaye da jera godiya. Sai kuma ta
kashe mata ido dan ta fahimci yanzu ma fa ta sake kamewa ne ta juya ta kalli Tajwar Eshaan
da ke kallonsu da alamar nuna jin dadin canjawar komai akan fuskarsa. "Ka tayani godiya *_My Asad_* (Zakina), Ammie ta
fahimceni, na sanar mata komai kamar yanda na fada maka".
A hankali ya wani lumshe idanu da takowa gabansu. Gaban Malikat Bushirat ya tsaya tare
da kamo hannayenta cikin nasa. Firgigit ta dawo hankalinta kamar wadda aka kodama mari a
cikin barci. Cikin kamewar nan tasa dake boye dukkan sirrikan fuskarsa yake dubanta a nutse.
"Ammie nagode sosai, Nagode da kika fahimci abinda naketa son ki fahimta tun tuni.Fhareedah yarinyar kirki ce mai cike da tarin alkairai daban-daban, kuma nasan zaki sake
tabbatar da hakan anan gaba. Na miki alkawarin aiki tare da ita har sai duk wani markiyinmu ya bayyana batare da shi kansa ye sani ba. Ki cigaba da mun addu'a ke dai,gaskiyar danki na gab da fitowa zahiri ga kowa.Dan yanzu haka dukkan wasu bincike akan cases din nan suna'a hannuna, hatta wanda yay tushen bada madaran, da wanda ya sakata a ruwa duk sunzo hanun hukuma. Kallonsa tai da wani irin sauri, sai kuma ta hadiye tana mai kankame hanunnsa a cikin nata. Idanunta ta lumshe hawaye sukai wani irin zubowa. "Ashe zanga wannan ranar, wanna ranar zatazo gareni haka Saiful-malik?". Ta fada cikin subutar baki.
Ko kadan Tajwar Eshaan bai fahimci kalaman nata ba, ya fassarasu ne akan nuna farin cikinta na zataga wannan raar da za'ai walkiya halin wanda batai zato ba ya fito. Sai kawai ya saki murmushi da kai hannu yana share mata hawaye. "Zaki gani Ammie. Ai dama komai yay farko zakiga karshensa na zuwa. Ki cigaba da mun addu'a ke dai indai nasarorin ne yanzu kika
fara gani. Sai kin zama mafi kololiwar uwa da zatai alfahari da haihuwar da daya tilo tamkar da
dubu insha ALLAHU"
"Na yarda da hakan Bin Haysam Abdul-majeed, tabbas na yarda, ALLAH ya makaalbarka kuje dare nayi ku huta ma karasa dasafe".
15:44
Godiya a sake mata da dan lallashi, hakama harda durkusawarta. Kafin ta wani kananna de ma Malikat Bushirat ido a kaikaice ta sakar mata gwalo. Tajwar Eshaan na juyiwa ta fuske kalar tausayi. Hannunta ya kama a hankali yana mai kallon fuskarta ya sakar mata murmushin nan nasa mai narke zuciyarta. Murtani ta maida masa da dan saka hannu ta kare fuskarta ita a dole taji kunya ne. Duk Malikat Bushirat na kallonsu. Suna ficewa ta zube kasa yarafff wani irin mahaukacin jiri na dibar idanunta. Sai kawai ta fashe da kuka tana kiran sunan Uwa.
Tantabaru biyu iyayen soyayya da alkawarin kam suna fita ya duke kasa ya bata bayansa alamar ta hau. Idanu ta waro masa waje alamar mamaki. Ya dan juyo yana kada mata kai da lumshe idanu. Babu yanda ta iya ta tattare rigarta kadan ta hau tare da makalkale masa wuya dan sam bata iya gardama ba. Takun nan nasa yake a hankali cikin izza da kasaita har zuwa sashensa tana a bayansa kwance luff mamakinsa na neman kasheta, duk wanda yasanshi a Shahan-shan din sa bazai taba mafarkin abinda yake mata yanzu zai iya ba.Koda suka shiga elevator ma bai sauketa ba sai boye fuskarta da tai a wuyansa. Aiko gaba daya numfashin da take busa masa ya nema birkita masa lissafi.Maimakon ajiyeta a daki da ya shiga sai kawai ya wuce da ita bathroom ya direta ta bude idanunta. Da sauri ta kallesa a dan rude gain inda ya kawosu. Sai kawai yay wani luuu da idanunsa cike da basarwa ya danne makunnan shower ya sakar musu ruwa a kansu mai dumi. Babu shiri ta zabura ya rikota a hankali, jikinsa ya matsota ya rungume ruwan na cigaba da sauka a kansu.
Kusan mintuna uku suna a hakan kafin ya bude idanunsa ya sauke a kanta yana mai kai hannunsa saman veil din ta ya shiga warwarewa a hankali. Tanaji tana gani ya raba jikinta da kayan da suka gama jikewa sharkaf shi ma ya cire nashi. Jikinsa ta fada kawai nata na rawa ga wata matsananciyar kunyarsa na ratsata. Sosai hakan da tai yay masa dadi, dan ya samu damar sake gain tawadan ALLAH din nan ta bayanta yanda ya kamata, yanda har sai da ya haddace ta. Ita kam har aka kammala wankan bata yarda ta bude idanunta da ta rufeba..
"Nagode"
Ya fada a hankali lokacin da yake goge mata laimar ruwan fuskarta da towel zuwa wuya da bayan keyarta. Dan dago idanunta tai ta dubesa, itama a hankalin ta ce, "Akan mi?".
“Ammie"
Ya bata amsa a takaice. Baki ta dan tura masa tana narke fuska, a dan shagwabe ta ce,
"Saboda Ammien ka ce kai daya?".
Murmushi ya dan yi da lakace mata hanci. "K ta musamman ce".
Baya ta juya masa tana murmushi, hannunta ya kamo ya sake juyo da ita. Ya dago fuskarta da kyau ta hanyar dago da habarta. "Baki yarda ke ta musamman ba ce?"
Tana dan danne murmushin ta ta ce, "Ka dan dai", Yanda ta fada da yin kamar zata dan kashe ido daya sai kuma ta jujyasu wani luuuu hakan nan zuwa gefe ya sashi jin jikinsa duk ya saki,amma sai ya kanne yayi dan murmushi kawai da sake rankwafawa suka zama dai-dai tsaho. "Zan tabbatar miki k ta musamman ce Mrs Eshaan.Dan bazaki sake rayuwa babu Eshaan a gefenki ba har abada insha ALLAHU"
Cikin dan waro idanunta kadan ta ce, "Har a kurkuku idan na koma".
"'Koda a tandun mai ne Babie. Hukunci na gama yankuwa zamu tafi can abunmu muyi zamanmu har sai kin haihu".
Takwaf-takwaf tayi da fuska kamar zata sakar masa kuka. "Wai da gaske kake sai ka maidani kurkukun?".
*kyar ya iya danne dariyarsa, a zahiri ya dan Kara tsuke fuska da daga mata gira. "Way,miki ko Mrs Eshaan zata tsira da ga hukuncin Shahan-shan ne. Ai sai munje kurkuku dole, irin wanna laifi haka da muka rakitowa kammu".
Baki ta bude a hankali zata sake magana ya manne lips dinsu waje guda, dole ta hadiye. Duk da a tsorace take da shi batai yunkurin hanashi ba, sai dai kuma bata bashi kowane irin gudunmawa ba har yay kidansa yay rawarsa ya barta. Da ga haka bakin ya mutu suka hau shirin barci, dama da biyu yay hakan dan ya gaji da maganar. Ya fara kula yarinyar nan so take tamaidashi parrot na karfi da yaji su Jaddah su sami abin masa gori. Wasu shegun kayan barci da bata san ina ya samo su ba ya dakko zai sakamata. Tako zaro ido zatai magana dan bakin faya fara dawowa (lols 😂)). Yatsansa ya daura saman bakinta ya ce, "Shill!!!". Dole ta hadiye abin cewar tanaji tana gani ya saka mata su. Ina kasa Iffah ta shige ta buya kota huta da kunyar da bawan ALLAHn nan ke dawainiyar jefata ciki itakam. Shiko gogan naku ko'a jikinsa. Sai ma nasa shirin da yay cikin pyjamas dinsa shima marasa nauyi ya jata suka fito. Zaunar da ita yaya daya daga kujerun dakin shima ya zauna kusa da ita. Idanunsa da basu ko kyaftawa a kanta ya motsa a kasalance. "Zaki sha madara?". Bawani tana jin yunwa bane, dan haka ta daga masa kai batare da ta yarda ta kallesa ba ita. Dan harga AllaH tsoron ma kallon jikin nan nasa take a tsaye, ga shi ya sa kaya marasa nauyi da gaba daya suka bayyana ainahinsa. Shi da kansa ya zuba madarar ya bata, ta amsa tana fadin, "Nagode". Shi dai nasa kawai kallonta. Yanda take shan tata a takure harya kammala ita bata gama ba, dan haka suka dan jima wajen a zaune har ta fara hammar barci.
Koda suka kammala brush suka sake yowa ya ce mata ta kwanta dan ya fahimci barci takeji sosai. A darare ta kwanta har fuskarta na bayyana tsoronsa. Yi yay kamar bai lura da ita ba, yama koma cikin sofar da ya tashi ya zauna.Itako luff tai zuciyarta cike da toro da kuma mamakin abubuwan da tai yau a sashen Malikat Bushirat. Ta jima da sanin akwai wasu lokuta da take ganin abu baro-baro a zahiri bayan ta gansa a mafarkinta, amma fa yau ita kam kawai jitai tana zano zantuka ga Malikat Bushirat din wanda itafa kamar ana nuna mata su ne cikin idanunta a lokacin, sannan tana jin wani karfin iko da izzar fadar tasu babu o dar tattare da ita. Ta dafe kanta da ke dan mata ciwo kasa-kasa, ga wani barci da ke rinjayar idanunta mai nauyi. Dole ta tattara tunanin da tsoron ta hakura tai addu'a sai ko barci.
Shima da ke zaman kallonta duk dahankalinsa nakan waya ne a zahiri sai ya shirya tattarawa ya bar dakin, dan ya tabbata idan fingilar rigar barcinta ya dagata sama kadan cikin sa'a ya iya ganin abinda yake son ga Hoton wajen ya dauka da waya ya maida mara rigar a yanda take ya mike yana sauke ajiyar zuciya. Dan ya tabbata ido biyu bazata yarda yay hakan ba cikin sauki, maybe ma tafassarashi da wani abu daban...
Maimakon shiga wani dakin barcin ya kwanta karamin falonsa na hutawa dake rukunin dakun barcin ya shiga, agogo ya kalla, ganin sha biyu ta dan gota kadan ya dauke kai. Wayar dake gefensa ta landline ya dan daddana, batare daya dauka yakai kunne ba harta shiga ta yanke.Cikin abinda baifi mintuna biyar ba sai ga amintaccensa da butar shayi. A saman lips ya amsa sallamarsa batare daya dago ko motsa daga abinda yake ba. Koda ya gaisheshi ma bai ko amsa ba, ya dai daga masa hannu kawai, shiko bai damuba ya ajiye komai yanda ya dace ya zuba masa a karamin cup yasa yar zuma kadan dan yasan baima cika shan wannan shayin da komai a ciki ba. Bayan ya kammala cikin girmamawa kansa a risine ya ce, "Ko akwai abinda shugabana ke bukata?". Yaja kusan minti daya da rabi sannan ya daga masa hannu. Duk wani yaren jiki da Tajwar Eshaan zai yi magana da shi hadimin nan ya haddacesa, dan haka cikin risinar da kai ya furta, "A huta lafiya, ALLAH ya kareka da kariyarsa". Daga haka ya fice...
DAUDAR GORA
Book two ( 52)
Duk da barcin dake cikin idanunsa tattaresa yay ya ajiye gefe guda ya tattara dukan hankalinsa kan littattafan da Malikat Haseenat tabashi. Inda zuciyarsa ke zallon zuwa kawai ya nufa bayan ya dan karanta tarihin mafarin komai. Babu bambanci da wanda Mammah ta bashi, dan haka ya ajiye gefe da burin sai ya nutsu zaiyi komai daki-daki. Bai san adadin shekarunta ba, amma sai ya kiyasta da adadin shekarun da yake kallonta da su. Yaci karo da kusan hudu da yay dai-dai da hasashensa, a ciki uku na mata daya na namiji, gefe ya maida na namijin, ya dauka wayarsa yana kallon natan da na sauran matan uku kozai dace da wanda zasuyi dai-dai. Wani irin masifar harbawa zuciyarsa tayi gain tambari na karshe bashi da banbanci da natan. Bayanin dake kasan tambarin na tabbatar da dashi aka haifeta, a duk ma wanda aka haifa a tsakanin lokacin ita kadaice wadda aka haifa da shi sauran duk yimusu shi akayi. An haifi mai tamarin a daren ranar juma'a 22 a shekarar 2003 uku ga wata.Sai dai ita kuma ta rasu ne bayan haihuwarta da kwana uku. Wani irin kai hannu yay saman kansa ya yamutsa sumarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya akai haka? Ta yaya ma? Idan har ya tabbata ita din ce ya akai take raye bayan ance kuma ta mutu? Idan kuma wadan can dinne Iyayenta tayaya suka bar masarautar ma?bata mutum ba suka boyeta sukace ta muturn? Kai ina akwai dai abinda ya kamata ya sani, farkoma shekarunta ita. Sannan sanin asalin iyayenta.Lokaci yayi da zaisa a maidosu kasar ruman.
**
Kanta sara mata yake da cio mai azaba. Ga wani irin ja da idanunta sukai. Kofar da suka fita kawai ta tsurama ido tamkar suna a wajen har kusan awanni uku bayan fitarsu. Sosai take jin kuna mai radadi a zuciyarta. Har yanzu ta kasa yarda a ido biyu take, ta kasa yarda a zahiri komai ke faruwa, ta kasa yarda ita ta-kurya wata ta tsaya a gabanta tai mata wannan in kashir.Ta kasa yarda ita ta kurya yau wani ke tabbatar mata yasan itace silar mutuwar matan danta. Ta kasa yarda, ta kasa yarda da komai.
"Ta-kurya!!".
Muryar UWA ta shiga cikin kunnenta a bazata.Firgigit ta kai dubanta ga inda taji sautin kuryar.Ita dince kuwa, zaune cikin kujerar nan tata.Yanda fuskarta ke tsuke hancinta na fidda hucin bacin rai sai ta kara muni ga mai kallo. Idanunta jajurta kara budewa akan Malikat Bushirat itama kallonta kawai take babu alamar jikinta na aiki bayan fitar numfashi.
"Kin bani kunya ta-kurya. Kin bani kunya da har kika kasance a haka kan wata karamar barazana da ga yar cikinki. Ashe bazaki iya yakin ba kika amsa takardar gayyata? Dama duk baki shirya zuwan irin wadan nan ranakun
ba…
"Uwa ya kike so nayi? Ya kike so na kasance?.Ni fa yarinyar nan ta kalla cikin idona ta fadamin abinda bayan ni da ke babu wanda ya sani a kaf duniya. Ni yarinyar nan ta shiryama makirci a gaban dana dana zama sanadin zuwansa duniya, wanda dukkan gwagwarmayata akansa ne da tabbatar da wanzuwarsa a matsayin da yake yanzu, wanda da shi take ado, da shi take takama da jin kanta ita har takai mace abar kallo. Uwa shiyyasa nace miki ki kasheta tun a farkon farawarta amma kik....
"Na fada miki na kara fada miki kashe wannan yarinyar kai tsaye ba abune mai sauki ba. Domin akwai wani boyayyen al'amari da yake zagaye a kanta. Tsaye nake kuma akan ganoshi dare da rana dan ba dake kawai ta shirya yakin ba har dani nan kaina. Sai dai abinda bata sani ba ni nafi karfin iyawarta, zan kuma tabbatar mata da hakan nan kusa. A cikin sharuddanmu kin tafka kurakurai da yawa ta-kurya, ciki harda kasa bamu alkyabba da ke a sashen mai babban daki. Tun a ranar farko kin kasa shayar da yarinyar nan madara, bayan gagara yimata wankan turare da saka mata alkyabbarmu. Kinyi yunkurin kasheta da hanunki bayan na sanar miki hakan babban kuskure ne amma kika ki jina. Kinyi kuskuren kasa saka ido har aka kaita sashen Ajlaan bada saninki ba. Kinyi kuskuren kasa hadiye abubuwa da dama dangane da ita.Wadan nan abubuwan dama wanda ban lissafaba sun taimaka mata wajen bude kofar samunki ta inda bakiyi zato ba. Babban na karshe daya bude komai kasancewarta da jininki matsayin abu guda, bayan kuma tun a farko mun sanar miki mune zamu bama Ajlaan matar aure mai kwaranye kishinsa...
"Na amsa dukkan laifina gareki Uwa, ina kuma mai neman afuwa da agajinki karki barni na fadi kasa a gabar da makiya ke burin ganin bayana. Ki fadi mi kuke bukata na diyyar laifukana komai wahalarsa zan zama mai cikashi da gaggawa ni bazan kasance mai butulci irin wanda akai miki a baya ba. Ina son yarinyar nan tayi nadamar sanin kanta ma balle ni a karan kaina".
"K mai kokarin cika sharudda ce ta-kurya shiyyasa bana iya dogon fushi da ke. Kije an miki, sai dai ki shirya dan shirinmu na yanzu zai zama a saman a bayane. Zaki biya diyyar kurakuranki da jinin bakaken shanu goma, na rakuma goma, na bakaken karnuka goma suma. Jariri sabuwar haihuwar kwana uku kamar yanda akai a wancan karon mai tambarin masarautar nan. Bayan sati guda zaki cika mana da jinin barin ciki na mata biyu masu sabon shigar ciki dan watanni hudu. Tare da namijin hadimi sabon aure shima da yay kwanciya da mace sau daya. Da ga yau madarar da Ajlaan zai koma sha zata dinga fita da ga hanunki ne, akwai shayi da yake sha a kullum kisa a nemo miki mai masa nomansa ya noma da wannan irin amaimakon wanda yake noma masa, dakin zai dawo tafin hanunki komai sai da umarninki zai aikata shi. Tana makirci da danki a tsakkiyarku,kenan sai kibi ta karfin ikon shi da ke a hanunki da ga yau. Zamu sama mata amintacciyar hadima, dan haka ta koma sashenta da zama.Muna akan bakanmu, waccan yarinyar zata shigo domin da ga gareta kawai muke bukatar magajin daular ruman kiyi gaggawar gain an kulla aurensu. Da ga shi har ita ki tabbatar sun sha wannan ruwan, shine zai hanasu sake kasancewa da juna har abada".
Cike da farin ciki Malikat Bushirat ta amsa tana jera godiya ga uwa cikin gurfana. Ji take a daya duk wani bacin ranta da tashin hankali sun kwaranye kamar ma ba'ayi ba
"Uwa sai dai akwai hadimin nan daya sakata a ruwa, Saiful-malik ya tabbatar min yana haninsu".
"Wannan bashi da wani muhimmancin da zai dameki, dan baisa ke wacece ba ai".
"Amma Uwa ita ai ta sani, baki ganin zata