Showing 84001 words to 87000 words out of 180087 words
Chapter 29 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
saka cikin nata yana murmushin nan nasa na iya lips, yana shaƙar numfashinta da busa mata nasa tana shaƙa itama.
“Miyasa baki so mu zama abu ɗaya?”. Kanta ta girgiza masa alamar bata sani ba. “Magana nake so”.
“Ba komai”.
Ta faɗa cikin muryarta da ke a matuƙar ɗashe dan gaba ɗaya wani irin kalar tsoronsa take ji.
“Dole akwai dalili, gashi ni kuma na kai matsayar da bazan iya amsar uzirinki ba balle tunanin zan dakata. Sai dai zan miki alkawarin kasancewa da ke ina mai lallashinki daga nan har lokacin da hawayenki zasu daina kwaranya Niazmina. K ba MATATA bace kawai RAYUWATACE, ke RAYUWATA ce ki riƙe wannan ki faɗama duniya da ƙarfin iko”. Ya nisa a hankali yana ɗan kai hannu saman goshinsa ya murza alamar ya gaji da maganar dauriya kawai yake. “Bazan so tilastaki ba, ba kuma zan iya barinki ba. Am so sorry zan baki sirrina da ban taɓa koda kwatanta bama wata ba a duniya, sirrina da nake ɓoyewa a tsahon rayuwar hankalina gaba ɗaya, sirrina da nake faman adanawa domin ke dana ɗauka tsahon rayuwar hankalina ina addu'ar samuwarki da ƙyawawan suffofi matar ƙwarai. ALLAH ya tsare miki ni ne domin wannan ranar Fhareedah, kamar yanda kema nake ji a jikina ya killacemin ke domin ni kaɗai, mijinki bai taɓa koda kwatanta aikata Zina ba, wata mace daba muharramarsa ba bata taɓa raɓarsa ba, mijinki ya jure wahalar ƙishin yini da tsahon dare domin ya kasance naki ke kaɗai, ke kaɗai ɗin da nake fatan ki zama ke kaɗai har ƙarshen numfashina, ki yarda zan baki wannan sirrin domin *KECE SIRRINA* Fhareedah bint Zayyan...”
Kalamansa masu tasiri ne ga rauninta, ita bamai jayayya bace mai saurin sallamawa ce. Ita bamai taurin kai bace mai saurin karɓa ce. Ita ba mai saurin ƙaryatawa bace tana da rinjayen gaskatawa musamman ga mutum mai daraja irinsa da ƙarfin iko. Bata da zaɓin da ya wuce shigewa cikin jikinsa ta sake masa siririn kuka mara sauti da tasirinsa yafi amsa kuwwar baradan mayaƙa dubu bisa dubu a katafaren filin gumurzin yaƙi na ƙarƙashin daular mulkinsa.
“Karka cutar da ni”.
Ta faɗa tana mai ƙara ƙanƙamesa cike da sallamawa baki ɗayanta. Hannu biyu ya amsheta cikin tsumar jiki ya ƙara matsota ya rungumeta jikinsa da ƙyau, “Eshaan ba mai cutarwa bane ga maƙiyansa ma balle ke da ke ce rayuwarsa my Farishta (My Angle)”.
“Na baka amanar rayuwata, na baka tukuycin hidimata domin ALLAH da girman hidimtawarka gareni da zuri'ata”.
“Ni shugabane, bama kowane rai kariya a cikin ƙasata dolene gareni balle zuri'arki Niger. Ba ahalinki kawai ba, ko ƙasar gidanku idan wani yace zai damƙa da cutarwa baza'a sake jin labarinsa ba a duniya sai dai wani ba shi ba”. Ya faɗa yana ƙoƙarin rabata da duk abinda yay masa shamaki da ainahinta. Tai ƙoƙarin kanƙamesa amma yaƙi bata damar hakan, ga lips ɗinta ya riƙe cikin nasa alamar baya buƙatar sake jin komai da ga gareta kuma. Daga haka dukkan labarin ya canja kansa. Canjawa mai girman da girmansa ya wuce fassara da baki ko rubutu. Abinda kawai na sani shine Iffah ta zama Eshaan, Eshaan ya zama Iffah a wata gaɓa mai wahalar hasashe ga duk masu iya zama ƙololuwa a hasashen. Da gaske itace ɗin sirrinsa, sirrinsa da ke matsayin sirri mafi girma a duk cikin zagayen sirrikansa....
★★..... ★.....
Duk yanda doctor ya so fahimtar da Miran Jasim da ya matsa a sallamesa ya ƙi saurarensa, akan dole ya sallamesa a daren. Motar asibiti ta kaisa har ƙofar sashensa. Duk ruɗewa matansa sukai da ganinsa, sai dai ko kallon inda suke baiyi ba ya shige ɗakin shi. A falonsa ya samu Miran Arshaan na faman kaiwa da komowa. Bai yi mamaki ba dan yasan shegen ruɗewa irin na Miran Arshaan ɗin, shi sam bai iya controlling tashin hankali ba ta siyasa a wani lokutan. caraf kawai yaji Miran Arshaan ɗin ya cafki hannunsa ya nufi bedroom ɗin sa da shi abinda bai taɓa faruwa ba.
“Anya kana lafiya kuwa Arshaan?”. Ya tambaya yana dafe wuyansa da ke masa zafi ko magana yayi, cikin gatse Miran Arshaan ya ce, “Haukacewa nai”. Dai-dai da shigarsu ɗakin. Miran Jasim ya fisge hannunsa yana mai dalla masa harara, “Ai na fahimci hakan tun ɗazun, nikam ka ajiye wannan shirmen naka kamun bayanin da zan fahimceka kasan ban cika son hauka ba fa”. Wata irin shegiyar dariya Miran Arshaan ya kwashe da ita yana nuna Miran Jasim, “Idan hauka nake kaima wlhy yanzu zaka fara Jasim.......” tiryan-tiryan ya kwashe komai ya sanar masa. Ashe kam haukan Miran Arshaan ɗin ƙarami ne da gaske. Dan take Miran Jasim ya rikice yana rantsuwar lasar takobi akan sai ya datse numfashin Tajwar Eshaan da Iffah kafin su su tona musu asiri.
“Wannan duk bashi ne mafitarmu ba in faɗa maka, neman barbushi a wannan daren shine. Sai dai kuma akwai matsala, dan a haƙe wancan matsiyacin yake da son ganin wanda zai fita a daren nan. Shawara ɗaya gareni muyi fitar rana kuma a daban-daban”.
Miran Jasim ya gamsu da hakan, anan suka tsaida maganar Miran Arshaan ya wuce. Sai dai a wannan daren kam babu wanda ya rintsa a cikinsu. Dan hatta Jasrah kasa gane kan Miran Arshaan tayi gaba ɗaya.....
★★.. TA-KURYA ★....
A wani irin matsanancin firgici ta farka da ga mummunan mafarkin da ya nema zama sanadin bugawar zuciyarta cikin barcin jiran uwa da ya figeta. Sai kuma ta zabura dan farkawar tata dai-dai da dirowar UWA kamar wadda aka jeho. A gaban uwa ta zube babu alamar tana cikin hayyacinta, “Uwa ki tabbatar min mafarki nake, kice min ba Saiful-malik ɗina ba, kar kicemin tabbatacce al'amari na gani......”
“Tabbatace ne, tabbas tabbatacce ne. Taci nasara, taci nasara ta-ƙurya taci nasara a kanki Ajlaan ya sallama mata. Ƴar shilar kanari ta zama mai nasara saman nasararki, ya bata sirrinsa fiye da girman kowane sirrinsa da wani ya sani a duniya, kin karya mana alƙawari da sakacinki. Dukkanin wahalarki ta baya ta rusa. Kina cikin matsala. Ke ce a matsala Ta-ƙurya, dan mu ba'a karya mana alƙawari ta-ƙurya, ba'a saɓa mana alƙawari, domin mu sharaɗinmu baya tashi hhahaha!!!!!.....”.
Rawa jikin Malikat Bushirat yake kamar mazari, ga zufa tai mata wani irin mahaukacin sharkaf a jiki. Idanunta kam duhu-duhu take gani a cikinsu, tun tana iya jin furucin Uwa a kusa da ita har ya fara nesa-nesa, a cikin mintuna biyu tai rufff tare da yin baya yarafff ta zube alamar babu rai.......✍️
_Tofa abin na gaske ne. 😱🏃🏃🏇🏇🚴🚵🚲🛵🏍️🚙🚗🛻🚐🚚🚛🚜🏎️🚒🚑🚓🚕🛺🚌🚈🚝🚅🚄🚂🚃🚋🚎🚞🚊🚉🚍🚔🚘🚖🚆🚢🛳️🛥️🚤⛴️⛵🛶🚟🚠🚡🚁🛸🚀✈️🛫🛬🛩️Wanda duk wanda ya shirya yazo mu ware kawai😷😷🙆🙆_
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (44)
........Bai fahimci gagarumar ɓarnar da ya aikata ba sai da ya dawo jayyacinsa. Tun-tuni azaba tasa Iffah ta sume masa batare da ya farga ba. Ba ita da dama ya zama dole ta jigatun ba, hatta da shi kansa a jigacen yake kasancewar wannan shine lokaci na farko a tarihin rayuwarsa. A kallo ɗaya zaka fahimci tabbas maza sunyi laushi, laushi bana faɗuwa ko gazawa ba, laushi na jin-jina girman UBANGIJI da godiya a garesa dan shine mai azurta bawa da ni'imomin kala-kala iri-iri daban-daban da kai kanka baka fahimtar girman wannan ni'imar sai randa ta isa gareka. Babu ɗan gata a ma'aurata mace ko namiji sai mafi ƙololuwar iya riƙe kansa da nisanta kansa da ga ZINA har sai randa ALLAH ya azurtaka da halal ɗinka. Ya shaida yau kam ya shaida. Bayan uwa da uba da kakarsa bayajin ya taɓa jin ƙauna da soyayyar wani mai tsananin ƙarfi a zuciyarsa kamar yarinyar nan. Ƙololuwa yake jinta, ƙololuwar da in har akace yay fassara ba lallai masu jinsa su iya yarda ba ko zaman saurarensa har ya kai inda yake buƙatar gamsar da su. Badan kar ace ya bada maza ba da shimafa kukan zai fashe da shi kawai a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya ɗagota yana ɗan bubbuga fuskarta da kiran sunanta cikin sarƙaƙaƙƙiyar muryar sa. A baɗini a birkice yake, amma a zahiri da zaka iya ganinsa a nutse yake komai tamkar ma koman da mai kallo zai kalla komai bai zama komai ba. Iya jijjiga da kiran sunanta da yayi babu alamar rai tare da ita. Ya rumtse ido da ƙarfi tare da kai hannunsa saman goshinsa yana murzawa tsabar baima san miya kamata ace yayi ba. Shifa ɗan gata ne, ɗan hutu ne, ɗan lele ne, tunda ya tashi bai san komai ba sai ai masa cikin bada umarni, a inda ya rayu zagaye yake da masu hidima daban-daban da ko abinci inda zai yiwu tauna masa za'ai a zuba masa a cikinsa. Sai da yay matuƙar yaƙi da iyayensa kafin ya samu wasu damammaki na dogaro da kai dan shi yafi son tsayawa a kan ƙafafunsa koda ace shine mafi zama ƙololuwar gata a wannan rayuwar. Bai taɓa ƙyamatar rayuwar talakansa ba sai ma birgesa da basa tausayi yake. Shiyyasa ya zaɓi shiga cikinsu ta hanyar ɓadda kama, ya kuma ƙir ƙiri wasu hanyoyin tsaya musu a duk lokacin da ya fahimci ana zaluntar su.
Bashi da zaɓin da ya wuce sake maidata a jikinsa kawai ya rungume tsam-tsam ya shiga bata wasu irin manya-manyan sumbata masu daraja da ba'aima macen data ɓarar da darajar a wajen marasa daraja. “Kiyi haƙuri, kiyi haƙuri na tuba my Ashna”. Ya faɗa cikin kunnenta yana ɗan hura mata isaka a sautin muryar nan tasa da ta sake disashewa matuƙa cikin maƙoshi kai kace zata iya jinsa. Kamar ko wani siddabaru sai kawai tai wani irin zaburowa da jan numfashi a fisge. Da sauri ya janye hannunsa da ke saman goshi ya dubeta, sai kuma ya sake riƙota da ƙyau cikin jikinsa da take neman kufcewa yana ambaton sunan ALLAH a daburce. Wani irin siririn kuka data sake birkita masa lissafinsa ta sake sakar masa tana ƙanƙamesa da jera masa magiyar roƙon ya barta, ya barta zata mutu, dan a rayuwar Iffah bata taɓa cin karo da azaba makamanciyar ta wannan gaɓa ba.
“Am sorry relax, cool down babie” ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta cikin jikinsa da tura yatsun hanunsa cikin birkitacciyar sumar kanta da ya gama harmutsawa. Har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahi bai daina lallashin da bai san taya zai mata magana mai tsahon da zata fahimcesa ba. Shi gaba ɗaya ma ya wani mance kansa a matsayin Shahan-shan, duk ta gama harmutse masa ɗan sauran lissafin da ya rage masa da rikicinta. Yasan zai fiskanci ma fiye da haka in dai yarinyar nan ce, ba'ace mata kule ba ma tace cas inaga yau shi ya taro fitinarta da karan kansa, ai yasan a darunta ma bata fara komai ba kam dan har yanzu bata gama dawowa a hayyacinta ba ballema ta fara. A hankali yay ƙoƙarin kwantar da ita domin sauka ya samu mafita amma ta ƙanƙamesa ta na sake sakar masa wani sabon kukan da ko muryarta ma ba'a iya ji tsabar yanda ta gama galabaita. Ji yay kawai murmushi mai sanyi ya suɓuce masa, sake riƙota yay yasa a cikin jikinsa yana hura mata iska a kunne cike da soyayya da ƙaunarta da ke neman fallasa kansu a zahirinsa. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa jikinta na saki kaɗan-kaɗan, da ga haka wani wahallen barci yay awon gaba da ita. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da ita a hankali sannan ya sauka a gadon.
Cikin ƴar sassarfar da a zahiri bazaka taɓa gani ba, dan babu abinda ya canja a salon tafiyarsa ta ƙasaita ya nufi bathroom, ƙarƙashin shower kawai ya shiga, babbar gaba ɗaya ya kunna ma kansa tare da dafe bangon glass ɗin da aka zagaye wajen shower ɗin kamar wani ɗan ɗaki. Duk da sanyin da garin ya ɗauka na hadarin da aka haɗa ya ƙare da isaka da ɗan yayyafi ya baje dana ruwan baya jinsa ma. Cikin ƙanƙanin lokaci ruwan yay masa sharkaf, tattausan yalwataccen gashin kansa duk sun kwanta masa a goshi har wasu na ɗan taɓa saman idonsa saboda ɗan tsayin da suke da shi. (She's my everything. Ta daban acikin daban ƙololuwa!....) Kawai yake iya maimaitawa a zuciyarsa hakwaransa cije da lips ɗinsa kamar zai hudasu kawai ya huta. Sai da ya kwashe kusan mintuna bakwai a ƙarƙashin shower ɗin sannan yasa hannu ya danne makunar yana sauke numfashi a jajjere. Har lokacin hannunsa ɗaya dafe da bangon glass ɗin. Jin atshawa na taso masa sannan ya buɗe idanunsa da sukai wani irin jajir da ƙanƙancewa. Sanin in har ya fita da wannan sanyin a jiki zazzaɓi salamu alaikum ya sashi sake kunna shower ɗin, sai dai yanzu ruwan ɗumi ne saɓanin ɗazun. Sumar kansa ya shiga yamutsawa a kasalance ruwan ɗumin na ratsashi da ƙyau, da ace zai iya kuwwar tattaro hankalin mutanen duniya baki ɗaya zai faɗa musu itace komansa, idan yace komai, komai da komai yake nufi akan komai. Sake jin kiran salla ya sashi ƙarasa komai a gurguje ya fito..
Yana fitowa a kanta ya fara sauke birkitattun idanunsa da launinsu ya zama abin firgitarwa ga mai kallo. Tuni barcin da ya ɗauke ta ya ƙara nisa, barcin da shi a karan kansa yasan na wahala ne kawai. Janyewa yay ya cigaba da takowa cikin ɗakin sannu a hankali kamar mai sanɗa, dan gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi kona sisin kwabo. Sai dai jarumtarsa ta ɓoye komai bayan canjawar launin idanunsa baka isa fassara yanayinsa ba. A gurguje ya busar da kansa domin rage laimar cikinsa ya shirya cikin jallabiya mai taushi fara tas, ya ɗaura baƙar alƙyabba irin ta sarakunan Saudiya da mayafi a kansa tare da daɗaɗan ƙamshi kamar ba sallar asubahi zai fita ba. Gaban gadon ya tako a hankali, barcin kam da nauyi ya ɗauketa, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar wahalce takeyinsa, dan sai yamutsa fuskarta da yake ɗan gani a hasken ɗakin da yake dimmm take ga ajiyar zuciya da take ta faman saki a jajjere. Idanunsa ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kanta yana sakin guntun murmushi da jan jikinsa baya a hankali ya fice fara gabatar da salla kafin ya dawo su ɗora daga inda suka tsaya dan yasan sabon daru kam zai fuskanta. Shi kuma ko a yanzu badan yana jin tausayinta ba sake zuwa mata zai a yanda yake jin kansan nan.
★Ana idar da salla ya baro massalin, dan gaba ɗaya hankalinsa na gareta saboda yasan tana matuƙar buƙatarsa kusa da ita da taimakonsa a wannan gaɓar. Yanda ya barta haka ya dawo ya sameta. Yanzun ma baiyi wani motsin da zata farka ba har ya kammala zame kayan jikinsa ya canja da ƙananu. Bathroom ya nufa ya haɗa ruwa na musamman sannan ya dawo gareta. Kai tsaye ya kunna wutar ɗakin da ta haske ko'ina ko allura kuwa ka yarda kaga abunka. A hankali yake bin ɗakin da kallo tamkar yau ne karo na farko da ya fara kasancewa a cikinsa. Ya ɗan saki murmushi yana mai lumshe idanunsa da sake buɗewa. Shi kansa ɗakin ya ƙara zama mai wata irin daraja da kima ta musamman a garesa, dan ya zamar masa ɗaki mafi zama ƙololuwar sirri sama da duk sauran sirrikansa. Dubansa ya kai ga gadon inda Iffah ke ƙudindine sai faman sauke ajiyar zuciya take yi cikin barcin wahalar da take yi. Magiya roƙo neman agajin da ta dinga jera masa na dawo masa daki-daki, da'ace gilashin ɗakin nan ba mai hana fitar sauti bane babu abinda zai hana a daren na jiya gaba ɗaya daular ruman su jiye masa sirrinsa, dan bakinta bai mutu ba sai da ta sume masa. Ya ɗan sake murmusawa da takawa sannu-sannu kamar wanda baya so zuwa gaban gadon ya zauna gefenta. Fuskarta da tai luɓu-luɓu na kukan data sha ya shafa yana kaima lips ɗinta da sukai bushewar wahala sumbata. A firgice ta farka tamkar ɗazun, ta saki wani irin wahallen kuka da jujjuya kanta tana mai jero masa roƙon ya barta, dan ALLAH ya barta karya kasheta bazata iyaba. Yanda take yi ɗin dole ne ya baka tausayi, dan a kallo ɗaya zaka fahimci har yanzu bata cikin hayyacinta. Shi baima san ta ina zai fara ba duk da ya jima da shiryama irin wannan ranar ba tun yau ba, amma a yanda yaje mata shi kansa yasan ya jigata ta, irin jigatawar da da'ace wani ne ya aikata aka kawo masa ƙara sai ya hukunta mutum. Sai gashi