Showing 75001 words to 78000 words out of 180087 words

Chapter 26 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (39)



.........Zuwa yanzu labarin abinda ke faruwa da iyalan Miran Jasim ya gama kewaye cikin masarautar. Hasalima babu wani ka-ce-na-ce dake kai kawo sama da zancen. Musamman da ya kasance Umm Husam na ƙarƙashin kulawar likitoci har yanzu, duk da dai Alhamdullah sun sami nasarar mata ɗorin karayar data samu a cinyarta. Amma taji mummunan ciwo a ƙashin bayanta da bama a saka ran zata iya ƙara cigaba da takawa da ƙafafunta. Malikat Haseenat ta fita dubasu a asibitin har shi Miran Jasim ɗin dan shima dai ya jigatu a hannun Husam ƙwarai da gaske. Lokacin da take fitowa bisa rakkiyar Daneen Ammarah da hadimanta amintattu irin su Banou tawagar Tajwar Eshaan ke gabato Clinic ɗin shima. Malikat Haseenat ta kafeshi da idanu na tsahon lokaci, yanda yake tafiya ɗaɗɗaya cike da ƙasaita da izza, ga wani mayataccen ƙamshinsa da tun kafin ya iso shi ya iso hancinansu. Sai dai fuskar ciɗin-ciɗin fiye da kullum alamar akwai ɓoyayyar damuwa tattare da shi. Idanu ta ɗan lumshe tana ɗan murmushi da jin tarin ƙaunarsa na sake mamaye zuciyarta. Tana ma jikan nan nata so mai ƙarfin gaske da itama bata san adadinsa ba. Zubewar Hadimanta bisa gwiwunsu ya fargar da ita isowarsa gab da su. Itama ƙasa tai da kanta alamar girmamawa garesa. Tun kusantowarsu wajen idanunsa shima na'a kanta, sai dai bashi da damar tsayawa gareta kasancewar a Shahan-shan ɗin sa ya fito ba jikanta ba. Har cikin ransa yana ƙaunar wannan baiwar, ƙauna irin wadda shi kaɗai ya barma zuciyarsa sani.
     Sai da suka shige sannan ta dubi Daneen Ammarah tana murmushi. Itama murmushin tai mata sai dai batace komai ba suka nufi motar da suka zo Clinic ɗin a ciki.

         Fuskar nan a matuƙar tsuke cike da barazanar da ke sake fidda ainahin kwarjininsa yake duban Miran Jasim da gaba ɗaya yake jin ya ruɗe bazai iya ma haɗa ko ido da shi ba. Gaba ɗaya yaron ya sake masa wani kwarjini mai ban mamaki fiye da da. Duk da ya tako zuwa Clinic ɗin ko uffan bai furta ba sai kaifafan idanunsa da ke sakaye a gilashin nan dan ɓoye yanayinsa da ya zuba masa. Sai su Sayeed Fayzul-haq ne ke tambayar lafiyar tasa da yawun Tajwar Eshaan ɗin. Shiko ko sau ɗaya ma bai motsa lips ɗinsa ba a wajen, hasalima shi hankalinsa kamar rabi da rabi ne a tare da su nan kawai. Basu wuce tsaiwar mintuna biyar ba suka nufi ɗakin da Umm Husam take itama. Itako ganin Tajwar Eshaan da kansa yazo dubata sai ta fashe da kuka. Idanunsa ya ɗan lumshe kawai, sai Sayeed Fayzul-haq ne ke bata haƙuri. Nan ɗin ma dai basu wuce mintuna biyar ɗin ba suka fice.
         Da ga shi sai Miran Arshaan da Sayeed Fayzul-haq suka koma sashensa, sai amintaccen hadiminsa da baya rabo da shi a koda yaushe, jami'an da ke bashi tsaro biye da su kowanne hannu ɗauke da mahaukaciyar bindiga. Tako ina hadimai zubewa suke, sai dai ransu fari tas da ganin sarkinsu duk da ba suna ganin fuskarsa bane. Amma suna jin alfaharin sun taɓa ganinsa, koba komai suna jin shauƙi da sanin fuskarsa sau ɗaya koda bazai sake buɗeta a gare su ba har abada.

         Shigarsu da ƴan mintuna shugaban jami'an tsaron ya nema iso. Kasancewar Sayeed Fayzul-haq ya san da zuwansa cike da girmamawa yake sanar da Shahan-shan tare da neman afuwar sanar masa a ƙurarran lokaci. Alama yayi ta abashi izinin shigowar kawai. Takaici ya sake kume Miran Arshaan da ke zaune shima. Ya ballama Sayeed Fayzul-haq hararar gefen ido yana ƙwafa a zuciyarsa.
     Cikin girmamawa shugaban jami'an tsaron ya miƙa gaisuwa, amintaccensa ya amsa a madadinsa. Zaune ya kai a inda Sayeed yay masa nuni, cikin sake risinar da kai na girmamawa ya miƙa files na hannunsa guda uku. “ALLAH ya ƙarama adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana masu albarka. Alhamdullah mun kammala binciken da mukai alƙawarin yi yanda ya kamata, sai dai muna mai neman afuwar jinkirin da aka samu bisa wasu dalilai. Wannan files ɗin na cases ɗin ne duka uku. Alhamdullah mun sami nasarar gano hadimin da ya ɗakko Zawjata-almilk daga kurku ya jefata cikin swimming pool, a yanzu haka kuma yana hanunmu dan a daren ranar litinin muka cafkesa yana shirin guduwa da ga cikin masarautar nan. Mun gano shine ta hanyar zanen yatsun hanunsa da muka samu a jikin ƙofar kurkukun daya kasance ɗaya da ga cikin shaidun mu. Ya tabbatar mana da cewar sakashi akayi sai dai shima bai san wacece ba, amma ta jima tana sakashi ayyuka masu kamanceceniya da wannan tun ba yau ba. File na biyu akan kisan Sayeed Khairul-Bashar ne....”
     Wani irin bugawa mai azabar ƙarfi ƙirjin Miran Arshaan yayi kamar zuciyarsa zata faso ta faɗo. Shugaban jami'ai da bai san yanayi ba ya cigaba da faɗin, “......shima mun gano an kashesane ta hanyar kaisa ɗakin baya da ke a can wajen tsohon kurkukun can akai masa kisan gilla. A binciken da mukai cikin ɗakin ne muka gano zobensa da ɓalin gilashin jikin eyeglasses ɗin idonsa daya fita, tare da suffar hadimin da ya dinga azabartar da shi har ya mutu a gwajin ƙwayoyin idonsa da muka bibiya. Jinkirinmu ya samo asaline ma a dalilin binciko hadimin kasancewar yana rufe fuskarsa ne a lokacin aikata laifin. Shima dai kamar wancan ya tabbatar mana sakashi akayi, sai dai shi yanada matuƙar taurin kai dan yaƙi faɗar waɗan da suka sashi, da alama kuma shi ya sansu sani na zahiri saɓanin wancan.”
       Fitsari kawai ya ragema Miran Arshaan ya saki, amma illahirin jikinsa tsuma yake yana ƙoƙarin dannewa. Shugaban jami'ai ya cigaba da faɗin, “File na uku tushen samuwar madarar da aka kai sashen Zawjata-almilk ne.....”
          (Kun mutu Arshaan) zuciyar Miran Arshaan ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali. Da ƙyar ya iya haɗiyar busashen yawu da fisgo numfashisa da ke neman suɓucewa da ga gangar jikinsa. Shugaban jami'ai ya cigaba da faɗin, “...madarar ta fito ne da ga sashen gidajen kuduncin wannan daula, dan an ɗauke ta daga can ne zuwa sashen uwar masu gida saboda yin ɓadda kama. Dan haka suspect ɗin mu dole zai kasance a ɗaya da ga waɗan can gidajen guda shida dake a cikin file ɗin. Domin a daren ranar ɗaya daga cikin jami'an mu ya ga wani a suffar ɓadda kama ya fito ta wata ɓarauniyar hanya da muma bamu san da ita ba a gidan nan. Munbi diddigin masu bin hanyar a tsahon kwanakin nan daya tilasta jinkirinmu, mun samu mutane huɗu sai dai har yanzu bamu tabbatar da fuskokinsu ba kasancewar a shirin ɓadda kama suke fitar. Amma hakan ba matsala bane saboda hanyar tabbatar da su ɗin su waye tana a hanunmu muna kan sake tabbatarwane gudun samun kuskure. Albishir dai da zamu bayar akan shi wannan case ɗin a yanzu haka wanda ya samar da dafin macizan yana hanunmu. An kamosa ne kuma a safiyar yau”.
      A karan farko Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ya saki wani malalacin murmushi da ya nema sumar da Miran Arshaan da ke jin kamar ya rumtse ido ya gansa a sashen sa ko clinic wajen Miran Jasim ko ma wajen boka Barbushi shi ma bai san ina yafi so yaga kansa ɗin ba. Sayeed Fayzul-haq kam kansa kawai yake faman jinjinawa ransa na mamakin waɗan nan abubuwa abin kamar wani shirin film. Amintaccen hadimin Tajwar Eshaan kam abun ya masa daɗi, musamman ganin murmushi mafi tsadar gani a fuskar shugabansa adali, sannan koba komai a su kansu ma amintattun hadimansa suna fatan kowaye ɗin kodan wahalar da suka fuskanta ta kusan wata guda a kurkuku. Shi dama ya daɗe daji a ransa Zawjata-almilk bazata iya aikata abin nan ba sai da jagorancin wani sheɗanin da ya fi ƙarfinta. Dan haka kawai yake jin ƙaunarta matuƙa musamman da ya fahimci wani abu ɓoyayye da ke tare da shugabansa game da ita duk da yana ƙoƙarin ganin ya danne. Amma kuma shi a yanzu babu wanda ya kaisa sanin wanene Tajwar Eshaan, koba komai barci ne kawai ke rabasu sai ko idan ya shiga ciki ko ya yini bai fito a bedroom ba. Kuma ko'a hakan tabbas tabbas sai ya gansa a yinin sama da sau biyar. Zai iya cewar da ga matarsa a yanzu sai shi ko a mafi ƙololuwar ganin Tajwar Eshaan ɗin.
        Wani irin kirari ya shiga jeroma shugaban jami'ai, tare da jinjinar ban girma na ƙoƙarin sa da yawun Shahan-shan da bayan murmushi babu alamar zaice wani abu. Magana da ga bakin amintaccen Tajwar Eshaan tamkar kai tsaye ne da ga bakin sa, dan yana cewa ne da say ɗin sa bawai raɗin kansa ba. Sannan koba komai shima a idanunsa Tajwar Eshaan ɗin ya saki murmushin nan da zai iya rantsuwa bai fi a karo na ƙalilan kenan ya taɓa gani ba. Hakan na nufin da gaske Shahan-shan ɗin ya yaba da ƙwazon jami'an tsaron gidan koda bai furta ɗin ba. 

       Jiƙewa iya jiƙewa jikin Miran Arshaan ya gama yi da zufa. Ga wani irin hajijiya da idanunsa suka fara gani. Kaɗan ya saci duban Tajwar Eshaan da babu alamar hankalinsa a kansa yake, hakama Sayeed Fayzul-haq. Yawu ya haɗe masu kaurin da har yanajin suna kamar ɗaɗa masa maƙoshi. Da ƙyar ya iya jarumtar cigaba da zama har shugaban jami'an tsaro ya gama ya fice. Babu alamar Tajwar Eshaan zai sake cewa wani abu akan batun, hakan yasa shima Sayeed Fayzul-haq haɗiyewa ya ɗakko zancen Miran Jasim da iyalansa, sai ɗansa dake a sashen Malikat Haseenat har yanzu. Ba ƙaramin dauriyar danne tashin hankalinsa yay wajen saka musu baki ba gudun kar Tajwar Eshaan ya harbo jirginsa. Dan ya mugu-mugun sanin hatsabibancin yaron nan, babu abinda ya baro a halin ubansa sai ma finsa taurin kai da yayi. Tattaunawar ta ɗan jasu wani lokaci dan har gab da magrib sannan suka tashi..........✍️


______________


Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏


__________________



   
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (40)


______________

Lifestyle_Nig for everything that makes your lifestyle complete ..👌
Furnitures
Decoration
Kitchen items &
Boutiques
Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna
Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot
Instagram Lifestyle_Nig
Facebook Lifestyleng
Tik tok Lifestyle_Nig
Delivery nation wide 08036414048
Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah

_______________



..........A bala'i bala'in matsanancin tashin hankali Miran Arshaan ya nufi clinic, yaji daɗin samun Miran Jasim da ke tambayarsa lafiya ganinsa a firgice shi kaɗai. Maimakon amsa masa sai ca yay, “Kasa a sallameka da ga clinic ɗin nan a daren nan”. Cikin kallo mamaki Miran Jasim ya ce, “Kamar ya nasa a sallameni, kai bakaga yanda shegen yaron nan nawa ya fasan kai ba. Ga wuyana tsabar yanda ya nema karyashi sai da aka samun wannan abun”. Ya kare maganar da nuni da abin wuyansa. Tsaki Miran Arshaan yayi yana ji kamar ya sake shaƙesa shima. “Shaƙar da Husam ya maka ba komai bace akan wacce ke tunkaro rayuwarka”. Ya ɗan ƙara waw-wai-gawa alamar gudun kar wani ya jisu. Cikin sake ƙasa da murya ya cigaba da faɗin, “Idan ka bari ka sake awa biyu anan nadamace ta har abada zata zama abokiyar rayuwarka in har ma matsiyacin yaron nan ya Barka da ran naka kenan”. Yana ƙare faɗa ya ficewarsa da ƴar sassarfa dan dama yay amfani da lokacin shiga sallar magrib da akayi ne......

         ★.... ★....

     Bayan idar da sallar isha'i koda ya nufi sashensa maimakon ƙarasawa ciki sashen Malikat Haseenat ya nufa ta ɓoyayyar hanya. Tayi sallamar wutiri kawai sai ganinsa tayi. Ba yau ya saba mata irin wannan zuwan ba na sirri, sai dai yafi yinsa a bayan sallar asuba. A nutse take dubansa bayan shafa addu'ar data taƙaita cike da kulawa. Shima sai ya taso a hankali da ga zaman ƙasaitar da yay a bakin gadonta ya dawo inda take kan lallausan carpet ɗin dake fes babu datti sai ma tashin ƙamshi da yake da ɗaukar ido na sabunta. Ga taushi matuƙa da ko'a ido zaka iya fahimtar hakan. “Barka da dare Jadda-ti”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi ya na kaiwa kwance bisa carpet ɗin ya ɗaura kansa kan cinyarta ya wani lumshe idanunsa da a kallo ɗaya ta fahimci damuwar dake tattare da shi a cikinsu tama ƙaru fiye da ɗazun. Murmushi ta saki mai sanyi a ranta tana faɗin, (Yau kuma ƴan shagwaɓan ne a kusa haka), a zahiri kam hanunnta kawai ta ɗaura kan ƙyaƙyƙyawar baƙar sumar sa siɗik ta fara ɗan tausa masa kan kaɗan-kaɗan. Idanun ya sake lumshewa da ƙyau har yanajin barci-barci na ɗibarsa. Tsahon mintuna kusan uku sannan ta magantu cike da kulawa.
         “Waya taɓamin kai Niger?”.
     Shiru bai motsa ba har wasu sakanni. Kafin ya buɗe idanunsa da suka ɗan fara shanyewar barci a hankali. Sai kuma ya ɗan ɓata fuska yana ƙoƙarin kaudawa gefe. Riƙo fuskar tai cikin tafukan hanunnta tana murmushi da faɗin, “Oh oh  beautiful Hafidi na faɗamin kaji”.
         Idanunsa ya ɗan lumshe da jujjuya mata kansa kaɗan ya motsa lips ɗin da ƙyar da maganar nan nasa kamar ta dole, “Kawai ina son jin ɗuminki ne”.
     “Uhyim, ita kuma Hafida-ti na aka barta ita kaɗai”.
  Shiru yay kamar bazai tanka ba. Sai kuma ya yamutse fuskar daɗa duniya har cikin zuciyarsa ne ya wani kauda kai gefe, “Tanada hayaniya, gata da surutu”.
           Mi Malikat Haseenat zatai banda dariya. Cike da nutsuwarta da ƙasaita ta shiga yin abinta. Ta ce, “Wayyo ni kai kuma gashi baka son hayaniya da surutu. Nikam ai ta burgeni, gara ta koya maka hayaniyar tata da surutun ko zamu samu ka dinga amsa mana magana biyar cikin goma. Naji daɗin hakan, dan itace dai-dai da kai”. A yanda take maganar zaka san lallai tana matuƙar jin daɗin. Shima dai acan ƙasan ransa murmushi kawai yake, dan ya sake tabbatar da kakar tasa mafi soyuwa a ransa na matuƙar ƙaunar ƴar hayaniyarsa da gasken gaske. Dama shi baya shakku a kanta, dan duk abinda Malikat Haseenat ta so to da gaske tana sonshi ne har cikin rai, idan kuma ta nuna ƙi to da gaske take ƙin nasa. Kamar tasan abinda yake tattaunawa da zuciyarsa ta cigaba da shafa kansa har yanzu da sauran murmushin dariyar da tai akan fuskarta. “Eshaan da gaske ina son yarinyar nan har cikin raina batare dana san dalili ba nima. Halayyarta kuwa na tuna min wasu abubuwa masu yawa. Yarinyar nada shiga rai, sannan tana da ɓoyayyun abubuwan ban mamaki tattare da ita. Karo na uku kenan ina aikawa nemomin iyayenta batare da kowa ya sani ba amma ana tabbatar min wai basa gidansu, a binciken ƙarshe ne na samu cikakken bayanin dalilin barinsu gidan, nasaka an bibiyar min kakaninta a ƙauyensu da aka tabbatar min su suna nan amma sai suma aka taki rashin sa'a. Na fara jin tsoron kar wani a cikin masarautar nan ne ya shirya cutar da su, dan tabbas abinda ya faru tsakaninka da yarinyar nan aike ne.. Bazaka tabbatar da hakan ba sai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login