Showing 15001 words to 18000 words out of 180087 words
Malikat Bushirat ɗin keyi. Ta dai aika Yumma (ƙanwarta da take tare da ita) taje ta duba Jasrah a randa tai ɓari...
★★..... ★.....
A hankali ya janye idanunsa da ga kallon inda taken cike da basarwa yana amsa sallamar Doctor Afif da ya shigo ɗakin akan lips. Dr Afif ya ƙaraso cikin ɗakin yana mai rissinawa ya gaishesa, da idanu ya amsa masa kawai alamar ƴan izzar na kusa. Shima Dr Afif ɗin bai damu ba, dan a ɗan zaman jiyyar nan har ya fara haddace magana da idon nan. Gaban gadon ya ƙarasa yana sake rissinawa a cikin girmamawa ya miƙa masa file ɗin hannunsa.
“Wannan shine file ɗin dukkanin bayanan nata da likitocin suka tattara. Sai dai suna kan sake bincike akan rashin farfaɗowar tata kan lokaci da ya kamata ace tayi tun kwanaki biyu da suka wuce”.
File ɗin ya amsa batare da yace komai ba, ya ɗan dudduba, sai kuma ya ɗago idanunsa ya sake zubasu kan Dr Afif ɗin. Sai da yaja wasu sakanni kafin ya iya furta abinda ke bakinsa da ƙyar. “Kai mi ka fahimta akan hakan?”.
Tsaiwa Dr Afif ya gyara yana mai sake rissinar da kansa. “ALLAH ya ƙara maka lafiya da tsohon rai mai albarka ni ina ganin ko za'a sake neman wani ƙwararren likitanne akan al'amurin nata da ya fi waɗan nan ɗin ƙwarewa. A yanda suka san aikinsu bai kamata ma ace sun gagara gano wani ƙwaƙwƙwaran abu guda ɗaya ba har zuwa yanzun, dan dole akwai abinda akai mata, dan bazai yiwu ace ta kasance a wannan halin babu ƙwaƙwƙwaran dalili ba”.
Ɗan murmushi Tajwar Eshaan ya saki a karo na farko, batare da ya cema doctor komai akan bayaninsa ba ya ziro fararen ƙafafunsa zuwa ƙasa. Slippers ɗin dake ajiye gaban gadon ya saka, murya a dake ya furta, “Zan ganta”. Da sauri Dr Afif yay gaba yana faɗin, “Bismillah ranka ya daɗe”.
Gaba ɗaya suka fito a ɗakin da yake tasa jiyyar, shi yana gaba doctor na biye da shi, duk da a jikin ɗakin da yaken ne koma ace ɗakinne kawai aka raba da glass sai ya zam ƙofar shigar sai kayi kamar ɗan taku biyar zuwa shida ne. Anan ɗin ma ƙofar ta gilashi ce, doctor ya buɗe masa yana ɗan ja baya. Sai da ya fara shiga. Tsaye yay a bakin gadon batare da ya zauna a kujerar da Doctor ya gyara masa ba. Sai da ya fara kai dubansa kan na'urorin dake aiki a jikin nata, gadai bugun zuciyarta normal na'urar ta nuna, sai dai nunfashinta baya tare da ita a zahirance. Ɗauke idanun yay da ga na'urorin ya maida a kanta. Lumsassun idanunsa ya tsura mata. Har yanzu tana kwance a yanda yake hangota daga ɗakin jiyyarsa tun ɗazun, tayi wani irin fayau da ita ga uban haske data ƙara. Ƙoƙarin saita yanayinsa da ke neman fallasa kan fuskarsa yayi, batare da yace komai ba cike da basarwa yay wani irin shegen murmushin takaici mai nunin ma'anoni daban-daban da ya saka Doctor Afif yin suman tsaye dan mamaki. Shi baima san Dr Afif ɗin nayi ba, sai ma idanunsan da ya ɗan lumshe yana haɗiye murmushin ya taka a sannu gaban gadon sosai tamkar ba shi ba. Yatsunsa guda biyu ya kai kan jijiyar kanta da tai ruɗu-ruɗu kusan na minti ɗaya, kafin ya janye ransa a dagule ya dubi Doctor Afif. “A cire mata duk wata na'urar jikinta”.
A ɗan firgice Dr Afif ya waro manyan idanunsa. Har lips ɗinsa na rawa wajen faɗin, “Ranka ya daɗe na'urorin mam sune ke taimakamana ganin ɗan sauran abinda ya rage yana aiki a tattare da ita. Cirewar zata iya zama haɗari a gareta. A gafarceni idan na shiga hurumin da ba nawa ba”. Kamar ma bai fahimci bayanin doctor ɗin ba ya sake furta, “Nace a cire”.
Sake daburcewa Dr Afif yay, sai dai bashi da damar cigaba da jayayya duk da ya san bazai yuwu Iffah ta cigaba da rayuwa ba in har babu waɗannan na'urorin. Wayarsa ya ciro a aljihu yay kiran wata nurse da ke aiki a clinic ɗin masarautar, cikin ƙanƙanin lokaci sai gata tazo. Razana tai da ganin mai gayya mai aiki a ɗakin, tuni ta zube gwuyawunta a ƙasa tana kwasar gaisuwa cikin tsumar jiki. Da hannu yay ma Doctor nuni tai aikinta kawai batare da ko ya dubi sashen da take na. Cikin sauri Dr Afif ya ce ta miƙe, shine ya shiga nuna mata yanda zatai komai. Hannunta na ɗan rawa dan kasancewarsa a ɗakun kwarjininsa ya cika ko'ina. Abune kuma da zatace bai taɓa faruwa ba a rayuwarta duk da itama ɗin dai jinin gidan ce. Ta gama janye komai da ga jikin Iffah'r bisa umarnin Dr Afif batare da ya nemo Doctor ɗin da ke kula da ita ba. Shiko gogan na tsaye kamar wani soja idanunsa a kan duk yanda suke komai har aka kammala. Fita nurse ɗin tayi, shima doctor ya koma gefe yana son ganin ikon ALLAH.
Kanta ya ɗan rissino a hankali ya kama duvet ɗin gadon ya sake gyara mata, batare da ya dubi Doctor Afif ba ya nufi ƙofar fita yana faɗin, “Ina buƙatar ganin Sayyid Fayzul-haq yanzu nan”.
“Umarninka shine abin jirana”. Doctor ya faɗa da sauri yana buɗe masa ƙofa.
★A mintinan da basu ƙarasa goma ba Sayyid Fayzul-haq ya iso. Cike da girmamawa ya miƙa gaisuwa. Kai kawai ya ɗaga masa batare da ya janye idanunsa da ga kan system ɗin gabansa da yake sarrafawa ba, dan tun shigowarsa ɗakin ita yay zaman sarrafawa. Ɗakin ya cigaba da ɗaukar shiru na tsawon wasu mintuna kamar bashi yasa ai kirasa ba. Sai da ya mula dan kansa kafin ya buɗe baki da ƙyar batare da ya bar abinda yake ɗin ba. “Ina buƙatar ruwan zam-zam, da waɗan nan abubuwan”. Yay maganar yana masa nuni da takardar da ke gefensa batare da ya ɗago ɗin ba dai. “An gama, umarninka shine abin jirana. ALLAH ya ƙara maka lafiya da rayuwa mai albarka”. Sayeed ya faɗa yana matsawa kansa a rissine ya ɗauka takardar. Sai kuma yay masa sallama duk da yasan ba amsa zai samu ba ya fice da hanzarinsa domin gaggauta cika umarnin shugabansa.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa dukkan abinda ya buƙata aka kawosu..
Ya hana duk likitocin sake taɓata a wannan yinin, sai ma Daneen Ammarah da ya saka aka nemo masa. Tasha mamakin magungunan da ya nuna mata da ganin an cire duk wata na'urar da ke tare da Iffah'r, sai dai yanda ya tsuke fuska babu alamar wasa ya sata shanye duk abinda ke a ranta ta ɗauka abinda ya batan bisa umarnisa. Dan duk da kasancewarsa ɗan ɗan uwanta a yanzu shi ɗin shugaba ne, akwai gaɓar da kuma yake tafiyar da wasu al'amuran a tsakaninsu matsayin shugaba ɗin. Hakan baya damunta, dan kowa ya san ALLAH ne ya bashi, ba dan kuma ya kasƙantar da su a kansa bane ya fifitashi da jarabawar mulkin.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (09)
.........Yanda ya umarcetan haka tayi akan Iffah, dan dole ta kasance a tare da ita har zuwa lokacin da ya bukaci ta kai tare da itan. Komai dake faruwa kuma akan idanunsa ne, sai bayan wucewar Daneen Ammarah da kusan mintuna talatin ya ɗauka Alkur'aninsa ya fito cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufi ɗakin. Zama yay a kujerar da ke gaban gadon shanyayyun idanunsa a kanta, ya mata kallo na wasu mintuna tamkar mai nazari kafin ya fesar da ɗan huci ya ɗauke kansa. Alkur'anin ya buɗe yana mai ƙara tabbatar da nutsuwarsa gaba ɗaya garesa sannan ya fara raira karatu cikin daddaɗar muryarsa da bama kowane harafi hakkinsa cikin ƙwararren larabci yanda ya kamata.
Ya ɗauki tsahon lokaci yana karatun, kafin ya tsagaita ya rufe ya ajiye. Kujerar da yake zaunen ya sake matsarwa gab-gab da gadon, tamkar wanda baya so ya kai hanunsa kan bargon ya ɗan yaye kaɗan. Kauda idanunsa yay da ga kallon inda suka sauka ya maida a fuskarta, ɗan bakin tsiwar nan duk ya bushe. Ya ɗan ja wasu sakanni a kallon nata, sai kuma ya kaudar yana sake tsuke fuska ya fara karanto addu'oi yana tofa mata. Haka ya kasance tare da ita har gabannin asubahi, dan sai da katafaren agogon masarautar ya buga cikar ƙarfe uku dai-dai sannan ya bar ɗakin ya koma nasa. Dole ya kai kwance dan shima ba jikin nasa ya gama komawa normal bane, a yanzu hakan ma jiri-jirin da ya fara ji yana rinjayarsa ne ya sakashi haƙura ya dawo nan ɗin.......
★★... WASHE GARI ★★....
Ƙoƙarin rufe system ɗin gabansa yake dai-dai da shigowarta da sallama doctor Afif na take mata baya kasancewar hadimanta basu da hurin biyota har nan. A kallo ɗaya zaka fahimci ɓacin ran da ke shimfiɗe kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Doctor Afif ya gyara mata kujerar da ke gaban gadon jiyyar Tajwar Eshaan ɗin, sai da ta zauna ya juya ya fice tare da zuge musu ƙofar gilashin duk da wajene da bana shiga kowa da kowa ba.
A hankali ya ɗan risinar da idanunsa alamar girmamawarsa gareta, sai kuma ya motsa lips ɗinsa a tausashe ya furta “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki ya Ammie-na”.
Duk da ɓacin ran da ke zagaye da zuciyarta hakan bai hanata ɗan sakin murmushi ba, ta kai hannunta kan nasa ta riƙo, itama cikin sauƙaƙa harshe da nuna kulawa ta amsa. “Tare da kai Bin Haysam Abdul-majeed. Ya ƙarfin jikinka?”.
Suna mafi soyuwa da yakan so ji da ga bakin mahaifiyarsa, sai dai kuma a duk sanda ya jisa da ƙarfin izzar harshenta ya kan saurin gane ɓacin ranta a bayyane. Ganin damuwarta kam shine abu mafi ƙona zuciyarsa dan shi karan kansa bai san irin tarin ƙaunar da yake ma mahaifiyar tasa ba. Kaɗan ya gyara kishingiɗar da yay har lokacin idanunsa na kanta, ya juya yatsunsa da ke riƙe da nata ya maida nasa a ciki, a sannu yake tausa mata gaɓɓansu da kulawa da lallashi batare da ya sake cewa komai ba. Tsahon mintuna suna a haka har ta fara sauke ajiyar zuciya alamar saukar fushin nata. Ganin ta koma kamar yanda yafi buƙatar ganinta ya ɗan sake mata murmushi.
“Nafi buƙatar ganin murmushin akan ƙyaƙyƙyawar fuskar Ammie-na a kowace daƙiƙa ta numfashi na. Akasinsa kan ƙona zuciyata fiye da yanda wuta ke narkar da kitse.”
Kalamansa koda a taƙaice suke zinarai ne a zuciyarta, shi ɗin yafi hasken diamond walwali da ƙyalli a cikin idanunta a duk sanda take dubansa, ta so abubuwa da yawa kafinsa ciki harda mahaifinsa sai dai shi tamkar shafine dake shafe dukanin fejin sauran fejikan baya a littafin rayuwarta. Kafin ka buɗe a bangonta shine, a shafin farko da shi take shimfiɗa, tsakkiya da ƙarshe shine mafi girma a ababen yabonta da ƙaunarta. Ta sake sakin murmushi zuciyarta na sake risina da ga fushin da ta baro sashenta a ciki.
Malikat Bushirat wata irin mace ce da gane halinta sai wanda ya santa, tana da abubuwan ban mamaki ta na da kuma na ban tsoro harma dana ban sha'awa da suka kasance mafi rinjaye a yimata ado. Hamshaƙiyace ta gasken gaske dan ko'a cikin manyan matan dole a kirata *_ZAKANYA UWAR ZAKIN ƘASAR RUMAN_*. A yanzun ma halin dattakon nata ta nuna, ta hanyar shanye dukan tarin abubuwan bakin nata ta cigaba da bama ɗanta magajin mijinta mai amsa suna shugaban sarakunan ƙasarta kulawa har zuwa lokacin data gamsu zata iya magana da shi babu fushi a harshenta. Ta tsatstsaresa da idanunta masu kaifi irin na uwa, yayinda shi nashi ke a rissine gareta risina irin ta ɗa a gaban mahaifiya.
“Na kasa gane komai da ga Mammah dangane da al'amarin yarinyar, a sanina ita ke fara hukunta duk wanda ya zaɓi cutar da kai koda da mummunar magana ne, kuma koda ni da na haifeka ce. Amma a wannan lokaci sai ta zaɓi bama mai son kawar da numfashinka kariya batare da fahimtar da ni kaina hujjarta akan hakan ba. Shin taya ake tunanin zan iya haɗa numfashi a ƙarƙashin runfa ɗaya da wadda ta shirya kawarmin da abinda bani da madadinsa ko samin madadinsan ba har abada? Taya ake tunanin zan iya kawaicin barinta da cigaba da kallonta a matsayin Zawgatu al-ibn duk da yunƙurinta na son ganinta ta tarwatsani da tai? Idan har igiyar aurenka da ke kanta ne katangar da ake iya min nuni da ita bango gareta ina son ka rusheta, ka yanketa, yankewa ta har abada ibn Haysam Abdul-majeed. Dan hakan shine kawai zai iya bani nutsuwa na manta da komai”.
Da ɗan ƙarfi ya matse idanunsa yana mai sakin numfashi a harɗe, sai dai mai kallo da ido bai isa fassara kamilar fuskarsa ma'abociyar annuri da kwarjini ba hatta ita dake amsa sunan mahaifiya a garesa.....
“Yanke hukunci cikin fushi da rashin haƙuri akan bincike ba itace ɗabi'ar shugaba nagartacce ba”. Daneen Ammarah ce dake tsaye mai maganar tana ƙoƙarin shigowa ɗakin, da alama ta ji dukkan kalaman Malikat Bushirat ɗin. Bai motsa ba, hakama bai buɗe idanun nasa ba harta ƙarasa shigowa garesu, sai dai ya sauke wata irin ɓoyayyar bahaguwar ajiyar zuciya acan cikin maƙoshinsa. Jin shiru ya ratsa ɗakin ya sashi buɗe idanun sannu-sannu. Dukansu cikin ɓacin rai suke kallon juna kowa najin ya isa yana kuma da ƙarfin iko akan yaƙin. Abune da babu wanda zai ce ya taɓa gani a tsakaninsu sai a wannan lokaci, ciki kuwa harda shi kansa. Daneen Ammarah ta sake katse yanayin nasu ta hanyar ɗora hannunta a kafaɗar malikat Bushirat da alamu suka nuna ta gama kaiwa maƙura a fusata..
“Úht!”.
(sunan data kan kirata da shi wani lokacin)
“Ban sanki da garaje ba, ban sanki da kasa fahimta ba, ban sanki da munana zato ba. Ban sanki da dagiya ba. Ina roƙonki ki danne, ki jure, ki zama mai ƙarfafa gwiwar mai ƙarfin da ba ƙarfin akafi son ya gwada ba kai tsaye, saboda amsa sunansa na shugaba. Bazan musa miki sunan Fareedah matsayin mai laifi ba, amma zan so ki kasance a yanda na sanki wajen tabbatar da gaskiya akan kowane ne kafin zartar da hukunci. Muma ba burinmu hana a hukunta ta ba, ko fifitata sama da gudan jininmu kuma shugabanmu ba, so muke kawai abi tsarin da ya dace da dokar shari'a da muke fata bayan ita za'a iya tono waɗan da ma suke aikata ɓarnar baya mai barinma gudan jininmu baƙin fenti da tabo a rayuwarsa da rayuwar mulkinsa. Ki fahimci Mammah ba fifita Fareedah take sama da abinda ta cancanci fuskanta bane, kariya take bata matsayinta na tamkar makamin da zai iya zama zaren da zai jamu ga duk ɓoyayyun masu laifin da muke fatan kamawa a cikin hannayenmu. Shin baki ji a ranki wanda suke aikata ta'asar baya nada nasaba da na yanzu ba? Baki ji a ranki yanke mata hukunci a kallonta ita kaɗai mai laifin tamkar basu ƙwarin gwiwar cigaba da aikatawar bane koda kuwa a yanzu basu da hannu kan abinda yarinyar ta aikata? Shin baki tunawa shi shugaba ne ba mai azaba ba?. Da yawan mutane gani suke sakacinsa da ƙin bama abu muhimmanci koda mai muhimmancin ne halayyarsa, sai dai yanda yake yi shine cikar zama cikakken duk wani shugaba. Shugaba da shanyewa aka sansa koda ɗacin na ƙona makoshinsa, da haɗiyewa aka sansa koda raɗaɗin na azabtar da hanjinsa, da ɓoyewa aka sansa koda girman al'amarin yafi girman zuciyarsa, da nazarta aka sansa koda ƙarfin yafi ƙarfin ɗaukar ƙwaƙwalwarsa. Ba ko yaushe yake ihu ba, ba ko yaushe ake gane ainahinsa ba, ba ko yaushe ake iya karantar zuciyarsa ba koda a ƙwayoyin idanunsa ne.....” ta ɗan ja numfashi ta fesar a hankali da cigaba da faɗin, “Idan har mu a karan kammu zamu kasa fahimtar kammu taya wanɗanda ke zagaye da mu zasu fahimcemu?. Idan har uwa zata iya shanye wa da daurewa akan halayyar ƴaƴanta da duk girman adadinsu bazasu haura ashirin ba mai zaisa shugaba mai mulkin ƙasa baki ɗaya kamar ruman za'a so ganin zahirinsa a dole dan kawai farin cikin wani ɓangare ko munanama wani ɓangare? Tayi laifi an yanke mata hukunci,