Showing 153001 words to 156000 words out of 180087 words
Chapter 52 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
taki ta cika iyawa, da kin iya a gabar da Iffah bata san komai ba sai UBANGIJIN da ya halliceta. Indai har wannan jinjirar yar kwanaki uku da haihuwa zata bacema ganinki da jinki, basirarki ta toshe a gabar da kike gab da isa ga nasararki ki sake dawo da ita a inda karfin ikonta ke a saman naki to ki sake tabbatar da k ba komai bace face batacciya mai jahilin tunani. Ni wlhy da ga lokacin dana san kana gaba daya sai kika kara komawa kasa wanwar a karkashin kasan tsinin takalmana. Ashema ke karamar kwaruwa ce tunda har sai kin jinginu jikin raunin wasu a fagen cimma burinki. Ashe ke ba komai bace face makaskanciya da dan yanzu UBANGIJI yace mutu dole ki amsa kira a shafe babinki kamar yanda aka shafe na uwar data haifeki harta nuna miki wanna hanyar shiga wutar. To wai ni banda ke din jahilar dabba ce a cikin kaskantattun dabbobi a wannan shekarun naki kike tunanin mulkar kasa irin ruman wai harma da duniya. Oh oh lallai kin cika babbar aladiya wih...
"K! Karamar halittar da muka samar da samarwarmu!!…
"K! Babbar dakikiyar da ALLAH ya halitta domin zama makamashin wutar jahannama in har bata tuba ba!!!!'". Iffah ta katseta a tsananin tsawacen da har sai da ta zabura acikin kujerar tsafin nata. Cikin rufewar ido da nunata da dan yatsa ta cigaba da fadin "La'ananniya gatalalliya butulu. K! Har wacece da kika isa samar da koda halittar kwarkwata tsinanniya mai kwana da tashi da tsinuwar UBANGIJI tattare da ita.Why wihy ina miki gargadi na karshe, da ga yau idan
kafarki ko wanna kujerar tsafin naki ta sake rabar inda nake sai na sabauta miki rayuwa. Sai na miki kisan gilla irin wanda ya kamata ama mushirikai batattu irinki a doron kasa". Ta wani irin rarumi wani dunkulallen abun fulawa na tangaran irin mai tsananin kaurin nan bakinta da bismillah ta wulwula sai gashi ya tarwatse a saman fuskar Uwa. Yanda kasan ta jefa wuka mai kaifin masifa ko mayen karfe sai ga hancin uwa a kasa ya gundulo gaba daya namansa. Dama gashi katon gaske mara fasali. Wata irin gigitacciyar kara uwa ta fasa jikinta ya hau kakkarwa ta dafe fuskar da tai faca-faca da jini da duka hannayenta biyu. Wani Iffah ta sake rarumowa, tana ambatar bismillah kafin ta wulwula uwa ta bace kamar walkiya, sai hancinta da digo-digon jininta da ya faffalatsa kasan harma da bango. Bata fasa wulwulawa ta jefa ba sai ko a keyar uwa da ke kokarin ficewa ta jikin bango ta salon tsafinta.
"Karamar yanyan ki tsaya mana, ki tsaya kiga yanda ake jifan shedan a zahirin rayuwa",. Ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ke kumbura da cika da batsewa ba da. Sai da tayi mai isarta harda fadawa gado. Sai kuma ta dan dafe kanta dake mata ciwo har yanzu. Dai-dai nan akai knocking kofar, damar shigowa ta bada dan tasan hadimarta ce. Ita dince kuwa dauke da madaran da ta saka a dafa mata. Cikin girmamawa ta ajiye a inda ta nuna mata. Kafin ta bata umarnin gyara wajen da jinin uwa ya faffalatsa, sai dai abun mamaki yanzu babu bantalen hancin uwar da alama dai ifiritan aljanunta sunzo sun dauke..
**....
Kamar wadda aka wurwuro kwallo da ga nesa haka ta fado da ga ita har kujerar tsafin nata a tsakkiyar wasu irin bakaken bukkokin bamboo da ke a jajejin. Firgitaccen ihunta da gumzar azabar da take yasa dajin amsawa, kamar busa kaho wasu irin mutane marasa kyawun gani da mummunar suffa irrin tata suka fara tururuwar fitowa. Duk dinsu babu mai kaya a cikinsu, tsirara suke yara da manya maza da mata, sai dan ganyen da suke rufe iya al'aurarsu kawai. Matan ko da ga samansu ma duk a bude yake tun daga yammata har tsoffi. Cikin kankanin lokaci duk suka zagayeta, yayinda wasu tsoffi da bazasu kaita shekaru ba suka rufu a kanta su kusan biyar maza biyu mata uku. Dagata sukai gaba dayanta ita da kujerar, daya da ga ciki kuma yay saurin yafa mata jan kyalle a saman fuskar datai kaca-kaca da jini. Daya da ga cikin dakunan Bamboo din suka shiga da ita, shikam da yar sabuntarsa kuma babba ne, sai dai cike yake da da was irin tarkacen bakaken gumaka da akaima ado da ja. Kujerar suka ajiye tare da fara zagayata suna was irin surutai da dukawa da tashi kamar wanda zasuyi ruku'u. Tuni nacan waje ma sun tattaru a kofar dakin yara da manya a layi, idan wadan can suka fadi surkullen sai su kuma su amsa musu da ga waje suma suna dukawa da mikewa. Gaba daya jajejin babu wani sauti da kakeji sai wanna surkullen nasu. Haka suka dingayi tsahon lokaci kafin a ciki su fara dibo was ruwa dake a manya-manyan randunan kasa na cikin akin suna zubama Uwa da cigaba da zagayeta cikin surkullen. A haka suka wanke mata jinin fuskarta tsaf, hancin dai ya fita babu kyawun gani sai fuskar ta kara munancewa fiye da da can. Amma jinin ya tsaya. Magunguna suka sassaka mata a ciwukan dan duk ta yayyanke dan ba hancin kawai ba. Bayan sun nutsa itama ta daina mummunan nishin da takeyi sai dai har lokacin a wajige take. Cikin mummunar muryar nan tata ta shiga kwala kiran wasu irin sunaye, jif!! jif!! jif!!! Kakejin abubuwa na fadowa cikin dakin, babu alamar toro a tattare da su, sai dai duk suna gabanta a tsaye kawunansu a kasa alamar girmamawa a gareta, Da wani irin zafin rai ta shiga nuni da bakaken hallitun dake ta fadowa. Ta nuna na farko cikin karaji da fadin, "Keje jajjal, da ga yau na baka umarnin, karka sake barin ta-kurya barci lafiya, a zagaye jikinta da kuraje masu warin da babu wanda zai iya rabarta koda danta ne, a dinga firgitata a ido biyu da cikin barcinta".
"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".
Ya fada yana mai zabura a guje kamar iska ya bace bat. Na kusa da shi ta nuna, shima cikin bada umarnin, "Zurnini kaje ga dan da muka samar mata(Shahan-shan 😱), da ga yau karya sake tunani irin na mutane, a maidashi majanuni, yayta dariya da soshe-soshe. Ya tsani shegiyar matarnan tasa fiye da komai a duniya, nanda kwanaki kadan jininsa halattacene garemu".
"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".
Shima ya fada yana bacewa. Ta sake nuna na kusa da shi shima "Rudde! Kaje ga tsohuwar can (Malikat Haseenat 52 ), ka taya Banou aikinta, da ga nan zuwa kwana uku jininta halattacce ne agaremu".
"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".
"Zambo kaje ga karsugumar shegiyar yarinyar can,ka zukemin gudan jinin da ke jikinta, ka ringa
firgitamin ita da wajiga rayuwarta, har saita san wacece Uwa kafin masana nayi gareta".
"Fadi naki, Cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".
"Gamberu! Ina bukatar jinin shegun iyayen da suka haifi yarinyar nan da umarnin mu (Wa'iyazubillah)".
"Fad naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".
Wani irin mahaukaciyar dariya ta shiga babbagawa da fadin, "Sai na ga bayansu, sai na haukata rayuwarsu, saina gigitasu. Yanda suka hanamu zama cikin alkaryar kasarmu suma basu isa su rayuwuba. Sai na mulki ruman, sai na mulki duniya, zan zama mafi girma a karfin iko. Matsiyacin tsoho (Kaka) gani nan gareka, nice da kaina zan tsireka a tsakkiyar kasar ruman. Hahahahaha!
Gaba daya na wajen suma suka dauki dariya. Dandanan dajin ya dauki amsa kuwwa. Tako ina dariyarsu amsawa take a cikin dajin..
*****
"Akia, an taba ciwo babu cin abinci, ki daure ko kadan kisha madarar nan sai kisha magani". Jasrah da dawowarta kenan da ga gidansu tun bayan tashi a kotu data tafi sai yanzu take dawowa, ta sanar ma babban yayansu komai yay mata alkawarin zuwa kuma duk da dama Shahan-shan ya tura masa sako, dan yana daya daga cikin mashawartansa ma akan yankema su Miran Jasim hukunci, kasancewarsa babban malami masani. Kai tsaye dakin Malikat Bushirat ta nufi, shine ta iske ta farka. Ganin jikin nata duk babu karfi tai zaman fara bata madara mai dumi akan tasha kafin ta watsa ruwa sai tai sallolin azhar da la'asar da suka wuceta. Amma Malikat Bushirat din taki amsa sam, gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Lallashinta Jasrah ta cigaba da yi har ta samu ta dan sha madarar kadan. Magungunan ma da kyar tasha. Mikewa tai zuwa bayi ta hada mata ruwan wanka sannan tazo ta kamata ta kaita. Fitowa tai ta barta da rokon tayi wanka koda ruwanne kawai ta zubama jikinta kozai danyi karfi.
Kamar jira ake Jasrah ta fita aka fara kyalkyala dariya. A firgice ta fara waige-waige sai dai bataga komai ba. Kuka aka fashe dashi kuma. Nama duk ta kidime tuni ta mike zumbur kamar ba itace aka kawo bayin da kyar ba. Sake kwashewa akai da dariya. Sosai jikinta ke wani irin rawar mazari kamar zata amayo zuciyarta ta baki. Tako ina waigawa take amma babu komai sai ita kadai a bayin. Da mugun sassarfa ta nufi kofa da nufin ficewa. Amma ina kofar ta rufe gam-gam babu alamar zata bude, Tanata kiciniyar budewa akai mata wani irin harrrrr!!! Daga jikin kofar sal ga mummunar suffa ta bayyana, baya taja a razane ta kwalla wata irin kara mai tsananin firgitarwa data saka Jasrah dake gyara mata gadon kafin ta fito zabura itama tayo bathroom din a razane….✍️
DAUDAR GORA....!!
Book 2
Chapter: 82
..A guje Jasrah ta fado toilet din da tunanin ko faduwa tayine tunda taga jikinta babu kwari. Wanwar ta sameta a tsakkiyar bayi sume harta farke hannu da wani dan karfe da akaima bayin ado da shi. Ai batama san ta fasa razananninayar kara ba tai kanta itama a kidime. Jijjigata ta shigayi amma babu alamar rai tare da ita. Sai kawai ta sake fashewa da kuka, dan a rayuwa tana matukar kaunar yar uwar tata, itace ta zame mata uwa a lokacin da suka rasa mahaifiya. Ta mata gata irin na Va da uwa bata taba banbantata da dan data haifa ba. Zama ta iya cewa ta fishi samun gata dan shi an dauke sa a gabanta.Itako tunda tasan kanta a gabanta take,duk abinda tace tana so shi take yimata.Idan tashin hankali yay tashin hankali baka tuna-mai ma ya dace kayi, kuka kawai take faman rusawa tama manta a bayi suke.
Diwa da ke tsaye a bakin kofar dauke da kayan lunch da ta kawo ma Malikat Bushirat din ce ALLAH ya jiyar kukan Jasrahn. Dama kuma itace tace ta hado abinci mara nauyi ta biyota da shi. Bata da hurumin shiga dakin sai da izini, ga kuma kukan tashin hankalin da takeji Jasrah nayi. Tray din ta ajiye cikin dan rawar jiki ta fice zuwa sashen Malikat Haseenat. Suna zaune a falo Daneen Ammarah na faman lallaba Ummu ta sake kwana itako ta ce yau sai gida zataje suyi shirin tarbar amarya gobe insha ALLAHU sai ga Diwa ta shigo a firgice. Kallon mamaki gaba daya suka bita dashi, Daneen Waheeda Sarkin masifa ta daka mata tsawa dan abinda Diwar tayi babban tsaurin ido ne. Malikat Haseenat ce ta katseta da fadin, "'a Waheeda wannan ba dai lafiya ba bita a hankali. K! Miya faru ne?". Kuka Diwa ta fashe da shi tana nuna bayanta bayan ta zube a kasa. "Ku gafarceni ranki ya dade, babu lafiya ne gaskiya. Ga Aunty Jasrah can nata kuka a dakin Malikat, da alama akwai matsala ne why, tabbas akwai matsala, dan dama likita nata zaryar dubata tsakanin jiya da yau"
Babu wanda gabansa bai fadiba
a cikinsu, dan dama basu jima dayin maganar rashin ganinta a kotu ba. Daneen Waheeda ce make cewa kila bata da ra'ayin zuwan ne yau tunda sun san halinta. Gudun kar maganar tai tsaho ga Ummu da take bakuwa a tare da su yasa Daneen Ammarah kauda zancen ta dako wani.
Gaba dayansu suka kunduma sashen Malikat Bushirat, Ummu kawai aka bari. A gaban idon Banou da ke tsaye da wata bakuwar fuska a jikin fulawoyi suka wuce.Da wani mummunan kallo suka bisu, sai dai babu wanda yace komai. Su Malikat Haseenat da basu san sunayi ba ko mota suka shiga zuwa sashen Malikat Bushirat din. Sun sami Hadiman sashen Jigum-jigum, dan zuwa yanzu kusan duk sunji irin kukan da Jasrahn keyi. Babu wanda ya saurari gaisuwar hadiman sukai ciki da hanzari, dan suma dai suna shigowa da kukan Jasrahn suka fara cin karo. A bathroom din suka sameta har yanzu, da kyar Daneen Ammarah ta dagata, rungumeta tai cikin jikinta dan ta sami nutsuwa, Malikat Haseenat kuwa inda Malikat Bushirat ke kwance wanwar ta nufa, tattabata ta shigayi. Daneen Waheeda dai na tsaye babu alamar damuwa tattare da ita. Sai ma bin toilet din take da kallo baki a labe. Da kyar Daneen Ammarah ta lallashi Jasrah har ta dan musu bayani a takaice. Dole aka kara kiran Doctor sannan aka saka hadimai shigowa suka kakkamata aka fiddota aka kwantar saman gado.
Zuwan doctor ya tabbatar musu ba mutuwa tai ba, ta dai suma ne. Ajiyar zuciya suka dinga saukewa, shi kuma ya shiga kokarin ganin ta farfado, yayinda Malikat Haseenat ke faman tofa mata addu'oi. Wani irin numfashi ta kawo tare da zabura mai karfi, wadda har doctor dole ya kai hannu a kanta domin maidata amma ya gagara shi kadai. Dole Jasrah da Daneen Ammarah suka matso domin taimaka masa. Amma fa sun kasa dan wani karfi na masifa ta musu, ga fisge-fisge tanayi na tashin hankali.
(Tofa al'amarin fa babbane) cewar Daneen Waheeda a cikin zuciya tana dan tabe baki. Suko da basu san tanayi ba sunata kici-kicin son gain ta lafa, Malikat Haseenat kuma na tofa mata addu'a. Da kyar suka iya tankwarata, har sun hada zufa sharban kamar yanda itama tayi.Numfashi suka shiga saukewa na jigata. Doctor kuma ya shiga aikinsa. ya sake maidata barci sai dai fa barcin yaki yiwuwa. Dan da ya dan figeta sai ta zabura sai sun sake dannata ta
koma kwance. Al'amari fa tun anayi da marmari harya fara gundurar kowa aka karo doctors da was alluran masu karfi sosai da sukafi na farko da akai mata..
Cikin kankanin lokaci zancen rashin lafiyar ya zagaye masarautar. Masu tausaya mata nayi masu farin ciki nayi. Masu kuma fassara al'amarin da wani abu daban nayi. Dan danan labarin ciwon nata ya zama latest topic à cikin masarautar. Dama ga nã hukuncin su Miran Jasim da bai gama disashewa ba.
***
Duk wanna al'amarin Iffah nacan kwance tana shan barcinta bata san bikin da ake ba. Dan sai la'asar ta tashi. Wanka tai tayi salla. Bayan ta kammala kimtsawa ta fito neman abinci dan yunwa takeji. Hadimanta da ke dan kus-kus din su suma akan al'amurin Malikat Bushirat din sukai saurin mikewa. Kallo daya ta musu ta dauke kanta, dan har yanzu zuciyarta babu dadi. Zama tai tare da bada umarnin a kawo mata abinci anan. Cikin ko kankanin lokaci amintacciyarta ta jere komai. Ta bude zata zuba mata ta dakatar da ita idanunta kur akan abincin. "Waya dafa wannan abincin?"Ta fada tana kallonsu. Cikin rawar jiki amintacciyar tata ta sanar mata itace da mai girki. Ta nuna mai abincin. Shiru Iffah tana duban wadda aka nuna matan sai faman sinkuy da kai take. Ai bama tasan ta daka mata tsawa ba tace ta dago. Ba ita da taima tsawar ba hatta sauran hadiman sun matukar razana. Dan abu ne da bata taba musu ba. Wani irin kallo Iffah take ma matar rai bace. Jikinta har tsuma yake ga idanunta sunyi jazur na tashin hankali. Duk wanda ya dubeta sai ya razana, idan ma irin su Bily ne fitsari zamu saki a zani😝Dan gaba daya ta juye tabbacin ba Iffah bace.
Wani irin shakota Iffahir tayi ta dauke ta da bahagon marin da ya idasa tsurar da sauran hadiman jikunansu suka fara rawar mazari. Marin matar nan Iffah take tamkar ALLAH ya aikota. Gashi ta shaketa da iya karfi. "Ubanwa ya aikoki nan?". Ta fada da wata irin gigitacciyar murya mai matukar razanarwa da amsa kuwwa. Cikin kakarin azaba matar da gaba daya ta gama jiyo kamshin mutuwa da kyar ta ce, "Uwa."
"Uwa. uwa. Iffah ta fada kamar mai bitar sunan, sai kuma ta kyalkyale da dariya ta kuma hade fuska. Cikin dage gira da zuba jajayen idanunta a tsakiyar na matar da ke a shake har yanzu a hanunta ta ce, "Ohhhyyyyo ita bata gane karatun kurma kenan. Bakuma ta gane gargadin makawo sai ya doka sandarsa. Shin wai dolene sai ta fusatani ne?!!!!!. Nace sai ta ga ainahina sannan zata tabbatar nafi Karfinta?!!". Ta sake fada cikin karaji tana gwara kan matar da centre table. Wata iriyar wahalalliyar kara ta sake illahirin jikinta na rawa dan fa ta bugu matuka duk da katako ne. Tuni hadiman sun fara sakin fitsari a wandunansu. Yayinda Iffah da bata san sunayi ba tana cigaba da maka kan matar nan jikin centre table. Sai da tai mata ligi-ligi har numfashinta na fita da kyar ga jini yay mata faca-faca sannan ta dagata tsaye, cikin daka tsawa ta dubi amintacciyarta tace a kira mata Ghazi guda biyu. Cikin kankanin lokaci suka iso kuwa. Jefa musu matar tayi taki zube yaraf a gabansu. Rai bace ta ce, "Ku dauketa, a dauremin ita a tsakkiyar masarautar nan". Cikin rawar jiki suka amsa mata da "Umarninki shine abin jiranmu ranki ya dade". Kota kansu batabi ba ta nufi dining, wajen wanke hannu ta nufa ta wanke hanunta da jini ya dan bata, har yanzu a birkicenta take. Bedroom dinta ta koma, babu jimawa ta sake fitowa cikin sabuwar shiga. Har yanzu hadimanta na lafe jikin bango a tsorace. "Ku biyoni da wannan abincin". A zabure duk suka mike, Itako tuni ta ma fice abinta. Kamar yanda ta saba tafiya duk inda take so a kafa yanzun ma hakane. Sai dai yau ko sau daya bata kula gaisuwar kowanne hadimi ba. Koma kallo basu isheta ba har ta isa sashen Malikat Haseenat. Anan din ma babu hadimin data kula Sai dai tana binsu da kallo daya bayan daya. Ganin babu wadda take nema cikin wata irin razananninayar murya ta kwala
kiran sunan "Banouuuu!!!"
Ba Banou din da taima kiran mafarautan