Showing 135001 words to 138000 words out of 180087 words
Chapter 46 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
zuciya ta dan saki. Bata ankara ba kawai ta gansa duke gabanta ya dan daga rigarta ya sumbaci cikinta. Da ga haka ya wuce abinsa cikin dakewa kamar bai aikata komai ba. Da kyar ta iya bude ido ta bisa da kallo, dai-dai zai fice ya dan tsaya a jikin kofar tare da juyowa suka hada ido. Kauda nata tai da sauri, shi kuma ya dan sakin murmushi a iya lips da fadin, "Idan kika bar sashen nan kafin na dawo sai na hukuntaki". Da ga haka ya fice ya barta da murmushi a fuska..
Bai shigo gida ba sai da aka idar da har sallar isha'in da asham, dan bayan idar da sallar magrib ya sha ruwa da dabino a can. Da ga haka yay zaman karatun Alkur'ani. Kowa yasan hakan yake yi a duk shekara, dan baya shigewa sai bayan an kammala salla baki daya kamar yanda yake yi idan ba'a azumi sai ani har sallar isha'i. Bisa rakkiyar su Sayeed Fayzul-haq ya dawo sashensa. Hadiminsa kam tun da yaji a bakin masu girki Zawjata-almilk tazo itamace taima Shahan-shan girki da kanta baiyi gigin biyosa har nan ba sai ya lake a 3 floor din. Babu kowa a faion sai sanyin ac da kamshi mai dad ba irin wanda ya bari ba. Bedroom ya nufa domin rage kaya, zuciyarsa na raya masa tama gudu kenan bataji gargadinsa ba. Sai dai yana murda handle din kofa itama tana budewa, kusan cin karo sukal da juna ALLAH dai ya kiyaye taja baya da sauri, sai kuma ta kusan faduwa sai da ya rikota jikinsa. A jiyar zuciya ta sauke cike da shagwaba ta ce, "Thanks you"
Maimakon amsa. mata godiyar cak ya dagata bisa kasa suka koma dakin. Tana watsal-watsal da kafafu da rokon ya sauketa ita yunwa takejl bai ma saurareta ba sai da ya direta inda yake bukata ya rufe bakin tsiwar dan iya yaren da zuciyarsa da kwakwalwar ke bukata kenan kawai…….✍️
DAUDAR GORA
Book2
71
_..Taji a jikinta kasancewar da gaske yunwar take ji,dan itama ruwan kawai tasha da dabino sai dan madara mai zafi da take matukar so a yanzu tunda akasha ruwan. Ta hakura ne tai salla dan tasan in har taci abu da yawa to tabbas bazatai sallar ba barci zatai. Duk yanda take wani tuttura masa baki na shagwaba bai kulata ba, da taimakonsa sukai wanka a tare sannan suka fito daning room din. Sai da ta tabbatar ta gam harare-hararen kwanikan abincin tsaf duk da tasan bayan sun ajiye babu mahalukin da ya sake shigowa nan sai shi bata aminta ba kai tsaye. Komai a tare ta hada musu, hatta shayi a kofi daya ta zuba duk da kasancewar dan mitsitsin nanne na larabawa. A haka suka dinga cin abincin kowa na ciyar da dan uwansa har sukaje iya inda suke bukata. Falo suka dawo, yana kokarin kuna Laptop din tasa ta fama ta je ta haye cinyarsa tana tura baki.
"Wai nikam kodai computer din nan kishiyata ce?".
A yanda tai maganar ma sai abin yaso bashi dariya. Amma dai ya gimtse bai yi ba ya dai tsareta da idanunsa kawai. Lumshewa yay ya dan bude tare da tallafo fuskarta cikin tafin hannunsa. A kasalance ya furta, "Ko dai ke ce ke kishi da ita".
'"Ai dai banyi laifi ba".
Murmushi kawai yay dan bashi da abin cewa kuma.Sai kawai ya dauka remote ya kunna musu television ya kamo babban gidan tvn kasar. Basu fara labarai ba, sai wani shiri mai suna * ZAUREN MUSULUNCI_*. sannin muhimmancin shirin yasa bai canja ba ya bar musu nan, itako harda gyara kwanciya a jikinsa ta lafe kamar wata mage. Shima sai ya gyara mata yanda zataji dadì sosai hannunsa saman cikinta da duk duniya a yanzu babu abinda yafi so da bukatar gani kamar girmansa da haihuwarsa. Koda wani takaici ya tuno a ransa daya tuna Iffah'r sa nada cikin gudan jininsa sai yaji nutsuwa ta saukar masa..
*
-*
Washe garin aka tashi da fatan gain watan salla,Iffah na zaune tana karatun Alkur'ani bayan idar da sallar asuba Tajwar Eshaan ya dawo da ga massalaci. Komawa yay ya dan kwanta dan barcine a idonsa sosai. Ta idar itama tana shirin hawowa gadon yake sanar mata sakonta ya iso yanzu Sayeed Fayzul-haq ke sanar masa. Fasa kwanciyar tai cike da doki ta mike ta hau shiri, shi dai kallonta kawai yake dan ya santa da barcin tsiya amma da ga cewa sakonta ya iso ta fasa yi. Ganin sauri-saurin nata yay yawa a hankali ya furta, "Madam a hankali karki jamin asara abuna baiyi kwari ba fa".
Ita kunya ma maganar ta bata, dan haka ta juya masa baya tana rufe fuska. Shima sai ya dan murmusa kawai ya lumshe idanunsa. Kirtsawa ta karasa yi ta zo gaban gadon ta manna masa sumba a goshi. Hannu ya kai zai damkota ta zille. Murmushi yayi da kara gyara kwanciya yana fadin (Fitinanniyar yarinya) a zuciyarsa…..
Duk da safiya ce sosai tuni kayan da aka shigo da su cikin manyan motoci kusan goma masarautar ta dauki dumi. Kowa jira yake ya ga da umarnin wa aka kawo kayan, dan abune dai sabo da ba'a san da shi ba, ga kuma wasu kayan da suka dan fitgito sun nuna suturu ne ma. Tuni fitowar Iffah da ga sashen Tajwar Eshaan Sayeed Fayzul-haq da amintaccensa biye da ita kallo ya koma sama, sal kuma ga tawagar matasan masarautar da ta saka suka mata aiki a wancan karon ma sun fito, a gabanta duk sukal rankwafawar gaisuwar girmamawa. Ta amsa musu itama da kulawa fuskarta da murmushi har da yar tsokanarsu wai kwanan nan zata fara saida form din aurar da samarin masarautar ta ga sun fara yawa. Dariya suka shigayi da barkwancin nata. Harda Sayeed Fayzul-haq da ke jin kaunar yarinyar, gata dai karama amma da halin manya, manyan ma sai an tona. Haka ma amintaccen hadimin Shahan-shan na jin kima da girmanta, dan yanda take kula da shugabansa kawai da sakasa farin ciki ma abin a jinjina mata ne. Shi baya ma ganin karancin shekarun sam sal wata kimarta da girma irin wadda yake kalion Shahan-shan da ita.
Ta musu bayani akan kayan suma da za'a rabasu kamar yanda aka raba kayan abincin azumi ne. Akwai kuma kaji da shanu suma zuwa yammaci zasu isa. Sai dai su baza'a kawosu nan ba a kowace jaha aka samar da masu kiwonsu aka siya idan kowane wakili yaje inda zai raba kayan da aka bashi zai amsa. Sai kuma wanda za'a rabama hadiman masarautar suma da nasu daban, sukam harda kudi wanna kuma Sayeed Fayzul-haq ne zai bada su sakone da ga Shahan-shan da kansa
Abdul-Shakhur in Khairul-Bashar shugaban tawagar ya share kwallar da suka ciko masa ido. Cike da girmamawa a gareta ya ce, "Lallai ke alheri ce garemu gimbiyarmu. Ke haske ce mai haskaka fararen fitulun da ke zagaye da daular ruman. Kasancewarki damu sake buda mana sanin wanene adalin shugabanmu yake da kyawawan halayensa a koda yaushe. ALLAH ya kara miki daraja, ya albarkaci rayuwarki data shugabanmu, ya zagayeku da kariyarsa da ni'imominsa. Yay riko da hannayenku ya baku ikon sauke nauyin al'umma da adalci. ALLAH ya bamu ikon muku biyayya ya karemu zaginku koda a bayan idanunku. ALLAH ya karya makiyanku koda jininmu ne ya azurtaku da zuri'a masu irin kyawawan halayarku da dabi'unku. ALLAH ya jika magabata, wanda suka rage ALLAH ya rabaku da su lafiya...
Haka ya cigaba da jero addu'oi sauran a amsawa da Amin tare da hadiman da suka zagayesu cike da farin ciki. Iffah kam sai taji har hawaye na ciko mata idanu. Tabbas babu abinda ya kai kyautatawa dad da soyayyar mutane. Da ace dan adam ya gane da ya kasance mai kyautatama mutane sabanin munana masu. Kyautatawa na bada muhimman abubuwa uku a lokaci guda. *_DARAJA. SOYAYYAR MUTANE.
SANNAN LADA A WAJEN UBANGIJI_* Cikin kankanin lokaci masarautar ta harmutse, bakin kowanne hadimi ka kalla a washe da farin ciki musamman idan ya kama yan kudadensa da kayan sakawa kusan kala biyar uku a hannu. Ga iyayen kaji da shanu an zube musu na girkin salla. Ga albishir na basu damar yin shagalin bikin sallarsu kamar yanda kowa keyi. Harda damar yin gyaran jikinsu matsayinsu na mata Iffah tabama matan, dama albishir din kawo masu gyaran jiki €ikin masarautar saboda hadimai matan kawai. Kai jama'a harda masu kuka, kaunar Iffah kam da Shahan-shan din kansa ba' magana a zukatansu. Sai sukejin kamar an yanta rayuwarsu ne da wani haske na musamman a yau din.
Ba cikin masarautar ruman kawal ba. A cikin al'ummar. kasa ma duk wanda ALLAH ya tsaga da rabonsa a kayan' nan ya tsinta kansa a farin ciki mara musall. Badai ta wadata kowa da kowa ba. Amma ta ragema was radadin talaucin da suke ciki. Ta faranta
ran marayu marasa iyaye. Duk da alkairi ne na sirrince da akaki bama yan jarida damar sani sai gashi ya fita karar wata amsa kuwwa a katafen yada labarai, Ya koma latest topic na wanna ranar harma da washe gari. Dan cikin aminci, UBANGIJI a ranar akaga watan salla washe gari aka tashi da farin cikin zagayowar wanna rana. Inda karfe tara dal-dai Shahan-shan da Kansa ya jagoranci sallar idi a massalacin Masarautar da mutane kasar suka ziyarta ta ko'ina a jar, harma abin ya bada mamaki, dan duk da ana cikashi dama duk shekara sai gashi a wannan shekarar ya ninka da ninki mai ban mamaki,. Talakawa da yawa sunzo cikin Dahab City yin salla domin kawai suga Shahan-shan.(Haka rayuwa take, duk kasancewarka mai mugun hali ko wanda za'a gogama bakin fenti da kayi alkairin da yay shura tsakaninka da ALLAH badan duniya ta gani ta fada ba ko a yaba maka sai kaga ALLAH ya saka soyayyarka a zukatan wadan nan mutanen dake aibantaka da kyararka a baya. Yan uwa mu dage da alkairi domin ALLAH, idan ka cire Naira dari a cikin dubu da ya baka sai ya sakama sauran albarka ya kuma daga darajarka. Dan shi alkairi da gaske danko ne baya faduwa kasa banza inji hausawa. Dan ko yayan cikinka kaima shi sake kaunarka suke, hakama iyayenka)
Tajwar Eshaan yayi addu'oi masu ratsa zukatan bayan idar da salla. Hakama lokacin khuduba kalamansa masu ratsa zukata ne da hikima a cikinsu da mutare duk jikinsu yay sanyi da yanda suke kallonsa a baya. Bayan kuma kammala addu'oin yay wani dan gajeren nasiha da Fatan alheri ga kasarsa da ma al'ummar kasar da musulman duniya baki daya. Ya rufe da musu Barka da shan ruwa.
Wannan jawabi a Tajwar Eshaan Ibn Haysarn Abdul-majeed Ally Qutb shine ya dinga amsa kuwwa a kafafen yada labarai, masu fashin baki nayl talakawan kasa da basu samu halarta ba nayin nasu suma,
*Duk gayun da Iffah taci domin kayatar da zuciyar Maleek dinta bata samu ganinsa ba har sallar zuhur. Bataji haushi ba, sal dal ta kagu su hadun. Duk da itama da kanta tai masa shirin fita sallar. Yayi matukar kyau kamar wani dan saurayin dawusu (lols 😉😂)) harda fada masa ita why kamarma ya fasa kishin fitarsa a kalle mata shi takeyi haka. Amintaccensa da ke jinsu (okacin da take bashi shayi sai kasa ya karayi da kansa kawai yana murmushi.
Bayan ta idar da sallar azhar ta fito domin zuwa gaida Jaddah da Malikat Bushirat da ya kasance dole tayi. Sai lokacin ta fahimci yanda masarautar ke cike. Ashe dole ne duk wani Tajwar a sauran jihohi sai yazo a yau din yayma Shahan-shan barka da shan ruwa, Hakama manyan attajirat da masu fada ajin kasar da dattijai. Zasuci abincin salla da Shahan-shan su kuma tattauna matsalolin kasa da shawarwarin magancewa. Gaba daya sai Iffah taji ta Kara tausaya masa. Dan lallai mulki ba wasa ba, yanda ta sanshi bal son hayaniyar nan yana can cikin takura ne.
Sashen Mallkat Bushirat ta fara nufa yau tawagarta zagaye da ita. Kowa ya kalleta sai ya sake kallo dan kyawun da tai cikin walliyar sallar tata mai tsananin kayatarwa da daukar idanun mat kallo. Ga kyawu da cikin jikinta ya sake sakatayi kamar ka saceta ka gudu. Tako ina hadimar da jami'an tsaron masarautar gaisuwa kawai suke mikawa. Itako fuskarta kawace da murmushi mai sanyi da ke sake saka kaunarta a zukatan talakawan nata masu jin yanzu kam babu kamarta a cikin masarautar bayan Malikat Haseenat da itama ta kasance adalar shugaba…..✍️
DAUDAR GORA
Book2
72
.....Cike Iffah ta samu sashen Malikat Bushirat da danginta da sukazo mata Barka da salla. Hakan ya mata dadi, dan duk wani wanda ke da alaka da Tajwar Eshaan a rayuwa tana ganinsa da kima da mutunci. Cikin mutuntawa suka tarbeta, dan sakonta da na Tajwar Eshaan yaje garesu har gida a jiya. Duk da suma sun kasance mafi yawansu basu nema komai na rayuwa sun rasaba. Amma alheri dadine da shi, musamman da ya kasance wani abu bai taba zuwa garesu ba ace daga dan yar war tasu kuma Shugabansu. Abinda ya basu mamaki da tabbatar da an samu sauyi yar uwar tasu ma sai da suka zo yanzu duk suke mata godiya har tasan Tajwar Eshaan din wai ya musu aike suma. Murmushin yake kawai ta musu, dan tun jiya dama a tunzure take da abinda Iffah'r tayi. Koda Iffah'r ma ta gaisheta cikin yake ta amsa gain yan uwanta duk sun zuba mata ido.Amma zuciyarta tafasa take da yanda suke ta sanya albarka da yaba abinda Iffah'r tayi, tare da tabbatar da shugabansu kuma dansu yayi dace da mace ta gari mai buda masa hanyar alkairi. Sukam suna farin cikin shigowarta cikin ahalinsu. Wasunsu harda kiranta gagara badau wadda tafi karfin duk wani shedanci a azzaluman masarautar.
Iffah da mur mushi kawal ta dingayi kasa-kasa. Tayi zaman kamar awa guda sannan tai musu sallama akan zuwa anjima zata aiko azo da su su gashe da Shahan-shan. Wannan zance nata na karshe ta sakasu sake shiga jin dadi, dan a cikinsu ma akwai wanda rabonsu da Tajwar Eshaan din tun kan a bar kasar da shi, Kuma uwa daya uba daya suke da Malikat Bushirat din, Sun baje babin hira da sanya albarka ga Iffah Jasrah ha kara basu labarinta. Babbar yayar su Malikat, Bushirat din da suke kira Akia Badiha cikin nuna jin dad) ta furta, "Al ni babban abinda ma ya sakani farin ciki fiye da komai wannan cikin na jikinta, dan zamu samu tsatson alkairi a zuri'armu, ALLAH dai ya raba lafiya".
Kusan a tare duk suka dubeta. Malikat Bushirat da ke kishingide tana shakar iska da fesarwa harda zabura. Jasrah ce tai karfin halin fadin, "Akia wal waye mai cikin? Kin samu a rudan!" Baki ta Kara washewa, cikin barkwanci ta ce, "Aw to tunda baku ramfo ba ku bada goron albishir tukkanna. Kudi sabbi kal-kal Jasrah ta sauke cikin tafin hannun Akia Badiha, cike da zumudi ta ce, "Muna saurarenki".
"Uhm wadan nan din ma babu laifi, sai dai da kanku ma zaku karo idan kunji. Insha ALLAHU muna gab da samun Miran, ko Daneen a wannan masarautar. Dan da alama Zawjata-almilk tana tare da shigar ciki".
"Whattt!!!!!!".
Suka fada cikin hada baki da hun murna. ALLAH ma ya sosu hadimai yau an basu freedom din kansu sai dai-daiku dakan dan shigo dan an bukaci ganinsu. To su sunama a falon Malikat Bushirat din nacan ciki ne iya su dan yau ranar baje kolin hirar zuminci ce. Wani irin diff-diff kirjin Malikat Bushirat keyi, zuciyarta kamar zata faso ta fito. Ga kanta da yay wani irin azababben sarawa, sai ta fara ganin falon na juya mata da su da ke ciki. Tashi tai da sauri ta nufi daki ta kulle kanta. Tana gama sakama kotar key ta daura goshinta jikin kofar tai wani irin fashewa da kuka mai tahowa irin gaba dayan nan mutum yaji kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa..
Bama su fahimci halin da take cikiba su balle tashinta, sunata murnarsu, sai da mai bima Malikat Bushirat din ta juyo tana magana idonta ya sauka a wajen zamanta wayam. Bata kawo komai a ranta ba a tunaninta duk murnarce ta kebe yin abunta dan sun san yar war tasu da shegen kasaitar son mulki kamar itace Shahan-shan din ba matarsa ko uwa ba…..
*A bangaren Iffah kam tana sashan Malikat Haseenat, taso ta samu Iftihal dan yau tayo mata tanaji sai dai aka samu rashin sa'a wai ta fita ita da Husam babban dan Miran Jasim. Anan ma Iffah ta jima sai bayan sallar la'asar ta baro, sunata shan hirarsu ita da Mammah da Mammy. Daneen Waheeda dai bata saka baki sai lokaci-lokaci...
Tattauna zancen cikin Iffah ga zuri' ar Malikat Bushirat ya sa ya fito har ya fara yawo a cikin masarautar. Dan danan fa aka fara wani karamin bikin murna da sam Iffah da Tajwar Eshaan da sai da akai sallar la'asar ya samu kansa basu sani ba. Hasalima suna can manne da juna abinsu hankalinsu kwance da jin tamkar suma kadaine a cikin duniyar (Su bily duk an mutu ashe 😏🤔👹). A kankanin lokaci zancen ya cigaba da shiga lungu da sako. Da ga masu shiga farin ciki sai masu shiga rudani da tashin hankali dan abune da basuyi zato ba...
"Aiko lokaci yayi da zaki bijiro da zancen auren nan Waheeda".
Malikat Ashwag ta fada cikin tashin hankali bayan gama sauraren Daneen Waheeda. Daneen Waheeda da gaba daya ita tasan kunar da zuciyarta ke mata ga rikicin Iftihal taja numfashi mai matukar zafi. "Hakane Ashwaq, amma kin san kafiyar Mammah, ga shi Ammarah sam nunawa ma take tafi son yarinyar nan sama da Iftihal din, taya kike ganin hakan zai yiwu cikin sauki?".
"Yuwuwarsa daya ce, mu nema su Sayeed Tasaddug-Husain da zancen shi da su Sayeed Hifzur-rahaman, da Sayeed Fayzul-haq tunda sune dai iyaye a gidan nan, duk da yake shugaba suma ai sama suke da shi, kuma dama a duk aure-auren nasa ai sune dai Mammah ke sakawa gaba ko da su Jasim".
"Eh hakane, kema kin kawo