Showing 141001 words to 144000 words out of 180087 words

Chapter 48 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

shigowarta masarautar nan suke tare. Dan ta kasance ma tarkar matarsa ce a yanda yake tarayya da ita a duk sanda ya yaso…

*Tsinanne kaima ai naga kana tarayyar da ita, kuma garama ni kafin tai aure ne, kaiko a cikin gidan nan tana matsayin matar Haysam din kake tarraya da it...

"Karya kake gatalalle, ban taba kusantar Haifah ba sai da Haysam ya rasu, ita kuma ta kawo min kanta da kanta bani a gayyato ta ba. Idan karya na mata gata nan ta misalta mana.......

Wani irin mahaukacin buga guduma Tajwar Eshaan yayi, sai da kowa ya zabura a cikin kotun har Miran Arshaan din da ya karbe Miran Jasim a fusace. Tabbas da ace idanunsa ba cikin gilashi suke ba babu abinda zai hana juyewarsu firgita kowa da ke a wajen. Sai dai fuskarsa fa tayi masifar sake tsukewa,

Sayeed Hanifud-Din da ya fahimci maganar ce baya bukatar a cigaba da yi, ya ce, "Kowa ya fahimta. Sai dai akwai abubuwan da bamuji da ga gareka ba,wanda kuma kowa yake ji a jikinsa kune kuka aikata din. Na farko ima Zawjata-almilk allura lokacin da take a kurkuku, sannan jefata a cikin ruwan shima".

"Tabbas allura mune, sai dai Bama allurar komai bace face ta sihiri da Barbushi ya bamu domin kame mata jiki ta kasa tsinana komai, dan haka mukai amfani da rigar da ke jikin Eshaan a randa ta bashi madara dan ta dauka shine, Haifah ce kuma tare da ni muka je mukai mata allurar a ranar. Amma jefata cikin ruwa wlhy bamu bane ba...."

"Karya kake kune Jasim, dan duk wanda ya aikata wadan can ayyukan to shine ya aikata wannan, kana son ka boyene domin kuwa al'amarin yayi iri daya da saka Miran Nayyar ruwa da akai shekarun da suka shude….

"Gaskiya ya fada basu bane ba!!".

Kusan a tare duk wanda ke'a cikin kotun ya dubi wanda yay maganar, yayinda Iffah ta mike a zabure dan wanna muryar ko'a mafarki bazata taba layance mata ba. Kaka kenan, dattijo ko muce tsoho mai ran karfe. Ya kara wani fes abinsa saboda canjin rayuwa da ya samu duk da jikin tsufarsa na nan tare da shi. A hankalin Tajwar Eshaan ya lumshe idanunsa da ke a cikin glasses, duk da shima dai abinda kakan ya fada ya girgiza mamakinsa, ga zuciyarsa dama a takure take da zancen su Miran Jasim na tabbatar da basu ke kashe masa mata ba kamar yanda Iffah ta taba fada masa..... Sayeed Hanifud-Din ne ya katse shirun idanunsa a kan Kaka ya furta,"Taya akai ka sani bawan ALLAH? Idan kuma har basu bane wanene?".

Kaka da ke fitowa da ga wajen zamansa ya tsaya gaban kotu yana mai sake jinjina kansa. "Tabbas kamar yanda na fada basu bane. Abinda kuma ya fada sun aikata iya shi din suka aikata sai wanda ALLAH ya barma kansa sani da su da suka aikata abinsu. Amma tabbas kamar yanda basu da alaka da kashe duk Zawjata-almilk da suka rasu, haka basu da alaka da kashe Miran Nayyar, itama kuma Zawjata- almilk Fhareedah basu ne suka sakata a cikin ruwa ba".

"To wanene?".

Murmushi kawai kaka yayi sai dai baice komai ba. Yayinda kowa ya zuba masa ido a cikin kotun. Malikat Haseenat son tuno inda tasan fuskar take. Malikat Bushirat kam zuciyarta wani irin mugu mugun harbawa take da masifar karfi kamar zata fito ta bakinta saboda abinda kakan ke fada. Sai dai zuciyarta kwantar mata da hankali take akan ta nutsu ko shi hadimin da ya aikata aikin bai isa ganita ba balle wannan shashashan tsohon da ke jiran ranar mutuwa….. Shirun kaka yasa Sayeed Hanifud-Din sake maimaita masa tambayar. Yanzu ma kaka murmushin ya saki mai sanyi sannan ya dago ya duba kowa da ke cikin kotun, idanunsa ne suka tsaya akan Iffah dake kallonsa tana jin kamar ta taso ta rungumesa. Murmushin ya sake sakar mata ya dauke idanunsa
"Ina rokon afuwa ga wanna kotu mai adalci akan kartsalandan da mai mata. Ban kasance anan dan sanar da wanda ya aikata abinda ake son ji ba, domin kowanene a wanna gidan yake kuma yana a cikin wannan waje sannan da kansa zai fallasa kansa a gabar da ya dace kowa ya sansa..."

"Tofa babbar magana, kotu zata so sanin miya kawoka baba?". Sayeed Hanifud-Din ya fada saboda inkiyar da Sayeed Tasadduq-Husain ya masa.

Gyara tsaiwa kaka yay da kyau, sannan ya ce, "Kamar yanda na fada a farko basu bane, tabbas basu din bane. Su kawai ALLAH ya jarbcesu ne ta hanyar bibiyar wata tushiya da suka zama sanadin samar da tsirranta a shekarun baya batare da sun
sani ba. Ta tafi ta sanadin su, sannan ta dawo ta sanadin su, duk da asali basu bane mafarin komai, dan suma a karan kansu suna aiki ne akan aikin daba nasu ba".

"Baba ka sake sanyani a rudani, ko zaka bayyana mana komai a bude dai-dai da fahimtar mu?".

"Mizai hana in har kotu ta bani dama?".

"Kotu ta baka dama, domin kana akan abinda take bukatar sani ne dan zartar da hukunci ga masu laifi, da yin adalci ga masu gaskiya".

"To Alhamdullah ". Kaka ya fada yana murmushi. Sai kuma ya maida dubansa ga su Miran Jasim da suke a rudanin son tuna inda suka san fuskar, dauke kai yay kamar bai gansu ba ya sake maidawa ga Sayeed Hanifud-Din. "Mune ahalin Zawjata-almilk Fhareedah. Mune kuma suka bada kwangilar halakawa, sai dai ALLAH ya kubutar damu tare da Barrister Abdallah Aas da ya dinga fafitikar taimkonmu tun sanda suka fara bibiyar mu". Ya karen maganar da nuna inda ya taso can karshen kotun.

A kusan tare Miran Arshaan da Miran Jasim suka zabura na tsabar kaduwa da gain Barrister Abdallah Aas da su Baby. Dai-dai kuma da zaburar Daneen Ammarah da idanunta suka sauka kan Babiy. Ba shekara ashirin ba, koda shekara dubu ashirin ce bata jin zata manta da wanna fuskar duk da ganin kwanaki goma sha uku kawai ta taba masa. An musu auren zalunci a wancan lokacin bada san ransu ba bada amincewarsu ba. Amma sun hade kai sunyi kuka tare, sunyi murmushin kuma a tare, sun kuma shaku a tare, sun kumaji radadin rabuwa da juna a tare, yayinda sukai kewar rashin juna a tare, Hankalin duk mutanen da ke a cikin kotun ya rarrabu, wasu akan Daneen Ammarah da ke nuna Baby cikin rawar lips alamar tana son magana ta kasa. Wasu akan su Miran dasim da suka rikice. Was akan su Ummu da ke fitowa:

"Zayyan!! Tabbas kai ne! Kai ne Zayyan ko bayan shekara ashirin sau ashirin ne bazan taba mantawa da kai ba!!!".

Wadan nan zantuka na Daneen Ammarah ne suka zaburar da kowa da kowa ido ya koma kanta har Babiy da kansa ke a duke bai san anai ba, sai dai zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri tunda ya shigo cikin masarautar dama a yau. Shima dai a karo na farko idanun nasa suka sauka akan Daneen Ammarah din, tsaf numfashinsa ya dauke, yay taga- taga zai fadi sai da Barrister Abdallah as da Hanash suka tarosa. Yan kananun magana ne suka fara tashi a kotun, yayinda Tajwar Eshaan ya kafe Iffah da idanu ta cikin eyeglasses dinsa, sosai jikinta ke tsuma itama kamar wadda take a rudani. Sai yaji ta bashi tausayi, wai a hakama bata san tushen al'amarin ba kenan. Ji yake kamar ya rufe ido ya gansa da ga shi sai ita kawal ya rungumeta dan sarar mata nutsuwa shima ko zai samu da ga radadin da zuciyarsa ke masa. Badan karya raba kan mutane ba da zai dage shari' ar nan ne har sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Amma sai ya hadiye komai kamar yanda ya saba dan shi a karan kansa so yake yaji ta inda aka fadi a ragaya, tunda dai gashi gwajinsu ya tabbatar da Daneen Ammarah matsayin mahaifiyar Iffah'r itama. Sannan yanayin Babiy da Mammyn mana yanzu ya sake bude komai a bayyane….✍️


DAUDAR GORA...
Book2
Chapter: 75



Da kyar da kyar aka samu kotun ta lafa, yayinda kalaman Daneen Ammarah dake kuka sukai matukar daukar hankalin kowa. Fadi take, "Wlhy Mammah shine, shine wanda suka cutar da mu a tare. Bazan taba yafe musu ba, wlhy bazan yafe musu ba, sun haddasa bakin ciki mai ciwo a zuciyata. Sun nisanta ni da shi bayan sun alakanta mu".

Sosai hankalin Malikat Haseenat dama duk wanda ke'a kotun ya tashi, dan yanda take kuka haka Babiy make kuka sai dai shi kansa duke yake a kasa. Ummu ma dai tasan komai da ya faru, dan a lokacin bai boye mata ba. Hakama lyyani. Iffah nason tashi taje garesu amma babu dama, dan ita Zawjata-almilk komai nata nada ka'ida da son nutsuwa. Dole ta hakura ta zuba musu ido kawai musamman Babiy da Ummu da Daneen Ammarah.

Tajwar Eshaan ya nisa tare da motsa lips dinsa a hankali, "Wannan kotu na bukatar Daneen Ammarah a gabanta, da son jin fassarar kalamanta".

Sayeed Hanifud-Din ne ya maimaita abinda Tajwar Eshaan din ya fada, dan haka Daneen Ammarah ta fito da taimakon Daneen Waheada,dan da alama abubuwan kanta ma neman sukeyi, idanunta har sun kada.

"Ko zamu iya sanin abinda kike nufi da kalamanki Daneen Ammarah. Sannan ko kinada alaka ne da wanna shari'ar?"

"Bani da alaka da wannan shari'ar face a farkon ta mai bada kariya ga Zawjata-almilk. Sai dai inada alaka shudaddiya da wannan bawan ALLAHn". Ta nuna Babiy.

'"'Ko zamu iya sanin alakar taku?"

"Mun taba kasancewa mata da miji kusan shekaru ashirin da daya da suka shude".

Ba Iffah kawai ba, mafi yawan wanda ke'a cikin kotun sai da suka waro idanu saboda razana.

Sayeed Hanifud-Din ya ce,
"Ta yaya?".

Shiru kamar batace komai ba, sai kuma ta nisa da share hawayenta. "Komai ya faru ne a cikin littafin kaddara ta. Na san duk wanda yake anan in har ya kai shekara talatin da biyar zuwa sama yason tabon da ke a jikin bangon littafin labarina da duka shafukan cikinsa. Bazan kirasa abin kaico ba, amma zan kirasa zalunci mai ciwo a gareni dama duk wanda yake cikin wannan masarautar. Faruwarsa kuma ta fara ne a bisa son zuciyar dan uwana Jasim dake a gaban shari’a a yanzu. Sun kulla min aure da wan nan bawan ALLAH bisa umarnin wata mushirika da ta shude ita da labarinta a wannan masarauta. Sai dai aure ne na kwanaki goma sha uku kacal suka saka ya sakeni. Bisa kudirar UBANGIJI kuma ya samar da haihu a tsakaninmu batare da shi ya sani ba ma, dan ban sake ganinsa ba tun wannan ranar sai a yau, sai dai ALLAH yayma yarinyar rasuwa a kwana uku da haihuwarta...

"BATA MUTU BA!!".

Kalmomi uku masu razanarwa da ga bakin kaka. Wani irin zabura Babiy da Daneen Ammarah, da Malikat Haseenat, da Iffah, da Ummu, da Daneen Waheeda, da Malikat Bushirat, da Miran Jasim sukai a lokaci guda kuma a tare kamar wanda aka saita da camara.Su dukansu kuma suka zubama Kaka da yay maganar idanu kowanne da irin kalar luguden dakan da zuciyarsa ke masa a zahirance da badini. Cikin karfin hali Malikat Haseenat ta furta, "Taya wadda naima wanka, na shirya a cikin likafani, aka sallaceta a gaban kowa, aka gina kabari aka sakata za'ace bata mutu ba. Kai wanene? Ya akai kuma kasan hakan?".

"ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai albarka. Nine mutumin da ya kora waccan bokanyar mushirikar a waccan raar dai da nasan bazaki manta ba".

Ya arrahaman! Bawan ALLAH dama kana raye? Amma ka sakani a rudani.

"Nasan zan saka kowama a rudani, sai dai wannan ranar ita naita rokon UBANGIJI zuwanta gareni kafin ya dauki rayuwata dan na cika wasiyyar mahaifina. Duk da burina ya cika na dawowar Fhareedah cikin zuri'ar mahaifiyarta a dalilin aure".

Kowa zubama Iffah idanu yayi, kamar yanda itama take kallon Kaka jikinta na dan rawa. Malikat Bushirat ma wani irin bugawa kirjinta keyi, hakama Daneen Ammarah da Babiy. Cikin rawar baki data harshe Babiy ya ce, "Baba na kasa fahimtar komai".

"Yanzu zan fahimtar da kai dama duk wanda ke anan. Kamar yanda Daneen Ammarah ta fada an aura mata miji kuma an saka ya saketa a sati biyu bisa umarnin mushirikar dake katantanwa da ikon wanna gida. Ba kowa bane wanda aka aura matan nan face Zayyan in Abbas. Zayyan dai da ne ga wani aminina da zan iya cewa ma ya zama jinina. Dan tunda muka taso babu abinda ke rabani da Abbas. Hatta aure an mana a rana guda ne, hakama haihuwar yaranmu tana zuwane a kusa da kusa. Sai dai shi nashi basa zama sai akan Zayyan. Sana'ar gidan su Abbas dinka kayan doki ne, dan haka ita ya gada ita kuma yake yi tunda yasan kansa, wannan dalilinne ya sani koyo a wajensa, danni gidanmu abinda na tashi naga anayi bana ra'ayinsa. Mahaifina babban mutumne mai bada magani sannan yana cire kowadanne irin aljanu a jikin mutum duk taurarin kansu. Ni kuma sai nake ganin kamar wani abun akwai kauce hanya, dan haka naki yarda na dingayi duk da tunda na taso yanayi a gabana na kuma san magunguna da sirrika kala-kala. Mukan dinka kayan doki ni da Abbas mu kawosu cikin Dahab City, anan ne muka hadu da wani bawan ALLAH da yay sanadin fara kawo wadan nan kaya namu cikin masarautar nan. A duk sanda muka kawo akan bamu kudinmu ne gaba daya, sai ma yazamindai mun dinka din nan kawai muke kawowa. A haka muka cigaba da rayuwa har shekarun yayanmu suka kawo girma, iyayrnmu suka bamu shawarar hada yaranmu aure. Munko yi farin ciki da shawarar, babu bata lokaci aka sha bikin Jumayma da Zayyan. ALLAH ya azurtasu da haihuwar fari da wuri, ta biyu ma haka, hakama ta uku. Zuwa sannan idan mun dinka kayan doki duk wanda zai o kawowa yakan taho ne da Zayyan da shine kadai keda sha'awar irin sana'ar tamu. Sauran yarana biyu maza kuwa suna nasu aikinne da sukafi so suma. A wata rana data kasance nine zan kawokayan da muka dinka masarautar a cikin azi sai na tashi da ciwo na zazzabi, dan haka Abbas ya amsa suka tafi kaiwa tare da Zayyan. Basufi awa takwas da tafiya ba sai gashi ya dawo min yana kuka. Hankalina tashe na tarbesa da tambayar lafiya. Bai boyen komai ba ya sanar min wai amma Zayyan aure da diyar Shahan- shan, cikin mamaki nace aure kuma? Wane irin aurene haka kamar auren kaza? Kuma da yar Shahan-shan guda anya kuwa?. Ya tabbatar min hakane, amma yanaji a jikinsa akwai dalili mai karfi nayin hakan dan yaji wasu yan samari da basu wuce sa'an Zayyan din ba na labari. Nan ya zayyane min komai dake faruwa ni da baba. Na lallashesa da kwantar masa da hankali na shirya a boye naje masarautar bisa umarnin mahaifina. Anan nake jiyo komai dama asalin dalilin hadin auren. Hankalina ya tashi dan na fahimci babban al'amari ne kam gashi ance Shahan-shan ma baya kasar shi da uwargidansa da Miran mai jiran gado. Kannensa ne da wannan aika-aikar. Na koma gida cikin damuwa mukai zaman jiran tsammani, tun muna irga kwanaki harya koma sati har sati biyu. anar kwatsam sai ga Zayyan ya dawo mana. Duk mun tarbesa da tambayoyin yaya akai ya kubuta. A take ya zayyane mana komai yana hawaye. Murmushi mahaifina dake kwance yana jiyya yayi, sai dai baice komai ba, sai daga baya 22:58
¡kirani yake sanarmin ya fahimci Zayyan ya kamu da soyayyar matar aurensa ta sati biyu dan haka a karo na farko yana son nayi wani abu, ya kuma tabbatar min ba shirka bace kamar yanda nake dauka dan shi ba mushiriki bane. Komai sai da ya zayyane mun, dan haka na dauka alwashin bibiyar al'amarinta har sanda zata haihu kamar yanda mahaifina ya bani umarni. Shi kuma ya sakashi baro cikin Jumna dan yace ya tabbata za'a iva zuwa nemansa, za kuma a nemesa a ko'ina dan haka yace yaje cikin Dahab City din inda bazasu taba tsammanin zasu samesa a kusa da su din ba, wannan ne dalilin dawowar Zayyan wanna gari, su kuma su Abbas ya sakasu dawowa cikin gidanmu yanda mutane zasuyi tunanin suma sun gudu. Haka kuwa akayi, bayan tafiyarsa da kwana biyu shi da matarsa da yaransu uku sai gashi anzo nemansa. Sai dai iya bulayi basu samesan ba, da ga baya dole suka hakura. A wannan dan tsakanin Abbas ya kamu da rashin lafiya ta kwana hudu kacal ALLAH yay masa rasuwa. Wannan mutuwa ta gigitamu matuka,hakama matarsa da Zayyan. A wajen zaman gaisuwar Abbas da Zayyan ke zuwa a sirrance ya hadu da Abu Musa, wanda shine silar masa hanyar kai zuma cikin masarauta dama abokinsa ne na yarinta. A tsorace yazo ya sanarma mahaifina abinda Abu Musa yazo masa da shi. Sai yay murmushi tare da kwantar masa da hankali tare da bashi kwarin gwiwa saboda wani hasashe da yace yayi akan hikimar cigaba da zuwan nasa masarautar. Duk da shima yana da mai kawomasa duk wani rahoton da yake so na cikin masarautar, a haka nema muka san samuwar cikin Fhareedatu, wanda kuma yay dai-dai da samuwar ciki na hudu ga diyata matar Zayyan itama. Abubuwa sun cigaba da kai da kawo har zuwa ranar haihuwa, a lokacinne kuma mahaifina yasa na shirya yin abinda ban taba yi ba. Wato aiki da kayansa. Alhamdullah sai kafin ma nai wani yunkuri sai ga kiran mahaifina da ga masarauta wai zasuyi aiki. Da farko banyi niyyar zuwa ba dan shi mahaifina bazai iyaba saboda ciwo, amma sai ya zaunar dani yay min bayanin komai dama ban hasaso ba. Tunda dama ni nayi shirin shiga masarautar ne kawai na dakko abinda za'a haifa na fito kamar yanda ya sani sai a yanzu kuma labari ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login