Showing 123001 words to 126000 words out of 180087 words
Chapter 42 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
Sai da taja kamar minti biyu falon shiru kafin ta nisa. "Na bukaci ganinka nan ne bisa wani dalili da bai gaza biyu ba. Na farko daga yau na dakatar da kawo duk wani ganyen shayi da sunan Maleek a gidan nan. Na biyu akwai aikin da zakamin".
Hankali tashe ya dan dubeta sai kuma ya rissinar da kansa. "Ranki ya dade ki gafarceni, wani abu ya faru ne?".
"Komai bai faru ba. An samu sauyin sabon tsarine kawai. Shin kozan iya sanin sunayen abubuwa da ake hada kayan shayin Maleek?"
"Sosai kuwa ranki ya dade, mi kike bukatar sani?"
"Komai"
Ta bashi amsa a takaice. Da sauri ya bude jakkar gefensa ya zaro wani littafi. Da sauri daya daga cikin hadiman ta amso ta kawo mata bayan ta kai har kasa.
A dake Iffah ta amsa babu alamar wani dar tattare da ita ta fara duba littafin Kavance dan babba.
Duk da yasan babu wani abu na cutarwa a ciki tunda a sirrance kuma aka bashi ganyen shayin da ya aiko jiya da dare a tsorace yake, dan harga ALLAH gizagon wannan baiwa da kwarjininta ya cika masa ido matuka har yana jinsa a takure cikin falon ma. Da din dadawa kuma wannan shine karo na farko da akai masa irin wanna kiran ma sabanin da da sai ya hada wani samfur na sabon ganyen shayi yakan zo ya gabatar kozai birge Shahan-shan.
Kusan mintuna biyar Iffah nabin littafin daki- daki har kusan tsakkiyar, dan gajerun bayanai ne akan yanda ake hada ganyayyakin da sunayensu. Rufewa tai tare da dan dagowa ta dubesa. "Uhm komai dake anan kam bashi da wani aibu, sai dai sabaninsa daga yanzu muna bukatar fresh ganyayyakin ne. Kuma za'a dinga noma su ne a cikin masarautar nan".
"Yanda kike so haka za'ayi ranki ya dade". Ya fada cikin tashin hankali a bayyane. Iffah da tai kamar bata fahimcesa ba ta mike, "Ka hada duk abinda ya dace a turamin, idan na kammala da nawa shirin zan nemeka".
"Godiya nake ya Zawjata-almilk. ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai amfani".
Hannu kawai ta daga mai tai wucewarta,hadiman da al'ajabi ya sandarar a tsaye suka
take mata baya da sauri….✍️
(Wato wannan yarinyar ko? Humm 🥱😂
DAUDAR GORA
Book 2
Chapter: 64
Tunda aka shigo da Arshaan dakin kurkukun da ke makwaftaka da juna da na Miran Jasim sukema juna kallon kallo, duk da dai shi Jasim bai ko motsa da ga zaman takurewa waje dayan da yay ba, su dukansu dakin babu yawaitar haske, sai dai ta dan hasken da ke lekowa sukan iya gain junansu. Sun kwashe awa guda a haka kafin Jasim ya mike cikin dan tangadi, dan baya cin abincin da ake bashi ga raunikan da ya jima kansa duk an masa tretiment dinsu. Jikin karfen da ya raba dakin nasu ya tsaya, sai kuma ya kece da wata irin dariya kamar wanda hauka ya kama. Cikin bacin rai da kunar zuciya Arshaan ke kallonsa, sai dai baice komai ba har yayi ya gama yay shiru dan kansa. "Oh!! Kai dama a tunaninka Jasim ne kawai ta karewa Arshaan? Lallai kai jaki ne bazan gaji da maimaita fada ba, why da ace uwarka na raye zuwa yanzu nayi imanin bakin cikin haihuwar wawa da tai irinka ne zai zama ajalinta. Kai anya ma kuwa bada cikinka ta shigo gidan nan namu b
"Jasimmmmm!!!!!!!".
Arshaan ya fada cikin karaji da wani irin girgiza karfen tsakanin nasu kamar zai babbagesa,amma da yake a gine yake cikin kasa ko gezau shegen baiyi ba. Ka dan Jasim yay baya yana dage hannaye sama kamar wanda yay surrunder, sai kuma ya sake kwashewa da dariya kamar zai fadi ya sake dafe karfen yana fadin, "Shegen kaya ashe kasan abinda kake. To to naji uwarka anan ta haifeka, sai dai wlhy bazan daina tantama ba nikan kodan kasancewarka kasurgumin annamimi, butulu,sannan rago mai labewa a bayan mace domin kubutar da kai. Shin nawa ta siyeka ne har haka?"
"Yanda aka sayo uwarka a gidan karuwai. Why da ga yau idan ka sake kuskuren zagin uwata, sai na maka lahanin da sai ruhin uwarka ya dawo duniya yana mai cikin garari Jasim.Wawa jaki kawai maybe ma uwar takace ta shigo mana da cikinka da ga wajen dan tsautsayi kawai. Ko an fada maka bamusan tarihin tushenta bane a gidan.
"Amma kasan zan iva kasheka na binne gawarka a cikin kurkukun nan ko? Idan ka manta bari na tuna maka wanene Jasim in Abdul- majeed Aliy Qutb, domin ni a gareka sai dai kallo sai kuma hange daga nesa koda bakin cikina zai ajalinka. Ko an fada maka ban san kulle-kullen da ka jima kanayi a kaina bane?, Kana goyamun baya domin in mun kauda shi nima ka kaudani, sai dai kuma kayi kuskure, domin kafin kaga biri shi birin ya ganka dan hau. Da ido daya Jasim ke barci,sannan a tafin hannuna kake, zakuma ka tabbatar da hakan nan gaba jadan". Ya kare maganar yana wata yar iskar dariya cikin rangaji harya koma wajen zamansa ya sake zama rigija yana dariyar har lokacin.
Shiru Miran Arshaan baice komai ba, sai dai yana tsaye kamar gunkin da aka ajiye dan tarihi idanunsa nabin Jasim din da kallo, da alama dai tattaro abin fada yake, ko kuma maganar Jasim din ce dai ke masa kaikawo dan bai taba tunanin yasan da wannan burin tattare da shi ba.
** BAYAN KWANAKI BIYAR **
Kwanaki biyar kenan da mika su Arshaan suma a makargama, Jasim kuwa sati guda. Sai dai kuma Tajwar Eshaan bai sake cewa komai ba game da su, hasalima a yau da ake saran ganin watan azumin ramadana ya dauka hutun fitowa fada har sai bayan salla. Tare da daura Sayeed Fayzul-haq akan komai dan zaije Umrah shi da iyalinsa kamar yanda ya sanar.Tabbas a wannan karon babu wasa a cikin al'amarin Tajwar Eshaan din, dan haka kowa ya shiga taitayinsa har su manyan masarautar. Duk da akwai abubuwan fada a bakinsu har game da karasa zaman shari'ar da aka fara amma sun gagara cewa komai har ya gama jawabin fara azumi da gamashi lafiya yay musu bankwana.
A lokacin da Tajwar Eshaan ke can yana bankwana da jama'ar fada anan Iffah ce cikin babban bitalmanin kasar ruman bisa jagorancin babban dan Sayeed Khairul-Bashar mai suna Abdul-Shakhur in Khairul-Bashar tana bada umarnin ware kayan masarufi nau'i-nau'i domin dorasa a jagorancin rabawa talakawan kasa. Sai matasan masarautar da ta saka shi Abdul- Shakhur din ya samo har su hamsin da zasu jagoranci sauran jihohi da wanda za'a kai wasu kasashen da yaki ya samarwa yan gudun hijira da ma iftila' in rayuwa na talauci.
Wannan al'amari ya matukar jjiga kunnen duk wanda ya samu labari a cikin masarautar, dan abinda bai taba faruwa bane, duk da duk azumi akan fitar da kayan masarufi a dan kai jihohi suma kuma ana da kasune ga Tajwar na jihohi bawai a wakilta wasu suyi aikin ba a cikin masarautar. Sannan a duk shekara tun ba hawan Tajwar Eshaan din Malikat Bushirat ce ke da wanna karfin ikon matsayinta na mahaifiya ga Shahan-shan. Sai kuma a yau labarin ya canja akaga Zawjata-almilk kan komai cikin kuma sauyi.
Kamar yanda labarin ya isa kunnen kowa kuwa yaje ga Malikat Bushirat din da take zaman tsara yanda zatai fitar da wanna abinci bisa tsarawar uwa kamar kowace shekara. Ba kuma a bada abincin ma sai bakwai da azumi, sai kuma gashi yau ana gobe saka ran daukar azumi za'a fara rabon. Kayan da aka fitar kuma sun ninka wanda ita take sakawa a fitar sau dari. Dan duk wani abinci dake shekara ta uku a cikin bital mali Iffah tasa an fito da shi ana da kasa a hannun wakilan. Su kuma kasancewar matasa masu zafin nama da son dama su nuna tasu baiwar amma basu da wanna damar sun bata goyon baya dari bisa dari, duk da kasancewarta karama a shekaru kuma sun bata girmanta matsayin Zawjata-almilk, to kwarjini da cikar kamalar ta da barazana ma bazai bari ko kaso kawo mata wargi ka iya aikata hakan ba.
Tsaf numfashin Malikat Bushirat ya dauke na wucin gadi lokacin da Jazaa tazo mata da mummunan labari. Ta wani zuba idanunta kamar mai son gano gaskiyar maganar a jikinta. Kafin ta yunkura ta mike cikin wani irin zafin rai ta shiga bedroom din ta. Cikin kankanin lokaci ta canja shiri, tana kokarin fitowa Jasrah ta shigo dakin da sallama, dan tunda aka sallamota da ga asibiti nan sashen ta dawo take zaune, a kallo daya datai mata ta fahimci bacin rai dake tattare da ita. Itama yanzu take jin labarin komai a bakin hadiman sashin, dan haka ta biyota daki sanin yanzu yayar tata zata birkice. Ita mamaki take da yanda gaba daya yanzu wasu halayenta ke neman canjawa. Tunda ta dawo sashen kokarin ganin ta fahimtar da ita wacece Iffah take amma taki fahimtarta, gashi kuma yanzu Iffahn ta sake dangwalo wani al'amarin.
"Akia Please kiyi hakuri, zuwanki wajen yarinyar nan a yanzu bashine mafita ba, sai dai maya zubar miki da mutuncinki. Ni a ganina nemanta ya kamata kiyi bayan tabar wajen sai muji dalilinta na zartar da hukuncin da kece ke zartar da shi, ko kuma ki tuntubi Abni kiji tunda dai bazatai komai bada saninsa ba".
"Bani hanya Jasrah".
Ta fada a zafafe kamar ma bataji mi Jasrahn ta fada ba. Cikin dakewa itama Jasrah tace,"Bazan barki ki fitaba gaskiya Akia, kiyi tunani abinda kike son aikatawa. Akia na miya canjaki haka? Bayan kuma a baya ba hakan kike ba. Karfa ki manta shekaru kusan hudu muna kuka akan matsalar dake zagaye da mu ta mutuwar matan Abni, amma a yanzu UBANGIJI ya kawo mana iyakar komai, a kanta komai ya canja har mutane suka fahimci makarkashiya ake masa sabanin da da shi kai tsaye kowa ke zargi. Kamata yay mu rungumi yarinyar nan muyi farin ciki da kasancewarta mata ga danmu bawai bore ga duk yunkurinta ba. Matsalarmu da ita dama can akan abinda muke zargin ta aikata ne, amma yanzu mun fahimci ba haka bane ba, to mizaisa bazamu manta komai ba mu maidata komai dinmu kodan farin cikin da yaronmu ke samu da ga gareta.
Tassss! Kake jin saukar lafiyayyen mari a fuskar Jasrah, idanu kawai ta rumtse tana mai kauda kanta, yayinda Malikat Bushirat ke wani irin huci. Abune da bai taba faruwaba, dan ko sanda Jasrah a karama bata taba dukanta ba, shagwabata tai kamar yar data haifa ba kanwa ba, ta kyautata rayuwarta tai mata raino kamar Kwai a cikin cokali. Idanunta da sukai jazur ta bude, ta dan girgiza kai tana murmushi mai ciwo. "Zan iya amsar duk hukuncin da zakimun Akia dan ke uwa ce a gareni ba yar uwa kawai ba. Amma why bazan taba barinki ki zubar da mutuncinki ba". Tana gama fada ta zare key din kofar ta fice da sauri ta maida kofar ta kulle
gaba daya. Duk kiran sunanta da Malikat Bushirat keyi cikin karaji batako kulata ba tai shigewarta dakin dake matsayin nata a yanzun tana hawaye. Ita kam ta fara shiga rudani akan canjin halayen yar uwar tata, ta sara mike damunta a yanzu. Anya ba masu son cutar da Eshaan bane suka dawo kanta suka saka kiyayya a tsakaninta da yarinyar nan. Ita kam yanzu ta fahimci Iffah, tanajin kaunar yarinyar a ranta kamar tun a da can farko, matsalar data biyo baya ma a dalilin abinda suke tunanin ita ta aikatane. Amma yanzu kunyar haduwarsuma take ji. Dan bata san da bakin da zata fara rokonta gafara ba. Amma koba komai ALLAH ya sakama yarinyar tun ba'aje ko'ina ba, tunda gashi wanda ta yarda da shi fiye da kowa da komai yau shine kecin amanarta da matar dan uwansa, wannan wace irin mummunar kaddara ce. Hawaye masu zafi suka silalo mata, dan abune dake mata matukar kuna da zafi a zuciya tunda ya faru, ga kunyar fitama da takeyi dan ko hadimai shune suke mata akaikaice matsayin matar mai neman tsohuwar matar Shahan-shan……..✍️
14:23
DAUDAR GORA
Book2
Chapter: 65
A gajiye tibis ta shigo sashen, yana zaune a falo harde kamshinsa ya karade falon. Da sauri amintaccensa da ke gefen kafafunsa zaune da ga kasa yana ware masa wasu takardu da suka barbaza ya sake kasa da kansa yana gaisheta.Da hannu ta amsa masa idonta akan zakinta da ke mata kallon kasan ido ta yanda ita kawai ke fahimtar hakan. A hankali ya motsa lips dinsa ya Bama amintaccensa umarnin tafiya. Zaram kuwa ya mike dan dama abinda yake jira kenan. Saboda a yanzu kam shigowarsa wannan falon sai da notis saboda yanda iyayen gidan nasa ke manne da juna akoda yaushe suna baje kolinsu yanda suka gadama. Shifa har mamaki yake da jin anya kuwa ba'a samu canji da ga Shahan- shan din nasu ba zuwa waninsa. Shifa yasan abinda yake gani kawai.
A hankali ya bude mata hannayensa alamar tazo garesa idanunsa kyam akan kyakykyawar fuskar ta dake a shagwabe kamar zata saki kuka. Kafada tadan noke tana tura baki, sai kuma ta fara takawa a hankali zata wucesa, a hankali ya riko hanunta da dan murmushin iya lips din nan nasa. Gaba dayanta ya jawo ta fado jikinsa. Wani irin sakin ajiyar zuciya sukai a tare.Tare da rungume junansu tsam-tsam kamar masu tsoron a rabasu.
K ta dabance".
Ya fada a hankali cikin kunnenta yana sake kankamta.
"Kai ne na daban a cikin daban ai Zakina". Ta fad itama tana sakar masa manya-manyan sumba a kan kirji. Sai kuma ta dago kanta suka zubama juna ido cike da kewar juna kamar ba da safe suka rabu ba. Cikin motsa lips dinsa da kyar ya ce" "Kin gaji ko?".
Kanta ta jinjina masa tana marairaice fuska, sai kuma takai hanunta kan kyakykywar fuskarsa tana shafa kwantaccen gashin wajen dan tana matukar son sa. "Amma tunda aikin lada ne banajin gajiyar". Dan sumbatar lips dinta yay a fisge ya ce, "Da gaske?"
"Yap".
Ta fada cikin fari da kashe masa ido daya.Murmushi ya dan saki da lakace mata hanci, sai kuma ya maida bakin nasa kan nata ya shiga bata kyakykyawar sumba, ba' a barta a baya ba ta shiga taimaka masa cike da nuna kwarewar haddace dukkan karatunsa. Kafin akai wani dogon labari gaba daya yanayinsa ya canja. Dan shifa Tajwar Eshaan bai san wani yaren dandani haukaci ba. In har aka fara sai an kai karshe.Sannanake iya samun kansa dari bisa dari kuma dalibar tasa da alama dai irinsa ce, dan zuwa yanzu duk da ta kasa zama mai juriyar mika wuya yanda yake so saboda rashin sabo tana kokarta kamantawa musamman a bashi hadin kai a duk sanda yace kule takance cas. Da ga baya kuma ta dawo tana masa raki da shagwaba, Shiko yay ta mata murmushin miskilancin nan na..
Bayan sun samu daidaito ta lallabasa yay mata kiran su Babiy, sun jima suna hirarsu dan a yanzu kullum ne sai ta saka ya kira mata su, sai dai kuma duk sanda za'ai wayar yana dakin, bai kuma taba yarda shi sun gansa ba ko tayi wata magana a kansa, tayi-tayi ya barta suna gaisawarsu ita bazatace komai a kansa ba yaki bata damar hakan, ya dai yarda ya kira mata su su gaisa suma jima suna hira yana da ga gefenta yana saurare da jin komai.
Bayan sallar magriba ta samu sakon kiran Malikat Bushirat da ga wajensa. Dama dai suna da shirin zuwa mata sallama, dan insha ALLAHU ana kai azumin farko a gobe zuwa dare jirginsu zai daga zuwa Saudiyya. Sanin abinda ta kullama ranta tace ya barta to ta fara vin gaba yazo da ga baya tunda zaije ya ma Malikat Haseenat ma sallamar, ita kuma da safe Insha ALLAHU sai tayoma su Malikat Haseenat din sallama. Bai wani kawo komai a ransa ba yace taje, dama yana bukatar yin magana mai muhimmanci da Mammah din kuma akantane baya kuma bukatar taji.
Tunda ta fito a mota hadimai ke fama zubewa gaisheta. Kafin ma ta karasa ciki an kaima Malikat Bushirat labarin zuwan nata. A zahirance dai batace komai ba har Iffahn ma ta karaso. Gaba daya hadiman dake zagaye da ita ma wani irin zubewa sukai bisa gwiwunsu lokaci guda, dan wani irin kwarjini Iffah'r ta musu naban mamaki, sannan koba komai ita din dai Zawjata-almilk ce. Hannu kawai ta dan daga musu dai-dai tana kaiwa cikin kujera da wani irin salon zaman kasaita na kafa daya kan daya. A hadiman babu wanda bai girgiza da salon Iffah'r ba, dan kowa yasan duk da take matsayin Zawjata-almilk a gaban Malikat Bushirat dole ta risina kuma kasa ne wajen zamanta. Sunta satar kallon Malikat Rushirat din da tunanin ko zatace abu, amma sai sukaji shiru, hasalimal sau daya bata motsa da ga zamanta ba balle a karanci wani abu da ga gareta.
Wani irin kallo Iffah ta watsa musu da masu alamar fita da yatsunta. Har ko rige-rigen fitar suke duk da sun so ganin yaya wasan zai kare. Falon ya dauki shiru na tsawon lokaci batare da wani cikinsu ya motsa ba, hasalima ita Iffah ta maida hankalintane ga wayar Tajwar Eshaan da ke a hannunta tsabar rainin hankali ma browsing abu takeyi hankalinta kwance kamar ta manta gaban wanda take.
Malikat Bushirat ta dago idanunta da sukai wani irin kadawar bacin rai ta zuba mata, tsahon sakanni kafin ta nisa da kyar cike da zafin rai. "K har kina ganin