Showing 30001 words to 33000 words out of 125808 words

Chapter 11 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

445

asabar bamu wuni a gida ba yawon guraren shakatawa muka tafi, ni Faty Naseem Nasmah da kuma Talatu, sai direba. sai yamma muka dawo niki niki da kayan makulashe, washegari ranar Lahadi ma muka kuma fita, shima sai yamman muka dawo a part ɗin su Inna wuro muka yada zango sai bayan isha muko koma side ɗin mu, ai ko muna shiga su Nasmah suka ɓingire da bacci.
koda gari ya waye dakyar nata da su Talatu ta tafi da su dan yimusu wan ka da shirin makaranta, dan tare jiya muka kwana da su.
kamar kullum na rakosu muna ɗagawa juna hannu suka fita.
ina komawa ciki wanka nayi nashirya cikin les copie colour da ɗan ratsin gold ajiki,
da misalin karfe 10 da rabi nasauko kasa da mayafi akai na sai ƴar karamar jaka mai ɗauke da wayoyina da wasu ƴan kuɗi dana saka ciki,
dinning area na nufa, in da na tadda Zulai tagama shirya komai na breakfast, a ɗan gaggauce nayi breakfast ɗin, ina yi ina duba agogo, dan fita zamuyi da Bappa zuwa asibitin da ake ginawa dasunan Inna ganin yan da ai kin ke tafiya, ina saurin ne dan jiya nace mishi karfi goma da rabi zamu tafi nasan kuma yanzu haka yagama shiri ni yake jira.
koda na fita a kofar masallaci dake ta nan cikin gida na taddashi zaune, na karaso in da yake tare da gaida shi, daga nan muka shige mota muka nufi asibitin.
masha Allah asibiti yayi kyau saura kaɗan a kammala aiki, bamu bar asibitin ba sai wajen karfe 12:20pm nacewa Yakubu muwuce makarantar su Nasmah mu ɗauko su.

Abakin get ɗin makarantar Yakubu ya faka mota yafita da sauri yana faɗin
"Bari naje na fito da su". yayi cikin makarantar da sauri, muna nan zaune can yafito da sauri kamar zai kife kasa yakaraso gefen da nake yace
"Hajiya wai an zo an ɗauke su."
ido na waro da mamaki nace "Wa yazo ya ɗau kesun bayan kai muna tare da kai ina ce kai ne me zuwa ɗaukar su."
Bappa yace "Zancen banza kai wani direban akayi musu sabo ne da zaizo ɗaukar su? ko dai bakaji abun da suka faɗa da kyau bane?."
yace "Wlh haka mai gadin yafaɗa Bappa."
da sauri Bappa ta buɗe motar yafita ai ko nima da sauri nafita narufa masa baya har ina haɗawa da sassarfa.
babu kowa cikin makarantar sai mai gadi da masu kula da tsaftar makarantar sai shara da goge-goge suke, hankali tashe Bappa ke tambayar mai gadi, mai gadin yace
"Ai ko minti goma basu da tafiya ba duk ɗazu muna tare da su anan da wasu ɗaliban mota tazo tafaka nan bakin get suna ganin motar suka zuba a guje zuwa gurin motar suna murna, da naso hanasu dan ganin ba ɗaya daga cikin irin motocin da ake zuwa ɗaukar su da shi bane, to ganin yan da suke ta murna sukayi gun motar a guje yasa nayi tunanin ɗaukar su a kazo, dama badaga gida akazo ɗaukar su ba!."
maigadi yakarashe maganar yana buga kirji.
Yakubu da gumi yafara keto mishi kamar zai fashe da kuka yace
"Ina ni ke zuwa ɗaukar su kuma gani a gaban ka sai kuma hajiya wata rana,ko mutumin yasako irin fuskata ce ya zo."

Bappa yace "Amma kuwa abun da mamaki amma ya kamata lokacin da kaga ba ɗaya daga cikin motocin da ake zuwa ɗaukar su da shi bane yazo kama yayi kaje kaga ko waye ne,amma wani abun mamakin da kace wai sun je gurin motar da gudu kuma suna murna to ko wani ne daga gida yazo ɗaukar su tun da sun san mun fita har da direba?."
ni dai kasa magana nayi sai ɓari da jikina yake cikin matukar tashin hankali tuni idanuna suka kawo ruwa kan kace me hawayen suka fara sauka.
murya na rawa Yakubu yashiga tafa hannu da salati yana faɗin
"Dama ance yanzu masu garkuwa da mutane sun canza salo akwai wani abun da suke yi sai dai kaga mutum na ta binsu kamar ya sansu harsu tafi da shi, wayyo Allah Naseem da Nasmah ko dai sune."
cikin gwalalo ido mai gadi yace
"Wayyo Allah nashiga uku wayyo ai kina shikenan dama ance idan aka sami matsala to abakin ai kina, ashe dama tsarin da masu garkuwa da mutane suka fito dashi kenan? shi yasa yarannan sukayi ta tsalle kamar doki suka ruga in da motar take, ashe jansu ake taciki kamar kuran karfe."
ɓarin jikina ne yakaru yayin da zuciya ta ke bugawa da karfi gudun hawaye na yakaru.
Bappa yace "Kai ya isa haka Falyakum khairan au yasmuq, in sha allahu babu abun da zai faruku muje gidan mugani wata kila daga gida ne akazo aka ɗauke su tun da sunsan bama gidan."
yadube ni yana cigaba da faɗin
"Kice Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un."
kalmar nashiga nanatawa kana muka juya gun mota, muka bar maigadin nan tsaye yana ta rafka salati dafaɗin shikam yau yasan ai kin sa yazo karshe har in sace yaran akayi.
acikin mota Bappa yarika zuba addu'o'i yakuma hanani kukan danake shirin yi yace nayi ta faɗin
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
a haka muka isa gida.

Muna isa Yakubu yayi hon maigadi ya wangale get yana kokarin wucewa parking lot nace
"Ka sauke mu anan."
dan gani nake kamar motar bata tafiya da sauri tsabar tashin hankali.
tun kan ya dai-dai ta parking muka fito daga motar maigadi yakaraso yana mana sannu batare da dukkanmu mun amsa ba Bappa yayi saurin cewa
"Wayaje ya ɗauko su Naseem a makaranta a cikin ku?."
maigadi yace "Gaskiya babu wan da yaje ɗauko su dan tun da kuka fita ma babu wan da yafita, yau kam sunsha zama a makaranta Yakubu yayi hanzarin zuwa ɗauko su."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un an ce anzo an ɗauke su kuma kace ba wan da yafi tun fitar mu an sace su kenan."
nayi maganar tare da fashewa da kukan da Bappa ketasa ni danneshi, nacigaba da faɗin
"Ina suke ina suka shiga waya ɗauke su.".
maigadi ya walalo ido tare da faɗin
"Iye! ansace su!."
Bappa yace "Ka tabbatar da babu wan da yafita."
yace "Wlh babu wan da yafita tun fitar ku ina bakin get ɗin nan........!





Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:55 - Ummi Tandama😇: An buɗe murfin motar, baya na ɗan yi da sauri dan kaɗan ya rage marfin ya bige ni, kasan cewar nazo daf da motar sosai. da sauri na ɗago dan ganin wan da ke cikin motar, ido na waro da ɗinbin mamaki ganin mutumin da su Nasmah suke cewa Daddy ne, tsayuwa ta na gyara ganin yazuro kafar sa waje yafito daga cikin motar,baki na buɗe cikin masifa ganin yan da yayi kusan bige ni da murfin motar sa, "Malam ya haka baka ganine?."
nayi maganar ina yi masa kallon sama da kasa.
tsayuwar sa ya dai-dai tare da mai da murfin motar ya rufe, kana yashiga nuna min yatsa tare da kaɗa yatsar yasoma magana.
"A kan wani dalili zaki rika birkita wa yara ƙwaƙwalwar su, kinyi yunkurin sauya musu School abaya, ba'a baki dama ba shine kika ajiye su a gida tsawon sati guda, sannan kika sauya musu Makarantar, ilimi kike so su samu ko kuwa birkita musu ƙwaƙwalwa kike son yi, kada ki kuma yunkuri da tunanin sauya musu makaranta kan wani dalilin ki mara amfani, idan kuma ba haka ba."
sai yayi kwafa tare da kaɗa yatsar sa.
kamar daga sama nake jin maganar nasa mamakin sa da furucin sa suka sani gyara tsayuwa ta ina yi masa kallon kacika mai karfin hali.
"Dakata malam."
nafaɗa ina ɗaga masa hannu, kana nacigaba da faɗin.
"A kan dalilan su ƴaƴana ina da ikon yin komai da su, dalilina mai amfani, kada ka kuma cewa dalilina bashi da amfani tun da baka sanshi ba,
ƴaƴa nawa ne nike da ikon yin komai kansu, malam kafita daga rayuwar ƴaƴana kana ta yau darar su da danganta su da kai, da suna mai kama da uba, ƴaƴana basu da uba kuma basa bukatar uba domin bazai yi musu amfanin komai ba, rayuwar su a haka tafiye musu rayuwa da uba sau dubu dan bashi da wani amfani a gare su."
sassauta maganar da nake nayi tare da haɗe hannaye na biyu kana nacigaba da faɗin
"Dan Allah kafita daga rayuwar ƴaƴana kada ka yaudare su da wannan kalma ta uba, dan basu da uba kuma basa bukatar uban, kuma ba shegu bane ƴaƴane tsaftatattu mafiya daraja."

Afusace yashiga matso ni, ganin yan da yanayin sa ya sauya gaba ɗaya, sai na shiga ja da baya, shiko maso ni ya cigaba da yi tare da nuna ni da yatsa, yana huci kana yasoma magana cikin ɗaga murya
"Idan kika sake cewa basu da uba sai ranki yayi mummunar ɓaci, idan kika kuma sako kallamr yaudara sakani na dasu!..."
sai yayi kwafa tare da kaɗa yatsar sa alamun gargaɗi,
mamakin ganin karfin halinsa muraran nake, wai ni da ƴaƴana ake nuna min iyakata a kansu,
bil hakki da gaskiya yake maganar dan kuwa fuskarsa ta nuna, niko
baya na kuma ja ganin yan da ya matso ni sosai yana maganar kamar zai kai min hannu,
wani irin kallon shekeke nabisa da shi sannan na ce
"Idan ba yaudara bace mene ne, kana cusawa yara abun da babu shi, cikin rayuwar su,
ina sanar maka da hakan ne sabo da matsaltawan ka kansu, na dai faɗa maka kafita daga tsafgar ƴaƴana idan kuma ba haka ba zan sa ayi maka gargaɗin da zaka fi fahimta."
ina kai wa nan najuya.

Shan gaba na yayi a fusace cikin muryar da yake nuni da tsantsar gargaɗi ya ce
"Yazamo na karshe fitar kalmar nan daga bakin ki, idan kika sake kika sake furta kalmar durkuso cikin rayuwar su, bazan sa ayi miki hukunci ba ni zan yi miki hukunci da kai na! ki sake nanata kalmar basu da uba kigani!."
yayi maganar cikin
fusataccen amon sauti, a zaburi namatsa gefe dan maganar nashi ta shige ni rabon da ayi min ihu da tsawa irin haka har na mance, shiyasa abun yazo min a sabo.
ba zato naji kafata ta ta dama ta wuce cikin abu kamar rami, da sauri na juyo sai kawai na tafi luuu gaba ɗaya, idanuna na rumse da karfi ina jiran najini a kasa, sai jina nayi zundum cikin ruwa,
kara na ƙwalla wan na hakan yayi sana diyyar wucewan ruwa cikin bakina,
fafutukan niman numfashi nashiga yi, da niman ceton kaina, duk buɗe bakin da zanyi sai ruwa ya wuce ciki, nayi-nayi na iya mike wa tsaye na kasa, duk da kuwa zurfin ruwan idan zan shiga da kafata iya kirji na yake zuwa min.
Shiko Ahmad da sauri ya faɗa cikin swimming pool ɗin ganin yan da ta ke bubbuga hannu da yin sama da shi
da alamun niman ceto.
hannu na ya ruko da karfi ya ɗago ni yamikar da ni tsaye.
ruwan da ke kunshe cikin bakina dana ki haɗiye shi dan cikar da ciki na yayi, na furzar da shi tare da sauke tagwayen numfashi, ina damke cikina da ruwa yacika shi, a wahalce na na ɗago hannuna ɗaya na share fuskata tare da tattaro gashi na daya rufe min fuska, na mai da shi baya,
ida nuna na sauke kansa, dai-dai lokacin daya kai
hannu ya share ruwan dake fuskar sa, sai a lokacin na lura ruwan dana furzar daga baki na a fuskar sa na fesa.
shima idanun sa a kai na tun daga gashin kaina yake bina da kallo har kasa, kasan cewar rana ya taso ya haske cikin ruwan ana iya kallon abun da ke kasan ruwan.
dogon tsaki na ja dan nakasa magana tsabar haushi, bugu da kari yan da cikina ya cike tam da ruwa.
a hankali na soma tafiya cikin ruwan har na isa bakin gaɓar gun matattakalar shiga da kuma fita daga cikin swimming pool ɗin,
a sannu na soma hawa maganar sa na jiyo,
"Ki tsaya a taimaka miki kirage ruwan da kika sha."
cigaba da haurawa ta nayi batare da
waige ko tsayu ba,
ina karasa fita da sauri nayi hanyar part ɗina jin zuciya ta na tashi, cikin sauri na shige cikin side ɗin direct sama na haura,
ina shiga bedroom ɗina da sauri nashige bathroom, ai tun kan na karasa bakin toilet nafara sheka amai tsakiyar bayin, zallar ruwa narika aman sa.
da kan sa aman ya tsaya kamar yadda yazo bazato ba sammani, numfashi narika sauke wa ina tallafe da cikina da yanzu nake jin sa wayam, sai dai ɗan murɗar da yake min.
a daddafe na tsaftace bayin na tuɓe kayan jikina da suka jike gaba ɗaya na wurgasu cikin wishing machine, nafito doguwar riga mara nauyi na zura, kana na isa bakin gado na zauna ina mai cigaba da sauke numfashi,
tsaki narika ja a-kai-a-kai tsabar haushin da nake jin kaina ciki, har lokacin kasa iya furta komai nayi.
idan na tuna ruwan da na hambuɗa a cikina sai naji kamar nayi ihu, sauki na ma ɗaya jiya-jiyan nan nasa aka fidda ruwan dake cikin swimming pool ɗin, aka wanke cikin sa a ka kuma zuba wani, ban kuma yi amfani da shi ba.
wani dogon tsakin naja yayin da na kai bayana na kwanta kan gado.
mamakin karfin hali da takaicin mutumin nan suka rika zuwar min,
wai ni yake yiwa gargaɗi kan ƴaƴana,
ya kuma yi sanadiyyar faɗuwa ta cikin ruwa, badun kwanana na gaba ba wata kila da yanzu ana kan shirin kai ni makwanci.
Dole nasa jami'an tsaro cikin lamarin dan ban amin ta da mutumin nan ba, awani dalili zai rika shiga min cikin gida kai tsaye har yarika yimin barazana kan ƴaƴana.

Mikewa zaune nayi tare da ɗaukar waya ta, number Mr Aliyu nakira wato P.A na, ko da ya ɗaga bayan mun gaisa na ɗaura da faɗin
"Mr Aliyu ina so a saka min jami'an tsaro a gidan nan."
da sauri ya ce "Madam meke faruwa akwai matsala ne?."
yayi maganar cikin nuna damuwa sosai kana yaci gaba da faɗin
"Ai Madam tun farko shiyasa nace azuba jami'an tsaro gida kamar wannan dole sai da manyan Security masu rike da bindiga, kikace abar mai gadi kaɗai ma ya isa, ina kuwa zai isar wa gida kamar wannan, yanzu kuwa zan fita in sha Allahu anjima zamu zo da su."
na ce "To Allah ya kaimu."
nakashe wayar, ina katse kiran kiran Bappa na shigowa, na daga da sallama daga cikin wayar Bappa ya ce
"HAMDAH ko kina bacci ne?." na ce
"A'a ba bacci nake ba Bappa." ya ce
"To kizo yanzu maza." da sauri na mike jin yana faɗin haka ya kashe wayar.
cikin hanzari na nufi side ɗin su Bappa da sauri na dan Bappa bai taɓa min irin wannan kiran ba nasan komai akayi akwai wata masalar, da ire-iren waɗan nan tunanin nashige cikin side ɗin.
turus naja na tsaya yayin da jikina ya kama ɓari ganin Yakubu durkushe yana kuma rungume da uniform ɗin su Nasmah,
cikin tsanani tashin hankali na karaso cikin parlour'n gaban Yakubu natsaya cikin rawar murya da kuka keson kwace min na ce
"Ina yara na?!."
nayi maganar cikin rawar murya sosai tuni hawaye yacike ido na.
Bappa da ke zaune kan kujera ya dube ni tare da faɗin
"Zo zauna nan HAMDAH." yanu na min kujerar da ke kusa da shi, ban iya bin umurnin Bappa ba dan kuwa hankali na yakai kololuwa wajen tashi, duba da yan da Yakubu yake ɓari yakuma rungume uniform ɗin gam-gam.
Inna Wuro ce ta mike tazo taruko faɗata ta jamyo ni ta zaunar da ni kan kujerar, tuni hawayen da suka cuko idona suka fara zuba. Bappa ya girgiza kai yana faɗin
"Muma mun shiga irin yanayin nan da kika shiga a yan da yashigo mana kamar an rakoshi a guje,
tam bayar da na fara mishi shine ina yaran suke ganin uniform ɗin su a hannun shi, da kyar ya iya ba mu amsar suna nan kuma suna makaranta, yaji tsoron ya tinkare ki kai tsaye shiyasa yazo nan."
kai Yakubu yashiga gyaɗa wa yana ɗan rarrafowa da guiwar sa yana kuma faɗin
"Dan Allah dan Annabi Bappa Malam ka rokar min afuwar ta wlh duk yan da naso na hana faruwan haka bai yuwu ba, wlh fin karfi aka nuna min muraran."
Bappa ya katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce
"Ya isa." kana Bappa ya juyo da kallon sa gare ni ya ce
"Lokacin da suka fita zai kai su makaranta a hanya suka haɗu da Ahmad Tijjani Sabil ya sai da su, yake tambayar su ina zasuje ganin ba hanyar makarantar su suka nufa ba, sannan kuma ga wata uniform ɗin daban a jikin su, to shine shi Yakubun ya shai da masa in da zasu, shikuma Ahmad yace kada ya kuskura ya kaisu wannan makarantar yawuce ya kaisu wan can makarantar su, to dai a takaice tare suka tafi da shi wancan makarantar da aka cire su yasa aka basu wani uniform, yakuma tuɓe musu najikin su shine yabashi wan da yacire musun yace ya mai do shi gida,
to shine ya dawo hankali tashe yakuma ji tsoron yaje ya tinkare ki da batun shine ya zo nan,
kafin na kira ki sai da na kira shi Ahmad ɗin sabo da ina da lambar sa dan ranar da yazo nan na karɓi lambar sa, ashe dai zatayi amfani gaba akuma irin wannan ranar,shine na kira sa dan ji dalilin sa na yin hakan,
ya bani tabbacin dalilin sa na yin haka, kuma na gamsu, yace yawai ta canza musu makaranta a karancin shekarun zai iya birkita musu ƙwaƙwalwa gara abar su idan suka gama can ɗin kan lokacin sun daɗa wayo sai suyi gaba, kuma nima nayi nazari naga hakan yafi abarsu a can ɗin, nayi masa maganar dalilin ki na canza musu makarantar yace za'a kara tsaro sosai babu wata matsala."


Yakubu da tun da Bappa ya soma maganar yake ai kin gyaɗa kai da buga bayan hannun sa cikin ɗaya tafin hannun sa, yayi kalar tausayi, Bappa na gama maganar shima ya ɗaura da faɗin "Wlh tallahi Hajiya na rantse miki da Allah, ba laifi na bane, na dage wajan ganin ba'a kuma samin wata matsala ba kamar yadda nayi miki alkawari, wlh Hajiya dana buɗe baki zanyi masa musu dawani yafito daga cikin motar sa, ya shake ni sai da naji kamshin kabari, shi ya hana mutumin da yanzu na sheka,
ki gafar ceni Hajiya ki tai maka kibar ni a bakin aiki na."

Numfashi na sauke jin akasin abun da nake tunani yafaru a kansu, dan Ni nagama tunanin hatsari sukayi sun mutu shine yakawo kayan su gida.
duban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login