Showing 120001 words to 123000 words out of 125808 words
amma wlh duk abun da ya faru karya ne Hajiya ce ta shirya komai tace mu faɗa."
Bappa yayi salati yace
"Akan kuɗi akan kuɗi kuka tarwasa aure kuka jefa yarinya cikin ukubar rayuwa Allah bazai kyale ku ba."
Salele yace "Wlh Alhaji lokacin can data bani kuɗi kan nayi shai da naki sai tace har idan na faɗa sai tayi min sharrin da bana sammani, sai tace har dani ta taɓa kama ni ɗakin Hajiya HAMDAH shi yasa naji tsoro ban faɗa ba."
Abbu yace "Yanzu kam komai ya zo karshe ita wacce ta shirya muku makircin bagata can kwance a asibiti Allah ya fara nuna mata iyakar ta ba, ai ba ayi wa Allah dabara, kukuma mai gadi da Habu da Sani yau za'a kurfanar daku gaban Shari'a kotu zata yanke muku hukun ci dai-dai da abin da kuka ai kata."
rokon Abbu suka shiga yi da magiya Abbu ya ɗaga waya ya kira yace a zo a tafi da su,
aka washe su akayi gaba da su. har aka gama magana
Ya SALEEM baice komai ba yana dai zaune yana kallon kowa da ido, har taron ya watse shima ya mike ya fita.
su Aunty Rafee'at kam sai murna wai yau asiri ya karasa tonuwa...
Da daddaren ranar da aka sallame shi, ina zaune a bedroom ɗin Ummi,
Ummi ta shigo rike da tray mai ɗauke da kayan motsa baki ciki tace
"Ke HAMDAH taso ki kaiwa yayan ku."
nace "Ni kuma Ummi a bawa Fauzan ya kai masa Allah bacci nake ji."
"Maza tashi ki kai masa Fauzan ɗin ne zai kai masa ke aikin me kike, in kin dawo kyayi baccin."
mike wa nayi ina faɗin
"Allah Ummi bakiji yan da na gaji ba bai ma fa ce zaici komai ba."
"Sai ya faɗa ne mutu min da bashi da lafiya."
karɓar tray ɗin nayi nanufi ko ina bubbuga kafa,
kai Ummi ta girgiza tana faɗin
"Allah ya shirya ko yaushe zaki girma oho."
A bakin kofar ɗakin sa na cikin gidan na tsaya, nayi sallama ya am sa ɗan tsayuwa nayi kaɗan dan ban mance dokar sa na idan kayi sallama ka ɗan tsaya kafin ka shigo ba,
guntun tsaki naja.
to ma wai sai nice zan kawo masa abinci.
wani tsakin na kuma ja ina shige wa cikin ɗakin, da sallama.
ya kuma amsa wa, ya ɗago tare da zuba min ido.
yana zaune bakin gado sanye da jallabiya, gashin kan sa ya na ɗiga da ruwa da alama fitowar sa daga wanka kenan.
su Nasmah suna kwance a kan gadon sa suna bacci,
nayi mamakin ganin su cikin ɗakin na ɗauka suna gun Ya Mas'ud ne.
a sannu na karaso cikin ɗakin na dire tray ɗin saman table ɗin gefen sa,
har lokacin idanunsa a kaina, mike wa nayi ina kokarin barin gurin.
naji ya ruko hannuna, a hankali na juyo na kalle sa muka haɗa ido, cire idanuna nayi daga nasa a hankali nace
"Ya jiki?." bai yi magana ba har zuwa ɗan wasu sekonni bai kuma sake hannuna ba, zuwa can ya motsa laɓɓan sa yace
"Naji sauki." hannuna na zame cikin nasa naɗan matso bakin gadon ina kokarin ɗaukar su Nasmah najiyo maganar sa,
"Ki bar su a nan." a hankali na juya nafita a ɗakin dan kallon da yake min yafara min yawa...
Washegari da safe bayan nayi wanka na shirya cikin doguwar rigar les nafito parlour, Ummi tana ta kiciniyar haɗa breakfast, tana gani na tace
"Yauwa HAMDAH zo ki kaiwa yayan ku breakfast ɗin sa."
baki na turo na rasa me yasa Ummi take son lallai sai ni zan rika kai masa abinci.
tace "Kiyi sauri mana kin san zai sha magani yakamata ya fara cin abinci kafin ya sha."
ɗaki na koma naɗau gyale nafito na karɓe tray'n data shirya masa kayan breakfast ɗin ciki na yi waje.
da sallama na shige ɗakin suna kwance kan gado shi da su Naseem sai zuba masa surutu suke, shiko sai murmushi yake binsu da shi.
na dire tray'n naɗa go ina faɗin
"Ina kwana, ya jiki?."
lumshe idanunsa yayi tare da buɗe su a kai na ya kura min ido sosai,
ganin haka da sauri na juya zan fita naji maganar sa
"Wa zai bamu breakfast ɗin idan kika tafi?."
baki na murguɗa a kasan raina nake faɗin "Jimin samin guri ko da ni nake bashi da zai wani ce wai idan na tafi wazai bashi, badun banson ran Ummi na ya ɓaci ba an faɗa masa zan zo ɗakin ne ma."
ɗan gajeren tsaki naja karaf muka haɗa ido da shi, farr nayi da ido na dan nasan yaji kuma nasan baya son tsaki.
ganin yana bina da kallon tuhuma na tsakin dana masa, sai na kaɗa kwayar ido na tare da murguɗa baki.
na dawo cikin ɗakin naɗan sun kuya nasoma haɗa musu abin karin,
da sauri na ɗago jin hannun mutum a kafaɗa ta na juyo cikin hanzari,
sai ganin sa nayi daf da ni,
ganin yan da mukayi daf da juna a hankali nayi baya da kafata ina kokarin matsawa baya.
sai ya ruko kafaɗu na gaba ɗaya,
ya jefa idanunsa cikin nawa yana yi min wani irin kallo, da sauri rumtse idanuna dan sam bana iya jure wa kallon nan nasa,
a sannu yashiga motsa laɓɓan sa yayin da nake jin idanunsa suna yawo cikin jikina
"Yau she kika zamo haka?."
cikin tsiwa na ware idananuna a kan sa nace
"Tun shekaru biyar zuwa shi da da suka wuce."
shiru yayi tare da sauke idanunsa kasa da alamun jikin sa yaɗan yi sanyi da abun da na faɗa,
na faɗi hakan ne kuma domin na tuna masa da baya da kuma abun da ya faru a baya, tun kuma bayan faruwar haka na daina jin tsoron sa.
a hankali ya sake kafaɗa ta ni ko na juya na fita...
Bayan kwana uku kullum ni Ummi take sawa na kai masa abinci ina kai wa kuwa zan juya, ko gaisuwa bana tsayawa yi masa zan fita, kullum su Naseem suna gurin sa a can suke kwana.
yanzu shirye-shiryen koma wa Abuja nake dan sai kira nake samu daga ma'aikata na.
Da daddare har na kwanta Ummi ta shigo tace na tashi na kai masa abinci, na mike na ɗau hijabi na saka kan kayan baccin da ke jiki na na nufi ɗakin sa.
yana zaune bakin gado su Nasmah suna kwance a gefen sa suna bacci,
na juya zan fita ya dakatar da ni ta hanyar rike min hannu,
na juyo gare shi zan yi magana, yakai waya kunnen sa tare da faɗin
"Mamie su Nusaiba su zo."
jim kaɗan Nusaiba da Fauzan suka shigo, yana rike da ni bai sake ni ba kuma baiyi magana ba,
yace da su su ɗauki su Nasmah su kai su gun Mamie.
suka kwashe su suka fita da su.
ya ɗan dube ni yace
"Ahmad fa?." "Yayi bacci."
nafaɗa ina mai mamakin yadda akayi yasan sunan sa.
a hankali ya saki hannuna ya mike ya taka zuwa bakin kofa ya rufe da key.
da sauri nace
"Ban fita bafa ka buɗe zan fita."
juyo wa yayi ya zo bakin gado ya zauna kana ya miko hannu ya ruko hannuna sannan yafizgo ni na faɗo jikin sa,
hannayen sa duka biyu ya saka ya zagaye ni da su, kokarin fisge jiki na nake da kyau ya daɗa gyara rukon da yamin, kana ya mike dani a jikin sa ya haye gado can kuryar gado ya dire ni.
da sauri na mike zaune nace
"Ka bani key na buɗe na fita."
kwanciya yayi a gefe na a hankali yake faɗin
"Nasan Ummi zata kula da Ahmad ki kwanta a nan bacci zaki taya ni."
cike da tsiwa nace "A sabo da me zan kwan ta anan ni ka bani key na tafi."
ya tsarsa ya ɗaura kan baki tare da faɗin
"Shiiiit ban son hayaniya kwanta nace."
yayi maganar yana tsare gira alamun ba wasa suffarsa na Ya SALEEM ɗin da na sani a da ya bayyana,
sai naji suffar tasa da kwarjinin sa ya cike ni,
kasa nayi da kai na batare da na kwanta ba ban kuma iya cewa komai ba.
a hankali ya mika hannu ya sauke kan nawa yaɗan matse a hankali cikin yin kasa da murya irin na mai jin bacci yace
"Kwanta mana HAMDAHHHH ko ke bakya jin baccin ne."
har cikin ƙwaƙwalwa ta najiyo sautin muryar sa da yan da yakira suna na, karo na farko a haɗuwar mu da shi na biyu ya kira ni da suna na a kuma irin yanayin da yake kira na a da, a duk san da ya kira ni da suna na sai naji kamar shi kalar yadda yake faɗin sunan da ban ne dana kowa.
ya janyo ni tare da gyara min pillow na kwanta gefen sa, a hankali yakuma furta
"A kwai maganin da zan sha cikin dare ina so ki tashe ni ne dan na sha."
mamaki ne ya kama ni wani magani ne kuma ake shan sa cikin dare ban taɓa jiba.
a hankali ya lumshe idanunsa, ido na ɗan kurawa fuskarsa yaɗan rame ya kara haske hancin nan nasa ya daɗa fitowa zarr sajen sa zuwa zagayayyen ɗan gemunsa a kwance suke luf-luf sai sheki suke, san da idanuna ya sauka kan lips ɗin sa da sauri na lumshe idanuna bana so na shagalta da kallon sa.
ɗan numfashi ya sauke kana a hankali ya ɗago hannunsa batare daya buɗe idanunsa ba ya zare hijabin jiki na sannan ya saka hannunsa ya zagaye ni,
nan ma wani numfashin yakuma sauke wa, jin a iya nan ya tsaya bai kuma yin motsi ba,
nakai tsawon awa guda idanuna biyu ganin dai baccin yatafi da shi sai nima na lumshe idanuna babu jimawa bacci yayi gaba da ni...
Washegari nayi nayi ya buɗe min kofa da asuba na tafi yaki, dana matsa yace kada na cike shi da surutu, a ɗakin duk muka yi salla.
koda gari yayi haske Knocking ɗin kofar da ake ne yasa shi mike wa yaje ya buɗe kofar,
Naseem ne da Nasmah sai Mamie da Abbu Abba Ummi da kuma Bappa.
ina ganin su da sauri na gyara zama ta, tare da sun kuyar da kaina kasa cikin jin kunya, Allah ma yaso da hijabi a jikina.
suka karaso cikin ɗakin suna yi masa ya jiki, yace
"Da sauki." cike da jin kunya nashiga gai da su Bappa, suka amsa suna tambaya ta ya mai jiki.
nidai bance komai ba dan kunya yaga isa ta, Ahmad dake rike a hannun Ummi
yashiga mika wa Ya SALEEM hannu yana tsalle a hannun ta alamun zaije gurin sa, cikin gwalaɓen sa yake faɗin Daddy Daddy.
wasu zafafan kwalla ne suka ciko ido na, cike da tausayin ɗan dan nasan gani yake kamar mahaifinsa ne Ahmad.
murmushi Ya SALEEM yayi ya mika hannu ya karɓe sa yana cigana da yi masa murmushi har sai da fararen jerarrun hakoran sa suka bayyana,
ina ganin su Abbu sun fita nima da sauri na mike nabi bayan su, su Nasmah kuma suka zauna a gurin sa.
har dare su na gurin sa har da Ahmad.
a daren ranar ma dana kai masa abinci, hana ni tafiya yayi yasa aka kwashi su Naseem da sukayi bacci a ka kaisu gun Mamie dukan su,
washegari ma har sai da su Abbu suka shigo duba shi kafin na fita, ina mai jin kunyar su...
Yau kam na ɗaura aniyar bazani ɗakin sa ba, da wuri nayi shirin kwanciya ta na haye gado, Ummi ce
ta shigo tarike baki tana faɗin
"Ikon Allah wai ke sai an ce ki kai masa abinci kafin ki kai masa, kwanciyar ki kikayi wazai je ya kula da shi, amma dai kin san ba lafiya yake da shi ba ko."
da sauri nace
"Ummi shi yaro ne da sai an kula da shi dan bashi da lafiya, nima kai na ciwo yake min a bawa Fauzan ya kai masa."
tace "Ungo naki tashi maza in kin je can ɗakin nasa kya sami magani ki sha, yo dan tsiya wazai kullar miki da shi kina matar sa abincin da nake masa ma taimakon ki nake ai kin san dai aikin ki ne, shashancin banza maza tashi ki kai masa."
baki na turo gaba na mike kamar na saka ihu ina buga kafa nayi waje,
nacika har wuya haushin sa ya kamani
"Sai kace wani karamin yaro."
nayi maganar a fili ina jan tsaki.
ina shiga ɗakin na dangwara masa abincin najuya da sauri, har na ɗaura hannuna jikin handle ina kokatin buɗe kofar na fita, najiyo muryar sa haɗe da ɗan tari tari yace
"Zo ki bani magani na a can na sha."
naɗan juyo ina kallon in da yake nuna min saman bedside,
kamar na tafi abina ganin yan da ya damie kirjin sa yana ɗan jan numfashi da taunar lips ɗin sa, sai na juyo a hankali naje na ɗau magani haɗe da gorar ruwa da cup dana gani a gun,
na zo gaban sa na mika masa maganin kana na siyaye ruwan cikin cup na mika masa, ina tsaye ya sha ya miko min cup haɗe da maganin.
ido na shiga rabawa cikin ɗakin ganin ban ga su Nasmah ba nasan har ya sa an kaisu gurin Mamie.
ina aje maganin na juya zan fita nakuma jiyo muryar sa yana faɗin
"Zo ki rufe ni."
koda na juyo naga yakwan ta yaɗan dunkule guri guda da alama sanyi yake ji, baki na taɓe a raina nace
"Ba dole kaji sanyi ba a sanyin nan singlet da gajeren wando ne ajikin mutum gakuma AC na aiki."
na iso bakin gadon na ja blanket na rufe masa jiki, zan juya sai jin hannun sa nayi cikin nawa ya janyo ni na faɗa jikin sa,ina kokarin mike wa ya gyara min kwanciya gefen sa tare da rufe ni da bargon ya janyo ni jikin sa sosai har muna gogar juna.
"Sanyi nake ji." yayi maganar yana tura hannayen sa duka biyu cikin
riga ta yana mai daɗa janyo ni jikin sa, tafin hannun sa sun ɗau zafi rau sai daɗa cusa su yake cikin jiki na yana niman mafakar da zai aje su,
gaba ki ɗaya jikin sa yayi zafi har ina jin zafin yana rasa ni, shiru nayi ina jiyo sautin bugun zuciyarsa, sai fidda numfashi yake da ɗan sauri sauri.
a ɗan tsorace ganin halin da yake ciki nace
"Ya SALEEM ko na kira su Abbu ne jikin ka yayi zafi sosai, ko za'a koma asibiti."
cikin ɗan jan numfashi yace
"A'a su ba zasu iya yimin maganin komai ba ke ce maganin ina jin sanyin sosai kiyi wani abu na daina ji."
ɗan shiru nayi ina tunanin maganar nasa,
kankame ni yayi sosai a jikin sa kana ya cigaba da magana
wan da maganar tasa a hankali yake fita haɗe kuma da sautin numfashi,
"Ki taima min wajen samar min da ɗumi a jiki na na tabbata ke kaɗai zaki iya."
shiru na kuma ina tunanin ta ina zan fara kamar yadda yace ɗin, sake ni yayi
a sannu yaɗan yunkura ya zame singlet ɗin jikin sa, kana ya ɗago ni ya zare rigar baccin dake jiki na, yarage sai bra da kuma wandon rigar.
da fari nayi kokarin dakatar da shi daga cire min rigar da yake yunkurin yi, sai dai ganin yadda yake rawar sanyi da faɗin sanyi yake ji, sai na hakura da kuma ganin bayyi yunkurin cire min bra ba.
rungume ni yayi kamar zai cusani cikin kijin sa yarika mannani da jikin sa, yayin da ya saka fuskarsa gefen wuya na yana juya fuskarsa da manna shi a fatar wuya na.
yarika yin haka har muka kwanta kan katifa,
ya kan kame ni gam-gam ko kyakkyawar motsi ba na iya yi,
magana ya soma cikin jan numfashi
"HAMDAHHHH kar kiyi nesa da ni dan Allah kada ki kara yin nesa da ni, na tabbata kika sake bari na babu ko shakka yanzu kam mutuwa zanyi,
ban san yanda zan misalta miki yadda nake ji cikin zuciya ta ba,
amma ki sani zan iya mutuwa idan kika kuma bari na,
kiyi min alkawarin bazaki sake bari na ba, zaki zauna dani duk wuya duk rintsi ina mai baki hakurin abun da ya faru,
amma ki sani bada sona hakan ta faru ba."
ture sa na shiga yi ina faɗin
"Idan bada son ka ba tilasta ka akayi, ka wulakanta ni ka tozartani kayi min kazamin kazafi da tabo mai muni, ka kazantamin ƴaƴa na kasa mahaifina yayi min korar kare kasa Ummi na ta zubda hawayen ta, kasa na shiga duniya rayuwa ta takusa salwanta har da na ƴaƴa na da basujiba basu gani ba,
Ya SALEEM bazan taɓa yafe maka ba, ka sani ka rabu da ni babu wani yafiya saka nin mu,
wannan komawar auren kaddarar zan karɓe sa zuwa san da zaka gama samin lafiya zan yi tafiya ta nayi nesa da nan bazaka sake gani na ba,
kaje ka zauna da matar ka mai gaskiya wacce bata karya bata kuma kawo maka wani gardi gida da cikin shege gida ba da auren ta, ni kuma zan zauna da nawa halin a haka da kuma ƴaƴan da basa da uba sai uwa a duniya."
da karfi na ke ture sa ina son kwatar kaina, ganin ko kyakkyawar motsi bana yi cikin hannunsa.
sai kawai na saki kuka ina cigaba da ture sa da faɗin
"Ka sake ni ka rabu da ni."
lips ɗin sa ya taune da karfi tare da rumtse idanunsa yayin da sautin bugun zuciyarsa ya karu.
fuskar mu ya haɗe guri guda, yana goga fuskar sa kan nawa, yaɗan fisgo numfashi kana yace
"Kiyi hakuri dan Allah ki mance da kukkanin abun da ya faru cikin duhu babu haske, ki kuma daina dan ganta min ƴaƴa na da mara sa uba."
nayi matukar mamakin jin fitar kalmar hakuri daga bakin Ya SALEEM wai ni yau yake baiwa hakuri, cikin tattausan lafazi da sigar lallaɓi da kuma neman gafara haɗe da sulhu.
ganin numfashin sa yana yin sama-sama da sauri na haɗiye kukan ina faɗin
"Ya SALEEM na kira su Abbu ko Dr Farooq?."
kai ya girgiza min yana ta kokarin janyo numfashin sa, tsoro ne ya kamani sosai ganin yan da yake yi sai na shiga jera masa sannu a kiɗime.
kansa ya ɗan ɗago da kyar yana kallon cikin kwayar idona yakuma yanyo numfashi da kyar kana yace
"Ke ce maganin idan kika yafe min nasan zan warke."
da sauri nace "Nayafe maka nayafe maka Ya SALEEM."
wani murmushi ya sake har sai da hakoran sa suka bayyana, a hankali ya sauke lips ɗin sa kan nawa ya tsotsi baki na sosai kana ya zare bakin sa tare da faɗin
"Nagode." kwanciyar sa yaɗan gyara batare daya sake ni ba, har kuma lokacin numfashin sa bai dai-dai ta ba,
lamo nayi a jikin sa ina jiyo bugun zuciyarsa,
a sannu a