Showing 81001 words to 84000 words out of 125808 words

Chapter 28 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

466

da nake ciki ta juya da gudu tayi waje.
ina ji ana kiran waya ta har ya kase ban iya ɗauka ba, har sau uku kiran na katse wa sai a na huɗu da kyar na mika hannu na janyo wayar, na ɗaga kiran tare da saka shi amsa kuwa, muryar Ahmad naji yana faɗin
"Kyakkyawa ta kina lafiya ya baby na?, hello kyakkyawa ta bakya jina ne."
wani irin hurɗa cikina yayi haɗe da baya na da sauri nakai hannuna na safe baya na tare da faɗin
"Wayyo Allah wayyo Allah Innalillahi'wa'inna'ilaihirrraji'un."
cikin wani irin birkitaccen murya yace
"HAMDAH me ke faruwa me ya same ki me nene!!?."
salati kawai na cigaba da yi batare da na iya furta komai ba,
jin yan da ya birkice yake ta tambaya ta sai na janyo wayar na kashe...
Inna Wuro ta shigo hankali tashe, ta iso in da nake tana faɗin
"Ikon Allah abun yazo kenan sannu HAMDAH Allah ya raba ku lafiya."
ta dubi Faty tace
"Je ki ce wa Zulai ta ɗaura ruwa a wuta, ki wuce kije ɗaki na ki ɗauko hulba cikin magungunan nan ki kawo mata ta zuba cikin ruwan ta girka, ta ɗura cikin flaks, yi maza yanzun nan."
da sauri tayi waje.
Inna Wuro ta shiga karanto addu'a tana shafa min a cikin da bayan da nake ta kukan sa...
ya turo kofar kamar wan da aka jefo sa da sauri haɗe da sassarfa ya iso in da nake ya rungumo ni yana faɗin
"Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un sai da na tambaye ki ko dawa matsala ce kafin na fita kika ce ba komai, meyasa zaki barni na tafi,
tun ɗazu jikina ya bani akwai abin da yake faruwa da ke shiyasa nakasa samin sukuni kan abin da nake, ya zaki min haka HAMDAH,
sannu kyakkyawa ta sannu kinji."
cikin sananin azabar nakuda na kankame rigar sa ina faɗin
"Wash wash wayyo Allah wayyo Allah na wayyo baya na."
Inna Wuro kam waje tayi da sauri, zuwa can ta shigo rike da kofi da hulba mai zafi ciki, har lokacin yana rike da ni a jikin sa.
ta mika masa cup ɗin tace "Bata tasha wannan insha Allah zai zo mata da sauki."
da sauri ya karɓa har hannunsa na ɓari, tace "Bata da zafin shi."
ya zauna ya mike kafafun sa ya saka ni sakiyar cibiyoyin sa, kana yasaka min cup ɗin a baki na yana faɗin
"Sha zaki haihu yanzu." Inna Wuro ta sake fita da sauri
ta koma sashin su, ɗakin Bappa ta shiga yana zaune rike da ƴar karamar kwarya a hannunsa yana ta tofe ruwan maganin dake ciki da addu'a,
yana ganin ta ya mike da sauri yace
"Ya dai?." tace "Har yanzu dai."
kwaryar ya mika mata yace
"Kai mata tasha insha Allah zai ta kai ta."
ta karɓa ta fita da sauri.
a in da ta barmu a nan ta tadda mu, da kan ta ta maso ta kafamin kwaryar a baki tace nasha da bismilla.
sai da na shanye duka kafin ta ɗaga kwaryar.
tana yimin sannu.
wani irin zabura nayi nan take wani gumi yashiga tsastsafo min ta ko ina yashiga ɓari a jikina,
yayin da cikina yashiga murɗa na ba ko kakkautawa.
kai kawai naje juyawa yayin da nakasa iya furta komai.
a zabure ya mike yaɗogo ni cak yana faɗin
"Inna Wuro mutafi asibiti kawai."
kan tace me yayi waje yana isa gurin motar sa ya saka hannu ya buɗe gidan baya yasaka ni ciki,
Inna Wuro ta karaso da ɗan sassarfa tashige motar ta zauna gefe na.
da sauri ya shige gidan direba yaja motar da mugun gudu ciki. hanzari mau gadi ya wangale get yasa kai da mugun gudu.
tamkar zai tashi sama haka yake sharara gudu batare da ɓata lokaci ba muka isa cikin asibiti, yana kashe motar yafito da sauri yazago gefen da nake yabuɗe ya cicciɓo ni, yayi dani cikin asibitin, Inna Wuro tabiyo bayan mu,
nurse's suka nuna masa ɗakin da zai shiga dani,
ya wuce ya dire ni kan gado cikin ɗaga murya ganin Nurse's ɗin sun rufu a kaina yace
"Kuje ku kira likita mace tazo ta duba ta."
nan da nan ma'aikatan sukayi waje batare da ɓata lokaci ba Dr mace ta shigo nurse's biyu na biye da ita.
duk yan da sukayi ya fita yabasu guri domin su gudanar da aikin su sam yaki, da kyar ya yarda ya fita ya tsaya daga bakin kofa yana leka ni.
wani irin nishi na sake tare da faɗin
"Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un."
dai-dai nan kan ɗan yasoma kunno kai,
ai da gudu ya shigo ya rirrike ni ganin yan da hawaye ke zuba min yace
"Sannu HAMDAH kiyi hakuri ina sonki."
kai na jujjuya tare da rike hannunsa da karfi, nace
"Wayyo Allah na zan mutu."
likitan tace "Kada ki dai na nishin ci gaba."
ai bata rufa baki ba sai ga ɗa yafito fut tare da calla kara.
nurse tana kokarin ɗaukar sa ya ture ta ya ɗauke sa ya rungume a jikin sa yana faɗin...........!







Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: 28






Yana faɗin "Masha Allah Allahu Akbar ya iso duniya! ɗana ya iso!!."
yawani sake rungume shi yana juye cike da matsanancin farin ciki mara misal tuwa.
da sauri Dr ta mika hannu ta karɓi ɗan dake ta faman calla kara tace
"Yi hakuri ranka shidaɗe bari a gyara shi, gashi ka ɓata jikin ka da jini, kaɗan bamu guri mu kimsa shi da mamarsa zamuyi mata ɗin ki wannan katon ɗan naka ya karata dole sai munyi mata ɗinki."
kai ya girgiza yana daɗa leko fuskar yaron da ta ke kokarin mikawa nurse.
niko numfashin wahala nake ta sauke wa a raina inayiwa Allah godiya daya raba ni da cikin nan lafiya.
matso ni yayi gaba ɗaya bakin sa yaki rufuwa ya damke tafin hannuna cikin nasa yace
"Sannu kyakkyawa ta Allah dai yayi miki albarka."
kai na rausayar gefe ina mai cigaba da sauke numfashi wahala.
kiss ya sauke min a goshi kana ya juya yafita sabo da maganar da likitar ta sake yimasa kan zasu fara ɗin ki...
ya fito yana ta washe baki,
jama'a sai kallon sa suke ganin yan da yafito jikin sa duk jini,
da sauri Inna Wuro ta iso in da yake tana faɗin
"Ahmad ya haka ya jikin ka da jini."
baki ya daɗa washewa bai damu da jinin dake jikin sa ba cikin sanananin tarin farin ciki yace
"Inna Wuro ta haihu kin ga babyn kuwa bakiji kukan sa ba?."
dariya Inna Wuro tayi tana faɗin
"Masha Allah Allah abin godiya, Allah yaraba su lafiya."
Ahmad yakasa zaune ya kasa tsaye bakin sa yaki rufuwa, mutane kuwa sai daɗa kallon sa suke da jikin sa da ya ɓaci da jini, da yan da bakin sa ya kasa rufuwa.
suna ta shan mamaki wai haihuwa aka yi masa yake ta irin wannan farin cikin.
wayar sa ya ɗaga yana ta daddanna wa yama rasa wazai kira ya faɗa masa abin farin cikin nan.
Rasheedat yakira ya sanar mata.
ai ko batare da ɓata lokaci ba ta iso asibiti da katon akwati, kayan jarirai ne tam ciki, da sabbin jiga-jigan dogayen riguna masu tsadar gaske, da sauran abubuwan bukata wacce mai jego da baby ya kamata suyi amfani da shi idan akayi haihuwa.
ta bawa nurse tace a je a shirya baby, da maman baby,
suna shiga da akwatin.
ta rungume Ahmad tana tsallen murna.
suna tsaye aka fito da jaririn an shiyar sa cikin tsadadden saiti cikin wan da Rasheedat tazo da shi,
har ana rige rigen karɓar sa sakanin Ahmad da Rasheedat da kuma Inna Wuro.
Karshe wa Rasheedat aka mika mawa dan gaban su ta wuce tariga mika hannu.
nurse ɗin tace "Muna tayaku murna an sami ɗa na miji."
Rasheedat tace
"Wayyo Allah masha Allah kawo shi kawo shi."
tana karɓar babyn ta ciro kuɗi masu yawa ɗaurin ƴan 1-1k cikin jakar ta ta mika wa nurse ɗin da ta fito da yaron.
tace tikun cin ta na sanar da abin da aka samu.
da sauri Ahmad yace wa nurse ɗin
"Ya take tana lafiya dai babu wata matsala ko."
tace "Eh babu komai yanzu za'a wuce da ita ɗakin hutu."
kai ya jinjina.
Rasheedat ko
ido ta kurawa yaron cike da matukar farin ciki da ɗoki tace
"Wayyo Allah kyakkyawan yaro, wannan yaron da ala kama da ni zai yi."
dariya Inna Wuro tayi tana lefo fuskar yaron tace
"Tabatakallah masha Allah wannan katon yaro haka duk kai kaɗan ka ka baje cikin kicin nan haka."
Ahmad yasaki dariya mai nuna zallar farin ciki ya mika hannu yace
"Kawo sa na gansa ɗazu ban gansa da kyau ba."
Rasheedat tace "Amma yanzu zaka bani shi ko?."
kai ya gyaɗa mata yana dariya, ta mika masa ɗan daya ke ta rarraba ido kamar ba yanzu yafito duniya ba, idan haske yaɗan dame sa sai ya rufa idon yakuma buɗe wa.
ido ya kura masa babu ko kiftawa sai daɗa washe baki yake,
yarika sumbatar yaron yana kuyi cike da shauki mai bayyana zallar jin daɗi da farin ciki..
dakyar ya mika wa Inna Wuro shi tana karɓar sa Rasheedat takuma caɓe shi.
a hannun Rasheedat yayi ta wa yaron hotuna a wayar sa, cikin kankanin lokaci yawatsa shi wa duniya,
batare da ɓata lokaci ba yafara ɗaga kiran yan taya murna..
sun so shiga su duba HAMDAH aka dakar da su akace tasami bacci su bari sai ta farka da kanta...
duk da haka Ahmad a akai-akai yake shiga ɗakin hutun da aka kai ta yana duba ta..


Sunan a cikin asibitin har wajen karfe uku, gaba ɗayan su babu mai gajiya bare jin yunwa.
sai a lokacin wata nurse tazo tace musu ta farka zasu iya shiga yanzu.
ina zaune a kan gadon da aka kwantar da ni, bayan Nurse ta taimaka min na shiga bayin cikin room ɗin wan da yake a tsaftace, nayi wanka da ruwa mai ɗumi na kimsa jikina, ta ciro min ɗaya daga cikin dogayen rigunan da Aunty Rasheedat ta kawo su cikin akwati, na fito fes dani kamar ba ni bace
ɗazu nake a hargetse,
ina zaune ina shan maltina da madarar da nurse's suka kuma haɗa min, su Ahmad suka shigo.
wani sassanyan murmushi ya sake min tun daga bakin kofa.
fuska na ɓata na turo baki gaba.
suka karaso ciki suna yi min sannu,
Inna Wuro tace
"Sannu kinji ƴar nan Allah ya raba lafiya sai fatan samin sauki kuma,
Allah ya kara miki lafiya."
murmushi kawai nayi mata.
da sauri Ahmad ya amsa da amin amin.
Rasheedat ta maso bakin gadon tace
"Sannu HAMDAH sannu da kokari yaya jikin dai?."
itama murmushin nayi mata a hankali nace
"Da sauki."
wani irin murmushi yakuma sakar min tare da kashe min ido, yaɗan matso ya rike hannuna ya matse cikin nasa yayin da ya gyara rukon babyn da ɗaya hannunsa,
a hankali cikin sassanyan murya mai ɗauke da zallar farin ciki yace
"Madam kinga kyakkyawan yaro na kuwa."
baki na murguɗa masa nace
"Baka tambaye ni gajiyar wuyan da ya bani ba sai ta tashi ma kake ko."
da sauri yace "Sorry kyakkyawa ta na isa gaisuwa ta ta musamman ne."
yayi maganar cikin yin kasa da murya sosai tare da kashe min ido.
da sauri na zare hannuna cikin nashi ganin hankalin su Rasheedat ya dawo kan mu.
yana rungume da yaron a hannunsa sai leka fuskarsa yake Inna Wuro tace
"Ahmad kawo shi a kwantar da shi, yan zu zai bukaci kwanciyar tun ɗazu yake hannu."
yace "A barshi dai zuwa anjima sai a kwantar da shi kamar bacci zai yi ma yana rufe ido."
kai Inna Wuro ta girfiza tare da yin murmushi tace
"Ai yayi baccin yafi a kirga yana farkawa a ganiye yake shi kansa yana bukatar hutu, kada jinin sa ya daɗa masa tsami."
sai da ya sumbaci goshin yaron kafin ya mika mata shi ta kwantar da shi gefe na,
sai a lokacin naga kalar fuskar yaron, kato fari soll da shi kyakkyawa mai kama da ubansa hancin dai nawa ne, dan kalar hancina ne zane a kan fuskarsa, numfashi na sauke a raina nace
"Ka gama wahalar da ni."

Da misalin karfe huɗu likitan ta shigo ta ɗan dudduba ni bayan tambayoyin da tamin ko akwai abin da ke damu na,
nace mata ba komai. tace zamu iya tafi tun da babu wata matsala tare da ni.
bayan magungunan da ta rubuta tace a siya narika sha...
Rasheedat ta ɗauki jaririn shi kuma ya taimaka min muka fito, Inna Wuro na janye da akwatin muka isa jikin mota,
ya buɗe min gidan baya na shiga, kana ya karɓi a kwatin yasaka shi a but,
Inna Wuro ta shiga ta zauna kusa da ni,
ya zaga mazaunin direba in da Rasheedat ta zauna a gefen mai zaman banza tana rungume da jaririn.
a sannu ya ja motar a hankali muka bar cikin asibitin...



Muna isa gida da sauri ya fita ya buɗe min kofa ya ruko hannuna na fito daga cikin motar.
tuni ma'aikatan gidan maza da matan su suka hallaro in da muke, suna yi mana sannu da tambaya ta ya jiki dakuma barka da samun baby,
suka rika rika leka fuskar yaron dake hannun Rasheedat suna sambarka da faɗin Allah ya raya.
ganin ina yamusa fuska yadube ni cike da kulawa yace
"Kin gaji ko muje ki huta."
yajanyo hannuna muna ɗan yin nesa da inda suke ya ɗaga ni cak yayi cikin side ɗin nan da ni.
bai dire ni ko ina ba sai cikin bedroom ɗina a kan gado.
yaɗa go yana bina da wani irin kallo mai cike da tarin so da kauna, a hankali ya kawo fuskar sa daf da nawa, a sannu ya haɗe bakin mu.
wani zazzafar kiss yake ai ka min da zafi-zafi kana ya zare bakin sa yana mai cigaba da yimin wannan kallon,
sai kawai ya rungume ni sam a jikin sa, yace
"Hakika bani da bakin da zan iya yi miki godiya amma ki sani ina sonki ina kaunar ki ke alkhairi ce a rayuwa ta."
sai ya sake ni ya ɗago jin hayanir su Rasheedat a parlour.
Inna Wuro ne tashigo da salla Rasheedat na biye da ita...
nan da nan Inna Wuro ta shiga kiciniyar yiwa yaron wanka, guri ya nima ya zauna yana zaune har aka fara yi masa wankan,
jin yana kuka da ganin yan da Inna Wuro take wanke shi yasa shi faɗin
"Inna Wuro ko dai zafi yake ji?."
dariya tayi tace
"Har ma yasan daɗin jikin sa kenan, ai ko dole a wanke shi sosai acire masa dattin da ya fito da shi."
shiru dai yayi yana kallon sa da alama dai ransa bai yi daɗi ba.
bayan an gama masa an shirya sa cikin wani sabon kaya tuni ya yi bacci cike da jin daɗin wankan da aka masa.
yaso ya ɗauke sa ganin yana baccin ne dai ya hakura ya fita..
Rasheedat ma tafita taje gurin su Talatu da suke kitchen.
Bayan Inna Wuro ta kwantar da shi tace na tashi muje nayi wanka..
wankan towel tayi min sosai nasha zafi kam amma bayan an gama naji daɗin jikina sosai.
Rasheedat ta shigo ɗauke da tray mai ɗauke da kayan abinci kala-kala,
masu in ganta jiki, Inna Wuro ta sani na zauna naci da zafi-zafin sa.
ai ko ina saka kaya nima na haye gado sai bacci...


Da daddare bayan ya maida Rasheedat gida, yadawo yashigo ɗakina yazauna bakin gado ya ɗau jaririn yana ta kallon sa.
Inna Wuro ta shigo ta kuma fita ganin yana cikin ɗakin,
da kyar na sashi yafita dan nasan so take ta kwanta dan tayi shin fiɗar ta a kasa a gefen gado..
washegari Bappa har parlour'n sama ya hauro, Inna Wuro ta kai masa yaron yayi ta masa addu'a da sanya wa rayuwar sa albarka, kana nafito muka gaisa yana tambaya ta ya jiki bana dai jin ciwon komai ko, nace ba komai, yace
"Masha Allah akwai manin da bawa Innar ku zata girka miki kirika sha."
nace "To Nagode Bappa."
ya mika min ɗan yafita, namike na koma ɗaki..
nakira Ukhtee na faɗa mata na haihu gudun kada taji a wani gurin tace ban faɗa mata ba.
Ukhtee tarika murna tace insha Allah zata zo Nigeria da ita za'ayi suna...

Ahmad ne yashigo rike da su Naseem a hannunsa yana ce da su
"Au bakuga yaron bane?."
kai suka gyaɗa masa suna washe baki.
murmushi nayi ganin su, ɗazu Inna Wuro take cemin sun shigo jiya ina bacci ita ta hanasu tada ni.
gado suka ɗale dukan su har da shi,
ya ɗauki yaron yana faɗin
"To ga kanin ku nan yafito duniya kuzo ku ganshi."
tsallen murna suka shiga yi suna faɗin
"Yeee Mommy ta samo mana yaro."
Naseem yace "Daddy kabani shi na rike shi."
yace "To gyara ka zauna na baka shi."
ya zauna har da tankwashe kafafu, yasaka masa yaron kan cinyarsa yana rike da shi batare da yasake masa shi ba..
Nasmah ma tace itama sai dai a bata, ya ɗago shi itama yasaka mata shi kan kafarta.
murmushi nabisu da shi ganin yan da
suke ta murnan ganin yaron. Ahmad ya dube ni yana faɗin
"Ya dai kyakkyawa ta komai normal ko."
baki na turo nace
"Ba kun sami baby kun share ni ba."
ido ya waro yace "Wane mu ai kece tauraron mu bakya taɓa disashe wa."
murmushi nayi shima murmushin ya bini da shi.



A ɓangaren
Hajiya Karima lokacin da labarin haihuwar nan ya isketa hankalin ta yayi mummunar tashi, Musamman da aka ce mata na miji aka haifa,
awani ɓarin zuciyar nata kuma shirin da suka haɗa kan kawar da ɗan ta tuno a fili tace
"Lokaci yayi."
a shirya taje gidan Inna Wuro ta fito mata da jaririn,
ta kafe shi da ido tana dariyar yake da faɗin Allah ya raya..


Ranar da muka cika kwana uku da safe bayan Inna Wuro tayi masa wanka muka shiga bayi nima tayi min, bayan mun fito na shirya cikin riga da zani na atamfa, ina zaune a bakin gado ina cin abinci,
yayin da jaririn ke rike a hannun Inna Wuro.
Ahmad ya shigo, ya leka fuskar yaron yana gai da Inna Wuro,
ta amsa da murmushi tana faɗin
"Gashi nan ai yana so yaji abibcin sa cikin baki, gara dai kabar ta itama ta ci dan ka samu ruwan nono mai yawa."
murmushi mai sauti yayi yace
"Kodai bai sha ba tun ɗazu shiyasa yake nima."
tace "A'a kam wannan acicin yanzu aka cire shi daga bakin nono shidai yafi son ko da yaushe ya kasan ce a bakin ci."
hannu ya mika ya karɓe shi yana ɗan jijjiga shi,
ya dube ni yana faɗin "Madam ayi sauri a ci a bashi yasha dan Allah, Allah sarki ga yana buɗe baki yunwa yake ji."
baki na turo nace "Ai nima yunwar nake ji."
yace "To ai ke babba ce zaki fishi dau riya."
cikin shagwaɓa nace "To Allah sai na fasa cin abincin kuma bazai sha."
ido ya waro yace "Asara biyu kenan, yi hakuri ci abincin ki ni bari na rarrashe shi."
kasa Inna Wuro tayi da kansa cikin yanayin shiga jin kunya.
ya juya yana faɗin
"Inna Wuro bari ayi masa huɗuba."
tace "Yakamata kam yau yau uku."
yayi waje rike da shi yashige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login