Showing 36001 words to 39000 words out of 125808 words
annurin fuska ta nayi ganin ba motar kai su makaranta bane wata motar ne daban ta shigo.
a sannu motar ta isa ta gyara parking a gefen farfajiyar gidan,
an ɗau tsawon minti 10 kafin aka buɗe motar,
ido na waro cikin tsananin mamaki da shiga shoc ganin wan da yafito daga cikin motar, cikin matukar kufula nake kallon sa yayin da yazaga ɗaya gefen ya buɗe, sai ganin Naseem da Nasmah nayi sun fito daga cikin motar suna ta washe ba ki.
"What! me nake gani haka, yaran da nasa a canza musu makaranta domin sa wai bin su yakuma yi?."
cikin matukar ɓacin rai nasaki labulen da sauri na juya nafita a ɗakin na nufi kasa,
da sauri na ke sauka har ina haɗa step cikin hanzari nakarasa sauka nayi waje da sauri.
Suna tsate jikin mota sai zuba masa surutu suke shiko sai binsu da murmushi mai haɗe da dariya yake,
tun kan na karaso in da suke nashiga faɗin
"Kai malam wai meye hakan ne, wai meye gamin ka da yaran nan ne kam?!."
dai-dai lokacin na iso in da suke, kugu na rike cikin masifa nacigaba da faɗin
"Meye da lilin ka na wani shishige musu da kake kana ta wani cusa musu
wani ra'ayi meye nufin ka da su?."
maganar nake a tsai-tsaiye kuma cikin ɗaga murya cikin masifa nakuma faɗin
"Bana bukatar wani ya raɓe su da manufa irin naka kagane ko malam?."
tun da na fara maganar ido kawai ya zuba min batare da yace komai ba, idanun sa kan lip ɗina, a sannu yaɗan yi baya ya jin gina bayan sa jikin mota hannayen sa ya sarkafe a kirjin sa, harshen sa yaɗan zuro waje yalashi pink lip ɗin sa,
har lokacin fuskar sa na ɗauke da murmushi wan da dimple suka daɗa kawata annurin fuskar sa.
cikin kuma ɗaga murya na dubi su Naseem nace
"Idan baku wuce kun shiga ciki ba na rantse sai na ɓaɓɓala yaro anan gurin ku wuce mutafi nace!."
nafaɗa ina nuna musu hanya.
Nasmah tace "Mommy ja mu jo."
ido na waro wato ma na jira su kenan sai sun gama abun da suke.
shiko wani murmuahi yakuma sakewa.
tsayuwar sa ya gyara tare da duban yaran kana ya mai da duban sa kai na sannan yafara magana
"Zaki ɓalla su?."
ya faɗa tare da kuma sakin wani murmushi kana ya ɗan sun kuya yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran ya dubi ko wannen su yace
"Kuje ciki ayi muku wanka kuci abinci ku kwanta ku huta kuyi bacci idan kun tashi kuyi karatu gobe zan tambaye ku karan tun da kukayi kun ji ko?."
kai suka gyaɗa masa suna faɗin
"Tom." yace "Yauwa to maza a je ciki."
Naseem yace "Daddy dakajo anjima?."
kai yagyaɗa yana mai cigaba da wannan murmishi wan da kamar da shi aka gina fuskar sa yace
"Sosai ma zan zo mana."
Cikin hatsala haɗe da ɓacin ran ganin yau ma kamar na ranar da na same su tare da shi a kofar makarantar su, ina nayi musu magana sukayi kamar basu san ni ba,
sai shi da suke ta biye masa suna bashi amsar duk abun da yace musu,
bugu da karin bacin raina kiransa da sunan dana hane su a gabana.
cikin tsawa nace
"Kai Naseem me nace maka waye Daddy'n ka wato bakaji ba ko, ban ce muku kada ku kuma cewa wani Daddy ba, wato duk maganar da nake muku aban za bakwa ji ko, idan naji kasake cewa wani Daddy sai na fasa maka baki,wuce mutafi nace!."
ko da nake masifar harlau idanunsa a kai na, sai ya saki wani murmushin gefen baki yayin da gefen kumatun sa na dama ya lotsa, har kuma lokacin yana rike da kafaɗar su.
a sannu yaɗan sun kuyo yadubi Naseem kana yakuma dubi Nasmah kana yakuma sakin wani murmushin sannan yace
"Naseem Nasmah mene ne ma suna na?."
suka haɗa baki wajen cewa "Daddy Daddy tunan ka."
yace "Kai yaran nan to Allah yayi muku albar ka, to maza ku tafi ciki ayi muku wanka kuci abinci maza kuje."
ya faɗa yana tura keyar su.
ai ko da gudu suka yi ciki suna dariya, ganin rainin wayon nasu da yawa yake wato umurnin sa ma zasubi ba nawa ba. nadube shi tare da rike kugu nace
"Kai malam kana ji ko, kada ka sake zuwa in da yara na suke kada ka sake kasake zuwa in da suke, kada ka sake cusa musu ra'ayin cewa wai kai Daddy'n su ne, kai ba Daddy'n su bane basuma san ka ba, ni ban gayyaci wani acikin lamarin ƴaƴana ba,karabu da harkar yara na idan kuma ba haka ba wlh zan ɗauki tsatstsauran mataki a kanka, kada ka kuskura ka sake zuwa in da yara na suke, kada ka sake yi musu karya kan abun da ba haka bane, bana kara kan haka dan ƴaƴana nice kaɗai uwan su kuma uban su,
dan Allah malam kada ka sake cusawa ƴaƴana wannan gurguwar ra'ayin, ka gane ko?!."
na karashe maganar da nuna masa yatsa haɗe da murguɗa masa baki, na juya a hatsale ganin duk maganar da nake madadin ya shiga taitayin sa sai ma daɗa sakin wannan murmushin nashi yake.
tafiya na soma cikin fushi dan nalashi takwabin yau sai na zane yaran nan tun da har ni zasu gwadan wani yafi ni muhimmanci agurin su har zasu ji maganar sa akan nawa.
sai jin maganar sa nayi daf dani
"Kece uwan su kuma uban su to ya akayi kenan hakan ta faru, ke kika ba kan ki cikin kenan,faɗa min da ma a she mace tana bawa kanta ciki da kanta, dama a she uwa tana bawa kanta ciki ita kaɗai batare da uba ba??."
wani irin juyi nayi jin sautin sa kusa dani batare da zato ko sammani ba, maganar yashige ni tamkar shigar shoc cikin jini na, wani irin mugun kallo na watsa masa tare da jan dogon tsaki, najuya na nufi kofar side ɗina da sauri...
shiko bayana yabi da wannan murmushin kana ya juya yashige motar sa yaja yabar gidan.
Koda na shiga banbi takan su Naseem ba dan nasan koda na yi musu hukuncin danayi niyyar ma bashi zai sa su dai na abun da na hanasun ba,
sai kawai nashige ɗaki nazube bakin gado, kamar an zabure ni kuma na mike na isa gaban mirror in da wayoyi na suke ajiye, number Yakubu na kira, nafara zazzage masa masifa
"Wato Yakubu dana ce kaje ka ɗauko su shine bakaje ba kabar wannan ɗan rainin wayon mutumin wai Ahmad yake ko wa yaje ya ɗau ko su ko?,
idan ka gaji ne kafaɗa sai a sallame ka."
da sauri yatari numfashi na da faɗin
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh yanzu haka ina hanyar dadowa ne ina ma kokarin kiran ki kenan sanar miki sai ga kiran ki, naje makarantar aka ce min yazo ya ɗauke su, ai Hajiya baki sani bama ɗazu da zamu kai su sabon makarantar yazo ya mai da su cikin makarantar yace mutafi mu barsu anan."
ido na waro da ɗinbin mamaki mai haɗe da mugun ɓacin rai,
ban san san da na dakawa Yakubu tsawa ba nace
"Dalla malam ya isa ni da kai na nace ayi abu kan ƴaƴana sannan wani can daban yazo yace ba hakaba kai kuma ka yarda, umurnin sa kabi kenan? ok to ka wuce gidan sa daga nan kaje can yacigaba da baka umurnin!."
nakashe wayar rai ɓace,
"Lallai ma wato ashe ma ba'a kai su makarantar ba shike nan ya hana ko me?."
Afusace na danna number shugaban makarantar yana ɗagawa nace
"Malama ya zan ce ga abun da nake so sannan kuma wani yazo ya hana kuma ku amin ce, to gaskiya daga yau bazama su sake zuwa makarantar ba ma sun fita kenan."
da sauri yace
"Ranki shidaɗe mahaifin su ne yazo yace kada a canza musu makarantar bawai yin kan mu bane."
kashe wayar nayi jin raina yadaɗa ɓaci.
dogon tsaki naja tare da yin kwafa nama kasa cewa komai saboda sabar bakin ciki,sai dai naci alwashin daga yau baza su sake zuwa makarantar ba,
zan mai da su *HAM'NAS* International School Of Science And Technology.
After 1 week
Tsawon sati guda agida suka yishi ranar Lahadi nasa aka kawo musu uniform na *HAM'NAS* International School Of Science And Technology.
washegari Monday da misalin karfe 7 aka gama kimsa su tsaf,
muna tsaye a parking space, daga can na ɗagawa Faty hannu da fito war ta kenan daga side ɗin su, nayi mata alama da tayi sauri, ta Kara so da sauri, tace
"Ina kwana Adda HAMDAH." murmushi nayi tare da faɗin "Lafiya lau antashi lafiya."
"Lafiya lau." tafaɗa tare da
duban su Nasmah tace
"Yau yara sun koma School ɗin mu."
hannun ta Nasmah tarike taɗago kanta tana duban ta tace
"Aunty Faty School inku akwai lilo?."
Faty tace "Eh har da abun zame-zame da mota mai lilo da doki mai lilo."
tsalle Naseem ya tuma yana faɗin
"Yeee nine zan shiga moto in tuka ku."
dariya duk mukayi, na dubi Yakubu dake ta faman goge mota, nace
"Dan Allah kabar goge motar nan haka in ba halitta zaka sake masa ba, kutafi haka kada kasa su makara,kuma dai kaji abin da na faɗa maka wlh aka kuma samin wata matsalar duk wani hakuri da magiyar ka bazai maka amfani ba."
nayi maganar ne cikin jin haushin sa na rannan dan da kyar na hakura da hakurin da yayi ta bani.
da sauri ya bar goge motar yabuɗe marfin motar yana faɗin
"Zo ku shiga Naseem, wlh hajiya in sha Allahu baza a sake samin wata matsala ba, wancan rabar ma tsautsayi ne, dakuma ganin shi babban mutum ne a kasar nan shiyasa ban masa musu ba, dan gudun kada yasa a kwashe ni akai ni gidan maza,
dan musu da babban mutu awannan zamanin haɗari ne."
tsaki naja tare da faɗin
"Kabari zai kai ka karshen ɗauri kenan."
najuya naso ma tafiya ina ɗagawa su Nasmah hannu da cigaba da faɗin
"Kadai ji abun da na faɗa maka."
yace "Kwarai Hajiya, ai daga yau bazaki sake jin wata masala ba."
ban kuma bi ta kan sa ba nawuce part ɗin su Inna Wuro."
A parlour na tadda su Bappa suna breakfast na zauna nima bayan mun gaisa Inna Wuro tazubo min kayan breakfast ta turo min gabana, nan nashiga ci muna ɗan taɓa hira.
Bappa yace
"Mutanen sun tafi makaranta ko?."
nace "Eh sun tafi." Bappa yayi murmushi tare da faɗin "Yanzu kam an bar kuka idan za'a tafi."
"Dama ai rashin sabo ne yanzu kam an saba."
cewar Inna wuro. Bappa yace "Hakane kam wai me yasa ne aka sauya musu makarantar ko yayi musu nisa ne? ko da yake *HAM'NAS* International School yafi shi nisa, me ya sane?."
"Babu tsaro yan da yakama ta a makarantar shi yasa."
nafaɗa a takaice.
Inna wuro tace "Hakkum gaskiya sabo da Allah kam ya kamata su kara sa ido kan ɗaliban su, susan duk wani wan da zai kawo ɗalibai yakuma zo ɗaukar su, duk da dai ranar Malam yace min mutumin kirkin nan ne Ahmad Tijjani Sabil yaje ya ɗauko su ake tunanin ko masu garkuwa da mutane ne, amma dai ya dace sosai su sa ido kan ɗaliban su."
kai kawai na jinjina batare da nace komai ba,akasan raina kuwa faɗi nake
"To waya sani ma ko mai satar mutanen ne dole zan sa jami'an tsaro cikin gidan nan tun da har ya fara shiga cikin gidan nan yana leken asiri."
maganar Bappa dana ji shi ya kashe min zancen zucin danake
"HAMDAH har yanzu banji kin ce komai ba kan maganar mu ta rannan,
Yakamata yanzu kam kiyi aure ki fidda miji na gari kiyi aure, domin darajar ki yadaɗa ninkuwa, kwanakin can munyi maganar nan bakice komai ba,
daraja da kimar hace baya ɓata cika cif har sai tana tare da abokin rayuwa wato mijin aure."
tea ɗin da na kurɓa ne nahaɗiye shi da kyar, sam bana son jin wannan kalmar gaba ɗaya naji nakoshi da abincin a hankali na mai da cup ɗin na aje kana a hankali nasoma magana.
Bappa aure kuma, ai ni bazan yi aure ba rayuwa ta a haka tafi min."
yace "A kul ɗin ki kada na sake jin wannan maganar, a wannan shekarun naki zaki ce baza kiyi aure ba, nutsuwa bata taɓa cika sai da abokin rayuwa, kiyi na zari sosai ga abokan kasuwancin ki da suke zuwa gidan nan, ko wannan Alhj Muttari nan ai mutumin kirki ne ko ranar yaso yimin zan cen sai dai bai fito muraran yayi maganar ba,
in yaso sai ku dai-dai ta kiyi auren ki kamalar ki ta daɗa cika."
Inna Wuro tace
"In ban da HAMDAH ma ai mutane basu taru sun zama ɗaya ba, dan wani abu yafaru da rayuwar auren ki na fari bashi zai sa nan gaba yakuma faruwa ba,ai Allah baya taɓa jarabtar bawan sa da abun da bazai iya ba, duk kuma musulmi an sanshi da karɓar kaddara me kyau ko mara kyau,
ki gode masa ta hanyar kuma kara yin wa ni auren."
"Hmm." kawai nace dan bana jin kamar abun da suke faɗan zai kasan ce, har can kasan kololuwar raina bana jin zan kuma aure, babu abun da natsana a yanzu kamar aure.
meye acikin auren ban da tashin hankali da musifa, in dai har aure nutsuwa ce kamar yan da suka faɗa to gara na tabbata ni bani da wannan nutsuwar.
Duk wani nasiha da jan hankalin da su Bappa suke jin su kawai nake,dan a yanzu babu abun da nafi tsana ma kamar aure!.
sai da na bari suka gama yi min nasihar kafin na mike nace dasu zanje na ɗan kwanta kafin su Naseem su dawo, abin cin da ban karasa ci ba kenan nafito.
ina fita daga side ɗin wata mota na shigo wa cikin gidan, a hankali na ke tafiya har na iso in da motar tayi parking kasan cewar dole sai nabi ta hanyar kafin na wuce side ɗina,
ina isa dai-dai in da motar take sai ji nayi an.......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:55 - Ummi Tandama😇: Da sauri cikin matukar tashin hankali tun kan ya karasa abun da zai faɗa na ce "Tamutu tamutu ko?!!."
nayi maganar hankali a mugun tashe dan nagama tsinkewa da yan da naji yake maganar.
ya ce "A'a Madam ba mutuwa tayi ba, dama bata da lafiya ne?,
tun zuwan su School ɗin Aunty'n su tace taga yanayin ta kamar batajin daɗi, shine ta tambaye ta sai tace mata wai kan ta keyi mata zafi, to tafita taje ta ɗauko magani a office kenan ta dawo ta samu tana rike da kanta tana kuka tana faɗin kanta zafi, kan tayi aune ma ta faɗi kasa a sume, tun ɗazu muna asibiti ban so kira na sanar ba sai ta farfaɗo amma har yanzu likitoci sun kasa shawo kan ta."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un wlh lafiyar ta lau ta bar gida."
na furta da karfi yayin da jikina ke cirawa cikin azama na duro a gadon wayar na kare a kunnena ina tambayar sa wani asibiti ne, yana faɗa min nakashe wayar batare da na tsaya sauraran abun da yake cigaba da faɗa ba.
wardrobe na buɗe na janyo mayafi na takalmi mara tudu na saka da sauri nafita na nufi ƙasa, bibbiyu nake haɗa steps,ina sauka na nufi kofa har ina haɗawa da sassarfa.
su Talatu suna zaune cukin parlour'n da sauri suka mike ganin yanda na sauko a firgice, tambaya ta me ke faruwa suka shiga yi suna biyo ni a baya,
tuni nayi waje ban tsaya basu amsa ba, har parking lot suka bini, suna tambayar abun da ya faru. sai a lokacin na ce da su "Nasmah ce ke asibiti asume."
salati suka shiga yi suna tambayar garin yaya.
wan nan karon ban tsaya basu amsa ba dan ji nake tsayuwa basu amsa ma ɓata lokaci ne.
kan kace me sabbin Security ɗin da aka zuba cikin gidan sun iso in da muke, ganin yan da su Talatu suketa rafka salati, suma duk tambayar da suke ban tsaya basu amsa ba, su Talatu ne suka sanar musu abun da ke faruwa.
Yakubu nashiga kwaɗawa kira,
da sauri haɗe da gudu yafito daga cikin ɗakin su, da sauri na shige cikin mota, yana ganin haka ya koma ɗakin da sauri ya fito rike da makullin motar cikin hanzarin yashige motar.
cikin matukar da muwa da rawar murya nace
"Yakubu kayi sauri ko ka bani key ɗin motar ni naja."
key yayi wa motar tare da figar ta aguje, da gudu mai gadi ya buɗe get muka fita a gidan, sai da muka haura titi kafin yake tambaya ta in da zamu nafaɗa masa sunan asibitin.
duk gudun da Yakubu yake gani nake kamar bayayi asibitin tayi min nisa.
Number da aka kira ni da shi aka sanar min da tana asibitin na kuma kira wayar tayi ta ring ba'a ɗaga ba,
kuka ne naji ya zo min nayi saurin toshe baki na a raina nake faɗin
"Shike nan ta mutu."
kokarin mai da kiran nake dai-dai nan najiyo muryar Yakubu yana faɗin
"Hajiya mun iso."
da sauri na ɗago dan ban san har mun iso ba.
da sauri na buɗe motar na fito batare da na jira faɗin da yake bari ya zo ya buɗe min motar ba.
da sauri haɗe da sassarfa nayi cikin asibitin, a kofar shiga cikin parlour'n asibitin na haɗu da Aunty'n su Nasmah tana kokarin fitowa cikin sauri take tafiya da ka ganta gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake.
tana gani na ta juya da sauri tana faɗin
"Madam ta farfaɗo amma tana ta kuka."
da sauri nabi bayan ta ina faɗin "Ina take."
tun da ga cikin parlour'n nake jiyo kukan ta, da gudu nanufi kofar room ɗin da nake jiyo kukan ta ciki,
wasu daga cikin ma'aikata asibitin sukayi yunkurin dakatar da ni, ban ko saurare su ba
na tura kofar na sa kai ciki.
ina ji Yakubu daya biyo ni yana sanar musu da ko ni waye.
Likitoci har guda uku a tsaye a kan ta suna rirrike da ita sai ihu take tana bige-bige, da gudu na isa in da take na kusa sakanin su na rungume ta,sai kawai nima na fashe da kuka ina faɗin
"Nasmah me ya same ki, me ya same ki Nasmah?!!."
kuka sosai na ke ina rungume da ita, itama kukan take tana ta fisge-fisgen nan kamar wacce bata cikin gayyacin ta.
Turo kofar aka yi da karfi yana gaba wani na biye da shi.
in da muke suka karaso da sauri, wan da ke biye da shi ɗin ya dubi likitocin da ke cikin ɗakin yana faɗin
"Wai har yanzu bakuyi wani abu a kai ba?."
cike da girmamawa sukace "Sir muna