Showing 60001 words to 63000 words out of 125808 words
tana ɗaga mana hannu.
muna isa gida kiran Hajiya na shigo wayata tayi min sannu da hanya nayi mata godiya.
Talatu tayi wa su Naseem shirin islamiyya suka tada daru su sam Daddy'n su ne zai kaisu ba direba ba, haka ya ɗibe su a mota ya kaisu makarantar,
ko da lokacin tashi yayi ma shi yaje ya ɗauko su....
da daddare ina kwance har bacci yafara ɗauka ta naji karar wayata, na ɗau wayar ganin mai kiran nawa sai na ɗaga da ɗan sauri nakai wayar kunne tare da yin sallama.
daga cikin wayar Hajiya tace
"HAMDAH kuna lafiya kada ace dai na tashe ki a bacci?."
murmushi nayi nace "A'a babu komai wlh lafiyar mu kalau."
tace "To madalla a gaida yaran."
nace "To mun gode sai da safe."
ina sauke wayar sai ganin mutum nayi tsaye a kaina, yaɗan tsura min ido sai kuma ya tsunkuyo kaina ya shafo gefen fuska ta, da sauri na ruko hannun sa nace "Kabar taɓa ni."
ido yakuma tsura min kana ya saki murmushi a hankali kamar maiyin raɗa yace
"Nataya ki bacci?." da sauri nace "A'a." sumbatar kumatu na yayi yami ke yana faɗin
"Kiyi bacci mai daɗi sai mun haɗu a mafarki."
baki na murguɗa lalkausan murmushi
ya sakar min ya juya yafita tare da jamin kofa...
Bayan kwana biyu yau ta kasan ce ranar asabar,
da safe ina zaune a ɗaki ya shigo cukin ɗakin cikin shiga ta alfarma yayi kyau sosai ga annurin fuskar sa da ke abaytane mai karawa fuskarsa kyau,
ya karaso ya zauna a gefe na,
plt ɗin da ke gabana mai ɗauke da kayan fruit mai sanyi ya kai hannu ya ɗau fork ɗin da nake ci da shi ya ɗiba ya kai bakin sa, ido ya numshe yana taunar sa sai kuma ya buɗe idon a kaina yace
"Kice kayan daɗi kike ci shine kika ɓoye a ɗaki kika barmu can parlour Babu ko ɗan tayin nan ma."
fuska na yamutsa a kasan raina nace
fruit ɗin ne shine kayan daɗin."
"Kayan daɗi ne mana baga shi kin ɓoye saboda kar muci ba."
ido naɗan waro dan banyi zaton maganar tawa ta fito ba sai kuma na taɓe baki.
ya ɗibo fruit ɗin ya kawo shi saitin baki na yace "Buɗe baki na sami kyakkyawa ta."
fuska na kawar ina tura baki gaba, murmushi mai sauti yayi yace
"To ni saka min gashi na buɗe baki na."
ya buɗe bakin wanda jerarrun fararen hakora sukayiwa kawanya ciki, harshe mai taushi yakara daɗa masa kyau gwanin burge wa.
fuska na ɓata na kai hannu batare da na ɗau fork ɗin da ya ci da shi ba naɗau yankakken ayaba na kai bakina, zaman sa ya gyara da kyau ya janyo ni jikin sa, hannayen sa duka biyu ya saka ya tallafo kaina da kyau in da bazan iya kwatar kaina ba,
da sauri na rufe idanuna ganin yana kokarin jefa fitanannun idanun sa cikin nawa,
saukar lips ɗin sa naji kan nawa kafin nayi wani yunkuri sai jin ɗumin harshen sa nayi cikin bakina,
a hankali cikin wani irin salo yake juya harshen sa cikin bakina, a sannu yashiga tsotsar ayabar haɗa da harshe na, wani irin fitinannen numfashi yake fiddawa da sauri da sauri ya ɓata tsawon mintu goma a haka, sai da ya tsotsi ayabar nan ta narke duka ya shanye ta. kana
a hankali yazare bakin sa a tare muka saki numfashi dukan mu,
baya nayi na jigina da jikin gado tare da hararan sa dan naka sa magana,
shiko murmushi yayi tare da kashe min ido yana mai jan numfashi da kyar yana mammatse fitinannun idanun sa da suka sauya kala, baki na turo gaba na kawar da kaina gefe.
a hankali ya shafo gefen fuskata yace "Kin wa hajiya alkawarin zaki je ranar weekend sai kirana take tun sassafe."
shiru nayi ban ce komai ba, dan jiya nima ta kira ni nace mata zamuzo ranar asabar ko lahadi.
yace "Sai ki tashi ki shirya ki cika alkawarin da kika yi mata muna jiran ki a kasa."
ya mike tare da sumbatar goshina ya juya yayi waje.
numfashi na sauke a hankali na mike na faɗa bathroom.
cikin minti 25 nagama shiri nafito na same su a kasa, ban ko kalle sa ba duk da tulin kallon da yake ta aika min da murmushin sa mai bayyanar da ainahin kyan fuskarsa, nayi waje suka biyo ni yana faɗin
"Ba jira ne Madam?."
nam ma ban tanka shi ba.
har muka shige mota yanata zolaya ta da jana da wasa wani bin,
idan yayi abib dariya sai na sinci kaina da yin murmushi amma aɓoye bana bari ya gani.
a haka muka isa gidan.
Yana dai-dai ta parking ya dube ni tare da ruko hannuna ya matse cikin nashi, yaɗan rankwafo ya sauke min kiss kan kumatu sannan ya ɗago,
fuska na ɓata na turo baki gaba
murmushi yayi yaɗan ja lip ɗin na kaɗan cikin kasa da murya yace
"Idan kika turo shi gaba kyau kike karawa, kamar nayi ta tsosa."
hannun sa na bige ina murguɗa bakin
ƴar karamar dariya yayi yace
"To ai hakan ma duk kyan yake kara mi."
hannu na yarfe nace "Ni ka kyale ni."
dariya ya kuma har yana tafa hannu.
sannan yace "Ni zan juya daga nan zanje wani guri idan kun shiga kice wa Hajiya zan dawo zuwa anjima."
ban amsa shi ba nayi sauri na buɗe motar nafita, su Naseem suka biyo ni.
Da sallama nashi cikin parlour'n kamar rannan mutane ne tam ciki,
yau kam ina yin sallama suka amsa har da yi min sannu da zuwa,
wasu ƴammata guda biyu suka dube ni da murmushi suna faɗin
"Sannu da zuwa Aunty HAMDAH matar Yaya Ahmad."
da sauri sauran ƴan cikin parlour'n suka waigo, wasu na faɗin
"La itace HAMDAH mai *HAM'NAS* Co Petroleum Nigeria Limited."
wasu daga cikin su suka basu amsa da faɗin "Eh fa itace."
nan suka shiga yimin sabuwar gaisuwa.
murmushi nayi ina faɗin "Sannun ku."
wata dake gefen su tana ai kin danna waya taɗago taja dogon tsaki tamike tabar cikin parlour'n, da mamaki nabi bayan ta da kallo, inata son tuna in da na taɓa ganin ta,
cikin kankanin lokaci na tuna anan gidan na santa ranar da na fara zuwa, itace wacce ta yi mana iso gurin Hajiya.
maganar ɗaya daga cikin ƴammatan nan naji tana faɗin
"Bari nayi miki magana da Hajiya."
nace to. ta shiga jim kaɗan ta fito tace "Kishiga tana ciki."
naja hannun su Naseem..
nayi sallama bakin kofar daga ciki ta amsa a hankali na shiga ina mai kara yin wani sallamar.
tana hakimce kan wani tattausan dadduma ta kishin giɗa da wasu filulluka na alfarma.
fuska ta faɗaɗa da murmushi tace
"A'a manyan baki ne haka, sannun ku da zuwa ku karaso nan ga gurin zama."
ta nuna min gefe da ita.
na karaso na zauna tare da gaishe ta ta amsa tana washe baki da shafa kan su Nasmah.
tace "Ina shi Ahmad ɗin?."
nace "Yace nace miki zai dawo anjima yatafi wani guri ne."
kai ta jinjina ta mike zaune.
hira tari jana dashi, niko sai binta da murmushi nake wani bin kuma na amsa mata, ina mai jin nauyin ta.
har aka kira sallar azahar muna zaune tana ta jana da hira, na ɗan muskuta nace mata zanyi sallah.
tace nashi ga bayin nan cikin ɗakin,
bayan nayi al'wala na fito na tarar bata ɗakin har da su Naseem, nagabar da salla, ina zaune ina tasbihi ta shigo wata na biye da ita da tray mai dauke da kayan abinci, ta dire a gefe na sannan ta fita.
Hajiya ta zauna tana faɗin
"Yaran nan sun sami ƴan uwan su yara suna can suna ta kan wasa."
murmushi nayi nace
"Ai su Naseem akwai son wasa."
tace "Yaran kenan ai kai babba wace wasa zaka tsaya yi, ai sai dai in akwai wasan nera to kaɗai zaka tsaya kayi shi."
"Uhm." kawai nace badun da fahimci karin maganar nata na karshe ba.
tray'n abin cin ta tura min gabana tace naci.
ɗan sakurar abincin nayi dan bana jin yunwa, na tura tray'n gefe ina faɗin
"Nagode."
tace "Nayi zaton zakici da yawa dan gidan nan babu kaɗan komai mai yawa ne."
"Nakoshi ne."
nafaɗa a takaice tare da yin murmushi..
Zaman ta ta gyara da kyau kana taɗan sunkuyo in da nake a hankali ta soma magana
"Ai ita kogi bata ki yayyafi ba komi akwai ɗin ka zaka so kari, ko ba haka ba?."
kai na gyaɗa ina cigaba da murmushi bawai kodun sanin inda batun nata ya dosa ba.
baki ta kuma washewa tana mai jinjina kai kana ta daɗa gyara zaman ta
kana a hankali tace
"HAMDAH."
takira sunaan, na amsa tare da duban ta jin yanda ta kira sunan nawa a sama, tace "Kuna lafiya dai babu komai ko."
kai na gyaɗa ina mai kuma amsa sabuwar gaisuwar nata.
ta mike ta fita jim kaɗan ta dawo, ɗauke da plt ta dire a gabana,
ta ce "Ki ci wannan wata kila zai fi miki sauran." kallon plt ɗin nayi tare da yin
murmushi dambun naman kaza ce a ciki sai tashi da kamshi yake,
nace "Nagode."
ɗan shiru tayi taɗan waiga gefe da gefe kamar mai duban wani abu sai kuma ta kuma mai da hankali ta kaina cikin yin kasa da murya tace
"Akwai maganar da nake so muyi yanzu mai mahimmanci ne zaɓi kuma a gare ki, moriya da amfanuwa duka."
kai na jinjina ina mai sauraren ta.
tace "Shi arziki kogini idan ka yi tsayuwan daka wajen niman sa samun sa bazai taɓa baka wuya ba,
kina da kuɗi kin san daɗin su na tabbata ayanzu irin su dubu idan zaki samu ba zaki ki son su ba."
shiru nayi ina sauraran ta cikin rashin fahimtar in da batun nata ya dosa.
a hankali ta mike ta isa can gaban gado ta ɗau Laptop saman bedside ta dawo in da nake ta zauna agefe na akasa in da nake zaune, kana ta kunnan Laptop ɗin ta daddannan sannan ta aje a gabana.
hotuna da bidiyoyin kaddarori ne suka rika bayyana ciki, manya manyan gine gine gidaje masana'antu daga nan gida Nigeria har kasashen ketare,
ido na ware ina kallon tulin tarin dukiyar, da bansan ma'anar nuna min shi da take ba.
zuwa can ta saki dariya tare da rufe Laptop ɗin tace
"Wannan kaɗan ne daga cikin dukiyar Alhaji Tijjani Sabil wan da ayan zu yazamo mallakin Ahmad Tijjani Sabil, bayan tulin dukiyar da shi kansa Ahmad ɗin ke da shi, HAMDAH."
takuma kiran suna na tana mai dubana da kyau sannan tace
"A rayuwar nan na yanzu baka da burin daya wuce kazamo abin kwatance aduk in da kake duk in da ka shiga arika nuna ka, kayi fintinkau cikin kawayen ka, misali kamar ke a yanzu da kika zamo abin faɗa,
na tabbata kina so kida ɗa fin haka,
idan kuma kinso a yanzu zaki fi hakan cikin sauki zaki daɗa mallakar dukiya mai tarin yawa, ki ɗaukaku a duniya, cikin sauki idan kina da bukata a yanzu zaki iya zamowa haka."
shiru nayi ina sauraran ta da ɗinbin mamaki cikin raina, taya za'ayi nasami wannan dukiyar datake ta misalta min shi ɗinnan? ai ko lokacin da nasami dukiya ban samu ta sauki ba sai da rayuwa ta dana ƴaƴana takusa salwanta, amma kuma take cewa zan sami ninkin ba ninki kuma cikin sauki, to ni wace ɗaukaka kuma ɗaukakar da Allah yayi min yanzu ma na gode masa..
katse min tunani tayi da faɗin
"Kin shiga tunanin ta ya hakan zai kasance ko?."
sai ta saki wani dariya tare da cigaba da faɗin
"Cikin ruwan sanyi ma kuwa, idan kika haɗa kai dani zakiji daɗi idan kuma kika bijire zaki faɗa cikin halaka, ina nufin rayuwar ki zata salwanta."
ido na waro da sauri na ɗago na dube ta,
wani irin hatsabibin murmushi ta sake kana ta girgiza kai tace
"Kwarai kuwa,
kin auri Ahmad bawai dun kina son sa ba sai dun son da shi yake miki, nasami labari sosai kan cewa bakya son shi kuma ina da tabbacin cewa har yau ba son na shi kike ba,
me zai hana muhaɗa karfi da karfe kibi ta wannan hanyar kici moriyar dukiya mai tarin yawa, ki kara kan naki, ki daɗa zamowa abin kwatance a duk faɗin kasar nan da ketare baki ɗaya."
Zuwa yanzu maganar nata yafara jefari cikin firgici da tsoro dan na rasa me take nufi dahar zata yi min barazana da salwanta rayuwa ta.
ɓari jikina ya soma a raina nake faɗin
"Innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un,abin da nayi gudu shiyake kuma tunkaro ni."
maganar ta najiyo tana faɗin
"Zaɓi yarage naki idan kin so a yau zaki iya aiwatar da komai."
ta mike tsaye taje taja drower har ta dawo ta zauna in da ta tashi kaina na sunkuye, yayin da firgici mai tsanani ya shige ni, sai nanata kalmar
Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un nake.
"Ungo karɓi rike wannan." da sauri na ɗago ina duban abin da take mika min ɗin
wani kullin magani ne cikin laida, hannu na na ɓari na karɓa tare da kura masa ido.
tace "Wannan maganin shine hanya mafi sauki da zakibi ki mallaki dukiya mai yawa ki kara kan naki,
ki zuba wa Ahmad a cikin abinci ko sha, idan yaci zai kwanta jinya ba kada kiji tsoro dan ko
likitoci bazasu taɓa gane wani abu yaci ba, kuma baza'a taɓa gane ciwon me yake damin sa ba a haka zai tafi daga nan kuma zance ya kare, zamu raba dukiyar biyu ki ɗauki rabi na ɗau rabi,
tun rabar dana sami labarin auren ku na kasance cikin farin ciki dan na tabbatar zaki iya aiwatar wa tun da ba son shi kike ba."
wani irin ɓari hannuna da ilahirin jikina suka ɗauka cikin tsananin mamaki tashin hankali na ɗago na dube ta murya na rawa nace
"Kashe shi za'ayi." wani irin kafurin dariya tayi tace
"Kwarai kuwa nasan aiwatar da hakan bazai baki wuya ba tun da bason shi kike ba, ko da ace kina son shin ma so ɗin banza kuɗi ai yafi miki shi, yana mutuwa kuma zaki sami wanda yafi shi."
gaba ɗaya ƙwaƙwalwa ta ya tsaya cak ya daina ai ki firgici da tashin hankali su suka dabaibaye ni,
ta ko ina ɓari yake a jiki na.
kisa nice zan kashe mutum da hannuna wai uwa ce ke son gusar da ɗan ta anya ba mafarki nake ba?, da sauri na mussuke idanuna ina mai ware su a kanta maganar ta na natsinkayo a sama
"Kada ki ɓata min shiri yin hakan babban kuskure ne, na tabbatar miki rayuwar ki dana ƴaƴan ki zasu salwanta,
kiyi tunani ki dubi tulin tarin dukiyar nan ace sudaɗa zamowa mallakin ki ki zamo abin nuni da faɗa a duniya, ba pillow zaki danne kansa da shi ba ba kuma wuka zaki daɓa masa aciki ba, wannan kaɗai zaki zuba masa cikin abinci daga nan shike nan arziki ya dawo naki."
hannuna mai maganin ta rike ta kalle ni tana dunkule min maganin cikin hannuna, cike da karfafa guiwa ta cigaba da faɗin
"Kada kiji tsoron komai ko ki tsaya tunani ki rika tuna tulin tarin dukiyar nan ki ai watar kada kiji komai babu wan da zai zarge ki dan babu ta in da za'ayi a gane, kuɗi yafi komai a rayuwa."
maganin ta karɓa a hannuna taɗau jakata ta jefa shi ciki tarufe tana faɗin
"Ki kula kada a sami matsala faruwan hakan babban matsala ce ga rayuwar ki."
kai na girgiza da sauri, murmushi tayi zata kuma magana akayi sallama daga bakin kofa, zaman ta ta gyara da sauri taɗan matsa gefe,
Ahmad ne rike da su Naseem a hannun sa suka karaso suka zauna,
fuska ta faɗaɗa da murmushi tadubi Ahmad tana faɗin
"Sannu Ahmadu numfashin Sabil an dawo."
yace "Eh Hajiya bar ka da gida."
tace "Yauwa Ahmad Allah yayi albarka ya tsare gaban ka da bayan ka."
"Amn amin." ya amsa yana mai murmushi. ya mike ya dube ni sannan yace
"Muje ko yau kinyi wa Hajiya wuni."
da sauri tace "A'a kam sai dai rabin wuni dai, tamayi kokari a hakan dan tafi wancan Rasheedat ɗin mai isa da kafafa."
murmushi kawai yayi, yayi waje tare da ɗaga kiran da ya shigo wayar sa yanzu.
jiki a sanyaye na mike, itama ta mike tare da ɗaukar jakata ta mika min sannan ta dube ni da kyau tace
"Ki kula ki ai watar da komai ya tafi dai-dai kada a sami wata matsala, ni zan kula da komai daga baya, ki kawar da abin da bakya so ki kuma sami karin dukiya mai yawa, ki ɗaukaka a duniya, kada kiji komai zan tsaya miki."
ta dafa kafaɗa ta tana mai kuma jaddada min.
yau ma har kofar parlour ta yi min rakiya tana,
ina dai-dai zama ta cikin motar na sauke numfashi da karfi har sai da ya juyo ya kalle ni.
a hankali na maida baya na na jingina da jikin kujerar motar, gaba ɗaya jiki na ya gama sanyi.
gefen da nake ya waigo ya dube ni kana ya mai da duban sa kan titi yace
"Madam ya dai?."
idanuna na lumshe batare da na amsa shi ba..
har muka isa gida idanuna a lumshe yake yana gyara parking najiyo Muryar sa daf da ni yana faɗin
"Ko na ɗauke ki nashi da ke ne?, naga kamar kin gaji."
a hankali na buɗe idanuna na jiki a sanyaye kai hannu na buɗe marfin motar nafita..
Ina shiga bedroom na wuce bathroom da sauri na shiga tube kayan jiki na dan gaba ɗaya wani irin a zabebben zafi nake ji, tun daga ta ciki na har waje.
na daɗe cikin ruwan sanyi kafin na fito, duguwar riga mara nauyi na zura a jiki na batare da pant ko bra ba,
na zauna bakin gado yayin da maganar Hajiya ke tayi min yawo cikin kwakwalwa.
jakata na ɗago na buɗe na ciro maganin ina juyashi a hannuna yayin da bugun zuciya ta ta karo.
"Innalillihi'wa'inna'ilaihirraju'un, me yamata haka take son kashe shi? sabo da kuɗi?, kuɗin da zaka mutu ka barshi meye haka da tsanani ɗanka ka kashe shi da kanka sabo da son abin duniyar da zaka mutu ka barshi,
ba zan iya kashe mutum ba ba zan taɓa zamo sanadin wata raiba, da ma nasan babu komai cikin rayuwar aure face kunci da bakin ciki,
gani na kuma faɗa wa cikin wani ahalin da suke son ganin bayan junan su, meye nawa da zasu so jefani ciki dama ni na sani a haka rayuwa ta zata kare."
wani irin kuka ne mai matukar tsuma rai ya kwace min, sai na toshe baki na nashiga rusar kukan.
a hankali aka turo kofa, da sauri na dunkule hannuna mai rike da maganin nayi baya da shi da sauri na ɓoye shi a bayana,
ɗaya hannuna dana toshe baki na nashare hawaye na da sauri