Showing 48001 words to 51000 words out of 125808 words
yimin nasiha, ina dai jin sa amma gaba ɗaya hankali na baya gunsa.
batare da ɓata lokaci ba Faty ta dawo rike da takardan, ta mika min nikuma na mikawa Bappa ya amsa da sauri ya fita.
nakai tsawon minti goma zaune a gun daga bisani na mike a hankali na fita na koma side ɗina.
koda na shiga bedroom ɗina akwatunan dana gansu a parlour'n nan su nagani jere cikin ɗakin,
kan gado nabi da kallo, wani dankararren leshi ne haɗe da gyare da jaka da takalmi,da sarka da ƴan kunne da abun hannu mai sheki da ɗaukar ido,
turo kofa akayi da sallama Hajiya Rahama ne ta shigo ta dube ni tana faɗin
"Ƴan uwan Ahmad suka kawo akwatunan nan kina bacci yasa ba'a ɗagaki ba, amma anyi musu sallama da tukuici na musamman, na sending musu 500k ta account ɗin su, an haɗa su da drinks katon ashirin haɗe da cincin da diblan da akayi jiya na ba'i sai dai babu yawa tun da ba'a san da zuwan su ba, boket shida ne kawai, yanzu nasa a karayin wani saboda wan da za'a baiwa ba'i, hakan yayi dai ko?."
nace "Yayi sosai ma bani account number ki na samiki kuɗin."
tace "A'a nima gudumawa ta kenan kibarshi, ga kaya nan an cire miki sai kiyi wanka ki saka."
nace to tare da yi mata godiya, tajuya ta fita,
na tuɓe hijabi na na shige bayi, wanka sosai nayi na kimsa jiki na da kyau sannan na fito,
gaban mirror na zauna nashiga mulke jikina da mayuka masu daɗin kamshi haɗin hajiya Lubabatu,
simple make-up nayi amma nayi kyau sosai dan nasha gyara sosai ga kyan
halitta ta da ubangiji yayi min.
a hankali na mike na isa in da kayan yake na ɗago su na soma sakawa, ɗin kin leshin riga da zani ne tsarin ɗin kin yayi, bayan na saka kayan na ɗau sarka da ƴan kunnen nazo gaban mirror na saka,sannan na murza ɗaurin ɗankwali, a hankali nabi jikina da turare natsaya ina kare wa kaina kallo tacikin mirror.
Kamar daga sama najiyo sautin babban masallacin unguwar mu ana faɗin "Fatihaaaa Allah yayi aure ya ɗauru Allah ya bada zaman lafiya da zuriya ɗayyiba."
kirji na ne yayi wani irin bugawa da har sai da na kai hannuna na dafe kirjina, wani irin jiri ne ya ɗibe ni na kwalla kara tare da zubewa kasa na rushe da kuka mai matukar tsuma zuciya tamkar zan shiɗe.
Faty ce ta shigo ta sha wankan ta rike da ɗankwali a hannu Aunty Nasiba ta dube ta cike da zulaya tace
"Duk a cikin gayen ne haka rike ɗan kwali a hannu."
dariya tayi tana faɗin
"Gun Adda HAMDAH zani ta ɗaura min."
ta haura sama ta tura kofar da sallama da sauri ta karaso cikin ɗakin ganin yan da na haɗe kai da guiwa nake ta faman rusar kuka,
tashiga girgizani tana faɗin
"Adda HAMDAH me ya same ki?."
ban iya bata amsa ba sai sautin kuka na daya karu,
a kiɗime ta sake ni tayi waje, tun daga saman step tashiga kwaɗawa Inna Wuro kira, sabo da hayaniyar jama'a yasa Inna Wuro bata jiyo kiran ba, da sauri Faty ta karasa sauka tazo in da Su Inna Wuro ke zaune ta ruko hannun ta tana yi mata nuni da sama da faɗin
"Adda HAMDAH."
"Me ya sami HAMDAH!?." Inna Wuro tayi tambayar hankali tashe ganin yan da Faty'n ta ruɗe tana nuna hanyar sama ta mike tsaye da sauri ta haye sama Faty na biye da ita.
Ina durkushe a gurin har lokacin kukan nake kamar raina zai fita. hankali tashe Inna Wuro tashiga faɗin
"Subhanalillahi HAMDAH lafiya me yasame ki?."
ta ɗago kaina dana haɗe da guiwa, sai kawai na zube a jikin tare da kuma fashewa dawani sabon kuwa, cikin muryar kuka sosai nake faɗin
"Inna Wuro wai da gaske an ɗaura auren Inna Wuro ina jin tsoro suma zasu cutar dani."
bayana tashiga bubbugawa jiki a sanyaye ta gyara zaman ta a kasan tadaɗa kwanto da kaina bisa kafar ta tashiga rarrashi na da kalamai masu kwantar da hankali haɗe da natsiha mai shiga jiki da karfafa guiwa. har sai da taga nayi shiru hankali na yado jikina kafin ta fita a ɗakin ta barni ni da Faty da itama tagama shan kukan ta...
Har yamma ina daki ban fito sai wajen sallar magriba bayan nayi wanka na sauko kasa, nan na tadda mutane sunanta watsewa, Hajiya Rahama da Aunty Nasiba nata sallamar mutane da kayan tsaraba.
nan na shiga tayasu har jama'a suka watse, yarage Hajiya Rahama da Aunty Nasiba da Hajiya Lubabatu,
bayan sallar isha Hajiya Rahama da Hajiya Lubabatu sukace zasu tafi, har gurin mota muka raka su ni da Aunty Nasiba, nayi ta musu godiya sosai bayan na sallami Hajiya Lubabatu da kuɗi mai tsoka.
sai da mukaga tashin su kafin muka juya, a tsakiyar gidan muka rabu da Aunty Nasiba tace min zata wuce sashin su Inna Wuro acan zata kwana, nayi-nayi mukoma side ɗina mukwana a can taki.
koda na koma ciki na tadda su Zulai sunata daɗa gyara cikin side ɗin suna gamawa suka tafi ɗaya side ɗin dan tun ranar da aka zuba sabbin kaya suka kwashe kayan su suka koma can.
tuni Naseem da Nasmah suka yi bacci saboda gajiya dan tun da safe da suka bi Ahmad ban sake sasu a idona ba sai yamma.
ɗakin su na shiga na gyara musu kwanci tare da yimusu addu'a sannan naja musu kofa na fita na koma ɗakina....
A ɓangaren Ahmad kuwa, cikin gidan sa cike tam yake da jama'a shigowar sa kenan cikin parlour'n sa bayan ya sallami wasu ba'in sa, jama'a sai zolayar sa suke dayi masa kirari, ɗaya daga cikin ɗakunan da suke cikin parlour'n ya shiga,
wasu manyan mata ne zaune cikin ɗakin yakaraso ya zauna tare da gaida su, suka amsa sunayi masa ya gajiyar hidima.
ɗaya daga cikin matan ya mai da hankalin sa gare ta yace
"Hajiya naga kiran ki ɗazu ina tare da jama'a ne."
tace "Eh dama na kira ne naji wata shirin ake kanyi na ɗauko amaryar naga dare nadaɗa yi ne, ga jama'a sun fara watse wa."
murmushi yayi tare da faɗin
"Ai Hajiya wannan amaryar baza ta ɗauku ba abar masu tafiya sutafi abin su kawai."
tace "Kamar ya ba zata ɗauku ba?."
zaman sa ya gyara sannan yace.......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama😇: HMD
WASA FARIN GIRKI
NA
RASHEEDAT S DIRECTOR
Ganin yan da nayi maganar da alaman shiga firgici dajin cewa Ahmad ne wan da Bappa ya karɓi sadakin sa, sai yayi saurin tarar numfashi na da faɗin
"Eh Ahmad in ban da abin ki HAMDAH ace mutum kamar Ahmad yataho niman auren ki ai abun alfahari."
"Bappa ni wannan mutumin fa.."
sai kuma nayi shiru batare da na karasa faɗan abin da zan faɗan ba.
murmushi Bappa yayi tare da girgiza kai ya ce
"Shi mutumin me yayi, kada kice komai kiyi addu'a zakiga alkhairin sa da yar dar ubangiji."
shiru nayi ban kuma cewa komai ba amma a kasan raina sam banji daɗin lamarin ba,
a tunani na ma wani ne daban yakawo sadakin ashe wannan ɗan anacen ne me shegen naciyar tsiya, wato dana ce yatafi da kuɗin sa shine yazo gurin Bappa ko.
kwafa nayi ina ciza laɓɓana na kasa.
haka Bappa yayi ta min nasiha, ina dai zaune ina jinsa sai da ya gama kafin na mike nafita...
Bayan kwana Uku Ahmad ya dawo gurin Bappa da tambayan sa rana, Bappa ya bashi wata ɗaya yace ya dawo bayan wata ɗaya a ɗaura auren.
Ina zaune a parlour ya shigo da salla, su Nasmah suna ganin sa sukayi gurin sa a guje, kamar kullum haka yayi ta biyewa shiriritan su.
daga bisani ya juyo in da nake, in da nayi kamar bansan yana gurin ba.
ganin irin kallon da yake min yasa ni jan guntun tsaki, idanun sa ya lumshe tare da sake buɗe su a kaina kana ya ɗan saki murmushi yace
"Kyakkyawa ta albishirin ki."
ban ko juyo in da yake ba bare ya sa ran cewa zan tanka masa.
murmushi mai bayyana zallan nishaɗi da jin daɗi ya sake sannan yace
"Wata ɗaya Bappa Malam ya yanke min na bani ke, duk da yayi min nisa amma ina cikin farin ciki sosai,
ke ya kama ta ki yanke min kwanakin amma sam kin ki saurara ta da lokacin bazai kai har haka ba,
shi kuma ina jin nauyin sa, kin ga abin da kika jamin ko."
ɗan sakai ta maganar nasa yayi kana ya mike tsaye, zato na tafiya zaiyi sai gani nayi yadawo kujerar da nake ya zauna,tare da leko fuska ta.
kawar da fuskata nayi gefe, yasaki murmushi mai sauti tare da faɗin
"Yakamata kibani aron lokacin nan naki mai tsada aro nace ba kyauta ba Please, zan maida miki kayan ki da zaran mun gama tattaunawa kan batun hidimar auren mu,
wace Kasa kike so muje a gudanar da shagalin bikin mu, dan Kawa tace bai kamata ayi bikin a Nigeria ba, wani kasa kike so aje a yi acan."
fuska na haɗe na ce "To ni me yada meni ina ruwana in yaso ayi a sama ba'a doron kasa ba."
Ido ya ɗan waro yace
"A sama kuma? wane mu ai bamu kai nan ba."
baki na murguɗa nace "Kada ka kaini da nisa dama yaushe kazo bare ka isa, ai sai isassu, saka saki nake nufi ba'a sama ba a kasa."
"Uhm igiya zaki ɗaura mana muna lilo koko a jirgin sama."
baki na kuma murguɗa wa namike ina kokarin barin gurin.
da sauri yace "Baza a bani aron lokacin ba kenan kyakkyawa ta?."
ban ko kulashi ba nayi gaba abina.....
Tun daga ranar kullum sai yazo bakuma zan kulashi ko na saurarare ba, hakan kuma bashi zai hanashi hobe ya fasa zuwa ba.
ana saura sati biyu bikin
Hajiya Rahama matar ministar Bukar tazo,
bayan mun gaisa nasa aka cike ta da kayan abinci da sha, tana ci muna ɗan taɓa hira cikin hirar take cewa
"Hajiya HAMDAH kin kimu ko nima a waya bare zuwa gida, sai kawai kwasam nasami labarin wai zakiyi aure abun farin ciki wai Ahmad Tijjani Sabil zaki aura, wlh kar kiga yan da nayi farin ciki amma nayi fushi wai sai a bakin wasu zan ji ai ko a waya zaki tura min da sako."
Muemushin yake nayi nace "Ayi min afuwa wlh abubuwa ne zukayi yawa sai a hankali yanzu."
tace "Haka ne kam shirye shiryen biki ga harkokin kasuwan ci abun kam sai a hankali,shiyasa nayi miki uzuri na taso na taho da kafata, Allah ya sa ayi da mu."
zaman ta taɗan gyara sannan ta kalli gefe da gefen cikin parlour'n kana cikin kasa da murya tace
"Amma ya banga karin wasu ma'aikata cikin gidan nan ba, ko zuwa suke su zo."
cikin rashin fahimtar abib da take nufi nace
"Wasu ma'aikatan kuma ai Talatu da Zulai sun wadaci ai kin cikin gidan nan."
tace "Ba waɗannan ma'aikatan nake nufi ba masu gyaran jiki na amare."
baki na taɓe nace
"Masu gyaran jiki kuma, babu wasu masu gyaran jikin da a kayyato."
ido ta waro tare da faɗin
"Wai kina nufin aure saura sati biyu baki fara gyara ba?, kin san wa zaki aura kuwa?, mutumin da akace matarsa ta mallake sa sai yanda tayi da shi, to wlh yakama ta ki farka tun da wuri kisan abun da kike ciki."
"Uhm nifa babu wani gyaran jikin da zanyi a barshi kawai."
tace "Mene kan kishiya zaki shiga kice bazakiyi gyara ba, matar da ake faɗan ta kowa sai yabada labarin ta, to ko ba komai bace ita ace mutum kamar Ahmad Tijjani Sabil ai dole ayi gyara sufa irin waɗan nan manyan mutanen tanan ne kaɗai zakabi ka mallake su, tun da kai ba hanyar shirka zakabi ba, idan ita da ake labarin nata tana yi sai taje can taci gaba da yi,
kai ma dai baza'a barka a baya ba,
akwai tawa shahararrir mata wacce ake kiran ta da Dr mata Hajiya Lubabatu tana da ma'aikata da dama tana tura su gari ya gari, ta kware wajen iya gara Yakamata a gaiyatota ba ma'aikatan taba ita da kanta tazo, hausawa suka ce idan kana da kyau kakara da wanka,
Yakamata kiyi huɓɓasa kifarka da wuri, bari yanzu ma na nime ta."
tana kaiwa nan taɗaga waya ta daddanna ta kara a kunne, jim kaɗan ta soma magana nidai ina jin amma sam ni ban so takira wata ba danni ban sa auren a ka ba.
bayan sun gama wayan ta dube ni tace
"Mun gama magana da ita zatazo gobe, dan ma yau tana gurin wani aikin ne amma tace zata aje ƴar aikin ta acan ita zata zo nan, dan na faɗa mata ko wace ce ke sai ki zauna da shiri gobe zamuzo da ita, zanbi gidan ta na ɗauko ta gobe idan Allah ya kaimu."
"Allah yakai mu." nafaɗa a takaice..
Washegari da safe kamar yanda Hajiya Rahama ta faɗa sai gata da Hajiya Lubabatu,
Hajiya Lubabatu ta bukaci dana ware mana ɗaki guda domin gudanar da aikin ta, ɗaya daga cikin ɗakunan sama nan muka yada zangon mu,batare da ɓata lokaci ba ta fara gudanar da aikin ta.
ranar sai da nayi kuka tuno da Aunty Rafee'at da Hajiya Lubabatu ta haɗa magunguna cikin cup ta ce nasha, sai na tuna ranar data kawo min magunguna a gidan Ya SALEEM tace daga hannun shahararriyan nan aminiyar ta Asma'u Jos ya fito,
ranan nayi kuka sosai tuno da ahlina, Hajiya Lubabati tayi ta rarrashi na da tambayar abin da ya sameni sai dai ban bata amsa ba da kyar ta shawo kaina nayi shiru, sannan taci gaba da aikin ta.
kwanan mu goma da Hajiya Lubabatu, duk wan da ya ganni sai sambarka, ni kai na nasan na sauya sosai, nakara kyau na kara cika ko ina na ya cika tup-tup, kullum muna tare da Hajiya Rahama da wasu kawayen ta, dan acewar ta itace babbar kawa ni dai ina biye mata a haka dan Hajiya Rahama ba sa'ata bace ta girme min nesa ba kusa ba.
Bana fita kullum ina ɗaki in nafita kuwa to iyakata parlour'n sama, kamar yanda Hajiya Lubabatu tace bazan fita ko nan da can ba har sai ta gama aikin ta.
shiyasa ma na sami sa'ida daga gun wannan ɗan anacen dan ko yazo iyakar sa parlour'n kasa yakaraci zaman sa yatafi dan bana sauka.
ana saura kwana uku bikin ranar tun da safe Hajiya Rahama da kawayen ta suka zo, Aunty Nusaiba matar Uncle Mahmoud itama da wasu kawayen ta sukazo, su Inna Wuro da Faty duk muna tare da su a side ɗina,
abin ka da taro ko babu yawane sai kaji hayaniyar nan ai ko parlour'n sama da kasa duk ya dauki hayaniyar jama'a.
wasuyan motoci guda biyar suka shigo gidan masu ɗauke da tambarin sunan Company'n Ahmad Sabil.
duk kanin su shake suke tam-tam da kaya.
shigar su ke da wuya kira ta shigo wayata, koda na duba mai kiran ganin bakuwar lamba ce, kamar bazan daga ba sai da kiran takusa yanke wa kafin na ɗaga da sallama, daga cikin wayar numfashi naji an sauke kana daga bisani a ka soma magana
"Kyakkyawa ta barka da safiya inad fata kina cikin koshin lafiya ke da yarana gaba ɗaya."
Shiru nayi batare da na amsa shiba sai murguɗa bakin da nayi kamar yana kallo na. yacigaba da faɗin
"Ga ba'i a waje suna niman izinin shiga."
kashe wayar nayi ina kunkuni kasa-kasa "To ina ruwa da an hana ba'in shiga ne ko kuma wani sabon sai da hali ne."
Aunty Nusaiba dake kusa da ni tafube ni tana faɗin
"Wasu ba'i kuma?." baki na turo gaba nace "Wai wannan Ahmad ɗin ne wai wani wai ga ba'i a waje ko da an hana su shiga ne da zai wani kira yana faɗa wa mitane."
tace "A'a kodai motocin da yanzu naji shigar sun nan ne naga mutane tsaye a jikin motar wata kila sune ba'in to ace su shigo mana."
Faty tashiga kwallawa kira Faty dake ɗakin su Naseem tafito parlour da sauri tace
"Yi sauri kije kicewa mutanen da suke wajen nan su shigo sai ki sauke su a parlour'n kasa."
tace To,
jim kaɗan ta dawo tace sun shigo suna parlour, Aunty Nusaiba ta sauka taje ta same su.
bajimawa ta dawo tace min
"Masu ai ki ne wai Ahmad Sabil ne ya turo su wai zasu fita da kayan cikin side ɗin nan su shigo da wasu."
kafin nace wani abu Hajiya Rahama tace
"To bismilla su fara mana, sai su fara daga kasan idan suka gama sai a koma kasan a basu guri su gyara nan ɗin."
tace "To haka ko za'ayi." ta juya ta koma domin sanar musu.
a raina nake faɗin
"Kamar wani an sashi ni shishshigi ne bana so."
Batare da ɓata lokaci ba ma'aikatan da suka kai wajen rai goma dukan su maza ne suka fara gudanar da ai kin su,
kan kace me sun gama kwashe kayan cikin parlour'n kasa, kama daga kujerun cikin parlour'n, bed and bedside drow dressing mirror wardrobe dake cikin bedrooms ɗin parlour'n, zuwa kayan kitchen and dinning.
kaf sukayi waje dasu suka jibge su cikin ɗaya side ɗin cikin gidan da bakowa ciki.
nan suka rinka shiga da kayan da suka zo dasu a mota suna shirya komai yan da ya kamata.
zuwa karfe 1 sun kammala komai sun shirya komai a inda ya kamata.
nan suka bukaci haurawa sama domin cigaba da aikinsu, muka dawo kasan muka basu guri.
lokacin dana sauko kasa sai nazamo ƴar kallo tamkar ba parlour na dana sani ba abun ba'a cewa komai tsaruwar sa ya wuci misali, kowa sai tabawa da sam barka yake....
Sai wajen yamma suka gama kammala komai sukayi mana sallama suka tafi.
abin kamar karya nake ganin shi sai daɗa zamowa gaske yake,ana gobe ɗaura aure Ahmad yaki rani lokacin ana yimin lalle, naki ɗagawa sai da yayi min missed call biyar kafin na ɗaga, yace
"Madam gani na shigo fito muje asibiti a bincika miki lafiya ta."
"Meye damuwa ta da lafiyar ka."
nafaɗa tare da kashe wayar.
ina kallon wani kiran nasa na kuma shiga haka naki ɗagawa, ga haushin lallen da aka bi aka dame ni da shi nifa in da anbi tanawa da duk waɗan nan fidda ficen da an barsu.
tsaki naja jin wani kiran ya kuma shigowa a fusace na ɗago wayar niyyata na gaya masa magana idan bai dai na dami na ba,
sai naga number Bappa ne ya bayyana kan Screen ɗin wayar, da sauri naɗaga wayar tare da yin sallama Bappa