Showing 33001 words to 36000 words out of 125808 words

Chapter 12 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

472

Bappa nayi ina shere hawayen fuska ta nace
"Yan zu Bappa ka amin ce da abun da yafaɗa kenan?, to shi ina ruwan shi da su me ya shafe shi da lamarin su da har zai rika shiga, har fa Daddy yake cewa surika ce mishi meye gamin sa da su."
murmushi Bappa yayi irin tasu na manya kana ya ce
"To in ban da abin ki HAMDAH ai wan da ya nuna yana son naka yagama yi maka komai a rayuwa, kuma da kike cewa yana shiga lamarin su basu kaɗai ba lamarin koma waye yana shiga, idan baki mance ba na taɓa baki labarin sa nazu wa rugar mu da yayi, muma ba lamarin mu yashiga ba yakuma jiɓanci lamuran mu, yayi silar magance mana wutar fitinar da take ta kunno mana,
ko jiyan nan da daddare munkalli labarai gidan TV wasu iyaye sun fito suna mika masa godiya kan gudumawar da ya bada kan ƴaƴan su, su iyayen ma basu ma sani ba ƴaƴan ne suka dawo gida suke faɗa musu alkhairin da yayi musu,
a makarantar gwamnati suke karatu ya cire su ya mai dasu na kuɗi,
sannan kin ce meye gamin sa da su,
ke da kike taimakon bayin Allah meye gamin ki da su?,
ai shi tai mako basai wan da kasani kake taimaka masa ba, duk wan da Allah ya sa da rabon sa yafaɗo ta kansa sai ka taimaka masa ladan ka na gurin Allah,
shiya sa Allah ya halittomu kala biyu mai kuɗi da kuma talaka hakan kuma jarabta ce, idan kai me kuɗi ne kayi kokarin cin jarabawar da yayi maka, wato kajikan na kasa da kai, ka kuma tsare dokokin Allah, to da yardar Allah babu shakka zaka shiga aljanna ta sanadiyyar jaraftar ka da yayi da arziki,
idan kuma kai talaka ne, karike talaucin ka kabi dokoki Allah, kai ma zaka wuce aljanna da yar dar sa.
shi tai mako ba sai wan da kasani kake yi masa ba.
kiran sa da sunan uba kuma da suke yi, ai duk ɗa nagari shike daraja nagaba da shi yakira sa Yaya wan da ya haifesa kuma yakira sa da sunan uba, wan da yayi jika da shi yakirasa da Kaka, abun alfahari ne ɗanka yazamo daga cikin irin waɗan nan ƴaƴan, ba ai bu bane dan sun kirasa da suna Daddy tun da yakai ya haife su, zaki so ace ƴaƴan ki suna da rashin kunya ko basu da tarbiyya?."

Shiru nayi batare da nace komai ba.
murmushi Inna Wuro tayi,dan ta fahimci in da maganar tawa ta dosa, kana tace
"HAMDAH kenan ai laifin wani baya shafar wani."
kana ta kawar da zancen da faɗin
"Sai kiyi wa Yakubu hakuri ya dai na wannan tafa hannu da ɓarin jikin da yake."
da sauri Yakubu ya daɗa rarrafo wa gaban mu yace
"Whl Innar Gida kada kiga shakar da mutumin nan yamin, tsaro biyu ne suke girgiza ni a jikina, tsoron kada Hajiya ta kore ni daga ai ki na, da kuma tsoron wannan basamuden mutumin da suke tare da Ahmad Sabil daya makuren makogaro."
yayi maganar yana ɗaga wuyar sa da nuna mana in da ya shako san.
dariya duk sukayi ban da ni dana murmusa kawai.
na yar da da dukkanin maganar da Bappa yayi, sai dai inajin abune me wuya na iya jure wa dajin kalmar uba na fita daga bakin su Naseem.
Bappa yacewa Yakubu ya tashi ya tafi anjima yaje ya ɗauko su a makarantar.
ya mike yana zuba godiya yayi waje.

Haka su Bappa sukayi ta jana da hira bani na bar side ɗin ba sai wajen karfe 12, gani lokacin dawowar su Naseem yayi nayi musu sallama nakoma side ɗina.

komawa ta bada jimawa ba su Nasmah suka shigo a guje, kalmar da suka fara furta min shine Daddy'n su ya ce gobe zai zo ya ɗauke su a mota.
ban iya ce musu komai dan ko na faɗan ma abanza ne...



A ɓangaren Ahmad Tajjani Sabil, tun da yabar gidan tuki yake kamar mai koyon tukin, a haka ya iso bakin wani katafaren get me girma da tsaruwan gaske, yayi hon batare da ɓata lokaci ba a ka wangale masa katafaren get ɗin,
a sannu ya dannan hancin motar sa ciki, ya ilahi ya lillahi gida ne mai matukar girman gaske, alkalami na bazai iya zana girma da tsaruwan gidan ba, FAN'S na barku ku hasasho da kanku.
a hankali ya isa parking lot in da motoci da suka kai guda biyar ke jere agun ya yayi parking, a sannu ya buɗe motar yafito,
daga can wasu matasa guda uku suka iso in da yake da sauri, suna faɗin
"Barka da dawowa master."
hannu kawai ya ɗaga musu tare da yi musu murmushi, batare da yace komai ba, yasoma tafiya a hankali ya iso ba kin wata kofa, jiki ba kwari ya tura kofar yashiga da sallama ɗauke kan laɓɓan sa.
wata kyakkyawar mace fara ƴan duma-duma ce ke zaune cikin katafaren kayataccen parlour'n, tana ganin sa ta ajiye wayar dake rike a hannun ta, ta mike da sauri,
ta nufo shi da ɗan sassarfa, tun kafin ta karaso ya buɗe hannayen sa ta shige cikin jikin sa ta rungume shi, hannayen sa ya haɗe yazagaye bayan ta tare da manna mata kyakkyawan sumba a goshi, ido ta lumshe tare da buɗe wa lokaci guda, kana ta ɗago kanta ta mannan masa kiss a kumatu.
yan da tayi shima haka yayi, ya lumshe idon tare da kuma buɗe wa, itako hannun ta tayi sama da shi ta sakalo wuyan sa taɗan langwaɓar da kai gefe kana ta soma magana cikin
shagwaɓa
"Aboki ka mance da nine?." ido ya waro da alamun maganar tata tayi girma, baki ta cuno gaba tace
"To shine nayi ta kiran ka a waya baka ɗaga ba, kuma baka neme ni ba tun da ka fita, ni da na nime kan kaki amsa kiran."
maganar take cikin shagwaɓa kamar zata fashe masa da kuka.
kuma tun ta ya kama yaɗan ja kana ya ce
"Na isa naki ɗaga kiran ki kinga wayar da na fita da ita ɗaya wayar tana gida ai."
yayi maganar yana nuna mata wayar dake rike a hannun sa.
murmushi tayi tare da faɗin
"Ai har da nayi fushi."
hannun sa ta ruko tana faɗin "Toho muje kayi wanka."
ta janyo hannun sa sukashi ge cikin wani kayataccen bedroom, suna shiya da kanta ta tuɓe masa kayan jikin sa, boxes kaɗai ta bari takuma janyo hannun nasa sukayi cikin bathroom.
Ta taimaka masa yayi wanka suka fito ɗaure da towel a kugun sa.
lokacin an fara kiraye-kirayen sallar azaha jallabiya ya zura ya jasu sallah nan cikin ɗakin,
ko da suka idar, zaman sa ya gyara ya jingina da jikin bayan sa da jikin garu-bango yana lazumi, ido taɗan tsura masa kana sai kuma ta mike ta fita jim kaɗan ta dawo ɗauke da tray mai girma a hannun ta, a gaban sa ta dire, kana tashiga buɗe kulolin da suke kan tray'n har guda uku,
wani daddaɗan kamshi ne suka fara tashi daga cikin kulolin, nan da nan ɗakin ya kaure da kamshin lafiyayyun girkin.
tazuba cikin plt tare da saka cokula guda biyu, ta gyara zaman ta da kyau ta maso gaban sa, in da ta saka plt ɗin a tsakiyar su, suka rika cin abincin gwanin ban sha'awa
sunayi suna ɗan taɓa hira da zolayar junan su, a haka har suka kammala, takwashe kayakin ta mai da su kitchen,
ko da ta dawo ta taddashi ya koma gado, yana ɗan danne-danne a waya.
kimsa in da suka ɓatan tayi kana tazo bakin gadon ta zauna, dai-dai in da kansa yake, ta gyara zaman ta da kyau ta ɗago kansa ta ɗaura kan cinyar ta, yayin da ta cusa hannunta cikin sumar kansa tana ɗan yamutsa shi cikin tsalon sa mutum yayi bacci.
aje wayar dake rike a hannun sa yayi, kana yayi sama da
hannun sa ya shafi gefen fuskar ta, a hankali cikin muryar jin baccin da yafara ziyar tar sa, ta sanadiyyar abun da take masa, ya ce
"Kawa nayi bacci kenan?."
kai ta gyaɗa tare da faɗin
"Eh nasan ka gaji."
numfashi ya sauke kana yayi kasa da hannun sa yadaɗa gyara kwanciyar sa da kyau a hankali yashiga sauke numfashi.
batare da ɓata lokaci ba bacci yayi gaba da shi da taimakon yan da take sarrafa gashin kansa da wasu sassa na jikin sa.
sai da ta tabbatar da baccin nasa yayi nisa, sannan ta ɗaga kansa a hankali ta janyo pillow ta saka masa kana ta mike tafita, domin sanya ido kan aikin da masu aiki suke
gudanar wa a gidan...


Da misalin karfe uku da rabi ya farka bathroom ya faɗa can yafito ruwa na ɗiga daga jikin sa da alama wanka yakuma,
gaban wardrobe ya tsaya yaciro kaya wani dakakken yadi ne wan da daganin sa ma kasan bana wasa bane sai dai manyan kam.
bayan ya saka ya isa gaban mirror
turo kofar a kayi daga cikin mirror yazubawa kofar ido, lallausan murmushi ya sake wan da sai da kumatun sa suka lotsa, lokacin da suka haɗa ido da ita tacikin mirror,
baki ta ɗan turo gaba kana ta tako zuwa in da yake,
ta ɗaura hannun ta kan hannun sa daya ɗaura kan turare yana kokarin ɗauka, ta amshi turaren sannan ta dube shi tare da faɗin
"Shine zaka yi wanka baka neme ni na taya ka bako?."
kai yaɗan langwaɓar sannan ya ce
"Nayafe miki ai nasan kin sha wuya wajen sani yin bacci."
turaren ta ɗago tafara fesa masa a jiki sannan tace
"Babu wani wuya gun ai kin lada ni dai wayo kayi min ka hanani samin wannan ladar."
"Kinfa tara ladan nan da yawa amma rabawa zamuyi ko?."
yayi maganar cikin tsigar zolaya yana kuma jan kuma tun ta.
kafaɗa ta make ta ce
"Naki wayon naka yafi nawa yawa ai."
dariya suka sakar wa junan su.
sai da ta fisa masa turaruka wajen kala uku kana ta gyara masa zaman hular kansa, ta ce
"Kafito sosai fa."
"Haba original mirror ai ba ma sai naga wannan jebun ba."
yafaɗa yana nuna mirror.
murmushi tayi kana taɗan tsura masa ido sai kuma ta ce
"Aboki me ke damun ka?." tayi masa tambayar cikin nuna tsantsar kulawa.
da sauri ya ce "Wani abun kika gani ne, to ni kuma me zai dame ni bayan ina da ke."
ya kai bakin sa kan goshin ta tare da mannan mata kiss.
numfashi ta sauke tare da ɗan yin shiru tana nazartar yanayin sa, kana ta ce "To shike nan muje na rakaka katafi masallacin gashi ana kan kiran sallah."

Hannun ta ya damke cikin nasa cikin son kawar mata da shakkon dake hangowa kan fuskar ta ya ce
"Babu komai fa." da sauri ta katse shi da faɗin
"Ban kuma cewa komai ba fa muje katafi masallaci......"!








Mommyn Twin ce
8/19/22, 10:55 - Ummi Tandama😇: Nan nake shai da masa bukata ta nakan canza su Naseem makaranta.
shugaban makarantar nasu yace "To ba bubu da muwa amma dan Allah muna so musan dalilin da yasa ake son sauya musu makarantar ko kuma makarantar tamu babu koyo ne yan da ya kamata?".
nace "Ko kaɗan ba haka bane ba kawai dai ina so ne na canza musu makarantar ba wai kodun rashin koyo ba, ai ba za'a ce makarantar ku babu koyo ba, yara suna fahimta sosai, kawai dai yaɗan yi nisa ne."
yace "To in dai kuwa haka ne to dan Allah kada a ciresu a makarantar gaba ɗaya, akwai ɗaya makarantar mu dake wata unguwa mafi kusa da ku in dai kina so sai a maida su can ɗin, ranar Monday idan suka zo sai ayi transfer ɗin su can ɗin."
shiru na ɗan yi cike da nazarin maganar sa, sai kuma nace
"To shi kenan a mai dasu can ɗin."
har munyi sallama zan kashe wayar yayi saurin cewa
"Dan Allah Madam a daure a kawo su sai a kaisu wancan makarantar, idan akace an cire su gaba ɗaya kokon to zai shiga zukatan iyayen yara zasuyi zaton ko wani matsala ce mai girma aka samu cikin makarantar, tun da bawai barin garin zakuyi ba,
zamu iya samun dakilewar customer, adai duba lamarin da kyau Hajiya."
"Babu damuwa in sha Allah za'a kawo su sai a kai su wan can ɗin."
godiya yashiga yi min kana mukayi sallama na kashe wayar.

Ina sauke wayar number Ukhtee na kira yayi ta ringing ba'a ɗaga ba,nakuma mai da kiran shima har yakusa yanke wa kafin ta ɗaga, da sallama.
na amsa cikin harshen larabci nace
"Oh kai Ukhtee ina kika aje wayar haka ina ta kiranki baki ɗaga ba?, ko yanga kike min an ce miki ni saurayin kine."
dariya tayi tare da faɗin
"Saurayi kuma haba dai kedai wayar tana bedroom ne nikuma ina parlour, nama shigo ɗaukar abune cikin ɗakin naji wayar tana ring, ai da haka zaki ta kira ma ban sani ba, ya kuke ina yarana suke?."
"Lafiya lau duk muna lafiya, yaran ki suna can gurin Bappa sunki biyo ni suna can suna damin sa da surutu, ni nagaji da hirar ne nadawo side ɗina naɗan huta suna can."
larabcin nake ina ta haryaɗa shi.
dariya tayi jin yan da nake ta kwamusa larabcin, tace
"Oh kin dawo kasar ku yaren kasar ku yana so ya korar miki da yaren kasar muko?."
nima dariyar nayi tare da faɗin
"Ashe kin gane inata yi da kyar amma fa su Naseem sunanan da shi a bakin su domin makarantar isilamiyyar su larabci zalla ake, shi yasa yake nan zaune a bakin su."
tace "Kai naji daɗi wlh gara ai su zauna da larabcin a bakin su, ke kizauna da yaren kasar ku tun da shi kika zaɓa."
nace "To ya zanyi mahaifa ta dole naso yare na ke ma ba kina son yaren kiba?."
tace "Sosai ma."
"Oh to shine nima baki so naso nawa yaren."
mukayi dariya. hira kukayi tayi sosai da Ukhtee wani maganar idan nayi ita zata gyara min shi dan larabcin bai gama nuna baki na ba.
sai can da jinawa mukayi sallama.

Yau Monday kamar yan da nasa ba na rako su Nasmah gun mota, Yakubu dake goge motar yayi saurin buɗe motar nasaka su ciki,bayani na yiwa yakubu kamar yan da mukayi da shugaban makarantar su idan sun je za'a haɗa su da wani domin yayi musu jagora zuwa ɗaya makarantar.
ina tsaye ina ɗaga musu hannu har suka fita...

Kai tsaye Yakubu yaɗau hanyar makarantar, kamar koda yaushe hira yake da yaran yanata washewa da dariya kamar yan da suma suke ta washe baki.
suna isa bakin get ɗin makarantar yayi parking yafito, kana ya buɗe musu suka fito, suna fita suka shige cikin makarantar direct office suka nufa daga nan aka haɗa su da wani malami da zai kai su ɗaya makarantar, suka fito tare.
suna fita bakin get ɗin school ɗin,
wata lafiyayyi zazzafar mota tayi parking a gefe, tun kan motar ta kakarasa parking Naseem yafara murna yana faɗin
"Laa ga Daddy yazo laa ga Daddy yazo."
Nasmah ma kuwa ihun murna ta sake tare da sa gudu sukayi gurin motar.
da sauri ya buɗe motar ya fito yaware hannayen sa ai ko da gudu suka shige jikin sa ya rungume su, duk suka saki dariya har dashi, kana ya mike yashiga ɗaga su yana cillasu sama sai kya-kya ta dariya suke.
sai da yayi wa kowannen su haka har sau uku kana yadire su kasa,
Yakubu ya karaso in da suke yana washe baki da faɗin
"Ranka shi daɗi barka da war haka."
amsa wa yayi fuska a sake sai dai gaba ɗaya hankalin sa na kan su Nasnah da suke ta zuba masa surutu.
shima wannan malamin da aka haɗo su da shi ya karaso yana faɗin
"Barka da zuwa yellaɓoi."
yace "Yau wa, yaya ji da ɗaliban?."
malamin yawashe baki tare da faɗin
"Muna kai kam."
yace "Masha Allah."
malamin ne ya dubi yakubu da kuma yaran yace
"To muje ko."
yayi maganar yana duban motar su.
sai a lokacin Ahmad ya ɗago da kallon sa kan yaran yadawo da shi kan su Yakubu kana yace
"Ina kuma za'a je ba makaranta za'a shiga ba?".
yayi maganar yana shafa kan su Naseem.
malamin yace "A'a zamu tafi da sune ɗaya makarantar mu."
duban sa Ahmad ya kuma da alamun tabbayoyi ɗauke a fuskar sa,
kana yace "Wacce makarantar kuma?."
yace "Ɗaya daga cikin makarantar mu ne za'a mai da su."
da fuskantar mamaki Ahmad yace
"Har sun gama wannan makarantar ne da za'a tura su wata makarantar daban?."
kai malamin ya girgiza tare da faɗin
"A'a ai za'a sauya musu makarantar ne anyi musu transfer can ne."
ɗan shiru Ahmad yayi kana yace
"Malam ɗin yana ciki?."
kai malamin ya gyaɗa tare da faɗin
"Eh yana ciki." yace
"Okay to muna zuwa." yafaɗa tare da gyara rukon Naseem da Nasmah a kowani hannun sa guda, ya janyo su suka shige cikin makarantar.

Malamin ya dubi Yakubu dake ta washe baki yace
"Wai nikam da ma ƴaƴan Ahmad Tijjaji Sabil ne kake kawowa makaranta?."
Yakubu ya daɗa washe baki yace "A'a ƴaƴan me *HAM'NAS* Company ne fa."
"Au ƴaƴan mai *HAM'NAS* Company ne to shi Ahmad Sabil dangin su ne? lallai Allah mai yin yan da yaso yahaɗa family guda da tarin dukiya."
Yakubu yace "Eh ƴan uwa ne."
yafaɗi hakan ne kawai dan bashi da amsar bashi, dan shi kansa bai isa yace suna da dangan taka ko basu da shi ba, a matsayin sa na mai ai kin gidan ba lallai dole yasan dan gin gidan ba, san nan kuma baya so ya disga kan sa gaban malamin, ko ba komai shi ma za'a rika yi masa kallon wani...
suna nan tsaye
zuwa can Ahmad yafito shi kaɗai batare da yaran ba.
ido suka zuba masa ganin yafito shi kaɗai, yakaraso in da suke, duban malamin yayi tare da faɗin
"Ka koma kacigaba da koyar da ɗaliban ka, kai kuma ka koma gida ka dawo da wuri ka ɗau ke su."
yakara she maganar da duban Yakubu.
Yakubu yace
"Ranka shi daɗe hajiya tace na tsaya sai mun kai su kafin na komo gida."

Yace "Kar ka damu kaje ka abin ka."
yace To. yashiga mota in da tuni malamin ma yakoma cikin makarantar.
shiko Ahmad a hankali ya isa jikin motar sa ya shige ciki...

Da misalin karfe 12
a hankali na mike na shige bayi wanka nayi haɗe da ɗauro al'wala nafito,nashirya cikin wani doguwar rigar atamfa pauda da man lip kawai na goga sai turare dana fesa a jikina,
a hankali na isa jikin window labulen window'n naɗan janye shi gefe tare da zuge glass.
ido na kurawa furannin da suke ta kaɗa wa gwanin ban shawa,
idanuna na sauke can bakin get jin karar buɗe get ɗin, da murmushi nake kallon kofar,
dan nasan su Naseem ne suka dawo, ɗan gimtse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login