Showing 114001 words to 117000 words out of 125808 words

Chapter 39 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

455

wayata, yana ci gaba da faɗin na kira masa Daddy.
kuka nafashe dashi na rungume yaran ajikina ina mai matuqar missing na Ahmad.
Ummi ce tashigo ganin ina kuka tayi saurin isowa tana faɗin
"HAMDAH lafiya?." kaina girgiza ina fadin "Ummi Ahmad yatafi bazan iya qiranshi a waya ba Ahmad yatafi kenan bazai dawo ba, bazan sake ganin sa ba, suma so suke su gansa."
kuka sosai nafashe dashi Ummi ta rungume ni tana rarrashi na, kana tace na tashi nahaɗa kayana zamu tafi Bauchi tare, baza ta iya tafiya ta barni cikin halin da nake cikin nan ba.
babu musu namiqe danni ma nasan tafiyar zai fi min bazan iya jure Ummi tatafi tabarni Anan ba.
ita ta tai makamin mukashirya kayanmu tasa su Talatu suka fita dasu,
gabadaya yan gidan suka rako mu parking lot,
nace Mama ta komo part ɗina tun da ba kowa ciki kafin mu dawo,
suna tsaye har
muka shiga mota, muna ɗagawa juna hannu muka fice a gidan.
muka dauki Hanyar Bauchi...
koda muka iso Bauchi naji daɗin ganina acikin yan'uwana domin kota'ina najuya sune basu kaunar ganin wata damuwa tattare da ni,
kowa yana iya bakin kokarin sa wajen ganin farin ciki ya samu gare ni.
Su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela kusan kullum sai sun zo gida sai dare su koma, Ya Mas'ud baya motsawa konan da can kullum muna tare idan ya dawo daga gurin ai kin sa, haka zai zauna muta hira.
yan'uwana suna matuqar qoqari wajen ganin sun sani farin ciki sun kuma ɗebe min kewa...
A hankali na fara sake wa, da muwar dake dankare cikin raina yana ta washe wa, yanzu kam alhmdllh na sake hankali na kuma nata kan daɗa kwanciya..


Zaune muke a parlour'n Mamie Aunty Rafee'at tafito daga kitchen rike da flaks da ɗan madaidaicin tray mai ɗauke da cup spoon da sugar, ta karaso cikin parluor'n,
duba na tayi tana faɗin "Bari na kai masa na dawo."
nace "Wa zaki kai masan Abbu ne?." tace
"Ya SALEEM." kai na jinjina tare da faɗin "Anan kuma yanzu yake shan shayin sa yabaro gidan sa yazo nan ina matar tasa take?."
baki Aunty Rafee'at ta taɓe tace "Ƴar wahala tana can asibiti kwance ita bata mutu ba batayi rai ba, tana kan karɓar hukuncin ta."
Ya Masa'ud yayi dariya da faɗin
"Ai yanzu Ya SALEEM gauro ne tuni ya kaɗa matar tasa, yana gidan nan bashi da lafiya."
shiru nayi ina jinjina lamarin a raina.
Aunty Rafee'at ta fita domin kai masa shayin ta dawo muka ci gaba da hirar mu na tuna baya ana ta dariya, da tuna yaranta ta da da nayi ta yin sa,
cikin muryar dariya Ya Masa'ud yace
"Ƴar gidan Inna iyaye shirme."
baki na washe nace
"Allah Ya Masa'ud da ne nifa yanzu na girma."
yace "Ah sosai ma kuwa dube ki fa kinfi na hannun dama nan nan girma yanzu."
yayi maganar yana kallon Aunty Jaleela da ke gefen sa ta gefen ido.
hararar sa tayi tana faɗin
"Zamu sami matsala da kai Masa'ud ban son raini."
nace "Ya Masa'ud baka sani ba jiya Uncle Habu da ya zo yace wai dama nice gaba da Aunty Jaleela ko."
dariya duk muka yi cikin muryar dariya Aunty Rafee'at tace
"Kai Masa'ud ka kiyayi kanka da haɗa rigima, ke kuma HAMDAH a ina Uncle Habun ya faɗi haka?."
dariya nayi nace "Ai ita tasan lokacin."
fuska Aunty Jaleela ta haɗe tana hararar mu tare da faɗin
"Ni ba sa'ar ki bace daga ke har Masa'ud ɗin."
"To gyanbo duk kin girme mu kice har da Aunty Rafee'at ɗin ma ke har da ma Ya SALEEM, wlh yanzu yasa na kai masa bulalar zane ki, ni kuma nace ya huta tun da bashi da lafiya yana zaune na tsumage ki."
kafaɗar sa Aunty Rafee'at ta buga tace
"Tashi ka bar nan tafi damuwar ka."
ya mike yana dariya yafita. Aunty Jaleela ta ɗaga murya tana faɗin
"Yan zu ma zaka iya ɗauko bulalar."



Bayan sallar Isha mazajen su Aunty Rafee'at suka zo ɗau kar su, har gurin mota na rako su,
Ya SALEEM na hango zaune kan kujera
Dr Farooq na zaune kusa da shi,
tun da nazo gidan sai yau na saka shi a ido na, ban ma san yana gidan ba sai ɗazu da su Aunty Rafee'at suke faɗa,
kai na na kawar daga kallon sa na mai da hankali na kan su Aunty Rafee'at.
Dr Farooq yaɗan ɓata lokaci a gurin sa ga dukkan alamu duba shi yake game da rashin lafiyar sa da aka faɗa, dan har su Aunty Jaleela suka tafi yana gurin sa, sai can ya mike ya taho in da muke suka shige mota ina yi musu sai da safe,
Dr Farooq yace
"Ƴar gidan Inna yaushe zaki zo mana?."
nace "Kuna zaune zaku ganni."
dariya yayi da faɗin
"Babu rana kenan ko da shike manya fitar su na da wuya sai dai a zo musu basu suzo ba."
"Akwai rana kai idan tazo shine zaku gannin ai."
yace to Allah yasa...
ina tsaye har suka fita.
a hankali na juyo zan ko ma ciki, Ya Masa'ud ya fito rike da Hannun su Nasmah, suna ta zuba masa surutu, in da Ya SALEEM yake suka isa, murmushi mai sanyi ya sake ganin yaran ya miko hannu yana kokarin ruko hannun su, murya na ɗaga nace
"Naseem Nasmah kuzo nan muje ku kwanta."
cak ya tsaida hannunsa kana ya ɗago a hankali ya kalli in da nake,
da hannu na kuma yi musu alama da su taho ina ci gaba da faɗin
"Ku wuce muje ku kwanta nace."
suka juyo suka taho in ds nake na ruko hannun su muka wuce sashin Ummi...

Washegari da safe duk muna side ɗin Mamie Ya Masa'ud ne kawai baya nan yatafi gurin aiki.
waya ta dake gefe na su Naseem suka ɗauka wai sam sai na cire musu a key sun yi game, sai da na cire musu kafin suka dai na fitina ta.
can anjima sai ganin su nayi sun shigo daga waje,
nace "Ku ina waya ta?."
Nasmah tace " Na guyin Uncle." nace "Wani Uncle ɗin?." tace
"Uncle ɗayan." "Wani Uncle ɗayan yaushe Ya Masa'ud ɗin ya dawo daga gurin aiki."
Naseem yace
"Ba yace shi Daddy ne ba Uncle ba."
yayi maganar ysna rike haɓa da ware idanu.
Nasmah ta gyaɗa kai tare da faɗin
"Eh yana guyin Daddy."
da sauri cikin ɗaga murya nace "Ku rufa min baki shi ba Daddyn ku bane Daddy'n ku ya rasu."
cikin tsawa Ummi tace "Ke HAMDAH baki da hankali ne kin san me kike faɗa kuwa, wani irin tarbiyya kike son basu, to wannan shine uban su na asali shi da kike faɗan ubansu uban su ba ubansu bane uban arone,
baki da ta in da zakiyi ki sauya musu uba."
Mamie tace
"A'a Ummin Fauzan wai ke laifin ta kike gani ne, sam bata da laifi kuma bata faɗi karya ba, Ahmad yayi musu abun da shi ya kasa iya yi musu a matsayin sa na uban nasu ai shi ya kamata a kira sa da uban aro,
basu san shi ba Ahmad suka sani a matsayin uba kuma har gobe zasu cigaba da ganin sa a matsayin uba,
tun da shi ya gaza a cikin rayuwar su."
mikewa nayi na nufi kofa na fita.
can na hango shi zaune in da jiya
na gansa yana zaune kan kujera ya ɗaura kafafunsa kan wata kujerar dake gaban sa, idanunsa a lumshe ya naɗe hannayen sa a kirji yayin da bayan ke jin gine jikin kujerar.
har na nufi sashin Ummi najiyo karar waya ta,
da ɗan sauri na juyo, sai naji karar daga inda yake yake fitowa,
kiran ya katse wani ya kuma shigowa, nasan me kiran bai wuce manajan gidan mai na ba dan ɗazu mun fara magana da shi bamu gama ba.
a hankali na juyo na nufi inda yake jin wani kiran ya kuma shigo wa a karo na huɗu, a sannu na iso in da yake daidai lokacin wani kiran yakuma shigowa,
kallon inda sautin wayar tawa ke fitowa nayi, sai ganin wayar nayi a cikin kirjin sa ya rungume shi har lokacin idanunsa a nufe.
kai na naɗan kawar daga kallon sa kana na mika hannu jin wani kiran ya kuma shigo wa, ina kokarin zaro wayar dags kirjin sa.
a hankali ya buɗe lumsassun idanunsa ya zuba su a fuska ta yayin da idanun mu ya sarkafu dana juna,
da sauri na janje idanuna daga nashi kana nayi hanzarin zare waya ta da ga kirjin sa, na juya da sauri jin zuciya ta yana wani irin tsalle haɗe da bugawa,
su Naseem na gani sun fito daga side ɗin Mamie da sauri naje na ruko hannun su na janyo su muka shige side ɗin Ummi.
tun daga ranar ban sake barin su sufita ba bare su haɗu da shi, idan ina side ɗin Mamie ne ma to muna tare da su bana taɓa barin su su matsa ko nan da can, bare ma su fita ya gansu har suje in da yake.
niko tun da na zo gidan gaisuwa bai taɓa haɗa ni da shi ba bare maganar baki...


bayan wata ɗaya

Zaune nake a parlour'n Ummi muna hira na waiga gefe da gefe na banga su Nasmah ba, da sauri na mike nashige bedroom ɗin Ummi nan ma basa nan da sauri nafita na yi waje ina kiran sunan su,
can na hango su rike a hannun Ya SALEEM sun fito daga side ɗin Mamie sun nufi get,
da sauri na biyo bayan su ina isa in da suke da sauri na ruko hannayen su ina faɗin
"Ku wuce mu tafi." juyo wa yayi batare da yasaki hannayen su ba yaɗan zuba min lumsassun idanunsa, yana bina da wani irin kallo tamkar yau ya fara sani na,
niko
hannun su nashiga ja ganin bashi da niyyar sakin su, yana rike da su gam niko sai daɗa jan su nake, a hatsale cikin kunar rai da tuno a bin da yayi min a baya nace
"Sake min yara ina zaka kaimin su."
nayi maganar cikin bushewar zuciya,
da mamaki yake kallo na nasan mamakin yadda na iya tsayuwa nake gaya masa magana babu shakka ko tsoro yake, niko a yanda nake jin zuciya ta zan iya gaya masa fiye da haka danni yanzu bana jin tsoro ko shakkar sa,
baki ya motsa kana ya soma magana kamar mai jin bacci
"Idan kika ji musu rauni sai nayi maganin ki, sakar musu hannu."
zan tafi da ƴaƴa na bazaki sake ganin su ba, bare kicigaba da nisantasu gare ni."
da sauri nace "Su ba ƴaƴan ka kane ban kuma yarje maka kafita min da su ko nan da kofar gida ba, babu in da zaka je min da su, ka sakar min ƴaƴa na."
nayi maganar ina mai daɗa jan su.
da sauri ya saki hannun su tare da fizgo ni ya har sai da na garu da jikin sa,
yarike hannaye na gam a hankali cikin yanayin nan nasa ya soma magana yayin da sautin maganar tasa ke fita da ɗan sautin numfashi irin na mara lafiya,
"Ƴaƴa na ne idan kika kara nesan tani gare su."
ya taune lips ɗin sa tare da girgiza kansa.
kokarin kwace kaina mashiga yi ins faɗin
"Su ba ƴaƴan ka bane ba kuma zasu taɓa zamowa naka ba."
maganar Mamie mukaji a bayan mu tana faɗin
"Sake ta ai ba karya ta faɗa ba, kai da kan ka kafaɗi cewa su ba naka bane tun suna ciki ba'a gama yi musu halitta ba, baka kuma isa yanzu kadawo kace naka ba ne, sake ta maza."
sake ni yayi ya juyo in da Mamie take kamar zaiyi magana miskilancin nasa ya hana shi iya cewa komai, sai dai bugun zuciyar sa daya karo.
da sauri na ja hannun su Nasmah muka wuce ciki...
ina shiga na soma haɗa kaya na, koda Ummi ta shigo taga ina haɗa kaya ta tanbaye ni, nace mata gobe zan tafi ana nema na game da harkoki na da gaggawa, washegari kuwa da sassafe nabar garin Bauchi..........!
8/19/22, 11:01 - Ummi Tandama😇: 38






Sai da na dawo Abuja kafin hankali na ya kwanta nayi masa nisa da yaran bazai sake ganin su ba bare ya sami bakin faɗin cewa su ƴaƴan sa ne.
yanzu harkoki na da na Ahmad karami kaɗai nasa a gaba, duk da ko mai bai canza ba ma'aikatan da suke ai ki karkashin Ahmad su suka cigaba da gudanar da aikin a karkashi na.
Bayan wani lokaci
sabuwar rayuwa na gina wa kaina, abisa rashin Ahmad na nutsar da zuciya ta na fauwala wa Allah komai na rungume kaddar rashin sa, idan na tuno da shi da rayuwar da mukayi dashi wani lokaci na zauna nayi kuka wani lokaci nayi dariya, sannan nayi masa addu'a, nakuma sawa raina nagama aure kenan a duniya bazan kuma maimaita kuka na uku a cikin aure ba, kamar yadda nayi a baya, da farko nayi kukan kazafi da wahalar rayuwa dalilin auren Ya SALEEM, daga bisa ni nayi kukan rabuwa da Ahmad a lokacin da na yi sabo da shi, yanzu kam zanyi rayuwa ta ce cikin salama ni kaɗai sai ƴaƴa na...👌🏻





A gajiye na dawo gida daga gurin mittin ɗin da muka gudanar yau da ma'aikata na,
a parlur na tadda Mama goye da Ahmad,
"Mama barka da gida Ahmad ɗin ne goye a baya har yanzu zai sa miki ciwon baya fa."
nayi maganar ina zama kan kujera,
Mama tayi murmushi tare da faɗin
"To ya zanyi tun da ai kin aure nake, ai wannan angon shi maganin sa goyo idan ba haka ba yarika haɗa kashi kenan da kiriniyar sa,
ɗazu wai shi zai sauko kasa da kansa kaɗan ya rage yayi dungure."
dariya nayi nace
"Tab da yau keya yasha kasa kenan."
tace "Ai kuwa."
Talatu ce tashigo parlour rike da da tray mai ɗauke da kayan motsa baki ciki, ta dire shi kan table wɗin gabana tanayi min sannu da dawowa, na amsa tare da yi mata sannu da aiki.
na gyara na soma cin abin da ta kawo min.
waya ta ce tayi kara murmushi nayi ganin Aunty Rafee'at ce ke kiran na ɗaga tare da yin sallama,
ta amsa jin yanayin muryar ta sauri nace "Aunty Rafee'at lafiya ya naji muryar ki haka?."
tace "HAMDAH Ya SALEEM bashi da lafiya muna asibiti ne jikin sa ya tashi sosai."
ɗan shiru nayi jin yanda take maganar kamar zatayi kuka cikin rauni sosai.
nace "To ikon Allah jikin har haka ne to Allah ya sawaka."
bata kuma iya cewa komai ba sai kashe wayar tayi,
fuska na yamutsa a kasan raina nace
"Fatan saukin ma dana maka albarkacin ƴan'uwan taka ce."



A can sashin su Bappa kiran Abba ne ya shigo wayar Bappa bayan sun gaisa, Abba ke sanar masa da SALEEM ba lafiya sosai yana asibiti.
hankalin Bappa yatashi sosai dajin lamarin, lallai ciwon babba ne tun da har aka kwantar da SALEEM a asibiti.
yace gobe yana zuwa insha Allah,
washegari da safe Bappa ya ɗau hanyar Bauchi.
koda ya isa asibitin da aka kai SALEEM yasa aka kai shi, hankali sa ya tashi matuka ganin halin da SALEEM yake, yana kwance baya ko motsi na'urori suna ai ki a jikin sa.
cikin matukar tashin hankali Bappa yake tambayar su Abbu me ya ke damun shi me likita yafaɗa game da ciwon nasa.
Dr Farooq ne ya shigo da wasu likitoci su huɗu suka dukufa a kansa kowa da kalar gwajin da yake masa, Dr Farooq yaɗan yi baya tare da faɗin "Ya salam." a cikin zuciyarsa, ya juyo ya kalli su Abba da Abbu da Bappa dasuke tsaye jungum-jungum, kansa ya kawar ganin sun kura masa ido suna so suji ta bakin sa.
ɗaya daga cikin Doctors ɗin ne ya ɗago tare da share zufa ya kalli sauran ƴan'uwan sa sukayi magana sakanin su kana ya juyo gasu Abbu yace
"Kuyi Hakuri a gaskiya yana cikin hatsari sosai zuciyarsa sa yana daf da bugawa, amma zamuyi iya bakin kokarin mu daga nan zuwa kwana biyu har idan ba'a sami wani sauyi ba, to gaskiya sai dai a ɗaga shi a kasar nan a cikin kwana kin nan."
salati Bappa ya sake hankali tashe yake faɗin
"Bugun zuciya kuma Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, garin yaya akayi haka yau she yafara ciwon zuciya da har zuciyar ke kokarin bugawa?."
Dr Farooq ya gyara tsayuwar sa yayin da likitocin suka fita,
Bappa ya matso jikin gadon da SALEEM ke kwance idanunsa a rufe yayin da yake fidda numfashi ɗaya na bin ɗaya, Bappa ya dubi su Abbu yace
"Tun yaushe yake cikin wannan halin kuma mene ne musabbabin sa?."
Dr Farooq ne yace "Tun ranar da HAMDAH ta bayyana tafiyar ta na wannan karon kuma shi ya haifo da wannan babban matsalar,
kuyi hakuri tun wancan lokaci ban sanar wa kowa bane sabo da ina sa ran zai iya samin sauki ta hanyar shan magani da kuma rage tunani,
sai dai a yanzu komai ya kwaɓe kuma na lura da tun ranar da HAMDAH tabar garin nan washegari dana kuma yi masa gwaji sai naga ciwon nasa ya ɗare na da, sai dai abin da na lura baya amfani da shawarwarin da na ɗaura shi a kai yawan tunani da kuma damuwa shi ya janyo sa izuwa wannan matakin."
da mamaki su Abbu suke jin maganar su sam basu taɓa sammanin haka ba,
Bappa ko kai ya jinjina yana mai cigaba da kallon SALEEM dake kwance numfashin sa yana sama yana kasa.
Dr Farooq yace "Sakamakon allurar da akayi masa shi yasa yasami baccin nan, zamu jira zuwa ya farka muga abin da ya dace, zamu ɗan bashi guri yasa mi baccin da kyau."
duk suka fita a ɗakin domin barin sa ya sami baccin...


Bayan wasu ɗan awanni ya farka daga baccin da yake, sai dai har yanzu babu abun da ya sauya daga halin da yake ciki,
bayan likitoci sun shiga sun daɗa dudduba shi suka fito, Dr Farooq yace wa su Abbu zasu iya shiga su gansa yanzu,
yana kwance har lokacin amma idanunsa a buɗe suke yanzu, sai dai babu in da yake na'urori ne ta ko ina ke ai ki a jikin sa.
suka karaso in da yake suna yi masa sannu,
Bappa yace "Sannu SALEEM ya jikin?." kwayar idanunsa kaɗai ya juya ya ɗan kalli Bappa kana ya ɗan lumshe su tare da buɗe su a lokaci guda,
Bappa ya gyara tsayuwar sa da kyau ya kalli sa kana yace
"Akan wani dalili kake son salwantar da rayuwar ka, kunshe damuwa cikin rai mai cutar wa bazai taɓa haifar da maslaha ba, ka dubi halin da ka jefa kan ka ciki, muma ka jefa mu.
SALEEM kana son komawar auren ka da ƴar'uwan ka, a kan hakan kake son salwantar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login