Showing 21001 words to 24000 words out of 125808 words
ji ko kuzo ku je makaranta".
kafaɗa suka make alamar o'o, rungumo su nayi dukan su ajikina ina murmushi kana nace
"Ina kallon da mukayi jiyan naaan na sojojin naaan, to waye meson zama irin su a cikin ku?".
da sauri Naseem ya mike a jikina yana washe baki tare da nuna kanshi yana faɗin
"Nine-nine". "Yau wa to har in kana son kazama soja to ko sai kaje makaranta, kaje makaranta kayi karatu sosai daga nan zaka zamo soja, in kuma baka so to kazauna kawai a gida ina baka so kazama sojan zauna abin ka kada kaje School".
kai yashiga girgizawa da sauri yace "A'a a'a Mommy ina so to danje School in nine toja".
"Yauwa to kada ka sake cewa bazakaje School ba dan soja baya fashin School, Nasmah ta kefa? baki son zama sojan ne?."
da sauri tace "Ina to." nace "To ke bama soja zaki zama ba Dr Nasmah ce a nan, ina kina so kizamo likita kirika yiwa mutane allura."
ta gyada kanta da sauri, nace "Yauwa kinga in kikaje makaranta kikayi karatu da yawa to zaki rika yiwa mutane allura".
kuma gyaɗa min kai tayi da sauri tun kan in karasa maganar, murmushi nayi ina shafa kansu.
kallon kofa nayi tare da ɗaga murya nace
"Talatu kawo musu uniform ɗin su saka".
daga can bakin kofar in da take tsaye ta waje ta amsa da to kana taturo kofar tare da sallam, nakarɓi uniform ɗin nafara sakawa Naseem rigar sa wan da shi dama ta saka masa wandon shine yagudu,gyara masa zamar rigar nake ina faɗin
"Um kaga soja wannan yaro zai iya rike bindiga in ya girma ya zama soja".
baki yarika washewa yana ɗaɗɗaga kafaɗa da faɗin "Nine toja ai nine toja". "Ai kam ga sojan gasken gaske".
a haka nagama kimsashi
kana nasakawa Nasmah ita ma inata faɗin mata itace Dr zata rika yiwa mutane allura.
nariko hannun su muka fito parlour nan muka iske Zulai da kayan break ɗin su, Talatu kuma ta ɗauko musu School bag ɗin su, muka nufi parking space, da murna suka shige cikin motar Naseem sai faɗi yake
nine toja, Nasmah kuwa ta dube ni tace "Mommy ni meye?". kumatun ta naja nace "Kece Dr me yiwa mutane allura".
sai washe baki suke cike da murna direba yaja motar suka tafi.
Wani sati na gewayo wa muka fara shirin tafiya ziyarar gani da ido nan muka ɗauki hanyar zuwa Lagos,
sai dai wannan karon bantafi da su Nasmah ba saboda School, ni da Bappa da wasu jagorori biyu muka tafi, mun isa Lagos lafiya awani kayataccen hotel akayi mana masauki, mun isa yau washegari muka nufi Company da ake ta kan ginashi tamfatsetsen Company wan da girman sa ya kai ya kawo, an kai ni gurare da dama acikin sa an nunnuna min, masha Allah komai yayi saura kaɗan a kammala.
a gajiye muka koma masaukin mu kansan cewar da kafa akayi ta yawo damu acikin Company'n.
kayan jikina na tuɓe nashiga baya na watsa ruwa kana nafito na sauya kaya na haye gado dan na ɗan huta, waya ta na ɗauka na laluɓo lambar Talatu bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga, da sallama bayan mun gaisa nace
"Ina mutanen naki?". tace "Gamu nan muna tare da su a parlour muna kallo, ungo Naseem karɓa ga Mommy tana magana."
tasaka masa wayar a kunne,
"Mommy da mu biki kijo jike da mu".
murmushi nayi jin muryar Naseem nace "To zan zo naje da ku, kuna karato sosai ko?".
kai ya gaɗa, Talatu tace "Ka amsa da baki ai bata ganin ka". yace "Eh." "To a dage sosai, bawa Nasmah wayar." ya mika mata Nasmah tace
"Mommy kina ina, damu biki kije da mu".
nace "Nasmah to zan dawo nazo naje da ku kinji."
"Mommy yaushe zaki jo?."
"Gobe zan dawo naje da ku kinji". to tace, haka sukayi ta zuba min surutu da gwalaɓen su ni ma ina biye misu kun kai minti 30 a haka daga bisani na kashe wayar.
na gyara kwanciya ta dan bacci nake ji.
kwanan mu uku a Lagos muka juya Abuja.
Yau asabar ba makaranta muna tare da ƴaƴana a parlour munata sharholiyar mu cikin farin ciki da jin daɗe, duban daular da nake ciki a rayuwa da nake yin ta yan zu nayi, Allah yabani duniya ya ɗaga ni ya ɗaukaka min daraja ta, a lokacin da duniyar ke kokarin suɓuce min a lokacin da rayuwa ta tazomo tamkar kwai a cikin tray, wan da yazamo baki-baki saura kiris ya suɓuce kasa ya tarwatse.
numfashi na sauke lokacin da tunanin Inna ta ya zomin, wasu zafafan kwalla ne suka zubo min,
Allah sarki Inna ta tabbas na yarda wani hanin ga Allah baiwa ce, ya ɗauke ta a lokacin da nake tsananin bukatar ta arayuwa ta, lokacin da duniya ta juya min baya lokacin da narasa madafar dafawa lokacin da na gwammaci mutuwa ta da rayuwa ta.
ya ɗaukaka darajata abayan bata nan ya azirtani da arziki mai tarin yawa, wa zai iyayin duk wannan in banda *RABBUSSAMAWATI WAL'ARDI*.
Allah sarki Inna ta Allah yakai haske kabarin ki ya sa mutuwa yazame miki hutu.
wasu kwallan nakuma sharewa lokacin da na kuma tunawa da wata uwar wato Mama mai awara, Allah sarki rayuwa
ta cito ni lokacin da duniya tafara wasan kwallo da ni, matar data jajirce wajen ganin an ceto rayuwa ta gun haihuwa, da awancan lokacin bata samo kuɗin da za'a min cs ba wata kila da yanzu na mutu da ni da su duka aciki, tarike ni tamkar ɗiyar da ta haifa a cikin ta. lokacin da tayi nisa wajen ceto rayuwa ta sai ta tsuɓuce min.
sai gashi yau Bappa yamaye gurbin su, yazame min uba kuma uwa, ya jajirce yatsaya kan lamari na yazamo silar isata matakin danake yanzu, matar sa ta zame min uwa ƴaƴan sa suka zame min yan'uwa.
Rungume su Naseem nayi a jikina ina jin wani irin kuna, rumtse idanuna nayi da karfi jin kaina yana wani irin tsara min, lokacin da tunanin abun da yayi silan rabani da ahalina yashiga yimin yawo a kwakwalwa da zuciya ta. zunbur na mike nashige bedroom ɗina, sam bana son narika tunawa da hakan duk ranar da na tuna nakan kwana cikin kunci da bakin ciki da matsanancin ciwon kai, dan ranar zan kwana ina kuka.
Zubewa nayi kan kado nakife fukata jikin pillow, kai na rika juyawa ina ta fafutukar son na mance da tunanin, amma ina sai daɗe tahomin yake, da karfi cikin karaji narika faɗin
"Wlh Allah Abba ban taɓa ai kata zina ba, Ya SALEEM ba wani ɗa na mijin daya taɓa sani na mace bayan kai, duk da karancin shekaru na Inna ta ta tsoratar dani haɗe da kyamatar dani illan dake cikin zina, Ya SALEEM kai ka sanar dani mene ne aure, a lokacin da kuma nasan mene ne auren akayi min kagen zina aka kuma sheganta min ƴaƴa, bazan taɓa aikata zina ko da ace bani da aure bare ina da shi ɗin."
wani irin kuka ne ya tsuɓuce min, na kankame jikin pillow'n ina cigaba da kuka mai tsanini.
nakai tsawon awa guda ina kukan kana da kyar na sai-saita zuciya ta na baiwa kai na da kai na hakuri, kana nagyara kwanciya ta wan da ba bacci nayi ba, sai tulin tunani daban-daban.
har yamma ina nan kwance, ganin tunani yana kokarin kassara ni sai na mike nanufi side ɗin su Bappa,
a can na iske su Naseem, har dare muna can sai wajen bayan sallar isha kafin muka koma side din mu.
zuwa lokacin kam naji saukin damuwa ta kwarai dan su Inna wuro sun yaye min shi da hirarsu mai ɗebe kewa.
Washegari Lahadi ma ban yarda na zauna a side ɗi na ba da sassafe na wuce part ɗin su Inna wuro acan mukayi breakfast, a nan nawuni muna hirar mu cikin jin daɗi.
Yau Monday da misalin karfe 7 narako su Nasmah har sai da naga tashin su kafin na koma ciki, ina gama abun da zanyi nawuce side ɗin su Bappa, ina shiga bayan mun gaisa Bappa yake cemin
"Dama yanzu nake da shirin niman ki, kan ai kin masallacin nan ne harfa an rigada an gama shi, wan da aka bashi kwangilar jiya yake sanar min da cewa an gama."
da murmushi sosai kan fuskata nace
"Kai masha Allah kai amma dai ai kin yamin sauri wlh."
Bappa yayi murmushi tare da faɗin
"In dai da kuɗi a kasa komai cikin sauki yake zuwa, in dai da kuɗi ai komai mai sauki ne Allah dai yaba da ikon cin jarabawar da yayi dan shi kanshi arziki babban jarabawa ne, yakan kai mutum wuta yakan kaishi aljanna, kuɗi kamar takwabi yake idan kayi jahadi da shi shigar aljanna mai sauki ne idan ka ai kata ɓarna da shi shiga wuta mai sauki ne, Allah yasa mudace."
Amin Amin. duk muka amsa da shi
cikin washe baki nace
"Bappa masallacin nan fa nagina ne saboda Inna duk ladar arika kai mata kabarin ta, shima asibitin da yanzu ake gina shi idan a ka gama komai kyauta za'a rika yi duk ladar arika kai mata cikin kabarin ta".
"Masha Allah masha Allah".
abun da Bappa da Inna wuro suka rika faɗa kena.
Bappa yace "Ubangiji Allah ya tabbatar mana da hakan Allah yajikanta da rahama ya kai mata dukkanin ladan kabarin ta ya kyautata namu bayan nasu, kai sannu HAMDAH kinyi tunani kwarai da gaske Allah ya saka miki da mafificin rahama."
Amin. nace ina mai jin sanyi da daɗin addu'ar da yake min.
Muna nan zaune a parlour ban ankara ba sai gani nayi karfe 12 har da ɗori,
wayata na ɗaga da sauri ina faɗin
"Ikon Allah lallai guri babu wuya dubi 12 har ta gota an yama Yakubu yadawo kuwa bari dai na kirashi naji."
nayi maganar ina laluɓo lambar sa, wayar tayi ta ring bai ɗaga ba, nakira yakai sau biyar bai ɗaga ba, na sauke wayar ina faɗin
"Oh to ya ajiye wayar a ina ne shi ga lokacin ɗauko su Nasmah daga School yayi, gashi nayi ta kiransa bai ɗaga wayar ba."
Bappa yace "Ko ina ya aje wayar to shi, ina yaje haka ayi ta kirashin baya ɗaga wa".
nace "Wlh ɗazu ne na ai keshi gidan Hajiya Firdausi matar ministar Bukar, akwai wasu kayan da tayi min tallar su wan da tayi odar su daga jamani, to sun yi min na tura da kuɗin to ɗazu take faɗa min direban ta baya nan ko zan turo nawa direban ya amso min, shine na tura shi to gashi har yanzu bai dawo ba nayi ta kiran shi ma bai ɗauka ba".
nayi maganar ina kuma ɗaga wayar nakuma niman lambar sa.
Hajiya Firdausi matar ministan Abuja ne,
na yar da idan Allah yayi maka rufin asiri babu irin mutanen da bazaka gani ba ka kuma yi tarayya da suba,
ire-iren irin waɗan nan matan manya muna hulɗa da su sosai wasu sun girme min nesa ba kusa ba, wasu ma sun haife ni sun juya amma haka muke cuɗan ya da su.
Mikewa nayi da sauri ganin na kuma kiran sa har sau biyu nan ma bai ɗaga ba, nace "Bappa bari naje kawai na ɗauko su har yanzu bai ɗaga wayar ba, kar suyi ta jira kasan mutumin ka yanzu haka yana kan musu rigimar zai dawo gida".
Bappa yace "Maza hanzarta kam ga guri nata kan tafiya".
da sauri nafita ina shiga side ɗina mayafi kawai na yafa dan dama a kimtse nake na ɗau ɗaya daga cikin makullen mota da suke cikin drower, da sauri na sauka na nufi parking space.
kana nashiga motar nayi wa motar key, tun kafin na karaso bakin get maigadi ya wangale min get yana fadin "Adawo lafiya".
Saboda yanayin gosulo na bata lokaci sosai a hanya dan har karfe ɗaya ta cika har ta ɗan gota, kafin nan na isa makarantar su.
tun kafin nakaraso get ɗin makarantar, na zubawa kofar makarantar ido sosai dan ganin wasu yara rike a hannun wani mutum "Kamar su".
nafaɗa a file, nayi saurin isowa gurin, da mamaki nazuba musu ido ganin suɗen ne, yana rike da su suko sai washe baki suke,
shikuma mutumin yana ta tafiya da su yana nufar wata mota dake fake taɗan can gefe da get ɗin makarantar, yayin da yake ta girgiza kai alamun yana jin surutun da suke ta zuba masa.
cikin hanzari na isa gefe nafaka cike da mamakin ganin nufar motar yake gadan-gadan na ɓalle marfin mota na fita da sauri, cikin hanzari nasoma bin bayansu ina faɗin
"Kai Naseem Nasmah!, malam ina zaka kaisu kuzo nan ku wuce mutafi".
mutumin bai juya ba sai su yaran ne suka juyo sai kuma suka kawar da kansu suka juya suka cigaba da tafiya suna cigaba da zuba masa surutu.
da sauri nasha gaban su gani yan da suka batsar kamar basu sanni ba nace
"Kai ina muku magana kuna jina ina zakuje kuwuce mutafi malam ina zaka kaisu?".
sai sannan mutumin yaɗan dukar da kansa dai-dai tsawon su kana yasoma magana
"Kunsan ta ne?." batare da yaɗago ko ya dube ni ba ya ce "Ke a ina kika sannu bamu hanya mu wuce."
ido na waro cike da mamaki jin abun da yafaɗa tare da mamaita kalmar nasa
"Nasan su? nasan su fa kace, da alla malam ka sake su ina magana kana cigaba da tafiya da su."
gefe na ya gota batare da yace komai ba ya karasa jikin motar nima da sauri na rufa musu baya ina cigaba da faɗin
"Kai malam ina tambayar ka ina zaka kai su wai kana tambaya ta nasan su ne, ni zaka tambaye ni nasan sune, tambaya ta kake nasan su? dalla kasake min yara muwuce,ina ne zaka dasu kake nufar cikin mota da su?,
idan baka sake suba yanzu-yanzu zan kira maka hukuma anan."
baiyi magana ba sai mika hannun sa yayi yabuɗe marfin motar, yaɗau ko kwalin chocolate yaciro chocolate guda huɗu yabawa Nasmah biyu ya baiwa Naseem biyu kana yace
"To ga tsarabar ku kuci wannan yanzu, wannan kuma sai kusa a aljuhu."
yafaɗa yana cusa musu wani chocolate ɗin cikin aljuhun wandon su.
da mamaki nake kallon su ganin yan da sukayi tamkar basu sanni ba, sai murna da tsalle suke suna faɗin
"Ye am bamu da yawa ye am bamu da yawa."
cikin takaici nakai hannu zan fisge chocolate ɗin, da sauri mutumin ya janye su gefe kana yaɗago kansa tare da zuba idanun sa cikin nawa,
wani irin dirrr naji a cikin jikina tamkar jan wutan lantar ki.......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:54 - Ummi Tandama😇: Mai gadi yashiga jan hanci yanaci gaba da faɗin "Sam babu wan yafita ai da nasani dana shiga ciki naje na karɓi makullin mota naje na ɗauko su ai, na ɗan iya mota ba sosai ba amma da wasu su ɗauke su gara ni naje a haka na ɗauko sun, wasu matsiya tane masu niman jaraba suka ɗauke su, duk tai makon da akewa mutane baiyi musuba har sai sun haɗa da sata, wayyo Allah Naseem wayyo Nasmah, ashe da rabon ragowar shayi da nama gobe bazan shaba, kullum sai sun kawo min na haɗa da nawa duk na kallame."
zuwa yanzu tashin hankalin Bappa yafara bayyana yashiga faɗin
"Kanu innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ahjirni fi musibati²."
bakina na toshe da tafin hannuna jin kuka mai sauti yana son suɓuce min najuya ina kokarin barin gurin Bappa yakira sunana najuyo ina hawaye yace
"Je ki zauna kada ki ɗaga hankali sosai na tabbata zasu kira kuma bazasu cutar da su ba dan kuɗi suke bukata za'a kuma basu babu komai."
kai kawai na gwaɗa najuya nasoma tafiya, maigadi yabiyo ni yana cigaba da jan hanci yace
"Anyi bako Hajiya."
ban iya juyowa ba bare nabashi amsa Bappa ne yace "Ina bakon?." yace "Gashi can a mota yana shigowa kuma kuka shigo,"
"Wanene?." cewar Bappa, yace
"Gashi can cikin mota ai da naso hanashi shiga ganin baiyi kama da irin waɗan da za'a dakatar ba shine na barshi ya shigo."
yayi maganar yana nuna wata mota dake fake gefe a farfajiyar gidan.
Bappa ya girgiza kai kana ya soma tafiya yana faɗin.
"Ana cikin wani hali ta ya za'ayi a saurari wani bako."
Cikin matukar da muwa da tashin hankali nake tafiya, "Me zaisa su ɗauke su in dai kuɗi ne akan su ɗauke su ni da sun faɗa min ko nawa ne zan basu, me yasa suka zaɓi su cutar da yaran da basujiba basu gani ba.
wlh Allah sai yabi musu kadin su tun suna ciki ake cutar dasu da zaluntar su, har suka fito duniya."
wasu zafafan kwalla ne suka rika wanke min fuska bana ko iya ganin gabana, tunani na ɗaya awani hali suke yanzu..
Bappa har ya wuce motar da mai gadi yace masa bako ne ciki, sai kuma ya dawo sanin da yayi kan cewa bako rahama ne,
gilashin motar ya kwankwasa, a hankali aka zuge glass ɗin.
cikin matukar mamaki Bappa ke lallon mutumin da waɗan da ke tare da shi, yana zaune a mazaunin direba waya na rike a hannunsa yana ta faman latsawa, Nasmah na zaune a gefen sa tasaka kanta jikin kafaɗar sa tana ta cin chocolate, Naseem kuwa na zaune a gefen mai zaman banza rike da waya a hannunsa yana buga game yana kuma taunar chocolate.
cikin tsananin matukar mamaki Bappa ke cigaba da kallon mutumin da mamakin ganin sa tare da su Naseem,
tabbas bazai taɓa mance wannan fuskar ba, mutumin daya samar musu da ingantaccen ilimi a rugar su,mutumin da ya yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin an cafke ƴan ta'addan da suke shiga rugar su suna kaɗa musu shanukai su kashe musu makiyaya.
cikin girmamawa mutumin yashiga gai da Bappa, Bappa ya amsa fuska ɗauke da annuri yana yi masa kallon sani, shiko mutumin ga duk kan alamu bai gane shiba, cike da al'ajabin ganin su tare da su Nasmah Bappa yace,
"Ikon Allah kai ne nan tare da su Naseem da muke zaton ko ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke su."
da sauri Bappa ya juya yana faɗin
"HAMDAH taho gasu nan."
cak naja na tsaya dai-dai lokacin dana ke kokarin ɗaura hannuna jikin kofar side ɗina, najuyo da sauri, magana Bappa yaci gaba dayi yana nuna cikin motar.
"Gasu nan cikin mota Allah yayi ikon sa."
dagudu na nufo gun motar ina share hawaye na da bakin mayafi na,
ina isa gun motar nawuce gaban Bappa da sauri batare da duban cikin motar ba duk da glass ɗin motar a sauke take, hankali na nakan murfin motar dana saka hannu ina kokarin buɗe motar sai jin