Showing 108001 words to 111000 words out of 125808 words
fizga yayin da maganar tasa tashiga harɗe wa.
wani kururuwa Na'ima ta sake tace
"SALEEM kasan abun da kake faɗa kuwa, kana nufin ka sake ni sakin da baza ka sake dadowa dani ba har abada,
haba SALEEM kada ka min haka wlh duk abun da nayi sabo da son ka nayi, ina son ka bana kaunar wata ta raɓe ka sabo da son da nake maka,
wayyo Allah SALEEM meyasa baka cewa HAMDAH ka haramta kanka har abada da ita ba, wayyo Allah na nashi uku
dan Allah SALEEM kada ka min haka."
dagudu ta juya ta shiga ɗakin ta, laidar kuɗin da Raliya ta bata aron sa ta ɗauka tana faɗin
"Boka kai zaka iya min komai kai zaka fitar da ni cikin wannan hali, dole SALEEN ka cigaba da zama dani dole boka yasa ka ka zauna da ni."
tafito da sauri, har lokacin yana durkushe dafe da kirjin sa.
tayi waje da gudu, tana duba mai abun hawa, babu ko alamar su a unguwar.
da kafa ta rika tafiya tana sauri kamar zata tashi sama bana ko ganin gaban ta burin ta kawai ta isa gurin boka,
har ta fito babban titi zata sallaka ta koma ɗayan gefen dan ta tari abun hawa,
wani mai babban mota ne ya sako kai bata ankara ba sai ji kake keeeee motar tayi ciki da ita..
salati mutane suka fara akayiyo in kan titin a can karkashin motar a ka ciro ta, gaba ɗaya halittar ta ya canza sabo da sabar jin ciwo, bata ko motsi tana kwance kamar gawa.
wasu suna faɗin ta mutu wasu suna faɗin bata mutu ba,
aka kwashe ta aka garzaya da ita wani mafi kusa da gurin....
Da daddare duk yanda Ahmad yaso yatafi masaukin da yasa a tanar masa shi da security sa, su Abbu suka hana suka ce ya zauna a cikin dangi dan shima ya zama ɗan uwa,
duk da sun san gida kamar nasu kam yayi wa Ahmad Tijjani Sabil kankanta.
parlour'n da su Abba suke zama su tattauna nan akayi masa masauki, kasan cewar akwai bedroom's ciki har guda uku, shi ɗaya Bappa ɗaya Uncle Mahmood ɗaya.
sashin Inna na gidan kuma akayi wa security masauki ciki,
inda mu mata kuma muke cikin sauran sashin wato sashin Ummi da Mamie, dan su Aunty Rafee'at ma anan gidan yau sukace zasu kwana....
Washegari duk a sashin Mamie muka hallara kamar jiya, anan mukayi breakfast, ana zaune ana ta hira,
Bappa yace a kira masa Ya SALEEM kowa na nan shine kaɗai ba ya nan,
ya kama ta yazo ya gan sa dan ganin da yayi masa jiya ko a hanya ya gansa yanzu bazai gane sa ba.
Ya Masa'ud ne ya kira sa a waya
ya ɓata lokaci mai tsawo kafin yazo.
yashigo sanye da kananun kaya a jikin sa Black jeans da yellow t-shirt.
kallo ɗaya nayi masa na ɗauke kai,
ya ɗan rame ya kara haske gashin kan nan nasa nanan yalan-yalan baki sutuf sai sheki yake, sai dai ya ɗan hargitse da alama bai sami damar tace shi ba ya fito.
fuskar nan tasa a ɗaure tamau yanayin nan nasa da yanayin suffarsa yana nan yana biye da shi.
Bappa yace "Zo zauna nan kusa da ni SALEEM kaga yan da Allah yake ikon sa ko ashe ku jinina ne."
Ya Masa'ud ya washe baki yace
"Ya SALEEM ashe shine kanin Inna da take faɗan nan, jiya kawai sai gashi da ɗayan wancan hoton Inna."
ya nuna hoton ta dake like a jikin garun parlour'n yana mai cigaba da washe baki cike da farin ciki.
shiko Ya SALEEM bai yi magana ba sai zama da yake a kuje rar gefen Bappa, duk maganar da ake baya jin su gaba ɗaya hankalin sa na kan su Naseem da suke jikin Ahmad.
waya ta na ɗaga nashiga daddan na ta,
ina jiyo gaisuwar da yake yiwa su Bappan kamar mai ciwon baki.
su Aunty Rafee'at suka gaishe sa, ya amsa kamar wanda aka sashi dole.
baki na taɓe a kasan raina nace ashe dai hali na nan.
Ahmad ya mika masa hannu da murmushi kan fuskarsa yana faɗin
"Barka da safiya."
"Barka." kawai yace a dakile batare da ya dube sa ba bare ya sa ran zai karɓi hannun nasa suyi musabaha.
Naseem da ya kafe Ahmad da ido yana kallon yan da ya mika wa Ya SALEEM hannu, sai ya washe baki shima ya miko masa hannu tare da faɗin "Baika ka da wai haka."
dariya duk aka saka ganin yan da yayi kamar wani babba, shima dariyar yayi yace
"Daddy haka ake yi." kai Ahmad ya gyaɗa masa yana dariya.
Ya SALEEM kuwa tun da Naseem ya miko masa hannu yakafe tafin hannun nasa da ido, har ya janye hannun yana binsa da kallo yayin da jikin sa da zuciyar sa suke wani irin fizga da jin yaran a cikin jikinsa.
Ya masa'ud ne ya miko masa hannu yace
"Zo mu gaisa my boy." ai ko da gudu suka dawo jikin Ya Masa'ud Nasmah tana faɗin
"Hai dani Uncle." hannayen su duka ya rike yana yi musu dariya yace "To munyi gaisuwar."
jiki na suka dawo Naseem yace min "Mommy ya sunan shi?."
ya nuna Ya SALEEM.
yi nayi kamar banji sa ba, ina cigaba da danna waya ta.
ganin ban kula shi sai ya shiga bubbuga kafa kasa yana faɗin "Mommy ya sunan shi ni ban sani ba."
batare da na ɗago daga kallon wayar da nake ba nace
"Uncle." Nasmah tace "La shima Uncle ne." sai suka juya suka ci gaba da tsalle-tsallen su a sakiyar parlour'n.
Ahmad ya mike tsaye sakama kon shi gowar kira wayar sa, ya ɗaga kiran yayi waje.
Nasmay ce ta bi bayan sa tana faɗin
"Daddy nima dan bika."
yace "Waya zanyi Nasmah ina zuwa."
tace to sai ta dawo.
goggo Hauwa ta dube su cike da sha'awar yaran ta dube ni tace
"Allah sarki HAMDAH wai nikam ina cikin da kika tafi dashi ne kam, ko wuya ya sashi zuba ne, tun jiya nake ta son na tambaya."
Aunty Rafee'at tayi murmushi tare da kallon yaran tace
"Gasu nan Naseem da Nasmah takwaran Inna da Abbu."
wani irin ɗago wa Ya SALEEM yayi yana mai ware idanunsa a kan yaran yana binsu da wani irin kallo.
goggo Hauwa ta janyo yaran tana faɗin
"Ikon Allah ikon gaske Allah mai girma ashe dai kune ƴaƴan SALEEM."
da sauri na ɗago tare da faɗin "Su ba ƴaƴan sa bane ƴaƴa na ne!."
Ummi tace "Ke HAMDAH baki da hankali ne."
da sauri Mamie ta tari numfashin ta tace
"Da hankalin ta karya ta faɗa ne?."
mike wa nayi na dubi su Nasmah nace
"Ku wuce muje nayi muku wanka."
ai ko da gudu suka riga ni fita na bi bayan su muka nufi sashin Ummi.
A parlour'n kuwa murmushi Abbu yayi kana yace
"Yarin ya ta faɗi gaskiya ƴaƴan ta ne tafi kowa iko da su ita tasan wuyan su, sannan kuma ai da bakin sa yace ba cikin sane, ta ya za'ayi su zamo nashi."
wani irin mike wa Ya SALEEM yayi yanufi kofa yayi waje.
Abbu ya bi bayan sa da kallo yana jinjina kai..
Muna shiga side Ummi kuwa bedroom na shige da su muka haye gadon Ummi, nace "Ku zauna a nan kuyi wasan ku."
nima nayi kwanciya ta.
kwanciya ta bada jimawa ba kiran Ahmad yashigo waya ta ina ɗagawa yace
"Kyakkyawa ta kina ina nashigo ban ganki ba?."
"Ina side ɗin Ummi."
yace "Shine kika bar Ahmad yana kuka zo ki karɓe sa."
nace to. kana na mike na fito.
ina fita na hango sa shima yana fito wa daga sashin Mamie rike da Ahmad karami a hannunsa sai dariyar sa yake,
tsayu nayi dai-dai kofar Ya Masa'ud ya karaso tare da miko min shi yace
"Karɓe shi ki bashi nono."
baki na turo nashiga yarfe hannu ina ɗan bubbuga kafafu na a kasa cikin muryar shagwaɓa nace
"Dama ba kuka yake ba kace wai yana kuka yaro yana wasan sa, baya jin yunwa."
yace "A'a kyakkyawa ta bashi nono yasha tun ɗazu da yasha ina lura baki kuma kara masa ba, yana da hakuri ne kawai shi yasa baiyi kuka ba."
"Allah ni nagaji da shan nonon nan har zafi yake min fa."
yace "Yi hakuri muje na hura miki shi zai daina zafin, muje na gani, idan ya daina sai ki bashi ya sha."
yayi hanyar side ɗin Ummi, na ɗaga kafa zanbi bayan sa, sai naji tari cikin ɗakin Ya Masa'ud kofar ɗakin na tura ina faɗin
"Ya Masa'ud wannan irin shakewa haka kasha ruwa mana ko..."
nayi maganar ina leka cikin ɗakin,
cak na haɗe ye ragowar maganar tawa ganin ba Ya Masa'ud ɗin bane Ya SALEEM ne yana dafe da kirjin sa, ina sako kaina idanunmu ya sarkafu da juna, da sauri na janye nawa
baya nayi da sauri nabi bayan Ahmad...
muna shiga ya zauna kan kujera na zauna gefen sa,
yaja riga ta sama ya ciro nonon cikin bra ya ɗaura shi kan kafa ta, yasaka masa cikin baki yaleko fuskarsa yace
"Sha a hankali bada zafi ba."
hannun na ya ruko ya haɗe cikin nasa,
ya dube ni tare da faɗin
"Kyakkyawa ta gobe zamu koma ko."
ido na waro nace "Gobe kuma." kai ya gyaɗa yana murmushi baki na turo nace
"Ni da zan yi wata uku." yace "Wata uku? ina ban isa ba, in kin daɗe kiyi sati ɗaya, gobe ni zan koma akwai abin da zanyi sati ɗaya zakiyi kuma kinci kwana biyu a ciki."
"Haba My sati ɗaya yaushe naje na yi ziyara har Dass fa zani, ni da nake so ma na wuce har Maiduguri garin su Ummi, sati 1 ai ba zai min ba."
"Kidai je Dass amma banda Maiduguri kibari zamu je musu na musamman,sati ɗaya babu kari, bari naje naga gari."
yayi maganar yana mike wa.
nace "Nidai sati 1 ya min kaɗan,wata ɗaya zanyi."
yace "Ni dai natafi ganin gari."
"Idan ka ɓata babu ruwa na." waje yayi yana dariya da faɗin
"Idan har na ɓatan ke zaki fara nima na." bayan sa nabi lokacin har yayi waje da sauri haɗe da sassarfa na iso in da yake naruko hannunsa ina dariya nace
"Ko neman ka bazan yi ba idan ka ɓata."
shima dariyar yayi tare da jan kumatu na yace
"To sake ni naje na ɓatan." kafaɗa na make ina kwantar da kaina a kafaɗar sa nace "A'a to ai ina son ka idan da bana son ka ne sai na barka ka tafi kaje ka ɓatan."
kiss ya manna min a gefen fuska a hankali yace
"Ko zamu tafi tare ne Allah nayi missing ɗin ki."
dasau ri na ɗago kai na ina kokarin barin gurin da sauri ya ruko hannun ya janyo ni yace
"Muje ni?." kai na girgiza ina dariya nace "Jeka kawai." "Zo kiji wani magana." yafaɗa yana kokarin haɗe jikin sa da nawa, yayin da hannunsa ke sarkafe cikin nawa dukkan mu dariya muke ina ɗago wa muka haɗa ido da Ya SALEEM,dake tsaye jikin motar sa da waya kare a kunnen sa da alama waya yake.
kai na nakawar tare da mai da dubana kan Ahmad nace "My ina fashin salla fa."
"Zo muje na gani da ido na."
da sauri na fizge hannuna na juya ina yi masa dariya na koma ciki.. a
ɓangaren Ya SALEEM kuwa da sauri ya shige motar sa ya bargidan da mugun gudu kamar zai tashi sama....
Washegari da safe Ahmad da Uncle Mahmood da iyalen sa suka juya, sabo da ai kin sa.
washegari nima na tafi Dass ni da in da Ya Masa'ud da Fauzan da Nusaiba suka yi min rakiya.
ranar da muka isa Dass nasha kuka gani na ɗakin Inna ta bata nan ciki.
na zaga gida jen ƴan uwa da abokan arziki tun da nazo muna yare da kawata Rabi da yanzu ƴaƴan ta biyar,
ranar da zamu dawo Bauchi ta raka ni lambun Baba na lambu, muka same sa yana ta ai kin ban ruwa wa kayan lambun sa,
ko da ya ganni bai gane ni ba sai da Rabi ta tuna masa ni.
yace "Allah sarki HAMDAH kece kika zamo haka sam ban gane kiba."
nayi murmushi bamu bar gurin ba sai da muka tuno da da na cire mayafi na nasha ɗammara na karɓi tiyo nayi ta bin layi layi ina zubawa shukan ruwa, cike da nishaɗin tuno da baya.
kuɗi na bashi masu yawa nace ya kara jari da su.
yayi ta min godiya yacire min kayan miya yacika min babban laida da su yace naje na sha miya..
Rabi da Mamar ta duk sai da nayi musu alkawarin, musamman Rabi da naga kalar yaruwar da take kuɗi masu yawa na bata nace taja jari da su tasami abin dogaro da kai ita da ƴaƴan ta, nakuma bada kuɗi domin a sasu a makaranta dan duk basu makaranta kuma sun fi su Naseem girma,
muka juyo Bauchi..
ranar da na cika sati Ahmad yakira ni wai sai dai na taso yau nace
dan Allah ya barni na kara wani satin.
da kyar ya amince nayi kwana goma, shima ɗin sai da ya haɗa da Ummi da kanta ta shirya mana kayan mu, ta sa aka kai mana cikin mota.
Ya Masa'ud ne ya shigo ina gyara mayafi na Ummi tana ta cewa nayi na fita kada muyi tafiyar dare, kada na bi na su Aunty Rafee'at mu ɓata lokaci.
hannun su Naseem ya kamo yace
"Wai ku zo." ya janyo hannunsu har sun kai bakin kofa nace
"Ya Masa'ud wake kiran su?."
"Ya SALEEM ne." yayi maganar suna fita daga parlour'n.
da sauri na bi bayan su Ya SALEEM ɗin yana tsaye jikin motar sa su kuma suna daf da isa in da yake.
sauri na kara na iso su narike hannayen su tare da janye su nace
"Ya Masa'ud kar ka kaisu sauri muke."
sai na juya gurin mota na buɗe na saka su ciki nima na shiga na mai da murfin motar na rufe.
yabi motar da ido.
su Bappa suka fito da duk mutanen gidan in da su Bappa suka shige motar da suka zo ciki.
Ummi tazo gefen da nake ta buɗe ta mika min Ahmad tana yi mana fatan isa gida lafiya,
muka yi bankwana da ƴan uwa har muka fita yana nan tsaye a gurin..........!
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 36
A kiɗime na mike tsaye ina faɗin
"My me ya same ka suwaye suka harbe ka My me ya same ka My kayi magana dan Allah!!!."
numfashi yaja da kyar cikin sarkewar murya yace "Nasan bazan rayu ba sun illatani da yawa, kiyi hakuri kyakkyawa amma ki sani da son ki zan mutu ina son ki ina son ki."
ya karasa maganar da jan wani irin. numfashi hade da yin salati.
kuka sosai na fashe da shi ina faɗin
"My kar kayi min haka dan Allah kada ka tafi ka barni dan Allah, ka jira ni zan zo yanzu babu abun da zai same ka zan zo yanzu gani zuwa My kana jina ka jira ni kaji, babu abun da zai same ka."
cikin yanayin jin azaba da fitar numfashi yace
"HAMDAH kada ki zo kinji kyakkyawa ta akwai wan da basu mutu ba a cikin su bazan juri ganin sun nimi illatar da ke ba, na rokeki kibarni natafi cikin salama bada kunar ran abun da zasu yi miki ba, kada ki bari Ahmad yayi kukan maraici."
maganar tasa ce ta sarke yayin da yaja wani irin numfashi mai haɗe da ajiyar zuciya kana salati yabiyo baya.
"Myyyyyy!!!."
na kira shi da karfi jin alamar faɗuwar wayan kasa,
nakuma sakin wani irin kuka mai tsuma rai.
da gudu nayi waje a kiɗime ina kuka da kiran sunan sa ina faɗin kada ka tafi ka barni.
a haka nafito sakar gida yanayin dare shiru babu motsin kowa, sai hasken daya haske ko ina na gidan.
masu gadi suna can bakin get,
kuka mai karfi na sake san da na kuma kiran wayan sa a karo na uku ba'a ɗagawa, direba nashiga kwallawa kira cikin muryar kuka mai haɗe da tsantsar tashin hankali, da iya karfi na nake kiran direba.
da gudu su security da direba suka iso in da nake a tare suna tambayar ko lafiya akwai wata matsala ce.
ban iya basu amsa ba sai cewa direba nayi
"Bani makullin mota." direba yace
"Ina kuma zuwa hajiya da daddaren nan yanzu fa karfe uku saura shin lafiya?."
cikin muryar kuka da karfi nace
"Ka bani makullin mota nace."
jin hayaniya yasa su Bappa fitowa daga sashin su Mama mai awara ma haka ta fito daga ɗayan side ɗin dasu Talatu, da sauri suka karaso in da muke hankali tashe Bappa da Inna Wuro da Mama suka haɗe baki wajen cewa
"Lafiya me ke faruwa?."
ganin yan da na birkice gaba ɗaya Bappa ya ruko hannuna yana faɗin
"HAMDAH ki nutsu mene ne a cikin sashin naki ina yaran suke?."
cikin jan shassheka nace
"Bappa Ahmad Ahmad zasu kashe shi."
cikin matukar shiga firgici Bappa yace
"Su waye zasu kashe shi ina Ahmad ɗin yake kin baro shi a ɗaki ne?."
a zaton sa Ahmad karami ne.
nace "Yana gidan sa Bappa sun harbe shi."
kuka ne yaci karfi na nashi kokarin kwace hannuna Bappa yarike ni gamgam yana faɗin
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un
ki nutsu HAMDAH ki tsaya tukun ba zai yiwu kifita a daren nan ba, ki bari hukuma suje dan zuwan naki akwai hatsari."
Bappa ya dubi security yana faɗin
"Kuje gidan ku kai masa ɗauki."
da sauri suka juya cikin zafin nama cikin hanzari suka shige motocin su suka nufi gidan Ahmad.
Bappa ya dube ni ganin yan da nake rusar kuka yace
"Jami'an sa ne dama shi ya ajesu a gidan nan batare da saninki ba zasu je su kula dashi,
babu komai in sha Allah babu abun da zai faru, ki kwantar da hankalin ki yanzu zasu je suzo miki da shi."
da kyar suka lallaɓa ni na yarda muka koma ciki...
Acan cikin gidan Ahmad
tuni wani makocin sa yayi waya wa jami'an tsaro dan gaba ɗaya unguwar ta ɗauka, sai dai babu wan da yayi yunkurin fita dan jin yan da karan bindiga ke tashi, sai dai kowa yana tsaye a kan kafafun sa a cikin gidan sa.
kan kace me sojoji sun iso unguwar suka zagaye gidan, koda security suka iso sun tadda sojoji a gurin, nan suka haɗe da sojojin.
wasu daga cikin jami'an tsaron suka shiga cikin gidan.
Rasheedat na ɗaki tana ta rusar kuka, jin harbin bindigan ya tsaya ba'a kuma yi ba daga bisa ni tajiyo jiniyar sosoji, sai ta buɗe kanta tafito hankali.
wani irin kaɗuwa tayi
ganin Ahmad kwance cikin jini, tayi kansa tana ihu da kiran sunan sa,
tana faɗin "Aboki sai da nace maka kar ka fito ka fita ta kofar baya wayyo Allah na karkayi min haka Aboki."
polisawan da suka iso yanzu suma motar su guda su suka dakar da ita batare da sun barta ta taɓa shi ba,
sabo da yanayin ai kin su da kuma gudanar da aikin su da suke a lokacin.
ta