Showing 117001 words to 120000 words out of 125808 words

Chapter 40 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

457

rayuwar ka ta hanyar ɓoye hakan acikin zuciyar ka."
"SALEEM." Bappa yakuma kiran sunan sa, kana yace "Kana son komawar auren ku da HAMDAH?."
shiru yayi tare da yin kasa da idanunsa yana wani taune leps ɗin sa,
Bappa yakuma faɗin "SALEEM kana son mai da matar ka?."
nan ma bayyi magana ba sai ɗago idanunsa da yayi ya kuma kallon Bappa, yayin da bugun zuciyarsa ya karo,
Bappa yagirgiza kai tare da yin murmushi irin nasu na manya kana yace
"Miskili kafi mahaukashi ban haushi, to ka faɗawa zuciyar ka ta sami nutsuwa za'a bata abin da take so,
basai tayi bindiga ta fashe ba."
idanunsa ya lumshe tare da jan numfashi mai ɗan tsawo a bayyane, a hankali ya ɗago hannusa izuwa kan kirjin sa ya kife tafin hannunsa kan kirjin nasa dake harbawa da sauri-sauri.
Abbu yace "Bappa shin ka mance abin da ya mata ne kayi hakuri da abin da zan faɗa Bappa, idan aka mata haka sam ba'a kyauta mata ba, kada mu kuma maimaita kuskuren baya,
ya kuma cutar da rayuwar ta,
sam bai cancance ta ba."
Abba yace "Hukun cin da Bappa ya yanke shine kaɗai mafita, shin zamu cigaba da zuba ido ne muna ganin sa cikin halin mutuwa ko rayuwa."
Bappa yayi waje su Abbu suka bi bayan sa,
koda suka fita Bappa ya dube Abbu kana yace
"Ka sani SALEEM bashi da laifi duk abun da ya faru sharrin ma sharranta ne."
Abbu yace "Da kuma halin sa, in da sharrin wasu har da ma halinsa, kada mu shiga hakkin yarinyar nan."
"Kada ku kuma cewa komai a kan gamanar nan na gama yanke hukunci." Bappa ya faɗa yana tafiya hanyar masallaci dake cikin asibitin."


bayan kwana biyu da tafiyan Bappa dasassafe yaqirani yace nazo Bauchi yanason ganina da gaggawa,
natsorata dajin qiran da Bappa yamin na gaggawa sai naqira wayan Ummi danjin mekefaruwa naji wayar Ummi akashe,
jin wayar Ummina akashe Hankalina yayi mummunar tashi atake nazari mayafina naja yarana mukayi waje tunkafin na isa parking space nake qiran Driver, ya iso da gaggawa nace masa maza yanzu mutafi Bauchi,
yana tambayar lafiya hajiya ban saurareshi ba na saka su Naseem cikin mota kawai nima nashiga.
nace masa tafiya mai sauri zamuyi ba ɓata lokaci yaja motar,
cikin awa huɗu da rabi muka iso cikin garin Bauchi saboda gudun da driver yake shararawa.
koda muka iso gida hankalina yayi mugun tashi ganin babu Kowa a gidan numbern Bappa naqira nace Bappa
"Na iso ina mutanen gidan?."
yace kizo asibitin Dr Farouq gamunan anan,
dasauri nafita nashiga motan piiiiiiiii naja motan ko Driver bantsaya qiraba bantsaya ko ina ba sai asibitin.
ina daidaita parking natsaya su Naseem suka biyoni dasauri ina shiga cikin asibin naga mami da Ummi Aunty jaleela Aunty Rafee'a Fauzan Ya Mas'ud
suna gani na suka mike duka suna faɗin
"Zuwan yau she kenan?."
murmushi nayi kana na karaso in da suke, na dube su ina faɗin
"Ina su Abbu da Abba ina Bappa?."
Ummi tace "Suna cikin ɗaki in da aka kwantar da SALEEM."
numfashin mai karfi na sauke jin kowa yana lafiya, nace
"Kai wlh har hankali na ya kwanta na ɗauka wani mummunar abune ya faru ashe dai kowa lafiya."
Ummi tace "Eh to gamu nan dai kowa lafiya amma SALEEM gashi can a kwance babu in da yake."
baki na taɓe tare da faɗin "Allah ya sawaka."
na juya ina kukarin zama kan kujera,
Ummi ta ce "Baki shiga kin duba shi ba kike kokarin zama a nan, je ki duba shi kafin ki zauna."
fuska na ɗan yamutsa tare da mike wa na nufi kofar da take nuna min.
da sallama na tura kofar,
su Abbu suna tsastsaye suka amsa min sallamar,
idaduna ne ya sauka kan gadon dake cikin room ɗin
Ya SALEEM na kwance idanunsa a lumshe numfashin sa yana sama da kasa na'urori suna ta ai ki a jikin sa.
a hankali na karaso cikin ɗakin. tare da soma gaida su Abba, suka amsa suna yi min sannu da hanya.
Bappa yace "Kin iso?." nace "Eh na iso."
yace "To madalla." ya dube Ya SALEEM da ke kwance tare da duba na yace "Kiyi masa sannu da jiki."
naɗan dube shi tare da faɗin
"Ya jiki?." idanunsa ne suka motsa
daga lumshen da suke a hankali yashiga kokarin buɗe su, har ya ida buɗe su a kai na.
a yanayin da yake ciki bana sa ran zai iya amsa ya jikin da na masa dan gaba ɗaya yagama fita hayyacin sa,
kai na na kawar daga gare sa, a hankali ya mai da idanunsa ya kuma lumshe su tare da sauke numfashi mai sauti.
Bappa ya dube ni tare da faɗin
"Zo nan HAMDAH ina da magana da ke."
yayi maganar yana juyawa tare da fita a ɗakin.
nabi bayan sa muka fita can farfajiyar asibitin,
gefe muka samu Bappa ya zauna kan dakali lima na zauna gefen sa.
ya dube ni da kyau yana faɗin
"Kun zu lafiya dai ko ya hanya?."
nace "Lafiya lau." yace "To madalla."
zaman sa yaɗan gyara kana yace
"HAMDAH."
ya jira suna na, na juyo gare sa tare da amsa kiran nasa.
yace "Mene ne matsayi na a gare ki?."
ɗan jim nayi dajin maganar nasa kana nace
"Ko a da da bansan kai waye a gare ni ba, matsayin uba nake ganin ka bare yanzu da ya kasan ce kai ɗin uba ne kuma kaka a gare ni."
yace "Madalla naji daɗin jin hakan ina kuma alfahari da ke, da biyayyar ki nasan bazaki taɓa bani kunya ba, HAMDAH ina son ki sani yau na mayar da auren ki da ɗan uwan ki."
wani irin dadammm kirjina ya buga da mugun karfi, na wani irin mike wa a razane a kuma zabure, ina bin Bappa da wani irin kallo.
Bappa ya ruko hannuna tare da maidani zaune, yace "Ki nutsu kiji abin da zan faɗa miki,
ɗan uwan ki yana cikin mawuyacin hali halin mutuwa ko rayuwa, kuma duk a ta sana diyyar ki ne, kin ganshi kuma kin ga halin da yake ciki, ke kaɗai zaki iya tsamo shi daga cikin halakar dayake dumfaro shi na bugawar zuciya, likitoci sun bamu tambacin har idan yau yagaza samin abinda yake muradi a ciki. zuciyar sa to ba shakka zuciyarsa zata iya bugawa ya mutu,
ke yake muradi a zuciyarsa sabo da gudun kada mu rasashi shi yasa na mai da auren ku da shi yau,
nasan wannan hanyar ce kaɗai zai iya kuɓutar dashi daga cikin halin da yake."
kai na shiga girgiza wa ina faɗin
"Sam bani ce cikin zuciyarsa ba, Bappa Ya SALEEM ya tsane ni baya kauna ta Bappa me yasa zaka mai da ni cikin halaka rayuwa da shi tamkar halaka ce, ina murnar rayuwa ta tasami salama ashe dai a cikin kunci da wuya zan tabbata,
Bappa bana son komawar auren nan dan Allah ka raba auren nikuma zanyi nesa da ku bazaku sake gani na ba tun da bakwa son ganin farin ciki na,
aure na da Ya SALEEM tamkar rugujewar farin ciki nane, wata a zabar zan kuma fuskanta ta sanadiyyar sa a karo na biyu."
kuka ne nafashe da shi tare da haɗe hannaye na ina faɗin
"Dan Allah dan Allah Bappa karaba auren nan wlh bana so."
numfashi Bappa ya sauke kana yace
"Kiyi hakuri ki ceci ɗan uwan ki kada ki bari ta sana diyyar ki ya mutu, babu abun da zai faru da rayuwar ki Allah bazai bawa azzalumai masara tsoron Allah nasara a kan ki ba,
ɗan uwan ki na bukan ki ke da ƴan shi."
kai narika girgiza wa ina faɗin
"A'a a'a Bappa dan Allah, ba ƴaƴan sa bane su ba ƴaƴan sa bane."
na mike zumbur da sauri naje na ruko hannun su Naseem na jasu da sauri nanufi mota, muka shiga muka bar asibitin...


Motar Bappa yabi da kallo kana ya mike yashiga ciki,
a bakin kofar ɗakin da SALEEM ke ciki ya haɗu da su Abbu har da su Mamie suna tsaye kowa yayi jungun-jungun, jiki a sanyaye Bappa ya iso in da suke yana faɗin
"Ya'ya lafiya?." Abba yace "Ina HAMDAH take......
8/19/22, 11:01 - Ummi Tandama😇: 39







Bappa yace "Ta tafi bata tsaya ta saurare ni ba, bata kuma taɓa yimin haka ba, HAMDAH, bata taɓa ketare magana ta ba, hakika tana cikin tsoro da tuno rayuwar ta ta baya tana tsoron kada ta kuma shiga halin da ta shiga a baya."
cikin rawar murya da zubda kwalla Ya Mas'ud yace "Bappa numfashin Ya SALEEM yana kokarin barin jikin sa."
salati Bappa yayi da sauri ya shige cikin ɗakin in da likitoti suke tsaye ca a kansa.
tuni kowa ya fara kwalla su Aunty Rafee'at har da jan shassheka,
Mamie tayi baya duk daure zuciyar ta da take sai da hawaye suka zubo mata,
ta zauna a gefe tana mai cigaba da zubda kwalla.
da sauri Ummi ta nufi kofar fita tayi waje,
direba ta saka ya kaita gida da sauri tana isa,
direct sashin ta ta wuce tun daga parlour take jiyo shesshekar kuka, da sauri ta karasa cikin bedroom.
ina zaune cikin ɗakin nahaɗa kai da guiwa sai rusar kuka nake,
a sannu ta karaso kusa da ni ta zauna gefe, a hankali ta dafa kafaɗa ta tare da kiran suna na tace
"HAMDAH na tabbata kinsan kuna da ɗacin rabuwa irin na mutuwa, HAMDAH ga uwa can tana kukan rabuwa da ɗan ta da yake kokarin barin duniya a ta sanadiyyar ki, shin bazaki zamo mai yafiya a rayuwa ba, shin kin san falala da tarin lada a gun duk wan da ya ceci wani daga faɗa wa wata halaka, ɗan uwan ki ne fa shi shin ashe bazaki zamo mai share mana hawaye ba, ni mahaifiyar ki ina mai rokon ki da kije ki ceci ɗan uwan ki, ba zanyi miki dole ba amma ki sani har idan SALEEM ya mutu duk ahali zamu rataya miki alhakin mutuwar sa a kanki,
sannan baza mu taɓa dai na ganin ki a matsayin wan da takasa taimakon ahalin ta ba."
Ummi ta mike tana sharar kwalla ta nufi kofa zata fita,
da gudu na mike naje na ruko hannun Ummi, cikin muryar kuka nace
"Ummi na kiyi hakuri kar kuyi fushi da ni Ummi ina jin tsoro ina jin tsoro ne."
kai ta girgiza min tare da share min hawaye ta ruko hannuna gam-gam
cike da karfafa guiwa tace
"Babu abun da zai faru da yardar Allah kisawa zuciyar ki hakan, zamu tsaya miki da karfin ikon Ubangiji babu abin da zai kuma faruwa."
kai nashiga gyaɗa wa alamun gamsuwa yayin da hawaye ke ci gaba da zuba a ido na.
ta janyo hannuna ta haɗo da na su Naseem muka fita.
koda muka iso asibitin hannuna Ummi ta kuma ruko wa tana ɗauke da Ahmad karami Naseem da Nasmah suna gaban mu, muka shiga asibitin.
su Mamie da Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Nusaiba Fauza suna tsastsaye a bakin kofar ɗakin da Ya SALEEM yake ko wannen su kuka yake da hawayen sa,
jiki a sanyaye muka karaso in da suke, hankali tashe Ummi ke tambayar su lafiya. cikin zubda kwalla
Aunty Jaleela tace "Ummi Ya SALEEM baya numfashi."
tuni hawaye yafara zuba a idanun Ummi,
niko jiki na ne ya ɗau ki ɓari, Ummi ta kuma ruko ni gam ta janyo ni muka shige cikin ɗaki.
doctors ne ke tsaye a kansa suna ta fafutukar ceto numfashin sa,
Bappa Abba Abbu Ya Mas'ud suna tsaye a gefe.
Bappa sai anbaton sunan Allah yake Ya Mas'ud ko sai sharar kwalla yake, lokaci zuwa lokaci Abba ke kai hannunsa karkashin idanunsa yana share ɗan guntun kwallar dake fito masa, a ɓangaren Abbu ma haka.
ɓarin jiki na ne ya karu lokacin da idanuna ya sauka kan Ya SALEEM dake kwance ko matsi baya yi babu alamun numfashi tattare da shi,
sosai jiki na ke kakkarwa, zuciya ta tayi rauni tausayi mai haɗe da kawa zucin ɗan uwa suka lulluɓe ni, ko ba komai Ya SALEEM jina na ne dole naji makamancin hakan a tattare da ni, domin ɗan uwa yawuci wasa koda ace kuwa a kullum yana kuntatawa rayuwar ka, ka gansa a gaban ka tamkar mutacce dole zuciyar ka ta girgiza.
da sauri na fizge hannuna da gudu na fasa sakanin doctors ɗin na faɗa a jikin sa tare da girgiza shi ina faɗin
"Ya SALEEM kar ka mutu ka tashi dan Allah ka tashi kar ka mutu Ya SALEEM Ya SALEEM Ya SALEEM".
na karasa da kiran sunan sa da karfi ina mai jijjiga shi.
tuni Naseem da Nasmah suka saki kuka suna kiran Daddy Daddy.
sosai nake gargiza shi ina kiran sunan sa yayin da nake rusa kuka mai karfi,
a raina ina ayyana shike nan babban yayan mu ya tafi ya barmu, duk miskilancin halin sa da rashin dariyar sa muna son sa a haka, ga ƴan uwa na da mahaifiyar sa tana kukan rashin sa, hakika rashin wani naka na da zafi, shike nan shima ya tafi bazai dawo ba, kamar yadda Inna da Ahmad suka tafi tafiyar da babu dawowa..
wani kuka ne nakuma sake wa da karfi ina faɗin
"Ya SALEEM kai kar ka tafi dan Allah kada ka tafi ka barmu ka tashi Ya SALEEM ka tashi."
nayi maganar ina mai girgiza shi da karfi.
fuska ta na kife cikin kirjin sa ina jujjuya fuskar tawa da gogashi cikin kirjin nasa ina mai ci gaba da kukan.
a sannu ya sauke wani irin numfashi mai tsawo kana yashiga motsi da idanunsa.
cikin matukar mamaki likitotin ke kallon ikon Allah, mutumin da numfashin sa ya tafi bugun a gogon hannun sa ne kaɗai yake iya tabbatar musu da yana raye shima bugun hannun nasa yana daf da tafi dan sai ya ɗau tsawon mintina masu dama kafin ya ɗan buga sai ka lura sosai kafin ga gane hakan shima,
da sauri su Bappa suka maso suna mai mamakin hakan suma, dan gaba ɗaya sun gama cire rai da shi suna jiran jin ta bakin likitotin kawai.
da sauri na ɗago kai na jin yana motsa jikin sa na kurawa fuskar sa iso, ganin idanunsa suna motsi a lamar yana son buɗe su.
da sauri nace "Ya SAKEEM buɗe idanun ka Ya SALEEM ka buɗe ka huɗe kada ka tafi ka harmu."
a hankali yashiga buɗe idanun nasa har ya ida buɗe su a kan fuska ta,
a sannu ya ɗago hannunsa ya sauke sa kan nawa ya rike shi gam, a hankali ya juya fuskarsa in da su Naseem suke yayi musu alama da hannu da suzo in da yake, suka matso bakin gadon suka kwantar da kansu a jikin sa, numfashi mai sauti ya sauke yana mai daɗa damke hannuna tare da shafa kan yaran da hannunsa guda.
gaba ki ɗaya ƴan cikin ɗakin farin ciki ne bayyane a kan fuskokin su,
hatta likitotin, ɗaya daga cikin Dr ya dube ni da murmushi yace
"Sannu da taya mu ai kin da ke kokarin gagarar mu."
"Itace maganin ai."
ɗaya Dr dake kusa da shi ya faɗa yana ɗan dariya...

Ya Mas'ud yafita da sauri sai gashi da su Mamie sun shigo har suna rige-rigen shigo wa.
fuskar Mamie ɗauke da murmushi mai bayyana tsantsar farin cikin ganin sa ya farfaɗo daga sammanin mutuwar da suka saka masa.
kowa sai sannu yake masa, sai dai babu wan da ya amsa shi, hakan bai dami kowa ba dan kowa yasan hakan halin sa ne.
hannu na dake cikin nasa na ɗan motsa ina kokarin janye hannun nawa,
dan irin kallon da yake min yasa ni jin wani iri cikin jikina, ga kuma idanun kowa a kanmu.
gam yada ɗa rike hannun nawa bai kuma fasa bina da irin wannan kallon ba.
Aunty Rafee'at da bakin ta ya kasa rufuwa dan murna ta juyo ta kalli mijin ta Dr Farouq, shima murmushi yayi tare da ɗan dungurin ta cikin kasa da murya ya ce
"Kin ga yayan ki ko so nason kashe shi ga kallon da yake mata kamar bashi bane ɗazu ke kokarin mutuwa."
hararar wasa tayi masa tace
"To an faɗa maka so karya ne."
yace "Ni zan bada shaida ba karya bace gashi ina kan fama da shi a kan ki."
ya karasa maganar da kashe mata ido,
dariya tayi tana ture kafaɗar sa...


Hannu na na zare cikin nasa da ɗan sauri cikin jin kunya ganin su Abbu sun matso kusa da shi suna yi masa sannu,
shiko idanunsa na kaina, yana yi min wani irin kallon cikin ido.
baya nayi ina mai jin kunya.
bayan wasu ɗan mintina likitoti sukace a ɗan bashi guri ya huta bayan sun masa allurai...
a ranan da yamma Ya SALEEM yace shi zai koma gida, Dr Farooq yace ya bari ya daɗa jin kwarin jikin sa,
yace shi sam zai tafi dan shi lafiyar sa lau,
sai da su Bappa suka sa baki kafin da kyar ya yarda.
kwanan sa uku a asibitin kullum a can muke wuni dukan mu, idan na shiga ɗakin yi masa sannu da jiki haka zai kafe ni da ido yata kallo na kamar bai taɓa sani na ba.
su Nasmah kam ko da yaushe suna jikin sa, sai dare idan zamu koma gida suke rabuwa da shi.
ranar da ya cika kwana huɗu yace bazai kuma kara kwana cikin asibitin ba, dun dole a ka bashi sallama.
nuka koma gida kowa hankalin sa kwance da farin cikin samun lafiyar sa.....


A ranar Abbu ya sa a ka kirawo ma'aikatan gidan Ya SALEEM dukan su waɗan da suka yi aiki lokacin ina gidan, wato waɗan da suka bada shaida kan sunga wani yana zuwa guri na lokacin da Ya SALEEM yayi tafiya.
dukkan mu a parlour'n Mamie muka haɗu,har da Ya SALEEM da Abbu yayi masa dole yabaro ɗakin sa na cikin gidan yazo gurin taron.
ganin ma'aikatan ya sani tuno wa da abunda ya faru a baya sai nake ganin kamar yau hakan ta faru.
bayan addu'a da Bappa yayi Abbu yayi gyaran murya kana ya dubi ma'aikatan ɗaya ba yan ɗaya,
Baba Mai gadi Sani direba Habu mai shara sai Salele wan da shi a lokacin bai bada shaidar ba sai dai kasan cewar yana aiki a lokacin yasa shima a ka gayyato shi.
Abbu ya dube su da kyau yace
"A wancan lokacin kunyi kokarin bata mana family kuka kuma yi sana diyyar raba aure da tarwatsa mana family, dukkan ku bazan kyale kowa ba zan ɗau mataki a kanku zakuyi bayani a gaban kotu, har da kai da girman ka mai gadi baka ji kunyar bada shaidar karya ba."
baba mai gadi yashiga jan hanci da matsar kwalla yana faɗin
"Allah ya huci zuciyar ka Alhaji ayi hakuri wlh sharrin shaiɗan ne, amma da fari na ki karɓar kuɗin da Hajiya ta bamu kan muyi shaidar, tace har idan bamu yi abun da tace to to abakin aikin mu shine naji tsoro na karɓi kuɗin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login