Showing 90001 words to 93000 words out of 125808 words
karami...
muna isa motoci suka kwashe mu suka kai mu masauki, ni da Ukhtee ɗakin mu ɗaya Naseem da Nasmah kam ma ban ga idanunsu ba.
a gaye muka shiga rage kayan kijin mu,
ganin Ahmad karami ya nata mita nasan cewa wan ka yake bukata, na tuɓe sa nayi nashiga dashi bayi nayi masa wanka cikin bathtub dan dole sai dai nan ɗin tun da ba bu wabon da zan masa a ciki, na naɗo sa a towel ɗin sa na sauya masa wani kaya, dan gani kawai nayi an biyo mu da akwatin mu.
sai da yayi bacci kafin na shimfida shi, lokacin Ukhtee tafito daga wanka, nima na shiga nayi wan ka, yau kam babu wani hira muna kwanciya dukan mu sai bacci..
washegari ban farka ba sai wajen karfe 9.
ko da na farka na tadda Ukhtee har tayi wanka, ina dire a gadon Ahmad na buɗe ido, sai da na fara yi masa wanka kafin nima nayi. kayan
breakfast ɗin da aka shigo da shi tun ina bacci, bayan na shirya na zauna muka yi breakfast ɗin, sai tan nan naje na ɗau wayata da na kashe ta tun jiya isowar mu na kunna.
ai ko ina kunnawa sai ga kiran Ahmad ya shigo, yace
"Kyakkyawa ta an tashi lafiya ya gajiyan jiya."
nace "Gajiya ya washe."
yace "Alhmdllh Nagode wa Allah, ina Ahmad ya tashi kuwa ga su Naseem har yanzu basu farka ba." nace
"Shikam ina tashi shima ya farka gashi nan yana ta rarraba idanu."
dariya yayi yace "Sa masa wayar kusa da shi naji numfashin sa."
wayar na kawo kusa da shi nace "Daddy na magana." murmushi yayi mai sauti yace "Shafa min kansa." nace To.
yace "Anjima karfe 12 za'a tafi gurin nan, karfe 2 za'a gama yau zamu koma gida."
nace "To Allah ya kaimu."
yace su Naseem su tashi bari ya yi musu wanka zasu shigo nace to...
Da misalin karfe 12 da kwata gaba ɗayan mu muka hallara a farfajiyar hotel ɗin.
nan motoshi suka rika kwasan mutane suna tafiya da su.
kamar yan da muka tafi wancan filin taron jiya motar mu ɗaya da shi yau ma haka,
tun daga wajen kamfanin har cikin sa an zagaye shi da adon fulawa, a katafare filin da ke cikin kamfanin aka gudanar da taron, wan da mai girma Gwamnan Lagos shine babban bako a gurin taron da sauran mukarraban sa.
an guda nar da taron cikin lumana da kwanciyar hankali in da ake nuna taron kai tsaye a kafafen sadar wa.
anan gurin aka tantance ma'aikatan da suka nimi yin ai ki a kamfanin, aka kara akan wan da dama can aka tantace su kwararru masana ai kin...
karfe 2:30Pm aka watse a taron kowa ya kama gaban sa, a ranar wasu suka koma kasashen da suka fito wasu kuma sai zuwa gobe.
da misalin karfe uku jirgin mu ta ɗaga zuwa Abuja.
muna isa yau washegari Ukhtee tace zata koma, Ahmad yayi mata cuku-cukun komawa sai dai ba'a sami jirgin da zai tafi Saudi kai tsaye ba dole na dubai daga can sai ta shiga jirgin Saudi.
har airport muka yi mata rakiya Ahmad na ta yi mata godiya, bayan cike ta da yayi da goma na arziki.
lokacin da ake sanar wa kan fasinjoji su shigo cikin jirgi sai muka rungume juna muka fashe da kuka, da kyar Ahmad ya ɓanɓare ni a jikin ta jin ana ta cigaba da sanar wan, ta wuce cikin jirgi muna ɗagawa juna hannu...
a mota yayi ta lallaɓe na har sai da yaga nayi dariya, ya dube ni fuska ɗau ke da sihirtaccen murmushi mai bayyana zallar so da kauna yace "Ina son ki kyakkyawa ta."
idanuna na lumshe kana a hankali na kwanto da kai na jikin kafaɗar sa a hankali cikin yin kasa da murya nace
"Nima ina son ka My."
wani irin wawan burji ya ja, da sauri na buɗa idanuna na ɗago kaina da sauri cikin hanzar na dafe gefen kujerar moton jin yan da nayi gaba kamar zan garo da gaban motar.
a gefen titi yayi parking, ya wani irin jan yo ni ya rungume tamkar zai cusa ni cikin jikin sa, yace
"Nagode kyakkyawa ta Nagode da jin fitar wannan kalma daga bakin ki, ako da yaushe zaman jiran sa nake naji yafito daga bakin ki,
ina son ki! ina son ki!! ina son ki!!!, ako da yaushe kamar daɗa kara min son ki ake."
sai ya shiga sumbatar fuskata ta ta ta ina yarika manna masa kiss,
ya ruɗe yagama zauce wa, sai kokarin daɗa nuna min yanda yake so na da kuma kauna ta yake.
sai da na janye jikina da karfi nace Ahmad na gida zai iya yiwa Inna Wuro kuka.
kafin ya ja motar muka bar gurin,
yana tukin sai ya juyo ya sumbaci kuma tu na, aha muka isa gida.
ranar bai matsa ko nan da can ba a yana like da ni, karshe Inna Wuro fita tayi ta bar mana side ɗin gaba ɗaya sai dare ta dawo....
Bauchi
Ranar da aka gudanar da toron buɗe Company HAMDAH duk ka family'n su suna gindin TV, Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela suna daga gida jen su suna waya a gida, cike da murna suna tambayar suma suna kan kallo ko.
Ummi farin cikin ta har ya gaza ɓuya duk tarin kawai cin ta.
washegari da sassafe Ummi ta tashi da shiri, Abba ya shigo ya same ta tana ta shiri, da ɗan mamaki ya dube ta yace "Shirin me kike ta yi haka?."
tace "Gurin ɗiya ta HAMDAH zani."
ta faɗa a takai ce ta cigaba da shirin ta.
Abba yaɗan yi gyaran murya kana yace
"Yan zu muka gama magana da Yaya Idris ya kama ta ki bari mu shir ya tafiyar duka."
da sauri Ummi ta ɗago ta dobe shi tace
"Babu abun da zai hanani tafiya yau sai ikon Allah, idan kana tunanin cewa ma zaka kuma dakatar da ni ne, kamar lokacin da kayi ahakan a lokacin da take bukatar taimako da mafaka, na amin ta nayi maka biyayya to ka sani a yanzu bazan taɓa hanuwa ba, zan fita naje na nimo ƴata tun da har Allah ya nuna min tana nan da ranta, sai dai daga nan kakuma cewa kada na dawo maka gida,
ko ban same ta ba na tabbata banyi asara ba."
shiru Abba yayi yana kallon ta yayin da jikin sa gaba ɗaya yayi sanyi,
tabbas yasan Ummi mata ce mai hakuri da kawai ci, duk da shi ya kori HAMDAH da kansa ko dai-dai da rana ɗaya bata taɓa nuna masa ɓacin rai ba, kuma bata gushe kan biyaytar da take masa ba.
yana tsaye tagama shirin ta ta ɗau mayafin ta, taɗau jakar ta tayi waje.
ya biyo yana faɗin
"To ki tsaya direba ya kai ki." bata ko saurare shi ba.
a sakar gida suka haɗu da Abbu ya tambaya ina zata, Abba ya faɗa masa, Abbu ya jinjina kai cike da yabawa da hakuri da kawai ci irin na Ummi yacewa Abba kada ya dakatar da ita da tafiyar, tafiyar nata shine zai samar mata da mutuwar data rasa shekarun baya da suka wuce tun barin HAMDAH gida, wan da ta rika dauriya da juriyar iya danne shi ta barwa ranta...
Ummi na fita a dai-dai ta ta tsara ya kaita tasha daga nan ta shiga motar Abuja, idan bata man ce ba anan taga taron bikin farko da su HAMDAH sukayi, kuma taji ƴan jaridun suna faɗin daga Abuja,
taɗau haryan Abuja da tunanin idan ta neme ta bata same ta ba zata wuce Lagos in da taga an gudanar da taron buɗe kamfanin ta.........!
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 31
Koda Ummi suka iso Abuja ta sauka a tasha, tunanin ta in da zata fara ta shiga yi.
mene ne abin yi tayi tambaya a babban gari irin wannan tana ganin kamar babu mafita a yin hakan,
to amma ai HAMDAH ta sanu a yanzu wata kila baza ta sha wuya wajen samo ta ba.
a da ire-iren irin waɗan nan tunanin ta tsare mai abun hawa, ko da mai taxe ya tsaya ya loko ta yana faɗin
"Hajiya ina zuwa?." tace "Malam ko kasan gidan wata da ake cewa HAMDAH?."
ɗan shiru yayi alamun tunani kana yace
"Gaskiya ban sani ba wace unguwar take?."
tace "Ban san unguwar da take ba." yace "To in banda abin ki Hajiya zaki tsari mai abin hawa baki san in da zaki ba, a gari irin wannan zaki tambayi wata batare da sanin adireshin ta ba ai ba lallai ki iya samin ta ba ko a kauye ba'a haka bare a birnin tarayya."
yaja taxes ɗin sa yayi gaba. Ummi tace
"In sha Allah zan same ta ko batare da adireshi ba."
wani ta kuma tsare wa shima irin tambayar da tayiwa wancan shi tayi masa,kusan irin amsar da wancan ya bata irin shi shima wannan ya bata.
ta tsari masu taxe da suka gai kusan guda goma duk kusan amsa iri ɗaya suke bata idan tayi musu tambaya kan sun san gida wata da ake cewa HAMDAH...
har yamma tana tsaye a bakin titi, wani mai taxe ɗon taxe yazo zai wuce da ido kawai ta bishi dan har ta gaji da tsare masu abun hawa, ta fara tunani ta sami masauki ta huta dan ma Allah ya taimake ta tayi salla cikin tashan lokacin da suka sauka.
har ya ɗan gota ta sai ya dawo da baya yace
"Ina zuwa Hajiya?. a ɗan gajiye ta dube shi tace "Masauki mafi kusa da nan."
yace "Hotel kenan?." tace "Eh." yace "To shigo muje." taɗau jakar ta tashige cikin motar da bismilla.
har sun fara tafiya sai me taxe ɗin ya ɗan waigo kana ya mai da idanunsa ga titi yace
"Babban hotel kike so a kai ki ko me ɗan dama-dama?." tace "Me ɗan saukin kuɗi dai wanda bazan kashe yafi dubu hamsin ba."
kai ya jinjina kana suka cigaba da tafi,
sun iso daf da hotel ɗin me taxe yace "Yau wa gamu mun iso bari na karasa da ke can basai kin tsallaka ba sai ki shiga."
tace to. baki ya washe "Amma Hajiya a garin nan fa komi dare ana samin mota duk garin da kike son zuwa zaki sami mota, ai da zai fi miki akan ki kashe kuɗi mai yawa gara ki shiga mota ki wuce gaba ɗaya,
ko da shike manya basu fiye son zaman mota da yawa ba wai shima wahala ce agurin su, kai talaka kam gara ka wuce ɗin ka adana kuɗin da zaka nimi masauki kayi wata bukatar da shi."
yakara sa maganar yana cigaba da washe baki.
Ummi tace "Allah ya rufa mana asiri duniya da kiyama, amma ba wani gari zanje ba iya ka ta nan garin idan ban dace ba kuma sai na wuce Lagos,
ni gidan wata nake nima tun ɗazu na iso garin nan gashi har yamma tayi, ina ta tambaya ban dace ba."
yace "Tambayar gidan wata a cikin garin nan, gaskiya zai yi wuyar samu in ba wai kasan adireshin gidan bane, to ke baki da lambar ta ne ki kirata tayi miki kwatance?."
Ummi tace "Bani da lambar ta."
yace "To gaskiya zaki sha wuya ne kawai wajen neman ta, manya ne waɗan da aka sansu akasar sune idan kashigo niman su cikin garinnan bazaka sha wuya wajen samun su ba, tun da sun sanu yawanci zakiga an san su, gaskiya zaifi ki koma gida ko kuma ki kira aturo miki lambar ta sai ki neme ta, amma ya sunan ta ko sunan take kusa da su wata kila manya ne tanan zaki iya dace wa?."
tace "HAMDAH sunan ta." yace "Wai to Allah yasa ki dace."
tace "Amin ngd." dai-dai nan yagyara fakin ta sauka ta biya sa kuɗin sa, taɗau jakar ta ta gangara hanyar da zai sada ta da cikin hotel ɗin.
har ta kai bakin get ɗin hotel ɗin taji ana faɗin
"Hajiya Hajiya Hajiya." ta juyo dan gani ko da ita ake sai taga mai taxe ɗin nan ne yayi ribas ya dawo da baya, kanta ta nuna alamun ita yace Eh.
sai ta juyo ta nufi in da yake.
kansa ya leko ta window motar yace
"Hajiya kika ce meye sunan wan da kika zo neman ta?."
tace "HAMDAH." yace "Babu wani inkiyar ta HAMDAH ɗin ne kaɗai?."
shiru Ummi ta ɗan yi tana son tuno sunan da taji an kira ta da shi a TV da kuma wan da ta taɓa gani a wani gidan mai.
mutumin yace "Dama akwai wata ce me irin sunan nan sai dai tana da inkiya, mutane da dama basu san ta da ai nahin sunan taba sai inkiyar nata,sau ɗaya nataɓa jin ainihin sunan nata shine nake tuna nin ko ita ɗin ce."
Ummi tace "Tabbas akwai sunan da ake kiran ta da shi amma naman ce."
yace "To wata kila ba ita bace ni wanda na sani idan kuma ban mance ba HAMDAH baji an faɗa amma sunan da aka fi sanin ta dashi shine wan da take amfani da shi kan kamfanoni da gidajen mai asibitoti da sauran su, shine *HAM'NAS* ita kuma matar Ahmad Tijjani Sabil ne."
da sauri Ummi tace "Kwarai kuwa tabbas ita ce so nake na tuna "*HAM'NAS* ɗin na mance, dan Allah bawan Allah kai ni gidan nata."
yace "To a gaskiya dai ni ban san gidan ta ba gidan Ahmad Sabil ɗin kaɗai na sani kuma ance gidan ta da ban ne, sannan kuma gidan sa a gaskiya akwai matakan tsaro ko na kaiki ma ba lallai bane a barki kishiga in ba wai an san da zuwan ki bane."
ɗan shiru yayi sai kuma yace "Amma dai shigo mu je tun da kin ce ita ce samun gidan ta bazai bada wuya ba sai muyi tambaya."
godiya Ummi tashiga yi masa da addu'ar samun nasara a rayuwar sa.
Tun daga gurin suka fara tambaya har suka sami wan da yayi musu kwatance har unguwar da take da kuma lambar gidan.
suna isa dai-dai gida mai lambar da aka faɗa musu ya tsaya yace da ita sun iso, ta sauka tayi ta masa godiya kana ta baki 5k, ya karɓa shima yana yi mata godiya, kana yaja motar sa yayi gaba.
ido ta zubawa katon gidan wan da tsaruwan sa ya kai ya kawo a ranta take faɗin.
anya kuwa gidan ne, anya ma kuwa HAMDAH suka gani a TV ko dai idanunsu ne ke yi musu gizo, ko dai wata ce me irin sunan ta suka gani suke tunaɗin ɗiyar su ce?.
kai ta jinjina yayin da jikin ta ya ɗanyi sanyi da tunanin afili ta furta
"Sai na ga wannan ɗin idan na tabbatar da ba ita ba bace sai na tafi na cigaba da niman ki HAMDAH."
a hankali ta karaso bakin get ɗin ta kwankwasa har sau uku, kana mai gadi ya taso ya buɗe karamar kofa ya leko kansa yace
"Wane ne?." tace "Nice." yace "Gurin wa kika zo?." tace "Gurin HAMDAH." ɗan shiru yayi kana yace "Tasan da zuwan ki ne?."
Ummi tace "Bata san da zuwa ta ba."
yace "To ba a bamu masaniyar cewa wata zata zo ba ki nimi izinin shiga kafin idan aka sanar mana sai ki shigo."
yana kokarin mai da kofar yarufe
tayi saurin cewa "Dan Allah kace mata Mamar ta ce ta zo."
yace "Maman ta haba Hajiya mun saba jin irin wannan."
ya mai da kofar zai rufe da sauri tamaso bakin kofar tana faɗin
"Ganin ta kawai zan yi idan ba ita bace bama ni zan tafi." wani
security ne ya mike daga in da yake zaune ya zo bakin kofar yana faɗin "Mene ne wa tazo gurin sa?."
maigadi yace "Wai gurin Hajiya ta zo wai ita mamar Hajiya ce, nace mun saba jin irin wannan masu neman taimako su rika fakewa da ƴan uwan ta ne sai sun shiga kaji babu abin da ya haɗa su."
jami'in tsaron yace "Ita ta gayyaci ki ina katin shaidar."
Ummi tace "Bata san da zuwa ta ba kuce mata mahaifiyar ta ce tazo."
sauran security suka mike daga in da suke tsaye cikin faɗa suka ce
su rufe kofar takira a sanar musu tukun abar ta ta shigo.
maigadi ya rufe kofar.
yana faɗin "Mutane babu godiyar Allah kaduba wannan matar kwata-kwata batayi kama da mabukata ba amma hali irin na mutum kabari a bawa na kasa da kai wai kai ma sai ka nimi kari."
Faty da ta fito daga side ɗin su zata je gidan makotan su gurin kawarta, ta nufo bakin get tana hango yan da security suke magana da faɗa-faɗa da alama dai da wani wanda ya nimi shiga gidan suke,
ta karaso bakin get ɗin, mai gadi ya mike ya buɗe mata get tasa kai zata fita, sai ta hango Ummi a tsaye a gefe tayi jigum.
sai ta leko tace wa maigadi
"Wace ce wannan ɗin?." mai gadi yace "Wai gurin Hajiya tazo kuma mu Hajiya bata bamu masaniya kan cewa wata zata zo ba, wai cewa tayi ita mamar Hajiya ce."
Faty ta dube ta kana ta karasa fita waje."
kana mai gadi ya mai da kofa ya rufe.
har Faty tazo zata gota ta sai ta ce mata sannu.
Ummi ta amsa da yauwa, kana ta wuce.
Ummi kuwa gefe da get ɗin ta nima guri ta zauna, a ranta take ayyana bazata tafi ba har sai taga wannan HAMDAH'N idan ba HAMDAH'N ta nane
sai ta tafi...
Har Faty ta gama zaman ta gurin kawar ta tafito lokacin yamma tayi sosai,
tayi mamakin gani matar nan har lokacin zaune a gurin.
har tazo bakin get zatayi knocking sai ta juyo ta dubi Ummi daɗan fuskantar tausayi ganin ta zauna shiru, tace "Wai wa Adda HAMDAH kika zo gurin ta."
da sairi Ummi ta juyo tare da gyaɗa mata kai, Faty tace "To ki kirata ki sanar mata kina bakin get zata sa mai gadi ya barki ki shigo, in ba haka ba security baza su barki ki shigo ba."
Ummi tace "Bani da lambar ta, amma dan Allah kice mata mamar ta ce ta zo."
kai Faty ta gyaɗa da mamakin matar jin tace wai ita mamarta,ita kuma wannan kalar nata salon kenan ko ba komai in ta faɗi haka ai za'a barta tashiga, gata kuma zubin ta baiyi kama da irin masu zuwa suna karyace-karyacen nan dan a barsu su shiga cikin gidan ba.
kai Faty ta jinjina.
sai tayi knocking maigadi ya buɗe ta shige ciki.
Ummi ko zama ta kuma gyara wa.
ganin lokacin sallar magriba saura kaɗan ga unguwar shiru babu ko motsin mutane, tun da ta zauna ita dai bata ga wani mutum yazo ya wuce ba sai dai motoci ɗai-ɗai su zo su wuce, unguwar shiru kamar