Showing 96001 words to 99000 words out of 125808 words

Chapter 33 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

464

ta, kin yanzu baya fita ko offece kullum yana ɗaki,
daga zaran bacci ya ɗauke sa zai fara kiran sunan ta, idan naji haushi na bubbuga shi ya tashi yana farka wa zai ruko ni yana faɗin
HAMDAH, ke Aminiya ina cikin babbar matsala dan Allah yanzu muhaɗu agurin boka ai, ko nawa yake so na kara masa ni zan basa, nifi son ai kin da za'a yi sha yanzu maganin yanzu, bana son ai ki mai jinkiri shi yasa nake son ai kin boka na kan dutu, ban so mutuwar sa ba da yana nan da duk haka bata faru ba,
dan Allah aminiya mu haɗu yanzun nan gidan boka gani nan fitowa."
ta kashe wayar ta mike ta zari mayafin ta da makullin mota tayi waje.
SALEEM na zaune gurin hutawar sa ya hango ta ta shige mota tayi waje,
da ido yabi ta har tayi waje, a zahirin gaskiya kuwa hankalin sa ba ya tare da shi, ya milla yayi nisa daga gare sa,
a hankali ya kai hannunsa ya dafe kirjin sa yayin da ya fara tari a hankali babu kakkautawa.
wani irin zafi da zugi zuciyar sa yake masa, a hankali ya mika hannu yaɗau ɗaya daga cikin wayoyin sa da suke aje kan table ɗin gaban sa wan da ya ɗaura kafafun sa a kai,
yayin da hannunsa ɗaya ke dafe a kirjinsa.
Dr Farooq ya kira bayan sun gaigasa yake Dr Farooq yake tambayar sa yaya jiki?.
bai amsa tambayar ya jikin da yayi masa ba sai cewa yayi
"Ka faɗa min sunan wani maganin da zan sha."
Dr Farooq yace "Wan can ɗin baiyi maka amfani bane?, to gaskiya kazo asibiti kawai zai fi a duba ka da kyau a baka magani, Please Ya SALEEM ka zo yanzu."
bai yi magana ba sai sauke wayar da yayi a kunnen sa,
a sannu ya mai da bayan sa jikin kujera tare da lumshe idanunsa har lokacin hannunsa ɗaya na dafe a kirjin sa.
Dr Farooq yakira sa har sau biyu bai ɗaga wayar ba, yana jin wayar tana vibrate bai ko buɗe idanunsa ba.
sai da yaji alamar shigowar message kafin ya buɗe lumsassun idanunsa ya ɗau wayar yana duba sakon da ya shigo masa,
Dr Farooq ne ya ai ko masa da sakon cewa dan Allah yazo asibiti kada ya ɓata lokaci.
bayan da ya gama karanta sakon sa sai ya mike ya kwashi wayoyin sa yanufi side ɗin sa.
sai da yayi wanka ya shirya kana ya ɗau makullin motar sa ya nufi asibitin, ko da ya iso asibitin.
bayan tambayoyin da Dr Farooq yayi masa kan ciwon nasa, ƴan takaitartun amsoshin da ya basa da shi yasamu damar yi masa gwaji kan abun da yayi hasashe bisa amsoshin da ya basa..
lokacin da Dr Farooq yaga result ɗin test ɗin ya jijjiga ba kaɗan ba,
ganin yana daf da kamuwa da ciwon zuciya,
hankalin sa a matukar tashe yake basa wasu shawarwari kan yan da zai gudanar da lamuran sa domin gujewa kamuwa da ciwon zuciya,
ya tausaya masa kwarai da gaske,
ya ɗaurasa kan magani.
har gurin motar sa ya rako sa ya, yana daɗa jaddada masa yan da zai kula da shan maganin sa, SALEEM yana kokarin shiga mota Dr Farooq yakuma duban sa yana faɗin
"Dan Allah Ya SALEEM ka kula da shan maganin ka, kuma dan Allah ka rage tunani idan Allah ya tai maka zai tsaya iya haka Allah ya sauwaka."
ya amsa da amin kana ya shige mota...



A ɓangaren Na'ima kuwa
zaune suke a gaban sabon bokan su, sun naɗe kafa gaban sa kamar masu niman gafara,
sun kura ido suna kallon yan da yake ta wani surkullen sa, yayi zane kan kasa ya bubbuga ya share ya kuma zana wa.
bokan ya ɗago ya dube su yace "Zata mutu mutuwar wulakanci amma aljanun da zamu tura su sun ce suna bukatar jini rakuma kosassu guda goma kafin suje suyi ai kin."
kirji Raliya ta buga tace
"Rakuma guda goma kosassu ayanzu fa kuɗin ko wani ɗaya zai kai miliyan uku."
bokan yayi wani irin dariya yace "Bazaku iya ba ku tashi ku tafi."
da sauri
Na'ima ta gyara zama tace "Boka zamu iya."
wayar ta ta ɗaga taduba balance ɗin account ɗin ta taga babu wani yawa sosai dan duk ta gama basa kuɗin.
ta yi masa transfer ɗin duka kuɗin zuwa account ɗin shi, kana ta aje makullin motar da tazo da shi a gaban sa tace
"Asai da motar a haɗa da kuɗin idan basu kai ba zan nemo cikon,
ni dai dan Allah boka ayi min kokari bana so a sami matsala, a iashe ta kawai shine samin kwanciyar hankali na, ko bacci mai daɗi bana samu yanzu."
boka yace "An gama mabi da matsala yau za'a sai da motar idan kuɗin ya cika, da daddare za'a bawa aljanu jinin rakuman a daren nan zasu kashe tai, dan kuma bai cika ba zamu neme ku."
suka mike suna ta zuba masa godiya a motar Raliya suka fito saga cikin dajin..
suna tafe Raliya ta juyo ta dube ta tace
"Aminiya amma yanzu idan boka yace a kawo ciko a ina zaki samu cikon?."
Na'ima tace "Agurin SALEEM ai da ma daga gurin sa suke fita, zan sa a ɗauke Ameer a nimi kuɗin fansa a gurin sa dai-dai kuɗin siyan rakuman, idan ya bayar sai na bawa boka cikon kuɗin narike sauran."
dariya Raliya tayi tace
"Kai Aminiya daɗina da ke kwakwalwar ki na ja, idan aka sace ɗan sa kam ai da gudu zai kawo kuɗin babu gargada."
Na'ima tayi wani murmushi mai cike da tarin makirci....






Abuja
Kullum a cikin lissafin tafin watannin ukun da Ummi tace na kara kafin nazo nake, sai nake ganin lokacin yayi min nisa. da kyar naga wata biyu yayi.
kullum idan muka yi waya da Ummi sai na ce mata
Allah Ahmad yayi wayo sosai yayi kwari nace kuma bari taji dariyar sa, sai nayi ta masa wasa yayi ta kyalkyalewa da dariya nace taji shi ko.
tace taji amma dai na bari na cikita wata ɗayan tukun..
idan Ahmad yaji muna waya da Ummi yarika yimin dariya kenan sai yace wai Ummi ta fiso na zauna na kula da su..
ranar da wata ɗayan nan ya cika, tun da na farka da asuba ban kuma iya komawa bacci ba,
a kwatunan kayan mu na sauke waɗan da na shirya su tun sati ɗaya daya wuce.
ranar Ahmad baya gida na, na kira sa a waya nace kasa mu fa mub gama shiri, yace na jira sa gashi nan zuwa.
ina zaune a parlour ya shigo su Nasmah suka rungume sa suna yi masa oyoyo, sai da ya ɗaga ko wannen su sama kafin ya dire su yana bin su da dariya.
in da na ke ya karaso ya ɗauki Ahmad karami dake kan kafata yarika cillashi sama yana kwalkwale dariya,
ganin yan da ya shagala da wasa da yaron yana kuma biyewa su Naseem da suke taya sa wasa wa yaron, na turo baki gaba
nace "My rana fa zatayi kana so muyi tafiyar dare ne."
zama yayi gefe na tare da manna min kiss a kumatu yace
"Kyakkyawa ta ki bar tafiyar nan yau."
ido na waro nace "Me ne!?."
janyo keken da ake saka Ahmad karami a ciki yayi yasaka sa ciki kana ya tura sa gefe ai ko da gudu su Naseem sukayi kansa suna yi masa wasa yana ta ɓalle musu da dariya.
janyo ni jikin sa yayi ya sakalo hannayen sa ya zagaye ni da shi,
a hankali cikin tattausan lafazi yace
"Ki saurare ni kiji abin da zan faɗa, ai tafiyar ba naki ke kaɗai bace har da ni da su Bappa,jibi ina da wani zaman da zamu yi kuma mittin ne mai muhimmanci, nayi miki alƙawari idan mukayi mittin jibi washegari zamu tafi."
kai na langwaɓar gefe zan yi magana yace
"Kar kice komai kika iya jiran wata uku kwana uku ne zai gagara iye kyakkyawa ta?."
yadda yayi maganar a marairaice tare da langwaɓar da kansa gefe,
sai ya bani dariya murmushi nayi nace
"Amma Allah kwana ukun nan kam idan yazo babu fashi."
yace "In Allah ya yarda."
kai na girgiza nace "To Allah ya kaimu."
daɗa rungumo ni yayi yana faɗin
"Amin Amin." ganin yana shirin haɗe bakin mu nayi saurin kawar da kaina gefe, nace
"My yarannan fa suna nan." ido ya kashe min yace "Su da suke wasan su hankalin su baya nan."
fuska ta ya juyo tare da haɗe bakin mu, idanunsa a kan yaran garin hankalin su na kokarin dawowa kanmu sai ya zare bakin sa ya sake ni,
ya mike yana faɗin
"Kuzo muje musha ice-cream."
ya ɗauki Ahmad karami ya dube ni yace
"Madam muje ko."
a sannu na mike kasan cewar da mayafi a jikina muka nufi gurin mota.
ya buɗe wa su Naseem gidan baya suka shiga, kana ya mai da marfin ya rufe sannan ya matso ya buɗe min gefen mai zaman banza, sai da na shiga kafin ya miko min Ahmad karami.
kana ya zaga ya huɗe driver seat ya shiga, yana kokarin ta da motar da sauri wani security ya iso,yaɗan leko gefen da nake cike da girmamawa yace
"Barkan ku da warhaka."
Ahmad ya ce yauwa, yace "Madam dama wata ce ta zo, wai tazo niman taimako ne ansan da zuwan ta ne."
kai na girgiza nace
"Okay bari idan muka fita wajen sai a taimaka mata."
yace to ya juya da sauri mai gadi ya wangale get muka, Ahmad ya ja motar muka fito a hankali.
matar tana ɗan rakuɓe a gefe kallon ta nayi saga sama har kasa, gaba ɗaya kayan jikin ta sun koɗe hatta hijabin jikin ta tagefe duk a yayyage, silifas ɗin kafar ta ya cinye kusan rabib kafar ta a kasa yake, tana rungume da bakko a hannunta.
Ahmad yayi hon da ɗan sauri ta nufo in da muke,
ido na kurawa matar,
da sauri na kai hannu na mussuke idanuna da kyau na zuba su a kanta, dai-dai lokacin da ta karaso jikin motar tagefen da nake tana faɗin
"Alhaji Hajiya a taimaka min da ko kuɗin mota ne na koma garin mu."
wani irin waro ido nayi da karfi na furta
"Mama!". ta ɗago da sauri ta na duba na,
juyo wa nayi gun Ahmad ina faɗin
"My ita ce Mama mai wara ita ce wlh."
sai kuma na juyo in da take ganin tana bina da kallon rashin sani nace
"Mama baki gane ni bane nice fa HAMDAH ce fa Mama."
da sauri na ɗago Ahmad karami na ɗaura kan kafar Ahmad na buɗe marfin motar da sauri na fita.
ido ta kura min tana nuna ni da yatsa murya na rawa tace
"HAMDAH kece HAMDAH kece haka ke kika zamo haka HAMDAH?."
rungume ta nayi a tare muka fashe da kuka cikin muryar kuka nace
"Nice Mama, Mama nayita niman ki har na ɓata."
ita ma tace "Nima nayi ta neman ki HAMDAH ashe darabon ganawa."
Ahmad ya fito daga cikin motar, na sake ta tare da share hawaye na na nuna mata shi nace
"Mama miji na ne shi." murmushi tayi tana share hawaye tace
"Shine SALEEM?." kai na girgiza mata. Ahmad da take ta binmu da murmushi yace "Sannu Mama." tace yauwa.
tace "Ina Naseem da Nasmah?." nace "Gasu nan cikin mota."
Ahmad ya buɗe musu suka fito na kamo hannun su na kawo su gaban ta nace
"Ga Mama wacce tasha ɗawainiyar ku tun kuna ciki."
hannunsu ta ruko tana faɗin
"Masha Allah Naseem Nasmah kune kuka girma haka."
Naseem da ya washe baki yace
"Ai Daddy yace mun gima ga kanin mu a hannun Daddy ni Yaya Naseem ne."
dariya dukan mu kayi, Mama ta dubi Ahmad karami da ke rike a hannun Ahmad sai washe baki yake kamar wan da yasan abun da ake faɗa,
tace
"Masha Allah kanin ku kenan yaya sunan sa?."
Nasmah tace "Ahmad."
nace "Mama mu shiga ciki."
tana rike da hannun su Naseem muka shige cikin gida, Mama ta rika bin katafaren gidan da kallo tana jinjina kai.
a parlour'n kasa muka zazzauna, Ahmad cikin girmamawa yashiga gaishe ta da taya mu murnar kuma haɗuwa, ya dube ni yana murmushi yace
"Yau maganar Mama ya kare ko." dariya nayi ina ɓoye fuska ta a jikin ta.
kira ce ta shigo wayar sa ya mike yafita yana faɗin sai ya dawo.
da kaina na fita naje side ɗin su Bappa na sanar musu da zuwan Mama mai awara.
a tare muka shigo parlour'n da su.
sunyi farin ciki kwarai da gaske haɗuwar mu da ita, cikin yanayin damuwa Mama ta dube ni tana faɗin
"HAMDAH ke da na ce miki ki jira ni ina dawowa shine kika tafi."
nace "Mama nayi ta jiran ki da banga kin dawo ba shine nace zan biki kawai, a hanyata na tafi Yola na shiga motar ɗan yankan kai."
ido Mama ta ware tabuga kirji tace
"Ɗan yankan kai kuma?."
kai na gwaɗa kana asannu na shiga bata labarin abun da ya faru daga lokacin da na shiga motar ɗan yankan kai ɗin nan har zuwa rana mai kamar ra yau.
mama ta rika hawaye cike da tausayawa halin da muka shiga bayan ta,
da ga bisa ni kuma tarika murmushi jin nasarorin da na samu bayan wuyan da muka sha.
nace mata na zo Jos domin neman ta wacce nake da tabbacin zan sami labarin ta wajen su wato Zainabu da mijinta Malam musa mai maganin macizai, na tarar da sun tashi a gidan dan dana sansu.
Mama tace "Nima lokacin da nadawo dan da ɗauke ki mu tafi na tarar da bakya nan, nayi tunanin naje Bauchi ko kin koma gun iyayen ki ne, nayi tunanin ban san ta in da zan fara niman ki ba tun da bakara min gari bane,
haka na koma Yola nayi ta rayuwar kunci ɗan gonar gado na da nake gadara da shi matar yaya na ta saida wai gadon ƴaƴan ta ne."
kwalla ta share kana ta cigaba da bani labarin rayuwar da ta fuskanta a can, da kuma abun da ya kawo ta ganinnan, tace niman ai ki tazo yau satin ta guda kenan, bata sami ai kin ba duk gidan da ta shiga wasu su kore ta wasu kuma suce basa bukatar ƴar aiki suna da su,
haka tayi ta kwana a kan titi shine ta fara yawon bara dan ta sami kuɗin mota ta koma Yola taje ta karasa rayuwar ta acan.
rungume ta nayi tare da fashe wa da kuka, mukayi ta kuka.
su Bappa ne suka yita bamu baki har mukayi shiru,
kana Nappa yayi ta kwararo addu'a yace
dama duk abun da yayi farko zaiyi karshe Allah ya tsayar mana haka.
duk kanin muka amsa da amin amin, sai da sukayi hira sosai da Mama mai awara kafin suka koma side ɗin su...
ɗakin da Ummi ta zauna na kai Mama nace tashiga bayi yayi wanka,
tare muka shiga na nunnuna mata in da zatayi amfani da bathroom ɗin kafin na fita.
waya nayi a *HAM'NAS* Store Camplex
nace a kawo min manyan dogayen riguna haɗe da atamfofi da mayafai da takalma marasa tudu, nafaɗi lambar takalmar da kuma adadin yawan kayan da nake so.
batare da ɓata lokacin ba motar ShopRite ɗin ta iso, da kaya niki niki cikin babbar jaka.
na shiga da shi cikin ɗakin da Mama take, lokacin har tayi wanka tayi salla tana zaune a kan sallaya,
a gaban ta na aje jakar na zazzage kayan, na cire atamfofin gefe nace ta kwada dogayen rigunan ko zasu yi mata in basuyi ba aje a canzu.
ta gwada zukayi mata Mama ta rika samun albarka tana hawaye.
na kira tela yazo ya ganta kana ya ɗibi zannunwan ya tafi da su,bayan na sanar masa cikin kwana biyu nake bukatar su...
muna zaune da Mama a parlour bayan mun gama cin abincin dare na kira Ummi bayan mungaisa nace
"Ummu ga Mama mai awaran da nake faɗa miki wacce ta rike ni tamkar ke da kika haife ni."
Ummi tayi ta murna tace na bata wayan su gaisa, nace to tare ma zamu zo.
bayan sun gaisa Ummi tashiga zuba mata godiya,
Mama tace ai ba ita kaɗai bace Mama ta itama Mama ta ce.
Ummi taji daɗi kwarai da gaske tayi mana fatan isowa Bauchi lafiya...
bayan kwana biyu tela ya kawo ɗin kin Mama, na haɗa na shirya mata wasu daga cikin kayan cikin ɗan madaidaicin akwati..


Kamar yadda Ahmad ya faɗa bayan kwana uku motocin mu suka haura hanyan zuwa Bauchin Yakubu.
motan mu daban ni da Ahmad da su Naseem duk muna baya in da direban sa ke janmu.
motan su Bappa daban, Bappa na gaba shida direba Inna Wuro da Mama da Faty suna baya.
har da su Uncle Mahmoud motan su daban shi yake jan motar sa da kansa shi da matarsa da ƴaƴan su ne ciki dan shima yace ba za'a barsu a baya ba.
sai motar security motar su guda, a hanya muka haɗu da su na fahimci biyo mu suke.
a jere motocin suke tafiya, motan su Uncle Mahmoud ne a gaba na su Bappa na biye da su in da moton security ne ke biye da mu......
da misalin karfe uku muka iso cikin garin Bauchi,
wani irin lumshe idanuna nayi tare da kuma huɗe wa a cikin garina mahaifata,
na shaki iskar dake kaɗa wa ina mai farin ciki da jin daɗin gani na cikin garin.
murmushi Ahmad yayi tare da jan kumatu na yace
"Yarinya tana murna tazo kauyen su."
dariya nayi nace "Nan ɗin ne kauyen me Abuja yafi shi da shi."
yace "Lalala birnin tarayya ne fa babu haɗi ai."
nace "Ba wanin nan."
yace "To dai nuna mana hanya ina zamu karmuje mu ɓata."
dariya nayi tare da soma yi masa kwatance ya kira Uncle Mahmoud ya haɗa mu da shi narika yi masa kwatance har muka shigo unguwar mu.
a bakin get Uncle Mahmood yayi hon mai gadi ya buɗe ya shiga muka bisa a bayan sa, a farfajiyar gidan motocin mu suka faka.
numfashi mai karfi na sauke gani na a cikin gidan mu.
su Aunty Rafee'at ne da su Mamie da Goggo Hauwa suka fito daga sashin Mamie da sauri suka nufo gurin motocin,
da saauri na malle marfin motar na fito da sauri muka rungume juna cikin matukar farin cikin ganin junan mu,
su Abbu suka iso gurin suna yi wa su Bappa sannu da hanya, kana a ka ɗunguma aka shiga side ɗin Mamie, security kuma aka shinfiɗa musu babban tabarma a gindin bishiyar anbulera dake gefe da tsakar gidan.
muna zazzaune a parlour sai gaisawa ake, tuni Mamie ta sa su Aunty Rafee'at suka cike mu da kayan ci da sha wan da aka tanadar domin mu, aka ɗibi wasu aka kaiwa security.
niko ina tsakiyar su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela da Ya Masa'ud, da ƴan kanne na Nusaiba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login