Showing 75001 words to 78000 words out of 125808 words

Chapter 26 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

453

da bacci yace "Sun gaji kiga baccin su nawa, kema kuma nasan kin gaji."
nace "Ni dai mutafi gida kawai."
yace "To shi kenan."
ya haura hanya muka ɗau hanyar Abuja...
kasan cewar da abincin mu muke tafe bamu sha wani wahalar yunwa ba,
ana kiran sallar magriba muna isa ciki Abuja,
yanayin gosulo da muka tarar bamu shiga gida ba sai bayan sallar isha.
koda ya gyara parking na buɗe marfin motar na fito,
ina saka kafata kasa naji wani jiri ya fisge ni, da sauri na dafa jikin motar, har yafita ya zaga yaɗau ki Naseem da Nasmah ina dafe da jikin motar,
yazo in da hake yana gyara rukon su yace
"Muje ko?."
a hankali na mike tsawo na yayi gaba nabi bayan sa a hankali ina jin yan da jirin yake ta cigaba da fizgata, a haka muka shiga ciki direct sama ya haura, niko a parlour'n kasa na zube kan kuje ra, tare da kife fuskata jikin pillow'n kujera, na rumtse idanuna da karfi jin juwan nadaɗa fisga ta.
ya kai su ɗakin su ya kwantar da su kana ya sauko kasa yazo in da nake ya zauna kusa da ni.
yasa hannunsa ya ɗago ni yana faɗin
"Shi yasa nace mukwana a cikib Jos sabo da nasan zaki wahala, kika ce sai dai mu juyo, kin ga irin ta ko."
murmushin karfin hali nayi dan yanayin da nake jin yana son wuce tunani nace
"To baga shi mun dawo ba, ai mun huta basai goben mun yi ta tunanin kuma hawa hanya ba"
Yaruko lips ɗina yace "Wannan baki da duk abin da aka faɗa sai yakawo hujja".
dariya nayi nace "To ai rainon ka ne."
shima dariyar yayi yace
"Au haka zaki ce."
gira na ɗaga ina murmushi. gefen fuska ta ya shafa kana ya ruko hannuna yace
"Taso na taimaka miki mu haura ki wasa ruwa zaki ji karfin jikin ki."
a hankali naɗan yunkura ya ɗago ni ya mikar da ni, idanuna na ɗan rumtse kana a hankali nashiga ɗaga kafata, yana tallafe da ni har muka haura sama.
a bakin gado ya zaunar da ni kana ya shiga taimaka min na rage kayan jikina,
ya kuma ruko hannuna muka muka shiga bayi wankan ma sai da ya taimaka min gaba ɗaya jikina ba kwari ga jirin nan yaki bari na, ga masifaffen ciwon kai.
muna fita daga bayin doguwar rigar bacci kawai na zura na haye gado.
bakin gadon ya zo ya shafo gefen fuskata a hankali na buɗe idona na zuba masa yace
"Kyakkyawa ta tashi kiɗan ci wani abu mana zaki daɗa jin karfin jikin ki."
kai na girgiza a hankali na mai da idanuna na rufe, ya hayo gadon ya kwanta tare da janyo ni kijin sa, a hankali bacci ya ɗauke ni...
can cikin dare jikina yahaɗa zafi rau sai ɓari nake,ina daɗa shigewa cikin jinin sa,
da sauri yabuɗe idanunsa ya daɗa rungumo ni jin yan da jikina ya ɗau zafi yamike da sauri yana faɗin
"Subhanalla kyakkyawa ta zazzaɓi ne haka Innalillahi."
gaba ɗaya ya ruɗe yarika rungume ni yana yimin sannu, ya ɗago ni yana faɗin
"Taso muje asibiti jikin ki yayi zafi sosai."
kaina na kwantar a kirjin sa na rirrike sa a hankali nace
"A'a dare yayi sosai kada muje zai sauka zuwa safiya."
a ruɗe yace "A'a kyakkyawa ta kijin ki yayi zafi sosai muje kawai."
duk yan da yaso mu tafi naki fir.
yana zaune ina rungumo a jikin sa a haka gari ya waye.
da asuba ya kaini bayi da kansa yayi min wanka a daddafe nayi al'wala shima yayi, bai barni na taka da kaina ba ya ɗauko ni ya fito da ni,
ya shinfiɗa mana sallaya a zaune nayi sallar in da shi kuma ya ja mana sallar.
muna idar wa na sulale kan sallayar.
shiko da sauri ya mike yaje ya ɗau wayar sa yakira family Dr su, yace yazo yanzu yayi masa kwatancen gidan.
kana yazo ya ɗaga ni a kasa ya mai dani kan gado.
batare da ɓata lokaci ba Dr ya iso, ya bada umurnin a barsa ya shigo,
har cikin parlour'n sama ya bashi umurnin shigo wa,
kana ya shigo ya saka min hijabi kan rigar baccin da yake jikina, ya ɗago ni ya tallafo ni jikin sa muka fito parlour, ya zaunar dani kan kujera kana shima ya zauna kusa da ni,
a hankali na kwantar da kaina jikin hannun kujera, ina jin Dr yana tambayar me ya sa me ni,
yace masa tafiya mukayi jiya mun wuni a kan hanya,muna dawo wa shine zazzaɓi ya rufe ta.
Dr ya ɗanyi rubuce-rubuce kana yaɗa go yace "Baza a bata magani ba sai anyi mata test." Ahmad
yace "To." kana ya dube ni yace
"Bari a ja jinin ki ayi test dan asan maganin daya dace da kisha ki warke da wuri ko kyakkyawa ta."
yayi maganar yana ɗan jan hijabin jikina ya ɗan tattaro shi yaciro hannuna ya ruko hannuna.
Dr ya taso yaja jinina kana ya tafi.
in da aka ja jinin yarika mulmula min a hankali,
shiru nayi ina kwance cikin kirjin sa, a haka bacci ya fara fizgata,
ganin haka sai ya gyara zaman sa da kyau ya gyara min kwanciya ta cikin jikin sa.
nan da nan bacci ya ɗau ni...

Acikin baccin narika jin magana, a hankali na buɗe idanuna, maganar Dr ne ya doki kunne na
"Congratulations ranka shidaɗi an sami karuwa Madam tana ɗauke da juna biyu."
wani irin waro idanuna nayi na mike zaune.
Ahmad kuwa mike wa tsaye yayi zumbur yana bin likitar da wani irin kallo mai cike da ɗin bin mamaki cikin rawar murya yace
"What! mekace!?, kasan me kake faɗa kuwa?."
sai kuma ya girgiza kansa sannan yace
"Kodai kunnuwa na sun jiye min ba dai-dai bane."
murmushi Dr yayi tare da mike wa tsaye takar dar dake rike a hannunsa ya mika masa yace
"Wannan shine sakamakon test ɗin da mukayi, kuma ya nuna tana ɗauke da ciki, amma idan ana kokonto za'a iya zuwa wani asibiti ayi gwaji ta hanyar yin scanning domin tabbatar wa."
takardar da ya mika masa yashiga dubawa har hannunsa na ɓari, wani uban kabbara ya sake, ya juya ya dubi gabar yasulale kasa yayi sujjada............!







Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu kanwa ta ce tayi ɓari so dole nice na zauna a kanta na tsawon kwana ɗaya da wuni ɗaya ban sami damar hawa online ɗin bama bare na shaida muku.










Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: 26





Ya ɗago tare da ɗaga hannunsa sama yace
"Ya Allah ya Ubangijin rama Allah nagode maka Nagode maka Allah, ya buwayi gagara misali ya Hayyu ya Kayyum, bana da tsumi bana da dabara maikowa mai komai duk kai kaɗai kake da su,
haki Ubangiji na mai girma ka azirtani da abin da bana da wayo da wayo da ikon iya bawa kai na,
duk arziki na bazan iya baiwa kaina ba kai kaɗai kake da ikon iya bani, Allah Nagode maka Allah na gode maka Allah Nagode maka."
yakuma mai da kansa yayi sujjada,
yana mai cigaba da kwararo addu'a da kirari wa Allah.
kana ya ɗago da sauri yamike yazo ya rungume ni tsam yana faɗin
"Hakika HAMDAH ke alkhairi ce a gate ni, ke fitala ce mai haske duhun dayayi shekara da shekaru, na gode wa Allah daya mallaka min ke amatsayin mata kuma fitila ga rayuwa ta,
HAMDAH ke ta daban ce ina sonki ina sonki HAMDAH inayi miki son dayafi wanda nakewa kaina!!."
yadaɗa kankame ni a jikin sa.
Dr da yake tsaye yana bin mu da kallo da murmushin taya murya,
yayi mana sallama yace zai tafi,
ai da sauri Ahmad ya sake ni yace
ya bashi account number ɗin shi, nan take yayi masa transfer ɗin 3 Miliyan.
yace tukuicin sa na sanar da kyakkyawan zance mafi girma, wan da tun da yake ba'a taɓa yi masa albishir da kamar saba.
likitar yarika murna dayi masa fatan isowar baby lafiya ya bar gidan bakin sa har kunne, bayan ya aje mana maganin da yazo da shi.

Ahmad daya kasa zaune ya kasa tsaye yara inda zai sa kansa dan farin ciki, yadube ni yana faɗin
"Me kike so kyakkyawa ta me kike so a duniyar nan? kifaɗa min ko mene ne shi ashirye nake nayi miki shi koda zai zamo gurfaniwar dukiyar dana mallaka da dukkanin kadarori na, me kike so nayi miki tukuici
da shi? motoci gidaje kamfanoni acikin kasar mu ko a kasashen waje, faɗa min duk abin da kike bukata zanyi miki shi koma mene ne, faɗa min yanzu kyakkyawa ta."
kai na rausayar gefe jin kai na nadaɗa sara min a hankali cikin yanayin jin zazzaɓi nace
"Ni bana son komai wayyo kaina."
na dafe kaina dake cigaba da sara min.
da sauri ya mike yace
"Bari na ɗauko ruwa kisha magani zai dai na in sha Allah."
da sauri yaje ya ɗauko gorar ruwa cikin fridge yadawo in da nake, ya tsiyaye ruwan cikin cup ɗin da ya haɗo da shi,
kana yaɗau laidar maganin ya curo su daga cikin laida, kamar yadda yagani a rubuce haka ya cicciro su.
kana ya tallafo kaina yace
"Buɗe bakin ki na saka miki."
da sauri na kawar da kaina yayin da naji zuciya ta ta hautsune jin warin maganin nace
"A'a zanyi amai."
yace "Ya ilahi bazakiyi ba, buɗe baki kisha ga ruwa nan kusa."
cikin zubda kwalla na girgiza masa kai da faɗin
"Zan yi mana kabar shi kawai zan warke a haka basai na sha magani ba."
ido ya waro da karfi ya furta
"Wane ni wlh ban isa ba, kin san kuwa zafin zazzaɓi yana iya zubda ciki, ki tai make ni dan Allah ki ceci rayuwa ta kisha maganin nan ki samu ki warke kada ya janyo min babban asara,
na roke ki dan Allah ki sha, ki taimaka min ni kaɗai iyaye na suka haifa ki tai make ni abin cikin nan yafito lafiya, naji a raina inada jinina aduniya."
ya juyo da fuskata yace
"Sha in Allah ya yarda bazakiyi amai ba."
idona na rumtse da karfi na ɗauke numfashi tare da buɗe baki ya zuba min maganin kana ya bisu da ruwa.
da kyar sai da nayi kamar ina yi kafin suka wuce.
ido na ware da karfi jin zuciya ta na wani irin tashi cikin hanzari na tallafe kansa tare da manna bakina da nashi nashiga tsotsar bakin sa.
a hankali a hankali nashiga sauke numfashi, yayin da aman yake kwanciya a hankali.
sai na lumshe idanuna a hankali ina mai cigaba da tsotsar bakin sa,
a hankali kasan tuwar mu da Ya SALEEM a irin wannan lokacin yafara zuwar min, sai na buɗe idanuna da sauri a sannu na zare baki na daga nashi.
shiko ido yakura min da yanayin mamaki sai kuma ya tallafo kaina yana kokarin kuma haɗe bakin mu.
da sauri na kwace kai na na turo baki gaba,nace
"Bana ce maka zanyi amai ba."
murmushi yayi yace
"To baga shi kin mai da aman ba, zo in kara kwantar miki da shi."
kafada na make ina mai cigaba da turo baki gaba.
da sauri ya mike cikin rawar jiki yace
"Ina zuwa bari naje na sanar wa su Bappa wannan dadda ɗan albishir ɗin."
ido na waro nace "A'a kada kaje."
kafin na rufe baki ma yayi gaba.


A kofar side ɗin su Bappa ya haɗu da shi yana kokarin fita.
ganin yan da yake ta washe ba yasa Bappa faɗin Ahmad "Wannan farin ciki haka me ya faru."
cikin matsananciyar farin cikin daya ke jin kansa ciki yace
"Bappa Malam HAMDAH tana da ciki, yanzu likita ya tabbatar min da haka."
Bappa ya faɗaɗa fuskarsa da annuri yana faɗin
"Masha Allah Allah abin godiya alhmdllh Allah mun gode maka, kai lallai wannan abin farin ciki ne, Allah ya ɗaiyiba yaraba lafiya."
Inna Wuro dake ta ciki tana jiyo duk abin da suke ciki,
tayi murmushi mai bayyana farin ciki, ta girgiza kai tare da faɗin
"Yaran zamani kenan wai shi ya ɗauki kafa yazo faɗar matar sa na da ciki."
takuma yin murmushi tana faɗin
"Dole kayi murna Ahmad lallai wannan abin farin ciki ne."


Anan kofa kuwa Bappa yayi ta zuba musu addu'a da fatan isowar abin dake cikin duniya lafiya, yajuya cike da ɗin bin farin ciki, shiko Bappa ya koma ciki, yana shaida wa Inna Wuro.
tayi dariya tace "Ai duk ina jin ku murna ya hana shi sukuni."
Bappa yace
"Ai dole yayi murna abune sabo a gare sa wan da ya jima yana sumayar sa sai gashi kwasam Allah ya ai ko masa da shi, kin ga kuwa dole farin cikin sa yagaza ɓuya."
tace "Haka ne kam lallai muma munyi farin ciki kwarai aure yayi albarka."
Bappa yace "Haka ne kuwa kwarai da gaske."
haka sukayi ta nuna farin cikin su
da sam barka da fatan isowar baby duniya cikin koshin lafiya...

Ahmad kuwa yana juyawa daga gurin Bappa Rasheedat ya kira a waya ciki farin ciki yasanar mata,
ihun murna Rasheedat ta sake tace "Ina HAMDAH haɗa ni da ita dan Allah."
yace "To bari na kai mata."
ai bata jira ya karasa maganar ba ta kashe wayar da sauri ta zari matafin ta da makullin mota tayi waje.
Ahmad yana tafiya yana daddanna wayar sa nan da nan yashiga posting wa ƴan uwa da abokan arziki, yana faɗin a taya shi murna..

Ina kwance a kan kuje ra in da ya barni yadawo ya same ni,
ya karaso in da nake da sauri ya sunkuyo ya sumbaci goshi.
ido na lumshe tare da buɗe su a kan a hankali nace
"Yanzu kaje ka faɗa musun ne?."
baki ya washe yace
"Eh mana ai dole duk wani wan da ya sanni yasan wannan labarin."
ya zauna ta gurin kafafu na kana ya ɗago kafafun nawa ya ɗaura su kan cinyar sa, a hankali yashiga matse su.
yana faɗin
"Sannu kinji kyakkyawa ta baki dai kin ciwon ciki ko?, iya ciwon kanne kaɗai?."
ban tanka shiba sai lumshe idanuna danayi..
kira yayi ta shigo wa wayar sa yana ɗagawa yana faɗin yagode yagode, gaba ɗaya bakinsa yaki rufuwa...

Acikin ƴan mintina Rasheedat ta iso gidan tana haurowa parlour'n sama ta taho da gudu ta rungume ni daga kwancen da nake, cikin sananin farin ciki tace
"HAMDAH kai sannun ki da kokari ashe dai zamuga jinin mu Allah ya fito mana da shi lafiya."
ta mike ta sauri ta rungume ta Ahmad tana fadin
"Aboki wayyo Allah narasa yadda zan sa kaina dan farin ciki,
tabbas yau ya daɗa yarda Allah bai mance da mu ba."
dariya yayi yana daɗa rungume ta a jikin sa yace
"Kwarai kuwa Kawa Allah baya bacci."

Haka suka yi ta nuna farin cikin su kamar zasu saka ni cikin jikin su.
suka rika tambaya ta me nake so, Aunty Rasheedat tace me nake jin kwaɗa yin sa ta dafa min. nace ba komai.
kan kace me labari ya karaɗe yan uwa da abokan arziki.
ranar wuni Aunty Rasheedat tayi a gidan sai dare ta koma.
washegari
washegari da sassafe Ahmad yaje gidan su,
yau ƴan gidan sun sha mamakin ganin yan da yashigo da farara hatta Sakeenat yau sai da ya amsa gaisuwar ta.
ɗakin Hajiya Karima ya shige, tana ganin sa ta faɗa fuskar ta da murumshi.
ya nimi guri ya zauna bayan sun gaisa ya dube ta fuska ɗauke da masananciyar farin ciki
yace "Hajiya wani albishir nazo miki da shi."
zama Hajiya Karima ta gyara ta washe baki tana faɗin
"To Ahmadu ɗan Sabil na bada goron kar ɓar albashir fari soll."
yace "Hajiya HAMDAH nada ciki Hajiya ashe nima zan haihu?."
wani irin zabura Hajiya Karima tayi, sai da ta zamo bakin kujera ta buga kirji ta waro ido tare da faɗin
"Me ne ciki!!?." wani irin murmushu yayi mai kunshe da ma'anoni daban-daban kana yace Hajiya kema kin ji abin a bazata ko? ai nima haka naji abin kamar almara."
dariyar yake tayi sai kuma ta kama kame-kame tashiga faɗin
"La..laa..ikon..Ikon.. Allah...to ciki..
ciki, kai masha Allah lallai kuwa wannan shine bazata bayan fidda rai ga samu sai ga samun kuma, kai amma nayi farin ciki naji daɗi sosai, ashe zanga jika na, kai Allah yayi albarka yaraba lafiya, Eh Allah ya raba lafiya."
"Amin amin." yafaɗa yana mike wa tsaye yace
"To Hajiya ni zan koma."
tace "To a gaida gida a gai da min me cikin."
yace to kana ya sa kai ya fita..
yana fita Hajiya Karima ta saki wani uban ajiyar zuciya tabigi kirji tace
"Tabɗijam ciki!? kenan hakan na nufi Ahmad zai haihu yasami magajin dukiyar sa, wato wannan shigiyar yarin yar tana kokarin zuguza min shiri shine har da yin ciki, bayan ban taɓa kawo hakan cikin lissafi na ba, nasawa raina bazai haihuwa ba shine zata zo ta yi kokarin haihuwa masa, ina bazai yiwu ba da sakel wlh!...."



Acan cikin garin Bauchi

Abba ne da Ummi tafe cikin mota a hanyar su na komawa gida bayan dawo war su daga asibiti dubiyar wata ƴar uwar Ummi da ba lafiya,
suka biya ta gidan mai domin su sha mai,
tun daga farkon shiga gidan man layi ne har cikin gidan man,
Abba da yake kokarin sako kan motar sa cikin gidan man yaɗan yi jim yana bin layin da ido.
Ummi tace "Abba'n Fauzan wannan layin idan muka shiga ai sai mukai kisan dare ma layin bai iso kan mu ba, duba fa gamasu garaku da suke acikin motoci sannan ga su motocin kansu, yaushe za'a basu har a bamu."
Abba yace
"Gaskiya kam bari mu koma gida kawai nasa direba yafito ya sha man ko ba a nan ba, tun safe ake layin nan motoci sai daɗa zuwa suke zamu ɓata lokaci kam muje gida kawai."
Ummi tace "To in ban da mutane ma ga wasu gidajen mai da yawa waɗan da naga babu ko layi wasu bai fi mota biyu zuwa uku ba, baza su je can susha man ba sai suzo nan suyi tayin layi haka."
Abba yace "To ai sauki ake so shiyasa ake wa gidan man layi, ai ba nan kaɗai ba idan da zaki zaga garin nan kiga gidan mai me irin sunan wannan gidan man zakiga layi kamar haka koma fin haka,
man su na da sauki sosai kuma litar su na da kyau,
an ce wai mai gida jen man ne tace a rika sai da shi a farashin da yanzu suke sai dawar shiyasa duk gidajen man ta zakiga irin wannan layin."
kai Ummi ta jinjina ta ɗaga kan ta tana duban sunan gidan man. tace
"*HAM'NAS CO PETROLEUM NIGERIA LIMITED* wato mace ce mai gidan man?".
Abba daya juya akalar tafiyar tasu izuwa gida yace "Eh mace ce."
tace "Lallai tayi kokari Allah yasaka mata."
Abba ya amsa da amin amin.
suna isa gida motar SALEEM na shigo wa, w kusan tare sukayi parkin suka fito,
ya tako ya zo in da suke ya shiga gaida su,
suka amsa cike da kuwala Ummi taɗan zuba masa ido nan da nan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login