Showing 45001 words to 48000 words out of 125808 words
yan da aka kawo mishi cikakken tarihin su, bai ɓoye ko rage mata komai ba kamar yadda baiyi da farko ba, bayan gama shaida masa abin da aka sanar masa a kan su sai ya cigaba da faɗin
"Kin san wace ce wannan yarin yar?."
kai ta girgiza jiki a sanyaye yayin da idanun ta suka cika da ƙwalla tap suna shirin zubowa.
taji bala in tausayin su da jin labarin su jikin ta yayi matukar sanyi.
ya ce "I ta ce mai Company *HAM'NAS*."
ido ta waro ta ce "Mai Company *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Nigeria Limited?."
"Kwarai kuwa ita ce."
kai ta jinjina tare da faɗin
"Allah mai iko wan nan shine sakayyar da mafificin rahama yayi mata sakamakon cin jarabawar da ya ɗaura mata tabbas labarin rayuwar ta abun a tausaya ne, a da yanzu kam Allah yayi mata sauyi da mafificin rahamar sa."
sai gata tana hawaye cikin matsanancin tausayin labarin rayuwar HAMDAH da taji, har da jan sheshshe ka.
ta kai hannun ta share hawayen ta tare da faɗin
"Allah kayi mana mai kyau kasa mu dace duniya da kiyama."
ya ce "Amin." sai ya saki hannun ta yakoma ya kwamta tare da lumshe idanun sa.
a sannu ta gyara ita ma sai ta kwanta gefen sa tare da yin pillow da damtsen hannun sa, a hankali takai hannun ta kan fuskar sa, a sannu tashiga shafa gefen fuskar sa, in da kayataccen saje ke kwance a gurin lub-lub gwanin ban sha'awa.
duban sa tayi da kyau cikin kulawa a hankali ta ce
"Aboki." idanun sa da suke lumshe yaɗan buɗe su a kanta sannan ya amsa da
"Na'am." in da ya am sa can cikin kasan mako shin sa, laɓɓan sa ne suka motsa tanan ta fahinci ya amsa kiran nata.
idanun ta cikin nashi, sannan tace
"Aboki bayan sanin labarin ta kuma sai me baka karasa bani labarin ba."
idanun sa ya lumshi cikin son kawar da zancen ya ce
"Wani labarin kuma ai na gama baki labarin."
murmushi tayi tare da faɗin
"Baka kara sa ba da saura dan acikin duk kanin labarin da ka bani baka bani asalin gundarin labarin ba, kawai dai ka ce min kana
jin wani abu a kanta mene ne shi?."
"Ba ko mai fa." yafaɗa a takaice yana gyara kwanciyar sa, tare da juya wa ya fuskanci jikin garu, yana faɗin
"Zanyi bacci ki tai maka min kisa yayi daɗi."
hannun ta ta cusa karkashin gashin kansa ta bayan keyar sa, yana jin haka da sauri ya juyo dan yasan jan masa sumar zatayi da karfi bawai tayi masa yan da zaiyi baccin ba.
dariya tayi tana faɗin
"Ai da baka juyo ba Aboki yau aski zan maka."
ido yaɗan waro ya ce "Aski da hannu."
farr tayi da ido ta ce "Zan nimo abin yin askin ai taɓawa nake naji ta in da zan fara."
ya ce "Faɗi gaskiya dai ƴar guntun muguntar ce ta motsa."
dariya takuma in da shi kuma ya murmusa yana kokarin mai da idanun sa ya lumshi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar faɗin
"Me zaka ɓoye min ne iye sai fa ka karasa bani labarin nan dan baka gama bani ba."
shiru yayi bai ce komai ba,
Murmushi tayi tare da faɗin
"To ni bazan karasa baka labarin, tun da yau ka aro hijabi ka sakata sakanin mu, zan yaye ta yanzu dan babu ita sakanin mu har gaba da abadan."
ɗan numfashi ta ja tare da cigaba da faɗin
"Tun da ka sanya ido kanta Ubangiji yayi ikon sa,ya datsa maka sonta, a lokacin da baka taɓa sammanin a kwai ranar da hakan zata kasan ce da kai ba, dan kai a tunanin ka ni kaɗai ce Ubangiji ya dasa maka sona cikin zuciyar ka, babu wata macen da zata kuma samin gurbi cikin zuciyar ka,
ka mance da cewa Allah shi ne sarkin mulki mai yin yadda yaso da bayin sa, nasan ka da son yara amma son da kake yiwa waɗan nan yaran na daban ne, kana yi musu irin son da uba yake yi wa ƴaƴan sa, haka ne ko?."
tayi magaran tana duban sa da murmushi sosai kan fuskar ta.
numfashi ya sauke kana ya janyo ta jikin sa sannan ya ce
"Haka ne." ya faɗa dan babu ɓoye-ɓoye ko karya sakanin su, ko yan zu ma dayayi kokarin yin hakan sabo da wani dalilin yasha wuya sosai da fama da abun cikin zuciyar sa.
wani yelwataccen murmushi ne ya baiyana kan fuskar ta, kana ta ce
"Kana son ta?." kai ya gyaɗa alamar Eh sannan ya ce
"Amma abar maganar domin bana jin zan iya haɗa ki da wata."
gyemun sa taja, sai kuma ta ɓata fuska sannan tace "Haka Allah ya ce, bana son ka canza daga halin dana sanka baya yi maka kyau,
dama kan haka kake masaltawa zuciyar ka aje damuwar da bata saba ba, shine har kake son ka koyi karya ko?,
kana son ta, tun daga farkon labarin ta naji nima ina son ta ina son ƴaƴan ta, ita ta musamman ce yarin ya karama mai halin man ya ba kasafai ake samun irin su a duniya ba, ni ma ina son ta, zan ku ci gaba da son duk wani abun da kake so har idan bai saɓawa Shari'a ba har karshen rayuwa ta zan cigaba da son sa."
mike wa zaune yayi ya lankwashe kafafun sa kana ya dubi ta da ɗin bin farin ciki da jin daɗin kasan cewar ta cikin rayuwar sa ya ce
"Haki ka babu wan da yakai ni dace da samun mace ta gari, da ace kowani na miji irin ki ya samo a matsayin mata shi da damuwa ko tashin hankali bazai gansa ba har karshen rayuwa, Allah yayi miki albarka matar aljanna, faran tamin da kike Allah kema ya faran ta miki fara ƴar duma-duma ta."
"Ameen Ameen ameeeeeen."
tafaɗa tana jan ɗan gyemun sa irin na gayun nan.
sai kuma da sauri ta saki gyemun ta ce
"Ka faɗa mata kana son ta kuwa?."
kai ya girgiza ya ce "Ban faɗa mata ba."
ta ce "To me ya sa?." ya ce "Sabo da baza ta amince ba."
"Kamar ya, zakace bazata amin ce ba, baka tin kare ta da batun ba ka bata laifi." tayi maganar tana rike haɓa.
kuma tun ta yaja kana ya ce
"Um to tana da masifa tsiwar tsiya ce da ita."
dariya tayi sosai tare da tafa hannu ta ce
"Masifa haɗe da tsiwa kuma, a'a kada kayi wa kanwa ta fin tsayi." shiko murmushi yayi yana faɗin
"Allah idan ta fara tsiwa sai kin sha mamaki."
dariyar ta kuma ta ce
"Zata amin ce kai dai je ka latsa ta kuma ka gani in sha Allahu zata amin ce, wata mace ce zataki tayin ka duk haɗuwar ta da dukiyar ta kuwa,
ai mijin nawa da farin jinin sa aka halitto sa, shiyasa ma har gida ake kawo masa hari, wannan bazawarar taka ma jiya ta zo."
dariya duk kanin su suka fashe da shi, zillo tayi gefe ganin yami ko hannu yana kokarin ruko ta, tasan sarai baya so tari yi masa maganar ire-iren waɗan nan matan da suke kawo masa hari.
janyo ta yayi jikin sa ya rungume yana faɗin
"Zakiyi baya ni." dariyar take tana daɗa shige wa cikin jikin sa.
Kissing yashiga ai ka mata yana faɗin.
"Hakika nayi dace da mace ta gari ƴar uwa ta jini kawa kuma abokiyar shawara,
tabbas duk wan da yasa mi mata kamar ki yagama more yaruwar sa har gaba da abadan,
ke matar aljanna ce insha Allahu da yar dar Allah zamu shiga aljanna ni da ke da kafafun mu."
Baki ta turo gaba ta ce
"To HAMDAH fa?."
ya ce "To har da ita." mumushi tayi tare da daɗa rungume shi ta ce
"In sha Allahu kuwa Allah ya tabbatar mana."
ya am sa da amee. nan suka shiga nuna wa junan su tsantsar kauna da soyayya in da zancen ya sauya suka lula duniyar ma'aurata...
Wane ne AHMAD?......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama😇: Ina fita daga cikin motar na shige cikin asibiti, batare da na jira fitar sa ba,
yabuɗe wa su Nasmah yaruko hannun su suka biyo baya na, a kusan tare muka shiga cikin parlour'n asibitin.
cike da girmamawa ma'aikatan asibitin suka shiga yi mana maraba da zuwa,
direct office ɗin Dr ya nufa bayan yace nazo mu shiga.
kamar bazan bisa ba har sai da yakai bakin kofar office ɗin kafin na biyo shi,
Dr na ganin mu ya mike da sauri yana amsa sallamar da Ahmad yayi.
Dr yace "Barkan ku da zuwa bismilla."
yanuna mana kujeru biyu da suke fuskantar juna wan da suke gaban table ɗin sa, sai da muka zauna kafin shima ya koma mazaunin sa,
bayan gaisuwar da ya mika mana cikin girmamawa kana ya shiga yiwa su Naseem da suke like jikin Ahmad wasa.
Dr ya dubi Ahmad yace "Rankashidaɗe an shirya za'a iya gudanar da aikin yanzu?."
yace "Eh." batare da ɓata lokaci ba Dr ya kirawo wasu Nurse's biyu mace da na jiki, in da macen taja jini na namijin kuma yaja nasa.
muna nan zaune can da ɗan jimawa suka dawo da Result ɗin test ɗin,
suna mikawa Dr suka fita, Dr yashiga buɗe takardun, shiru yayi tare da duban mu dukkan mu kana ya kuma mai da idanunsa kan takardan,
da sauri Ahmad da gaba ɗaya yanayin sa ya sauya a ƴan sakanni yace
"Yaya dai Dr me ke faru!?." yayi tambayar da yanayin shiga damuwa, jim kaɗan Dr ya ɗago da murmushi yadube mu yana faɗin
"Komai dai-dai babu wata matsala."
Ahmad ya sauke wani dogon numfashi kana ya mike tsaye fuskantar sa ɗauke da murmushi mai bayyana zallan farin ciki, Dr ya mika masa hannu yana faɗin
"Allah ya sanya alkhairi yabada zaman lafiya."
da sauri yace "Amen amee ameeeeeen ya rabbil izzati."
ya mikawa kowa result ɗin sa.
har gurin mota Dr ya rako mu sai da muka shige mota sannan ya koma ciki.
yaja motar muka fice daga harabar asibitin.
har lokacin fuskarsa sa na bayyane da zallar jin daɗi da farin ciki,sai zuba murmushi yake. niko lokaci zuwa lokaci sai na ja karamar tsaki dan acike nake tam.
ya juyo gefen da nake ya dube ni da murmushi kana ya mai da idanun sa kan titi yace "Kyakkyawa ta kin ji albishir mai daɗi ko, ina cikin farinciki sosai da kika sami kyakkyawar sakamako a kaina, ina da tabbacin zaki daɗa samin nutsuwa dajin inganci lafiya ta,
baki ji yan da naji ba ɗazu da Dr nan yayi shiru bai faɗi result ɗin ba yana kuma kallon mu,
tunani na ɗaya ace nine keda wata matsalar shike nan nasan baza a bani ke ba, niko ban damu ace kina da wata matsala ba ahaka nake so kuma zanyi rayuwa da ke."
annurin fuskarsa yakuma faɗaɗawa sannan ya kuma dubana yana faɗin
"Kyakkyawa ta bazakiyi farin ciki da jin result mai daɗi ba dajin ingancin lafiya ta."
baki na murguɗa nace "To ni inaruwana da wani ingancin lafiyar ka, mutum da lafiyar sa an sa yaje an wani ɓula masa jiki akarin banza, ."
nayi kwafa ina kawar da kaina gefe.
da sauri yace "Yihakuri Madam na tabbatar kina da lafiya dan kisan lafiya ta yasa mukaje asibitin ayi min afuwa a gafarce ni, juyo ki kalle ni ki tabbatar da gaskiya ta kinji kyakkyawa ta."
daɗa kawar da fuskata nayi ina cuno baki gaba haɗe da murguɗa masa bakin,
murmushi mai sauti yayi yana leko fuskata... awani katon ShopRite ya tsaya yajuyo gefen da nake yace
"Kyakkyawa ta sauko mu shiga."
ko kallo bai ishe ni ba bare yasa ran amsawa ta.
tare da su Naseem suka shiga can suka fito niki-niki da kayan ciye-ciye...
Muna isa gida tun kan ya karasa dai-dai ta parking nakai hannu jikin matfin motar zan buɗe najita gam, sai da ya dai-dai ta parking ɗin batare dana dube sa ba nace
"Buɗe min." nafaɗa a takaice,
jin yayi shiru baiyi magana ba ya sani juyowa gefen da yake a kufule, karaf muka haɗa ido da sauri na janye ido na, shiko numfashi ya sauke tare da faɗin
"kin ki faɗa min in da kike so ayi shagalin bikin mu."
"Da zai fi maka karike tambayar ka kadai na dami na da ita, danni babu abin da zai kai ni gurin wani biki."
ya ce "Shike nan an daina damin ki duk yan da kike so haka za'ayi,
wai duk wannan lallen wani akayi kai gaskiya naji daɗi na, amma yayi kyau sosai fa, shine ba'a faɗa min nabada kuɗin lallen ba bayan an san hakki nane, kawo na kara gani dole ma na biya kuɗin sa."
yakai hannu ya kamo nawa yana cigaba da faɗin
"Kice zan sha kallo gobe amma bari na fara tun yau."
da sauri nayi yunkurin fisge hannu na jin wani irin shock lokaci goda ya sarga min, sai dai yan da ya rike hannunan ban sami damar iya fizge wa ba.
"Sake min hannu Malam kabuɗe min kofa nafita." nafaɗa ina ta kiciniyar kwatar hannun nawa. yace "To naji amma muga wayar ki."
"Adalilin me zan baka waya ta?."
"Aro zaki bani yanzu zan duba abu na baki."
gyara rukon wayar nayi a ɗaya hannu na na ɓata fuska nace "Ka sakar min hannun kakuma buɗe min kofa."
numfashi ya fesa yajuya baya ya dubi su Naseem gaba ɗaya hankali su na kan kallon katun ɗin da ya saka musu a wayar sa tun fitar su daga ShopRite ɗin nan.
kana ya dawo da kallon sa gare ni a hankali yaɗan rankwafo in da nake har ina jiyo kamshin sa sosai, idanu ya lumshe tare da kuma buɗe wa a kaina, da sauri na rumtsa idanuna ganin yana ta kokarin saka nasa cikin nawa, ga yan da yamatso ni sai nake jin jikina yayi min nauyi wani abu mai kamada kasala nata kokarin ziyartata,
"Ka sake min hannu ka buɗe min kofa." nayi maganar cikin ɗan ɗaga sauti yayin da idanuna ke rumtse.
yace "Zan sake ki zan kuma bude miki bayan kin bani aron wayar ki."
da sauri na mika masa wayar dan yana yin yanata daɗa shiga ta.
ya amshi wayar tare da sakar min hannu, a tare muka saki numfashi mai sauti, nayi saurin gyara zamata na matsa tajikin kofa sosai.
shima zaman nasa ya gyara kana yashiga latsa wayata daga bisani yaɗau ɗayan wayar sa shima ya daddanna sannan ya mika min wayata yana faɗin
"Na biya kuɗin lallen da aka tsara min ɗin nan."
yana rufe baki kuwa saiga shigowar alat na 1 million.
fuska na yamutsa, shiko murmushi yayi tare da buɗe min kofar, nafita da sauri ina tafiya ina kunkuni,
bayan na yabi da murmushi har na ɓacewa ganin sa, yafito ya buɗewa su Nasmah yace musu su shiga ciki shi bari ya tsaya yayi salla dan lokacin ana kiran sallar magriba...
Ina shiga na tadda su Aunty Nasiba natakan ai ki sukayi min barka da dawowa na amsa inayi musu sannun su da aiki.
koda na haura sama kayan jikina na narage sannan na fita na shiga ɗakin da su Hajiya Lubabatu suke, tana ganina tace "Yanzu nake kan maganar ki yauce rana ta karshe ga sauran kayan ki da yawa ga su dai na haɗa karɓi kisha yanzu cikin dare kya karasa sauran."
tamika min cup mai haɗin magunguna ciki, na karba ina yamusa fuska na sha nan ta sani na kwaɓe kayana tashiga mulke ni da wasu sinadaran,
har wajen karfe biyu na dare idanun mu biyu dan a daren akayi min gyaran gashi,
bamu muka kammala komai ba sai wajen karfe huɗu na asuba bayan ta wanke ni da ruwan turare nan na wuce ɗaki na,
nafaɗa gado dan gaba ɗaya idona rufewa yake sabo da tsabar bacci,
na gyara kwanciya ta ina kunkuni kasan raina
"Haka kawai a hana mutum bacci akan karin banza."
batare da ɓata lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni....
Can cikin bacci najiyo muryar Faty tana bubbugani da kiran suna na,
mika nayi tare dayin salati na bude idanuna.
fuska na ɓata nace "Faty meye haka mutum yana baccin sa zaki kama tada ni."
kai ta langwaɓar gefe tace
"Ayya Adda HAMDAH kiyi hakuri Bappa ne yace nazo na tada ki yayi ta kiran wayar ki baki ɗauka ba."
a hankali na mike zaune tare da kuma yin mika haɗe da salati,
na dubi agogon dake like da mirror karfi 12:30, ido na waro nayi mamakin ganin yan da lokaci yatafi haka.
janyo wayata dake karkashin pillow nayi ido na waro kan wayar ganin missed call ɗin Bappa yacika wayar.
da sauri na sauko a gadon na ɗau katuwar jijabin sallah ta na zura nayi waje Faty ta biyo naya na,
wani irin daddaɗan kamshi ne yaziyar ci hanci na san da na kusa kai na cikin parlour, an gyara ko ina sai kamshi ke tashe, babu kowa cikin parlour'n sai kamshi da sanyin da ke tashi ciki.
step na nufa da ɗan sauri, na sauka kasa
mutane ne tam cikin parlour'n ka da wan da na sansu da wan da ban sansu ba, a sakiyar parlour'n kuwa wasu zuka zukan akwatuna ne da suka kai set 6 kaloli daban-daban, Inna Wuro na zaune gaban akwatunan tana gani na tayi min murmushi, nima na mayar mata tace
"An tashi ne HAMDAH?." nace "Eh Inna inasu Nasmah ne?."
tace "Ai yau su Nasmah ba zama anayi musu wanka suka fita wai Daddy'n su na jiran su a waje." kai kawai na jinjina.
can na hangi su Hajiya Rahama da Hajiya Lubabatu suna ta nuna wa wasu mata kusurwa-kusurwan cikin parlour'n in da zasu kunna turare.
nayi musu sannu na wuce su in da wasu suka bini da guɗa suna faɗin
"Kaga amarya ta fito hasken ta ya bayyana."
banbi ta kansu ba nayi waje.
ina shiga side ɗin su Bappa na taddashi tsaye yana gyara zaman babban rigar jikin sa yana gani na yace
"HAMDAH ina kika saka wayar ki nayi ta kiran ki baki ɗagawa?."
nace "Bappa bacci nake."
yace "Ina takardar sakamakon da likita ya baki jiya a asibiti? ga mutane can an fara hallara ana idar da sallar juma'a za'a ɗaura gashi lokaci ya tafi ɗaya saura yanzu yi maza ki kawo min."
wani irin rass naji gaban kirji na ya yanke jiki a sanyaye nace
"Yana ɗaki."
yace "Yi maza ki kaso min." nan da nan naji jikina yayi mugun sanyi, na dubi Faty nace "Faty je ki ɗaki zakiga takarda kan mirror ki ɗauko."
tace to ta juya da sauri ta fita.
niko
a hankali nayi baya nazauna saman kujera dan gaba ɗaya jikina yagama sanyi har nake jin jikina nason yayi wa kafafu na nauyi, a bun da nake ganin sa kamar wasa dai gashi nata kokarin zamowa gaskiya.
lura da yanayin da na shiga yasa Bappa yashiga