Showing 57001 words to 60000 words out of 125808 words
fuskarsa ɗauke da farin ciki kullum acikin dariya da fara'a yake, ikon Allah to shi wannan wani irin mutum ne haka?.
hawaye ni naji sun zube min jikina yayi sanyi na mugun tausaya wa rayuwar sa da yake cikin hatsari.
magana ya cigaba da yi
"Ta nimi Rasheedat da kusan irin haka sai dai ita bata kaiga bata magani ba, kasan cewar Rasheedat a gidan mu ta tashi tasan dukkan halin ta, tun da ta fara faɗa mata wasu maganganun da basu ɗauke ta ba, sai ta yi saurin bijire mata, shike nan tun daga ranar ta ɗau ki tsana ta kuma ɗaura mata, dan dama sam bata son auren mu da ita tun da naki amin cewa da auren ɗiyar kanin ta, ako da yaushe cewa take wai tayi mata rashin kunya."
Numfashi na sauke nakai hannu nashare ɗan guntun kwallar da ya zubo min a hankali nace
"Shine kake cin abincin ta baka jin tsoron ta zuba maka maganin ciki?."
murmushi yayi tare da jan kumatu na yace
"Kina ji min tsoro ne kyakkyawa ta?."
ido na lumshe tare da kuma buɗe wa.
numfashi yaɗan sauke sannan yace
"Bazata taɓa gangancin yunkurin yin hakan ba, dan ita a karamin tunanin ta idan ta yi haka za'a iya zargin ta, shiyasa bata taɓa yunkurin kwatanta hakan ba, sai dai tasa ayi,
kada kiji tsoron ta idan ta gane kinji tsoron barazanar da ta miki, zata kuma samin da mar cigaba da yi miki barazana, idan ta kuma tarar ki da maganar kice ta sallawantar da rayuwar naku in zata iya,
zata kuma yi miki barazanar da zai firgita ki kada kiji tsoro dan babu abin da zata iya."
kai na girgiza jiki a sanyaye, janyo ni jikin sa yayi tare da sakin ƴar karamar dariya yaleko fuskata sai ya kuma sakin murmushi mai sauti cikin yanayin sa na zolaya yace
"Har yanzu wayo da saura tukun ayi maka tayin dukiya mai yawa kaki karɓa."
baki na turo gaba tare da janye jikina daga nashi ina ai ka masa da harara, nayi yunkurin mike wa.
ya mai dani jikin sa yana dariya kasa-kasa.. yana yin sa yana bani mamaki shi da yakamata yayi zaman kunci amma ko da yaushe yana cikin walwala...
After 2 week
Hakan yayi dai-dai da watan Ahmad guda a gidan nan, a daren jiya ya koma gidan sa, tare da su Naseem ya tafi kasan cewar daren weekend ne jiya. zuwa yanzu nakan ɗan sake masa har idan ya na yimin hira nakan ɗan rika amsa masa, duk sona dana rika share sa amma sai yasan hanyar da yabi yasa na kula shi, Ahmad mutun ne mai saukin kai, yana da faram-faram da son yawan fara'a da zolaya bashi da ɗaure wan kai ko kaɗan.👌🏻
Zaune nake a ɗaki kiran Bappa yashigo waya ta, ko da na ɗaga yace idan ba abin da nake nazo nace to.
a hankali nafita, shiru parlour babu motsin kowa, daga jiya zuwa yau side ɗin yadawo wani shiru haka babu hayaniyar su.
na wuce sashin su Bappa bayan mun gaisa Bappa ya ɗaura da faɗin
"Jiya nasami kira daga jagororin da a ka ɗaura kan kula da ma'aikatan mulmula karfe daga Lagos, abun farin ciki suke shaida min an kammala ginin yau kuma da yardar Allah jirgi zata iso da kayan aiki."
baki na washe cike da farin ciki nace
"Masha Allah Allah abin godiya."
Bappa yace "Kwarai kuwa, yanzu in da a ce so shine samu ya ace jibi muna can a sauke kayan a gaban mu,
yanzu sai ki nimi izinin zuwa a gurin mijin ki idan ya barki jibin sai mu je, gobe sai aje a biya kuɗin jirgi idan Allah yakai mu jibi da safe sai mu ɗaga."
"Izinin miji sabon salo lallai ma."
nayi maganar a kasan raina
maganar sa na jiyo yana faɗin
"Idan bai barki ba kada ki matsanta ni zan tafi, duk randa Allah yasa ya bari kije sai kije daga baya."
da sauri nace
"Bappa sai ya bari ai dai yasan irin harkoki na kuma dan shi ai baza a fasa zuwa ba."
"Akul ɗin ki kada na sake jin wannan maganar yafito daga bakin ki, idan yasan harkokin ki ai da da yanzu ba ɗaya bane, kuma ba'ayi yarjejeniya dashi kan zaki iya tafi gurin harkokin ki a duk sanda bukatar hakan ta taso ba,
kin san girman aure kuwa? to kada ki kuskura kiyi wasa da shi, ko nan da kofar gida kika leka har idan bada izinin sa ba sai mala'ikan Allah sun tsine miki, aure ba abun wasa bane HAMDAH yazama dole ki nimi izinin sa a duk sanda fita ya kamaki, bijere wa hakan saɓawa dokar Allah ne, ki tambaye sa idan ya barki sai kije, kada ki kuskura ki tafi bada izinin sa ba, kinji ko?."
kai na gyaɗa, yace
"Yauwa Allah yayi albarka ki tashi kije idan ya barki sai mu tafi jibin."
nace to na mike na fita, ina tafiya ina magana
"Wai shi miji in za'a fita wai sai an tambaye shi."
na kaɗa harshe tare da yin kwafa..
ina shiga side ɗina na tadda su Talatu sun shigo yin aikin su na zauna nan parlour'n kasa suna aikin muna ɗan taɓa hira....
Washegari da yamma lis su Ahmad suka dawo, su Naseem suka yi ta cike ni da surutu da labaran abunuwan da sukayi aka kuma yi musu,
cike da kewar su narika biye musu ina dariya, suka rika bani labarin wai ɗayan Mamyn su tayi musu kaza wai ɗaya Mamyn su na ɗaya gidan Daddyn su har goyon su take.
ni dai sai binsu da dariya neke...
da daddare bayan sallar isha ina zaune bakin gado Ahmad ya shigo da sallama,
na ɗago na amsa masa sallamar tare da mai da kai na kan wayar dake rike a hannuna.
ya karaso cikin ɗakin a gefe na ya zauna, ya leko fuska ta yace
"Kyakkyawa babu ko ɗan barka da zuwan nan ne?."
baki na cuno gaba, murmushi yayi yace
"Yaushe ne zaki fara yin murna da gani na?."
baki na murguɗa ina kokarin kawar da fuska ta yiyi saurin juyo fuskar tawa ya sauke min kyakkyawar sumba kan lip, ya ɗan lumshe ido tare da buɗe su a kaina a hankali yace
"Suna da kyau da daɗin tsotsa."
yayi maganar da ɗaura hannu kan lips ɗi na,
hannun sa na bige ina cuno bakin gaba.
murmushi yayi mai sauti.
mike wa yayi zai fita har yakai bakin kofa naɗan kalle sa nace
"Bappa yace na faɗa maka zamuje Lagos jibi."
nayi maganar a takaice ina janje idona daga gare shi.
a hankali ya juyo daga in da yake tsaye yace
"Ayya Bappa Malam Allah ya tsare masa hanya."
a hatsale nace "Har da ni zamu tafi."
ido yaɗan waro yace "Wa har da ke ina ban amince ba bazaki jeba."
a hatsale na dube sa nace
"Bazan je ba? ka faɗi son ranka kasan dai da harkokina ka same ni tafiya kuma ba bashi."
murmushi yayi tare da faɗin
"Bazaki je ba haka na ce, shi harkokin naki sai na datse su a yau, duk ranar da kikayi wayon sanin iya tambaya ta da kanki ba basai an sa ki, ki tambaye ni ba wata kila na barki kije."
yana kaiwa nan ya juya yayi waje.
Wani shekeke nabi bayan sa da kallo abin ya ban haushi, wai nice yau zanje wani guri nake tambayar wani har yake ikirarin cewa bazani ba.
a fili nace "Idan nazo tafiya ka janyo ni na fito cikin jirgin dan kasamu ma na tambaye kan idan badun Bappa ba babu abin da zaisa na tambaye ka."
naja gajeren tsaki tare dayin kwafa.
washegari da safe Bappa ya kirani yace za'a je yin bukin na jirgi shin na tambaya an barni.
jin nayi shiru yasa Bappa faɗin
"Idan kin san ba'a barki ba kada ki yi gigin tafiya gashin kanki, ki hakura kawai."
a hankali nace "Bappa zai bari ma."
na kasha wayar da sauri na mike na fita na nufi kofar bedroom ɗina, har na ɗaura hannu kan handle sai kuma na tsaya, wai wannan mutumin me yake ɗaukar kansa ne na rantse sai na zana masa iyakar sa idan ba haka ba shi har wani ji yake wai shi miji ne.
da karfi na murɗa handle ɗin natura kofar da karfi,
yana kwance a kan gado, yana kwance babu riga a jikin sa ya rufe jikin sa da blanket daga kafafun sa zuwa cikin sa idanunsa a lumshe da alama bacci yake,
na karaso bakin gadon na tsaya tare da rike kugu.
nasoma magana a hatsale cikin ɗan ɗaga sauti
"Wai na ce zan tafi kana gwada min bazani ba a wani dalili?, kada kaga ina tambayar ka, karika son gwada min wani bushashen iko, narantse badun Bappa ya matsa min da sai na tambaye ka ba da ba abin da zai sa na tambaye ka, kuma yan zu ma tafiya ta zanyi ko ka bari ko baka bari."
duk maganar da nake idanunsa a rufe hannu na mike da zummar bubbuga shi ya tashi yaji matsaya ta, sai ji nayi ya fisgoni nafa faɗo jikin sa,
blanket ɗin jikin sa ya zare, babu komai jikin sa sai boxes, kokarin yunkurawa nake sai ya janyo ni ya haɗe ni da jikin sa, wani irin shack naji lokacin da na jini cikin fatar jikin sa, yayin da ɗumin jikin sa ya ziyar ci ilahirin jiki na.
ya saka hannayen sa gaba ɗaya ya zagaye ni da shi babu ta in da zanyi na kwace kaina.
a hankali ya buɗe idanun sa ya zuba su cikin nawa, numfashi ya sauke a hankali ya soma magana
"Yau she ne tafiyar naku?."
da sauri nace "Gobe." yace
"Allah ya kai mu kicewa Bappa na amince kuma nima zan faɗa masa dan kar yayi zaton kin faɗa ne kawai, hakan yayi miki?."
a hankali cikin sanyin jiki da jin yan da ya amsa min duk da yan da nayi ta masa maganar a tsaye, sai na gyaɗa masa sai.
murmushi ya sakar min yace
"To Allah ya kaimu goben." a kasan raina na amsa da amin, idanunsa ya lumshe a hankali ya buɗe su, a sannu ya sauke bakin sa kan goshi na ya manna mishi kiss,
a hankali ya shiga yawo da hannunsa a bayana, jin abun nasa yana kokarin zarce iyaka, sai nayi huff zan mike na kasa sai na shiga ture sa ina faɗin
"Sake ni ka dai na bana so."
yace "Ina bacci na kika zo kika tada ni, alhalin ke ba tayani baccin zakiyi ba, da kyar na samu wannan baccin ya ɗau keni shine zaki ɓata min shi, to ai biya na zakiyi ɗumi zaki bani zan iya komawa baccin wata kila, idan kuma ban koma ba to sai kin bani asalin ɗimin, dan bazaki ɓata min bacci kitafi ba."
yana karasa maganar ya zuge zip ɗin riga ta har kasa ya raba shi da mahaɗin sa, ido na waro jin yana kokarin rabani da rigar, kafin nayi auni ya zare ta a jikina, wani irin nannauyan numfashi ya sauke,
ido ya kurawa fararen nonuwa na da suke cikin bra, numfashi ya fizga da kyar,
da sauri ya haɗe kirji na da nashi tsam ya rungume ni.
niko turesa na cigaba da yi ina fadin ya sake ni, bai kula ni sai da muka kai tsawon minti 20 a haka,
kafin yashiga sassauta min rukon da yayi min, yayin da gudun numfashin sa yakaru.
da sauri na janje jikina na duro a gadon ban ko tsaya ɗaukar rigata ba nayi waje, sai da na koma ɗaya ɗakin kafin na sauya kaya....
Washegari da misalin karfe 9 muka fito parking lot, Inna Wuro da ma'aikatan gidan suna ta yi mana Allah ya tsare,
Ahmad da Bappa tuni sun shige cikin mota dan shi zai kaimu airport na isa jikin motar na buɗe gefen mai zaman banza na shiga, yaja motar suna ɗaga mana hannu muka fita,
dashi da Bappa sunata hira yayin da yake ta bina da kallon kasan ido, baki na murgaɗa masa na kawar da kaina.
har muka isa airport bai fasa bina da kallon ba.
yana dai-dai parking Bappa ya fita ina kokarin buɗe motar naji hannun sa kan cinya ta, yashiga murza shi da sauri na juyo muka haɗa ido, a hankali yace
"Zanyi missing ɗin ki." kai kawai na kawar na buɗe motar na fita.
bai bar airport ɗin ba sai da jirgin mu ya tashi..
ko da ya koma gida jiran lokacin tashin su Nasmah yayi daga school lokaci nayi yaje ya ɗauko su yawuce da su can gidan sa...
Ranar da muka isa Lagos washegari aka shiga da kayan aiki cikin katafaren Company, aka shirya komai a ma'ajin sa, aka rufe Company sai an ɗibi ma'aikata kafin ayi bikin buɗe Company.
Kwanan mu uku a Lagos muka juya Abuja.
ko da muka iso nayi mamakin ganin sa a airport ya kwashe mu yayi da mu gida.
muna isa gida baccin gajiya na kwanta dan tun da muka tafi ban sami nayi baccin kirki ba.
sai yamma lis na farka,
na faɗa bayi nayi wanka nafito naci abincin da naga an shirya saman dinning, nayi ta zuba idon gani su Naseem sun shigo shiru,
na mike na sauka kasa Talatu na tarar a kitchen tana gani na ta kara yimin gaisuwar yaya gajiya,
na amsa nace
"Su Naseem fa basu dawo bane?."
tace "Eh gaskiya ban gansu ba naga Alhaji ya shigo amma ban da su ina ga bai dawo da su bane."
ban kuma cewa komai ba na juya na koma sama, zuwa yanzu kam ina so na gansu duk da kullum sai munyi waya da su ta wayar Ahmad a rana fin sau biyar.
bayan sallar isha ina idar da sallar na shiga bayi wanka na kuma nafito ɗaure da towel,
turus na ja natsaya ganinsa zaune a bakin gado, fuska na ɓata na karaso cikin ɗakin ina ɗan jajjan towel ɗin kasa dan rabin cinya ta ya tsaya.
ido ya zuba min babu ko kiftawa.
tsayuwa nayi a tsakiyar ɗakin na ɗan dube sa nace
"Ka fita zan sa kaya."
ido yakanne yace "Ɓoye min halal ɗi na za'ayi, to shike nan bari na rufa idanuna kisa kayan ki."
ya kai hannunsa duka biyu ya rufe fuskarsa yana faɗin
"Narufe kisaka." ɗan guntun tsaki naja na isa in da hijabin salla na yake na ɗauka ina kokarin saka sai ji naya an fizge,
da sauri na waigo nace "Meye haka? ka bani hijabi nasa."
cilla hijabin gefe yayi yadaɗa matsowa daf dani sosai har muna gogan juna, a hankali ya sauke hannunsa kan kafaɗa ta yashiga murza shi a hankali, yace
"Me yasa zaki cigaba da sanya masa hijabi a sakanin mu, kyakkyawa ta bakya tausayi na ne? a koda yaushe zaman jiran ranar da zaki juyo gare ni nake, sam bana so nayi miki dole, har yaushe zamucigaba da irin wannan zamar, kin san daya nake iya bacci da ciwon sonki da bukatar ki,
shin kin mance ina da hakki a kanki ne, bakya tsoron Allah ya tambaye ki kan hakki na?."
da sauri na kai hannuna kan nashi jin yana gangaro da hannun izuwa saman kirji na, na janye hannun shi ina faɗin
"Wani hakkin ban san shi ba."
murmushi ya sake yace "Dagaske to bari na nuna miki."
cak ya ɗago ni yadire ni kan gado shima ya hau ido na rumtse da karfi jin ya sauke hannunsa kan kirji na yana kokarin kwance towel ɗin da ke jiki na.
da karfi na rirrike hannunsa nace
"Kada ka kunce na rantse idan ka kunce..."
cak na haɗiya ragowar maganar tawa jin ya..........!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: *HMDH*
*WASA FARIN GIRKI*
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
20
Nayi sallama ina kusa kaina cikin ɗakin, wata ƴar dattiju war mata ce ke hakimce a kan kujera, ta amsa sallamar tana mai faɗaɗa fuskarta da murmushi,
tace "A'a manyan ba'ki ne agidan namu? barkan ku dai sannu ku da zuwa,zo zauna nan ɗiya ta zo maza ki zauna a kusa da ni."
ta nuna min gefen kujerar da take kai na alfarma.
a hankali na karaso ina kokarin zama a kasa gefen kafafun ta tace
"A'a tashi ki zauna a sama."
kai na sunkuyar cike da jin kunyar cewa na zauna a sama in da take zaune sai na gyara zamata a kasa gefen kafafun ta ina mai cigaba da tsunkuyar da kai.
a sakiyar ɗakin ya zauna kan lafiyayyen carpet mai laushi da ɗaukar ido, in da su Naseem suka zauna a gefen sa.
a hankali cikin sunkuyar da kai nace
"Inayini Hajiya mun same ku lafiya."
fuskata ta leko tana faɗin
"Lafiya lau amarya kunzo lafiya?,
wato Ahmad sai yau yakawo min ke ko, ai ko Allah yayi albarka ace rayuwa tana yin dai-dai."
kai na daɗa sunkuyar wa ina wasa da ƴan yatsu na ina murmushi.
shima ya gaishe ta ta amsa tana mikawa su Nasmah hannu tace
"Waɗan nan kyawawan yaran sune jiko kin nawa kuzo kusa da ni, kai ma Allah ya nuna min ranar da zanga naka haka tafe da kafar su."
murmushi yayi yana amsawa da amin
Naseem ne kaɗai yaje gurin ta Nasmah kam kin zuwa tayi sai daɗa lafewa jikin sa tayi...
nan da nan ta saka aka cike mu da kayan ci da sha,
ta dube ni cikin kula tace
"Ban ga kinci wani abin kirki ba, ko da wani abin da kike bukata ne daban akaso miki?."
kai na girgiza nace "A'a waɗan nan ma sun isa nakoshi ne."
baki ta washe tace
"To madalla ai koshi shi mukafi so, ka shigo gida kamar wannan kafita bada koshi ba ai shigar batayi amfani ba."
murmushi nayi ina cigaba da wasa da yatsun hannuna.
murmushi yayi yana yimin kallon kasa-kasa.
hira sosai Hajiya tayi ta jana da shi har na ɗan fara sake wa can ya mike yana duba agogon dake ɗaure a hannunsa yace
"To Hajiya zamu koma." da sauri tace
"A'a tun yanzu? na ɗauka sai dare ai ku koma."
yace "Yaran suna da islamiyya ne ga lokacin zuwan su yayi sai ranar da babu makaranta zasu zo su wuni miki."
tace "Amma kam banji daɗi ba ace yanzu kuzo yanzu ku koma, to in za'a sake kawo min su a kawo su da wuri su wuni min."
yace "To insha Allah."
tace "Allah ya tsare min kai gaban ka da bayan ka yarabaka da sharrin makiya ya bada Sa'a."
"Amin amin." ya amsa da shi fuska ɗauke da murmushi yana kuma yi mata godiya,
Ummi na ne ta faɗo min "Hakika lallai uwa akwai daɗi Ummi na kiyi ta bina da addu'ar ki nasan a koda yaushe shi ke sani nutsuwa." kayan tsarabar da nayi mata na ajiye mata tayi ta godiya nan ta karɓi number ta mukayi sallama, har kofan parlour ta rako mu