Showing 93001 words to 96000 words out of 125808 words
babu bil'adam, sai sautin kukan karnukan gadi.
a hankali Ummi ta mike tazo jikin get ɗin ta kwankwasa.
mai gadi ya buɗe ido ya waro yace
"Har lau kece?."
a fusace security suka tambaye sa waye?
yace musu "Matar ɗazun ɗin nan ce." a fusace ɗaya daga cikin su ya mike yafito yace mata maza-maza ta bar bakin get ɗin nan tayi nesa da gidan nan tun bai sa bindiga ya harbe ta ba, ya ɗaga bindiga yana faɗin tayi sauri ta bar eriyan nan.
ai ko da sauri ta ɗau jakar ta tasoma tafiya, cike da takaicin wai ita ce ake yiwa korar kare irin haka, amma babu komai zata jure koma mene ne har idan zata samo ɗiyar ta...
Acikin gidan kuwa Faty na zaune a parlour ganin Bappa ya mike yana faɗin
"Lokacin salla ya kusa bari na shiga Masallaci."
da sauri ta mike tace
"La na mance wata mata tun ɗazu ta zo tana bakin get security sun hanata shiga, wai cewa tayi ita mamar Adda HAMDAH ce, na mance naje na faɗa mata ko zata sa a barta ta shigo wata kila taimako ta ke nima."
tsayuwa Bappa yayi kana yaɗan yi shiru yace
"Tace ita maman ta ce?." kai ta gyaɗa tana mike wa da faɗin
"Bari naje na faɗa mata Allah ta ban tausayi tun ɗazu take zaune a waje."
Inna Wuro tace "To shine tun tuni baki je kin faɗa mata ba kika zauna shiriri ta, ace tunruni tana waje ai ko kuɗin mota aka bata zata ji daɗi."
waje Faty tayi tana faɗin "Yan zu zanje na faɗa mata ai wata kila har yanzu tana waje dan ko shigo wa ta ma a waje na barta."
Ina daga parlour'n sama najiyo muryar Faty a parlour'n kasa, Ahmad na zolayar ta budurwar Ustaz tana ce masa ita bata ma sanshi ba,
ta hayo saman tana dariya.
na sako kai na zan sauko ita kuma zata shigo parlour'n sama tace
"Yauwa Adda HAMDAH dama gurin ki zan je, tun ɗazu wata mata tazo tana bakin get security sun hanata shiga tace wai ita mamar ki ce, su kuma suka ce karya take so take abarta ta shigo kawai."
ido na waro tare da dafe kirji nace
"Wai ita mama tace?." kai Faty ta gyaɗa min. da sauri nace "Tana ina?." tace "Tana bakin get." da saur na wuce ta ina faɗin
"Ina so na ganta babu wan da ta taɓa zuwa tayi karyar cewa ita mama na ne, sai dai suce su ƴan uwa na ne, ina so na ganta."
nayi maganar ina karasa sauka daga step da sauri, gaba ɗaya jikina ya ɗau kyar ma,
cikin hanzari na nufi kofa da sauri haɗe da sassarfa nayi waje.
da sauri Ahmad ya mike rungume da Ahmad karami yana tambayar Faty ta faɗa masa ko mene ne, bayan na yabi da sauri su Naseem suka biyo sa...
tun daga farfajiyar gidan naɗaga murya ina faɗin
"Mai gadi ina matar take."
har na karaso get ɗin, da sauri msi gadi ya mike yace "Hajiya an kore ta ta tafi."
murya a hargitse nace "Kuje ku kira ta yan zu ku dawo da ita ina so na ganta."
cikin hanzari biyu daga cikin security sukayi waje suka lelleka kana suka dawo suka ce, basu gan ta ba.
ganin yan da gaba ɗaya lokaci guda na ruɗe cikin tsawa Ahmad yace
"Kuje ku nemo ta yanzun nan kuzo da ita."
ai ko da sauri sukayi waje.
niko tsayuwa na gyara ina mai da numfashi kamar wacce tayi tsere.
Bappa ya karaso in da muke yana tambayar matar ta tafi ne?.
Ahmad ne ya iya bashi amsa nikam gaba ɗaya na ruɗe sai kyarma nake haka kawai naji ina so na ganta.
munkai tsawon minti 15 tsaye a gurin kafin aka turo kofa,
ganin security ne yasa ni ɗaga murya nace
"Ina take?." yace "Gata nan Madam sai da muka fita can farkon eriya kafin muka iske ta."
yayi maganar ne yana shigo wa ciki, niko leken bayan sa nake ina alla-alla naga matar.
a sannu ta sako kafar ta cikin gidan da sallama yayin da ɗayan security ke biye da ita.
kamar almara kamar a mafarki nake binta da kallo yayin da na wawwaro idanuna waje cikin matukar mamaki.
ido na kuma waro wa da karfi na furta
"Ummi Ummi na!!." da gudu nayi in da take na rungume ta ina faɗin
"Ummi dama kece Ummi kece."
sai kawai na fashe da kukan farin ciki ina daɗa rungume ta.
ita ma rungume ni tayi tana bubbuga baya na yayin da hawaye ke zuba a idon ta tana faɗin
"Kiyi hakuri HAMDAH kiyi hakuri........!
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 33
Bappa ya soma da addu'a bayan addu'a ya ɗaura da faɗin
"Alhamdulillah muna godiya wa tabakara maɗaukaki mabuwayi mai izza, wan da ya nuna mana wannan rana, muna niman tsari da sharrin masu sharri Allah ya kaɗe mana fitina, muna godiya wa Allah da ya nuna mana wannan rana, Allah ya daɗa kaɗe mana fitina duniya da kiyama."
kowa ya amsa da amin amin,
Bappa ya gyara zama tare da ci gaba da faɗin
"Abubuwa sun faru da dama bama fatan hakan ta kuma faruwa Allah ya kaɗe fitina, ya iyar mana abun da baza mu iya ba, Allah yayi mana maganin makiya da masu hassada kamar yadda ya nuna musu karshen sharrin su,
hakika addu'a makarin Mumini ne, a na son musulmi a duk in da yake a duk halin da yake ya kasan ce mai ruko da addu'a, domin addu'a takwabi ne mai kaifi ya kan tsare fitina da sharri da kaifin sa, hakika wannan abu da ya faru ya nuna ɗan dakacin addu'a kaɗan duk da Allah yayi taimako an farga da wuri, Allah ya da ɗa tsare mu ya yi mana katangar karfe da azzalumai."
Abbu ya jinjina kai cike da gamsuwa yace "Amin ya rabbil izzati, hakika addu'a takwabi ne mai kaifi hakika lamarinnan ya jijjiga mu ba kaɗan ba duk da bakin mu baya iya
furta wa amma zuciyoyin mu tana kuna."
ya ɗan sakai ta maganar tare da duba na kana yaci gaba da faɗin
"Kiyi hakuri HAMDAH duk da bamu kuma yunkurin niman ki ba amma zuciyoyin mu suna tare da ke a ko da yaushe."
kai Bappa ya jinjina dan ya san cewa ai kin sihiri kenan shi yasa ake so a koda yaushe mutum ya zamana yana cikin sarki da addu'a idan aka jefe ka da shi bazai yi wani tasiri a tattare da kai ba...
Abbu yace "Muna mai ci gaba da baki hakuri hakika mun ai kata rashin kyautawa wa rayuwar ki, a matsayin mu na iyayen ki da kike da hakki a kanmu da muka gaza sauke shi na wasu shekaru mu na ruko da ki yafe mana."
da sauri na shiga girgiza kai yayin da hawaye ke zuba a ido na
kwalla na share nace "Abbu bakuyi min komai ba, Abbu ka rokar min Abba ya yafe min dan naga kamar har yanzu bai yafe min ba amma wlh ni ban taɓa ai kata zina ba."
wani kuka ne ya tsuɓuce min na fashe da kukan, Aunty Rafee'at ta rungume ni itama ta fashe da kuka.
cikin matuƙar nadama Abba yake faɗin
"Ki gafarce ni HAMDAH tsananin kunyar ki ce ta hanani iya furta komai, tabbas nayi danasanin yanke hukunci cikin fushi, ki gafarce ni ki gafarce ni HAMDAH ina mai da na sanin yanke hukunci cikin fushi,
dana kore ki HAMDAH ina kika shiga ina kika shiga HAMDAH nayi da na sani nayi na dama HAMDAH ina kika je wani rayuwa kika yi?."
Abba yayi maganar cikin nuna nadama sosai kamar zai zubda kwalla.
in da yake na rarrafo tare da rike hannunsa gam kana a hankali nashiga basu labarin abun da ya faru, tun ranar da na sa kafa na bar gida da
rayuwar da na fara fuskanta,
da rayuwar da mukayi cikin daji ni da su Naseem da,
irin gwagwarmayar da na sha a rayuwa har na kai matsayin da na ke a yanzu.
tun da na fara bada labarin
gaba ɗaya parlour'n ya kacame da koke-koke su Aunty Rafee'at har da jan shassheka, Ummi Mamie gaba ɗayan su kuka suke wei-wei kamar kananun yara,
Abba Abbu Bappa Ahmad duk kanin su sai sharar kwalla suke.
Abba yana sharan kwalla yana faɗin na yafe masa,
kai na shiga girgiza wa
nace "Baka yi min komai ba Abba."
Mamie tana kuka ta rungume su Naseem da tun ɗazu take jin wani yanayi a kansu a kasan ranta take faɗin a she dai jinin ta ne su shiyasa tun da ta sanya idanunta kan su take jin su a cikin jikin ta.
su Abbu suka shiga yiwa Bappa godiya da irin kokari da jajirce wa kan lamari na da yayi yake kuma kan yi shi da matar sa wato Inna Wuro.
Bappa yace ai yiwa kaine, da ɗa da dukiya bana mutum ɗaya bane kuma ba'a yi musu keta.
sun yaba kwarai da gaske da irin kokarin da Mama mai awara ta yi a kaina suka kuma ɗau alkawarin niman ta suyi mata godiya.
Ahmad ma godiya suka yi ta masa suka kuma yi jinjina ga Rasheedat matar da ba kasafai ake samun irin su a duniyar mu ba....
A ɗaya side ɗin da babu kowa ciki wan da yanzu su Talatu suke kwana ciki, nasa su Talatu suka fita suka koma side ɗin su Inna Wuro suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan side ɗin wan da ba kowa ciki,
wannan side ɗin kuma nayi wa su Abbu da Abba Ya Masa'ud Fauzan masauki ciki.
ɗaya daga cikin
ɗakunan kasa kuma aka shigar wa Mamie kayan ta ciki, ɗaya ɗakin kuma Aunty Jaleela da Aunty Rafee'at da Nusaiba.
a ranar raba dare mukayi muna hirar bayan rabo da ahlina abu mafi soyuwa a rayuwa ta, Ahmad kuwa gidan sa ya tafi yace ya barni na gana da ƴan uwa na, bayan ya gama zolaya ta wai na share shi na nuna masa wariya...
kwanan su Abbu uku suka soma shirin komawa gida bayan na kaisu na nuna musu duk kanin kadarori na da suke cikin garinnan,
sauran na wasu gararruwan kuma a computer na nuna musu..
ranar da suka cika kwana biyar suka juyo Bauchi, amma banda Ummi dan ta ce ita tana nan sai ta yimin zaman arba'in tukun.
Abba ko da wasa bai yi yunkurin hana ta ba, sai dai ma karfafawa zaman nata da yayi, yace ta zauna tayi min wankan arba'in kamar yadda ake yiwa mai haihuwar fari dan na cancanci haka, duk da na sami ingantaccen kulawa gun Mama mai awara a haihuwa ta ta farko wan da ya kamata ace uwata ce ta bani wannan kulawar,
to amma guri bai kure ba, ta zauna nakuma kara samu agurin mahaifiya ta...
Ahmad yayi musu goma na arziki dan mota guda ce ta raka su da kayan tsaraba, bayan wan da nima nayi musu..
lokacin da suka iso gida Masa'ud ya shiga ɗakin sa, yayi matukar mamaki haɗe da razana ganin SALEEM cikin ɗakin a kwance ya dukunkune cikin bargo sai rawar sanyi yayi, lokaci zuwa lokaci kuma sai yayi wasu tagwayen tari ya dafe kirjin sa da karfi yana matse idanunsa.
a bin da ya daɗa bashi mamaki shine kayan jikin sa, kayan da yazo da shi gidan ranar da zasu tafi Abuja gurin HAMDAH, "Kenan tun ranar yana ɗakin nan?."
Masa'ud yayi maganar a ransa, da sauri ya karaso bakin gadon yana faɗin
"Subhanalla Ya SALEEM baka da lafiya ne?."
da ido kawai ya bishi barate da yayi magana ba.
ganin yan da ya kuma rumtse idanunsa yana daɗa damke kirjinsa,
da sauri Masa'ud ya fito dan yaje ya sanar wa Mamie halin da SALEEM ɗin yake ciki.
a sakiyar gidan ya haɗu da su Abbu da alama masallaci zasu tafi,
da sauri ya karaso in da suke yace
"Abbu Ya SALEEM bashi da lafiya yana kwance a ɗaki na."
da sauri Abba yace "Subhanalla me ya same shi?."
ya juya da sauri ya nufi ɗakin nasa Masa'ud ya rufa masa baya.
Abbu kam tsayuwa yayi yaɗan yi dimm kana ya girgiza kai yawucw masallaci abin sa..
Abba na shiga ɗakin ganin halin da yake ciki yashiga tambayar sa abin da ke damun sa,
ba wani kwakkwaran amsa ya samu a gurin sa ba dan tun da ya tambaye sa, me ke damun sa ya nuna masa kirjin sa bai kuma cewa komai ba duk tambayar da yake masa.
Abba ya ɗaga waya ya kira Dr Farooq yace ya zo yanzu.
batare da ɓata lokaci ba Dr Farooq ya iso.
bayan sudduba shi da yayi ya rubuta masa magani, Abba ya bawa Masa'ud kuɗi yaje ya siyo maganin ya kawo masa....
Abuja
Ina samun kulawa sosai wajen Ummi na, dan dole Ahmad ya tarkasa ya koma gidan sa sai dai yazo ya duba mu ya koma.
yanzu bani da wata damuwa a rayuwa ta hankali na ya daɗa kwanciya, na daɗa yin ɓul-ɓul da ni na kara haske da sheki na kara kyau,
kullum ina tare da Ummi na hankali na a kwance..
Hajiya Lubabatu na kira nayi mata aiken kuɗi ta turo min kayan gyara irin na masu jego.
kafin na cika arba'in kuwa idan ka ganni sai ka kara kallo na, shi kan sa Ahmad idan yazo yakan zauna ne yata kallo na, wai shi ya godewa Allah da ya kawo masa Ummi tamkar kara min kyau take,
dariya kawai na ke masa.
ranar dana ciki arba'in Ummi ta fara shiri washegarin ranar Ummi tace yau ba kwana sai Bauchi, na sha kuka na har na gaji, nace sai dai mu tafi tare,
tace a'a na bari sai jiki na ya daɗa karfi jaririn ma yadaɗa kwari sai nazo zan fi jin daɗin zuwan...
direba ya shirya kayan ta cikin mota da kayan tsarabar ta da Ahmad yayi mata, da wan da nima nayi mata.
muna tsaye a parking space dukan mu gudan sai hawaye nake sharewa, cikin tura baki nace
"Allah Ummi sati ɗaya zan kara na zo."
tace "A'a HAMDAH kibari ɗan nan ya daɗa yin kwari kada kirika kwasar sa kina yawo da shi bai yi kwari ba, kibari nan da wata uku lokacin yayi kwari sosai sai ki zo."
ido nawaro nace "Ummi har wata uku Allah ni dai a'a."
Inna Wuro tayi murmushi tace "To in ban da abin ki HAMDAH wata uku yanzu nawa yake kamar gobe ne agurin Allah."
Ahmad kuwa sai washe baki yake adole yaji daɗi an ce ba yanzu zan tafi.
Ummi ta shige mota direba ya ja muna ɗaga mata hannu har suka fice daga gidan.
na juya jiki a sanyayi cike da kewar ta...
ina shiga parlour Ahmad dake biye da ni ya rungume ni ta baya,
baki na turu gaba ina yi masa hararar gefen ido.
murmushi mai sauti yayi kana, ya cusa fuskarsa a gefen wuyana na ya sumbaci fatar wuyana a hankali yaɗan ja numfashi yace
"Kyakkyawa ta yaufa a shirya shirin karɓar bakwanci na."
baki na kuma turo wa tare da fizge jikina nace
"Ni ka kyale ni."
dariya yayi cikin zolaya yace
"Zo muje oh na rarrashe ki Ummi ce ta hana ki tafiya ko?."
baki na murguɗa nace "Ina har murna kake." yace "Allah sarki Ummi Allah ya tsare miki hanyar ki, taji tausayin Ahmad da Ahmad shi yasa tace ki kula da su kafin, muje a fara bani nawa kulawar yanzu."
kafa na shiga bubbuga wa, ya janyo hannuna muka haura sama yana dariya..
Bayan sallar isha, tsaye nake gaban mirror ina feshe jikina da turare bayan fitowa ta daga wanka,
Ahmad ya shigo ya iso ya rungume ni ta baya, daga cikin mirror ya kura min ido yayin da ya sako kan sa kan kafaɗa ta yana yimin kallon cikin ido, sanin manufar sa sai na ɓata fuska na zame jiki na ina tura masa baki.
murmushi mai sauti yayi ya ruko ni yana faɗin
"Wai ba ɗazu nayi rarra shin nan ba to zo na kara yanzu kam na Musamman ne, shi yasa nasa su Naseem sukayi bacci da wuri."
cak ya ɗaga ni ya dire ni kan gado,
ganin ya shiga zare kayan jikina da sauri nace
"Ban fa warke ba ni dai ka bari."
sai da ya zare doguwar rigar baccin jikina kafin ya ɗago har jikin sa na rawa yace
"Please kyakkyawa ta, kwanaki arba'in da ƴan kai kiji tausayi na mana."
cike da shagwaɓa nace "Allah My zafi zai min kamar bai warke ba."
yace "To bari na gwada na gani idan bai warke ba sai na hakura, a hankali zanyi kinji ki daure."
kai na gyaɗa masa,
har jikin sa na ɓari yashiga shafari da sumbatar sassan jikina,
ya birkice ya birkita ni sai na shiga mai da masa martani.
sai da ya jagula ni na jiku sosai kafin ya ɗago ya zare pant ɗin jikina, nan ma sai da yayi ta wasa da HQ ɗina kafin ya haye kaina.
idanuna na rumtse san da ya shige ni da tunanin jin zafin gurin ɗin kin da a kamin, sai naji akasin hakan.
tamkar yau yafara sanina haka yayi ta sambatu yayin da yake ta sama da kasa a kaina.
ya sharin tsawon lokaci mai tsawo a kaina yana abu guda, nayi ta daure wa domin ganin ya sami nutsuwa dan nasan yayi missing ɗi na sosai.
sai da ya sami ingantacciyar gamsuwa kana yayi lamo a kaina, duk kanin mu numfashi muke sauke.
a hankali ya ɗago yayi kissing ɗin goshi na yace
"Nagode sosai kyakkyawa ta Allah yayi miki albarka."
idanuna na lumshe tare da kuma buɗe su kan fuskarsa tare da yi masa murmushi, shima murmushin ya maida min kana yace
"Ina son ki kyakkyawa ta."
a hankali ya zare jikin sa ya mike ya ɗago ni muka shige bayi.....
washegari da safe ina manne da waya a kunne na muna waya da Ummi,
Fauzan ya karɓi wayar muka gaisa da shi.
ina kashe kawar Ummi, kiran Mamie na ahigo wa waya itama sai da muka gaisa har da Nusaiba, dan tun da suka koma kusan kullum sai munyi waya da su har.....
Bauchi a ɓangaren Na'ima kuwa
tana zaune cikin bedroom ɗin ta waya ce kare a kunnen ta tana magana da aminiyar ta Raliya, tana faɗin
"Aminiya nikam anya bokan nan ai kin sa na ci kuwa, nifa banga yan da ake ta faɗa kamar yankan kuwan ba, gashi bini-bini sai yace abada dubu ɗari kaza miliyan kaza kin san har account ɗi na yafara yin kasa kuwa,
ba wannan ba ma ban damu da koda kuɗin zai kare idan har zan sami biyan bukata duk abin da na mallaka zan iya ɓatar da shi har idan za'a kashe wancan shigiya annobar yarin yar, dan wlh ta zame min annoba, jiya muna kwance da shi da daddare yana bacci yana kiran sunan