Showing 54001 words to 57000 words out of 125808 words
ma ajin su cikin bayin.
a haka na ɗaura bai karasa kai min guiwa ba rabin cinyata a buɗe yake,
nafito najima tsaye cikin ɗakin na rasa ta yanda zanyi na fita a haka, gashi ina jin alaman jini na kokarin sauko min,
da sauri na nufi kofa ina jan tsaki dan bani da yadda zanyi pat ɗina na bedroom ɗina.
a bakin kofa na tsaya ina, shiru banji alamun motsi ba, a hankali na tura kofar sai da na leka kaina ciki babu kowa cikin ɗakin,
a hankali nasa kai nashiga gaban wardrobe na isa na buɗe, pant da pat na fara cirowa ina kokarin kwance towel ɗin, naji karar buɗe kofar bayi da sauri na mai da toewl ɗin na ɗaura,
da ɗan sauri na shiga ciro kaya na na juya zan wuce sai ganin sa nayi daf da ni,
kaucewa nayi kokarin yi yataro ni da sauri ya janyo ni na fado jikin sa.
"Meye haka!?." nafaɗa da karfi ina ture sa.
a hankali yacusa fuskarsa a gefen wuya na tare da shinshinar fatar wuya na yaja
numfashi, da sauri na shiga ture kansa tare da faɗin "Wai meye haka ne kam dalla ka kyale ni."
yaciro fuskar sa sai ya sakalo hannayen sa a kuguna yace
"Tun ɗazu nake cikin bathroom nakasa yin wanka ban iya yi ni kaɗan ba sai an taya ni, muje ki tayani kinjin kyakkyawa ta.'
ɓata fuska nayi nace
"Nice zan taya ka wanka? capɗi lallai bazaka yi ba, zaifi maka kayi gaggawar zuwa in da aka saba taya kan, sake ni malam."
nakarasa Maganar da buge hannunsa na juya da sauri sai ji nayi ya.......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama😇: *HMDH*
*WASA FARIN GIRKI*
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR
19
Washegari da safe bayan sun karya tace masa ya tafi, yace ba yanzu ba duk yan da taso yatafi da safen yaki sai da dare yayi bayan sallar isha kafin ya tafi.
Ina zaune a parlour sai ganin sa nayi, fuska na haɗe dan sam banso ya kuma zuwa ba,da baya gidan naji sakat na kwana ɗayan nan yazo ya takura min ya hana ni sakat nida gida na.
fuskarsa ɗauke da murmushi kamar kullum ya karaso,
daf dani ya zauna har muna gogan juna, ɗan rankwafowa yayi jikina har ina iya jiyo sautin fitar numfashin sa, ya ruko hannaye na duka biyu a sannu yashiga murza su cikin tafin hannun sa, ido yalumshi tare da buɗe wa sannan yace
"Kyakkyawa ta babu ko ɗan barka da zuwa."
gajeren tsaki na ja ina yunkurin mike wa, sai yayi saurin sake hannuna yasaka hannayen sa duka ya zagaye ni ta baya, ya janyo ni ya daɗa mannani da jikin sa sosai, a sannu ya kawo fuskar sa daf da nawa ya haɗe goshina da nasa, yayin da numfashin mu ke garwaya dana juna, ɗina a hankali ya manna bakin sa kan lip ɗi na yayi kissing nashi,
kokarin tura harshen sa yake cikin bakina da sauri nakawar da kaina gefe.
numfashi mai karfi ya sauke tare da rumtse idanunsa da karfi yakuma buɗe wa, daɗa rungumoni sosai yayi a jikin sa kana cikin kasa da murya da tausasa shi yace
"Please HAMDAH ko sau ɗaya kibani dama kin san yan da nake ji a kan ki kuwa?, ki taimake ni son ki na shirin illatar da ni."
"Ka sake ni ni ka sake ni nace."
nafaɗa cikin ɗan gaɗa murya ina kokarin kwatar kaina.
bai sake ni ba sai idon daya kafe ni da shi kamar zai cinye ni, niko narika mutsu-mutsu da tutture shi ina cigaba da faɗin
"Ka rabu da ni dalla Malam ka sake ni bana so."
bai ce kamai ba sai idon daya cigaba da bina da shi zuwa can a hankali yasoma magana
"HAMDAH me yasa bazaki saurareni ba, baki yarda da gaske ina son ki bane ban shigo rayuwar ki dan na cutar da ke ba, son da nake miki shi yakawo ni cikin rayuwar ki,
meyasa bakya sona mene ne aibu na?."
Da karfi na daddage narika ture shi ina faɗin
"Ka rabu da ni ka kyale ni bana son ka kaima zai fi maka ka daina so na."
daga saman step muryar su Naseem ke tashi yayin da suke saukowa da gudu suna faɗin
"Mommy kijo ki canja mana kallon ansa me dodo ne."
da sauri ya sake ni ganin yaran suna daf da sauko wa, suka karaso da gudu suka zube a jikinsa, da sauri na mike ina wasa masa harara haɗe da murguɗa masa baki,
murmushin nan nasa ya bini da shi sannan cikin ɗan ɗaga sauti kaɗan yace
"Kyakkyawa ta ina son ki son ki a nan ɗina yake yakuma haifu a sassan jikina, in da duk gilmawar da jinan jikina zai yi dake yake numfasawa."
ya nuna dai-dai sai saitin zuciyarsa sannan ya cigaba da faɗin
"Bazai fita ba baku ma zan taɓa dai na sonki ba, kema kuma zaki soni."
muryar Naseem na sinkayo yana faɗin
"Daddy muma kana son mu?."
dariya yayi yana rungume su a jikin sa yace
"Kwarai ma kuwa ina son ku, kuma son ku anan ɗina yake da ilahirin jikina gaba ɗaya."
yanuna ka san zuciyarsa kasa da inda yace anan nake.
murna suka shiga yi suna faɗin
"Yee muma Daddy yana son mu."
tsaki naja najuya na nufi sama,na barsu nan zaune suna ta tikar dariya har da shi.
dogon tsaki naja ina haurawa step's
"Mutum kamar mara zuciya duk abin da zaka masa bazai taɓa jin haushi ba, kullum fuska ɗauke da murmushi kamar gonar auduga."
nakuma jan gajeren tsaki ina shigewa parlour'n sama...
Da daddare bayan sallar isha nafito daga bedroom ɗina bayan na sarkake jikina nayi wanka tare da ɗauro al'wala dan yau nagama
period, sallaya na shinfiɗa na gabatar da sallar isha ina idanrwa na mike naje na saka kaya,
ina kokarin fita a ɗakin ya shigo ganin yana kokarin matsoni,na ɓata fuska tare da kaucewa nayi waje abina.
ɗakin da tun ranar da yazo na dawo kwana ciki, nashige nayi kwanciya ta ci ki.
sai da nagama danne-dannen wayata nakai wajen karfe 11 kafin bacci ya ɗauke ni...
can cikin bacci narikajin ana tattaɓa ni firget na mike zaune, ina ware idanuna, ni dana kwanta da haske sai na tsince ni cikin duhu yanzu,
hannun mutum naji yakuma mai dawa jikina yana daɗa laluma ni ai da sauri nashiga lalumo wayata, ina ɗauka nayi saurin danna shi ya bada haske, ai da sauri na duro a gadon nayi saurin kunna wutan cikin ɗakin.
yana zaune a sakiyar gadon yayin da yake ta jan numfashi da kyar cike da alamun zurfafa cikin matukar bukatuwa, zamowa yayi bakin gadon ya mike yana yunkurin maso ni da sauri na ɗaga masa hannu nashiga ja da baya ina faɗin "Me ya kuma kawo ka nan? kafita nace ka fita!."
Na karasa maganar cikin ɗan ɗaga sauti ina kuma yi masa nuni da kofa kan ya fita.
numfashi ya ja a wahalalce yace
"Kar kiyi min haka HAMDAH kar ki mance nifa mijinki ne ina da hakki a kanki, HAMDAH son ki da bukatar ki zasu iya yi min illa ki taimaka ko sau ɗaya ne ki bani dama."
da sauri na katse shi da faɗin
"Ban san wannan ba kafita kawai kar kasake ka matso ni."
"HAMDAH ki saurare ni."
"Babu abin da zanji daga gare ka fita kawai."
Kan sa ya dafe da hannaye sa duka biyu yana mai rumtse idanunsa da karfi, a hankali ya juya cikin jan kafa yafita a ɗakin.
numfashi na sauke da sauri na isa jikin kofa narufe kofar tare da murza key,
na dawo na kwanta, nakai tsawon lokaci kafin bacci yakuma ɗauka ta.
washegari bayan tafiyarsu Nasmah School ina yin breakfast na tafi sashin su Inna Wuro dan sam bana so na kasance inuwa ɗaya da shi.
a parlour na tadda su Inna Wuro da Bappa na zauna muka ta hira, daga baya Bappa ya juya hirar izuwa
nasiha, ya mai da hankalin sa sosai a kaina tare da kiran sunana ya cigaba da faɗin
"HAMDAH cikin gidan naku lafiya dai ko?."
kai na gyaɗa da faɗin
"Lafiya lau Bappa." yace "Masha Allah Allah ya daɗa dauwamar mana lafiya da kwanciyar hankali, to HAMDAH yanzu Allah ya kawo ki wani lokaci na musamman sai kin jajirce wajen gudanar da lamarin ki, Allah ya ɗaura miki wani nauyin da dole sai kin bada kulawa sosai wajen isarwa da kuma sauke wa,
kiyi kokarin sauke duk wani nauyi da hakkin daya rataya a wuyan ki,
ta nan ne kaɗai zaki da ɗa ganin falala da ci gaban rayuwa,
HAMDAH mijin ki yana da hakki mai girma a kan ki, kiyi kokari ki jajirce wajen sauke duk wani nauyin daya rataya a kanki,
ki guji duk abin da zai kaiki da halaka,
miji yana da hakki mai girma a kan matar sa kamar yadda itama take da hakki a kansa,
amma ki sani aljannar mace yana karkashin kafar mijin ta ne,
idan tayi masa biyayya ta sauke dukkan hakkokin sa, to babu makawa da yardar Allah zata shiga aljanna cikin sauki.
idan kuma ta bijire masa to tana cikin asara,
kiji tsoron Allah aduk inda kike kizamo mace ta gari in da zakiji daɗi ranar gobe kiyama,
aure ba abin wasa bane darajar sa yawuci duk in da ake tunani, idan kayi wasa da shi ko ka nimi ka wulakanta shi ko ka ɗauke shi abin banza, hakika zaka ga rashin daidai a rayuwar ka tun anan duniya,
yan da idan kayi biyayya ka tsare dokokin sa zai kaika ga aljanna, haka zalika idan ka hofantar da shi zai jaka izuwa wuta, Allah ya tsare mu da yin abin da zai kaimu ga shiga wuta."
Inna Wuro ta amsa da
"Amen ameen ameeeeeen ya rabbil izzati."
Bappa yaci gaba da yi min nasiha mai matukar shiga jiki da tsoratar wa, ba shakka jikina yayi sanyi zuciya ta ta kariya,
lallai duk kan musulmi mai imani babu wanda zai so ganin sa cikin azabar Ubangiji.
muna nan zaune Bappa bai gushe wajen cigaba da yimin nasiha ba.
har Ahmad ya shigo shima ya zauna Bappa yaci gaba da yi mana nasihar tare, babu wariya ko nuna banbanci...
Bappa ya ɗau tsawon lokaci yana yi mana nasiha daga bisani ya rufe taron da addu'a.
Ahmad yayi ta masa godiya kana ya tashi ya fita.
fitar sa bada jimawa ba,
Inna Wuro ta dube ni tace natashi naje ko zai bukaci wani abu ni ina nan,
na mike jiki asanyaye tare da yiwa Bappa godiya natafi..
A parlour'n sama na tadda shi yana zaune yana waya, na wuce shi na shiga bedroom ɗin dana koma kwana ciki, na kwanta bakin dago jiki ba kwari dan gaba ɗaya jikina yagama mutuwa da wa'azin Bappa,
shiga ta bada jimawa ba ya shigo, har ya karso in da nake ban ɗago ba,
ya tsaya ta gurin kafafu na
"Bacci zakiyi ne?." yayi maganar idanunsa a kaina,
tsintar kaina nayi da gyaɗa masa kai.
kai ya jinjina yace "Kiyi bacci mai daɗi ni zan fita akwai waɗan da suke jira na zamu yi zama, sai na dawo."
nan ma kai na gyaɗa ma sa, ya juya yafita da murmushi.
ina dai kwance badan bacci ya ɗauke ni ba har su Nasmah suka dawo daga school..
shiko tun da yafita bai dawo ba sai daf magriba, yana shiga kuma ya ja Naseem sukayi masallaci.
sai bayan sallar isha suka dawo..
Tun daga rana mai kamar ta jiya Ahmad bai sake tinkara ta da bukatar sa ba, yakuma dai na yunkurin taɓa jiki na, zai dai zauna a inda nake yayi ta jana da hira haɗe da wasa, tun ina yin banza da shi har yakai ga nakanyi murmushi da jin wani zancen nasa.
Yau kimananin satinsa biyu kenan a gidan,duk bayan kwana biyu yakan cemin zaije ya duba Kawa, idan kuma ya dawo zai zo min da sakon cewa tana gaishe ni.
Zaune na ke a ɗaki ina jiyo muryar su a parlour shi da su Naseem kasan cewar yau weekend ne, shima babu in da ya je har yanzu wajen karfe 12 da rabi, a hankali na mike jin an fara kiraye-kirayen sallar azahar,
nashiga bayi nayi al'wala na fito,
Nasmah ce ta shigo tace
"Mommy Daddy sun tafi masallaci yace nayi salla na a gida zan sami lada da yawa da yawa kamar haka."
ta kwatanta da faɗin hannayen ta biyu,
murmushi nayi nace "To je kiyi al'walar kizo muyi sallah."
tawuce da sauri tayo al'walar tafito mukayi sallar tare.
muna idar wa tayi waje dagudu wai zataje ta duba ko su Daddy sun dawo..
na mike na ninke sallayar na kaisa ma'ajin sa, kana na koma na kwanta...
turo kofa yayi da salla na amsa batare da na ɗago ba, ya karso cikin ɗakin abakin gadon kusa da kafafu na ya zauna, a sannu ya ɗago kafafuna duka biyu ya ɗaura kan cinyar sa, a hankali yashiga matse su yana ɗan jajjan yatsun tare da ɗan tankwashe su yana cigaba da matse su a hankali.
Idanuna na lumshe tare da buɗe su batare da na yi yunkurin hanasa abin da yake yin ba.
ɗan tsuramin ido yayi a hankali yace
"Tun jiya Hajiyar mu take ta tambaya ta ke wai bazan kawo ki ki gaishe ta bane, ko yanzu tafiya ta masallaci ma sai da ta kuma kira na, ya kama muje ki gaishe ta, ko bacci kike ji abari sai kin tashi?."
kamar nace Eh amma jin ya ambaci Hajiyar mu nasan cewa mamansa ke nan yake nufi, uwa kuwa ta wuci wasa dan kullum da nawa uwar nake kwana nake tashi, kai na girgiza masa alamun ba baccin nakeji ko zanyi ba.
yace "Okay to ki shirya muje a gaishe ta."
nan ne dai ban amsa sa ba ya ɗaga kafafu na a hankali ya aje su kan katifa kana ya mike yafita.
a sannu na mike na sauko a gadon bayi na shiga nayi wanka batare da ɓata lokaci ba na fito,
na zauna gaban mirror mai da pauda da man lip kaɗai na goga, na mike na isa gaban wardrobe ɗin ɗakin naciro doguwar riga daga cikin kayana dana kawo su ɗakin,
haɗe da bra da pant da sket ƴar ciki.
ina gama sa kayan nazo gaban mirror nayi rolling ɗin gyalen doguwar rigan a kaina, na fesa turare mara karfin kamshi sosai na ɗau wayata haɗe da hand bag, nasa takalmi mai ɗan tsini ba can sosai ba nafito, jin babu motsin kowa a parlour sai na nufi kasa,
tun daga saman step's ya kafe ni da ido, a hankali nake ɗaga kafata sabo da takalmin dake kafata gudun tsamtsin step ɗin.
a hankali na sauko, nan na tadda su Nasmah cikin sabuwar shiga da alama wanka a ka sake musu.
kai na na kawar gefe ganin yan da yake bina da kallo babu ko kifta ido, lallausar murmushi ya sake yace
"Kyakkyawa ta kinyi kyau sosai."
baki na taɓe ina mai cigaba da kawar da fuskata.
yamike ya ruko hannun su Naseem yana faɗin
"Ku taso muje ko, kada Madam ta gaji da tsayuwa."
suka nufi kofa nabiyo bayan su,
muna isa gurin motar da ɗan sauri yadawo gefen mai zaman banza ya buɗe ya dube ni sannan yace
"Madam bismilla." ba tare dana kalle sa ba na shige cikin motar, yana kokarin rufe kofar nayi hanzarin kai hannuna naja kofar da kaina na rufe.
murmushi yayi kana ya zaga ya buɗe wa su Nasmah suka shiga, sannan ya dawo gefen direba ya shiga yaja motar a hankali, mai gadi ya buɗe get yasa kai yafita a hankali...
A hankali muka haura titi in da yake tukin kamar bazai yi ba,
a bakin wani katafaren ShopRite muka tsaya, ya dube ni sannan yace
"Ko zakiyi wa Hajiya tsaraba?."
shiru nayi ban amsa shi ba sai kuma na buɗe marfin motar na fita,
shima ya fito kana ya fito da yaran ya ruko hannun su muka shiga ciki,
tarba na musamman aka yi mana cike da girmamawa a cikin gurin,
turaruka da sabulai masu kamshi da tsada na ɗiba cikin basket ɗin da na ɗauka, su Naseem kuwa suka rika jidar kayan zaki, shima yana taya su.
nazo gurin biyan kuɗi sai suka karɓi basket ɗin da sauri suka zuba kayan cikin laida, ATM nayi kokarin cirowa acikin jakata, ɗaya daga cikin masu amsar kuɗi yace
"Hajiya kibar shi." naɗago jin abin da ya faɗa lokacin su Ahmad duka karaso gurin da sauri suka karɓi basket ɗin hannun yaran suka juye kayan cikin laida, ɗaya daga cikin ma'aikatan gurin ya karɓi laidodin da sauri yayi waje nan muka bi bayan sa,ban kuma ga lokacin da ya biyasu kuɗin su ba.
acikin mota mutumin ya aje laidodin kana ya gaɗa hannu yana yi mana sallama,
ina dai-dai ta zamata cikin motar kamar ance na ɗago idanuna ya sauka can saman katafaren ShopRite ɗin,
sunan sa ne manne da manyan harufa.
baki na taɓe a raina nace
"A she dai nasa ne shiya basu amshi kuɗin ba."
a bakin get ɗin wani katafaren gida yayi hon, batare da ɓata lokaci ba a ka wangale get ɗin
muka kusa cikin gidan, gida ne katon gaske wan da girman sa yakai ya kawo.
a tsakiyar gidan ya paka motar in da mutane sukayi ta zuwa suna mika masa gaisuwa ba shi kaɗai ba har da ni.
har muka fita a cikin motar muka nufi ciki mutane nata tururruwan zuwa suna kwasar gaisuwa.
wani katafaren parlour muka bayyana cikin sa, da salla na saka kafata ciki.
wasu mata ne da ƴammata ke zaune cikin parlour'n, kamar bazasu amsa sallamar ba yayin da dukkan su hankalin su ke kan abin da suke, sai da ɗaya daga cikin su ne ta ɗago sai kuma tace
"La Ya Ahmad." sai dukan su suka ɗago suna mai amsa sallamar da faɗin
"Sannu da zuwa." wata daga cikin su ta dubi Ahmad tana wani karairaya tace
"Sannu sa zuwa Ya Ahmad."
bai amsa ta ba sai sauran da suke ta faman mika masa gaisuwa ya amsa kana yace
"Hajiya fa." da sauri wacce yaki amsa gaisuwar nata tace
"Tana ciki bari nayi mata magana."
da sauri ta wuce jim kaɗan ta fito tana girgiza kugu tace "Wai ka shigo."
hannunsa naji cikin nawa da sauri na wai ga in da yake murmushi ya sakar min yace
"Muje."
a hankali muka nufi cikin wani dogon corridor kana muka isa baki wani kofa, yayi sallama bakin kofar daga cikin ɗakin aka amsa yayi min alama da mushiga, na zame hannuna cikin nasa yafara shiga mukabi bayan sa.......!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: *HMDH*
*WASA FARIN GIRKI*
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
21
Kallon sa nake cikin matukar tausaya wa, tabbas rayuwar sa abin a tauya ne, yana ji yana gani ake niman hallaka rayuwar sa, kuma a haka yake rayuwar sa tamkar bayi da wasa matsala, kullum