Showing 102001 words to 105000 words out of 125808 words

Chapter 35 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

474

zan je na gani."
Nan da nan nasa su Zulai suka cike ta da kayan ci da sha..

Su Bappa da Ahmad suka shigo su ka zauna bayan sun gaisa da Ummi akayi ta hira.
gaba ɗaya nakasa zaune na kasa tsaye farin cikin ganin Ummi na yasa bakina ya kasa rufuwa farin ciki na yagaza ɓuya, ina jikin Ummi na naki matsawa ko nan da can,
a ɓangaren Ummi ma haka abun yake farin cikin da take jin kanta ciki yau bazai misaltuba, sai kallon ɗiyar tata take, yan da ta kara girma ta zamo cikakkiyar mace, ga ƴaƴan da take ganin su a gaban ta wai duka ƴaƴan HAMDAH ce, Allah mai iko buwayi gagara misali.
Bappa ya mike yace a barta ta huta ya fita, Inna Wuro Faty Talatu Zulai duk suka yi mana sai da safe suka tafi.
cike da girmamawa Ahmad ya mike ya lura Ummi nauyi take ji yasa ta kasa cin komai a gaban su, ya dubi su Nasmah yana faɗin
"Naseem Nasmah kuzo muje mu bar Ummi ta huta."
ya ja su suka haura sama.
nace "Ummi muje sama kiyi wanka kici abinci ki huta."
tace "A'a nan ma ya ishe ni ba sai na haura ba."
murmushi nayi dan nasan ganin Ahmad ya haura ne, na mike na ɗau jakarta nace
"To ki shigo nan Ummi." nayi maganar ina nufar ɗaya daga cikin bedroom ɗin cikin parlour'n.
ta biyo bayana rike da Ahmad karami da yayi bacci,
ɗakin a gyare yake tsaf dan kullum sai su Talatu sun gyara ɗakunan duka.
Ummi ta rika bin cinin ɗakin da kallo kana ta shinfiɗa Ahmad kan gado ta shige bathroom ni kuma na fito parlour,
abincin da aka kawo mata bata ci ba na kwashe na kai mata ɗakin,
ina zaune ta fito tayi wanka haɗe da al'wala, na shinfiɗa mata sallaya, ta gabatar da salla.
tana idarwa na zuba mata abinci tana ci muna hira sai da naga taci abincin sosai kafin na mike nafita.
na haura sama na tadda tuni su Naseem sunyi bacci Ahmad yana kwance a gefen su.
yana gani na ya mike ya janyo ni jikin sa, goshi na ya sumbata kana ya ɗago da murmushi yace
"An ga Ummi shine za'a mai da ni marayan gasken-gaske ko?."
dariya nayi tare da jan ɗan karamin gyamun sa nace
"Maraya kuma kana da ni da Aunty Rasheedat kake kiran kanka maraya."
hannunsa ya sakalo ta kugu na ya daɗa haɗe jikin sa da nawa kana yace
"To a sallame ni dan yau nasan ba lallai naji ɗumin jikin kiba."
murmushi nayi nace "Ai kuwa kamar ka sani gurin Ummi zan kwana."
yace "Na sani ai kuma na yafe dan nasan a yanzu Ummi ta fini bukatar ganin ki kusa da ita,amma fa zan yi fama sosai na rashin ki kusa da ni."
nace "Kaje guje gurin Aunty Rasheedat mana nima bana so na barka kai kaɗai."
yace "A'a ai da ni za'ayi murnar ganin Ummi'n nan." yayi maganar yana jan kumatu na.
dariya nayi kana a sannu na kai lip's ɗi na ka nashi, sai da na ai ka masa da kwararan sakwanni na wan da nasan zai sami bacci cikin nutsuwa kafin na zame jikina na koma gun Ummi...

Ina shiga na tadda tana waya tana faɗin
"Yanzu haka ma ina cikin gidan a ɗaki ina shirin kwanciya Yaya."
na karaso ciki da sauri tun da naji tace Yaya yasan Abbu ne take wayan da shi.
daga cikin wayar cikin matukar farin ciki Abbu yace
"Ina HAMDAH ina HAMDAH take?." Ummi da bakin ta ya kasa rufuwa tace "Ga ta nan bari na bata."
ta mika min wayar tana faɗin "Abbu'n ku ne." a gefen ta na zauna tare da kara wayar a kunne nayi sallama,
Abbu ya amsa yana faɗin "HAMDAH HAMDAH kece?." wasu zafafan hawaye ne naji sun zubo min a hankali naji saukar hannun Ummi kan fuska ta tana share min, sai na saki murmushi mai sauti nace
"Ni ce Abbu ina yini."
Abbu yace "Alhmdllh ita ce." hele najiyo daga cikin wayar da hayaniya idanuna na lumshe nakuma buɗe wa jin muryoyon ƴan uwa na, Abbu yace
"Masha Allah alhmdllh sannu sannu HAMDAH sai mun zo maganar waya bazata wadatar da mu ba."
muryar Aunty Rafee'at najiyo tana faɗin
"Abbu bani inji muryar ta." tace "HAMDAH." nace "Na'am Aunty Rafee'at." sai kawai ta fashe da kuka, nima kukan na fashe da shi.
Abbu ya karɓi wayar yana faɗin
"To yanzu kam hankali na daf da kwanciya Rafee'at Jaleela kowa ya tafi gida sai kuma ranar tafi."
cikin shessheka Aunty Rafee'at tace
"Abbu Ina gobe ne zamu tafi."
yace "A'a sai jibi kuje gobe a shirya jibi a tafi."
farin cikin da na tsinci kai na ciki bazai misaltuba jin muryoyin ƴan uwa na.
Abbu ya kashe wayar, Ummi ta rika rarrashi na ganin naci gaba da kukan har sai da taga na daina kukan.
ranar kusan kwana mukayi muna hira da Ummi...
washegari da kaina na shiga kitchen muka shirya abun breakfast iri-iri, na kwashi na Ummi na kai mata cikin bedroom ɗin da take, na ɗau na Ahmad na kai masa sama, sai da na tayasa wanka kafin ya barni na sauko.
ni dai a ɗakin Ummi nayi wanka dan na sauko da kayan da zan sa da na Ahmad karami, Ummi da kanta tayi masa wanka ta shirya shi.
su Naseem ne suka shigo da shirin tafiya school Ahmad na biye da su,
cike da girmamawa ya tsunkuya ya gaida Ummi da tambayar ta gajiyar hanya, ta amsa fuska a sake. nan ma Ummi tayi ta kallon yaran har suka fita, tabbas yaran suna mata mugun kama da SALEEM musamman Naseem yafi kama da shi sosai,
a ranta take faɗin ko dai sune cikin da ta tafi da shi, sai kuma ta kakkaɓe zuciyar ta da wannan tunanin, bayan ga ubansu nan tana gani,
ai dama HAMDAH kama suke da SALEEM dan ƴaƴan ta sun yi kama da shi ba abun mamaki bane.
na lura da kallon da Unmi take ta yiwa su Nasmah, nasan tarin bambayoyi ne tare da ita musamman kan yaran, sai dai har yanzu bamuyi wannan hirar da ita ba.
bayan munyi breakfast tare da Ummi, muka fito parlour.
Inna Wuro ta shigo, dan yanzu bata kwana cikin side ɗin nan tun da mukayi bakwai sai dai da safe ta shigo tayiwa Ahmad karami wanka,da yamma ma haka. bayan sun gaisa da Ummi nima na gaishe ta, nace
"Inna Wuro shine yau baki zo kinyiwa Ahmad wanka ba."
dariya tayi tace "Ai ni yanzu na sake wa matar sa tayi masa wankan arba'in ɗin."
hire sasoi muka yi ta yi, ina like kusa da Ummi na, a ranar da yamma Aunty Rasheedat ta zo yiwa Ummi barka da zuwa, bata bar gidan ba sai dare suka koma da Ahmad.
Ummi ta yaba da halinta kwarai da gaske tayi ta mamaki da na ce mata matar Ahmad ce....

Kamar yadda Abbu yace bayan kwana biyu da zuwan Ummi suma suka ɗau hanyar zuwa Abuja,
koda suka iso Ummi ta haɗa mu da su a waya nayi ta musu kwance har suka iso.
koda suka iso suka ce gasu a bakin get nan da nan nasa security suka buɗe musu get,
ina jin shigowar su da sauri na fito,
motoci biyu suka taho da shi na Abba da Abbu.
Aunty Rafee'at ne ta fara fitowa daga cikin mota, wani irin kallo muke bin junan mu da shi, Aunty Rafee'at kuwa kallon yan da na kara girma da cika take, da gudu ta taho nima nasa gudu muka rungume juna.
Aunty Jaleela Ya Masa'ud Nusaiba Fauzan Mamie Abbu Abba duk suka fito, sai na saki Aunty Rafee'at nayi gurun su, yan da na shiga rungume su sai ya tuna min da lokacin da suke zuwa Dass gurin Inna haka zanyi ta rungume su ina yi musu oyoyo, sai kawai na fashe da kukan farin ciki, duk kanin su sai da suka yi kwalla.
jiki a sanyaye na matso in da Abba yake tsaye, yana duba na cike da nadama a gaban sa na tsaya ban iya rungume shi.
sai ya miko min hannu alamar na zo, jiki a sanyaye na maso in da yake,
kai na yashafa tare da bubbuga kafaɗa ta.
kai na sunkuyar jin hawaye ya ciko min ido sai ga hawaye sharr.
Mamie ta matso in da nake ta janyo hannu na tare da girgiza min kai,
Ya Masa'ud ya leko fuska ta yace
"Kai ƴar gidan Inna har kin fi Jaleela girma yanzu."
dariya nayi hawayen na zuba.
Aunty Jaleela kuwa harararsa tayi tana murmushi, ciki duka mukayi har da su Bappa da suka fito,
muna shigs na kira Ahmad na sanar masa isowar su batare da ɓata lokaci ba suka iso shi da Aunty Rasheedat...
cike da sha'awa su Aunty Rafee'at suka yi ta ɗaukar su Naseem da suke ta zuba musu surutu.
Mamie ko ido ta rika binsu da shi lokacin da ta janyo su jikin ta, Naseem ta yi ta kallo ganin suffofin SALEEM lokacin yana karami tare da shi...
Su Abbu sun sha mamakin ganin Ahmad Sabil sun jinjina lamarin da ganin tabbas da gaske shi miji na ne....

Bayan gaishe-gashe daya gaba ta, cin abinci ya biyo baya,
daga nan kuma sallar la'asar aka tashi yi, in da su Abbu suka tafi masallaci, su Mamie kuma suka shiga ɗakunan da suke cikin parlour'n kasa sukayi salla.
bayan anyi sallar aka kuma dawowa parlour.
bayan an zazzauna Bappa yayi gyaran murya ya soma magana...........!





Kuyi mane ji ina da ba'ki yau idan Allah ya kaimu gobe na sami lokaci zan kara muku👌 wlh yanzu ma da kyar na samu nayi wannan ɗin
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 35





Bayan wani lokaci..
ranar wata laraba zaune nake a parlour'n kasa, najiyo sallamar hajiya Karima.
na amsa tare dayi mata barka da zuwa, ta amsa tana zama kan kujera,
wasa ta shiga yiwa Ahmad karami da ke zaune a kasa kan carpet rike da pida a hannunsa yana shan madara.
na gaishe ta ta amsa fuska sake tana tabbaya ta ya kwanan gidan da yaran.
nace kowa lafaya.
ta dube ni da kyau tare da gyara zaman ta tace
"HAMDAH nazo ne dama na nimi gafarar ki da kuma sulhu,
hakika nasan abin da na ai kata a baya ban kyauta ba, na gane kuskure na Ahmad ɗana ne, kullum cikin ladabi da biyayya yake agare ni,
me zai sa naso ganin bayan sa, i naso ki rufa min asiri kada ki faɗa masa komai, duk da nasan ko da kin faɗa masan ma bayar da zaiyi ba, sabo da irin ki sun sha faɗa masa baya yarda,
ina so na gyara kuskure na shi yasa nazo na sanar miki yanzu duk na zubda makamai na, me zai sa na so kashe Ahmad wanda yaɗau keni matsayin uwa, sharrin shaiɗan ne, yanzu zuciya ta ɗaya yake,
kuma zan same sa cikin dabara na nimi gafarar sa."
ɗan shiru nayi ina duban ta
yan da take maganar gaba ɗaya yanuna zallar gaskiyar ta take faɗa,
kai na jinjina kana nace
"Babu komai hajiya Allah ya tsare mu da sharrin shaiɗan."
na mike ina mai jin daɗin maganar ta ina ayyanawa a raina yanzu zan zo na kira Ahmad na sanar masa, Hajiya ta yada makaman ta, nasan shima yanzu zuciyar sa zata sami salama. na tufi kitchen domin na samo mata ɗan abin taɓawa, matar nan tana bani mamaki idan ka ganta tamkar mutumiyar kwarai amma zuciyar ta baki, gara da yanzu Allah ya ganar da ita tana da rabo...
kayan ci da sha na shirya su a kan tray kana na ɗauka na nufi kofa.
da sauri nakarasa fita daga cikin kitchen ɗin jin ana tafa hannu,
turus na naja na tsaya nan bakin kofar kitchen ganin Ahmad tsaye cikin parlour'n yana tafa hannu tare da dumfaro Hajiya Karima dake rike da Ahmad karami ta kawo fida daf bakin sa tana kokarin saka masa shi cikin baki, cak ta saida hannunta bata sauke hannun ba bata kuma kara sa dashi cikin bakin nasa ba, yayin da hannu yake rawa.
ya karaso gaban ta yana mai cigaba da tafa hannu ya dube da kyau tare da faɗin
"Da kyau Hajiya ya kika da kata kuma bashi ya sha mana."
da sauri na karaso in da suke na dire tray ɗin saman table nace
"My Hajiya ta gane gaskiya tace yanzu babu komai cikin ranta."
"Shiru HAMDAH." yayi maganar tare da ɗaura yatsar sa kan lips ɗin sa, kana ya dubi Hajiya Karima da gaba ɗaya ilahirin jikin ta ke ɓari sai ta shiga kame-kame tana faɗin
"Ah..la... Ahmad..kuka yake shine na ɗauke sa na bashi madarar sa, da na gani a nan."
hannayen sa ya naɗe a kirki yayin da idanunsa ke kan ta yace
"To sha fara sha kafin kiba shi ya sha, sha yanzu!!!."
yayi maganar cikin tsawa sosai,
daga ni har ita sai da mukayi wani irin zabura.
yadube ni kana ya soma magana cikin fusatacciyar murya sosai.
"Duk abun da ta faɗa miki yauda ra ce bazata taɓa sauyawa ba."
kana ya mai da duban sa kan ta yace
"Kin jima kina cutar dani, kin yi sanadiyar rasa mahaifa na,ni kaina kina bibiyar rayuwa ta, hakan baiyi miki ba har da ɗana cikin jadawalin ki!
to ki sani rayuwa ta dana ɗana ba a hannunki yake ba ke baki isa kiyi mana abinda Allah bai hukunta ba, mutuwar mu ba a hannunki yake ba,
basai kin kashe mu ba ki jira idan lokacin mu yayi zamu tafi dole ba makawa,
me wannan jaririn ya tsare miki da zaki zuba masa guba cikin abin shan sa, muddin ina numfashi bazaki taɓa kuma cin galaba kan ahalina ba!!,
duk wani motsin ki a tafin hannuna kike yin sa, lokaci na ɗebar miki,
domin hukun taki kan abun da kika jima kina ai kata shi, kuma lokacin yayi dan haka."
wani irin razana nayi da sauri na sunkuci Ahmad karami dake ta raba ido kan kafarta, na rungume shi ina duban bakin sa ko har ta bashi madarar.
kofa ya kalla tare da faɗin
"Kushigo."
da mamaki na maida duba na kan kafor, wasu mutane ne guda huɗu suka shigo, yace "Kutafi da ita."
suka dube ta suna faɗin
"Oya mike."
duk wani roko da magiyar da take wa Ahmad bai saurare ta ba yace a tafi da ita, suka saka mata ankwa sukayi gaba da ita...
Numfashi na sauke tare da duban Ahmad da ya zube kan kujera tare da shafa kansa.
jiki a sanyaye na zauna kusa da shi, na dube shi jiki a sanyaye nace
"My na ɗauka da gaske Hajiya ta tuba da bakin ta take faɗa min ɗazu har tace zata nimi gafarar ka." shafo gefen fuska ta yayi, yace
"Kyakkyawa ta ai tayi hakan ne dan ki yarda da ita har ta cimma burin ta, Hajiya bazata taɓa sauyawa ba sabo da son duniya ya rigada ya gama rufe mata ido,
kuma abun da bata sani ba sam bazata taɓa zamo silar rasa rayuwa ta dana ɗana ba, idan tayi hakuri ma zan tafi na bar mata duniyar dan ba mai tabbata a duniyar nan."
ya mika hannu ya karɓi Ahmad karami dake ta zame wa yana son zuwa gurin sa,
ɗan kwanciya nayi a gefen jikin sa ina mai jin son sa da tausayin sa yana shiga na, ɗan ɗago kaina nayi ina duban fuskar sa kana nace,
"My wai ya akayi ne kake san duk shirin ta, ya akayi ne ma kasan ta zuba guba cikin abun shan Ahmad?."
murmushi yayi tare da sumbatar goshin Ahmad karami, kana ya ɗan karkato ya ja kumatu na sannan yace
"Ai ki na ne fa a kan wasu bare kuma ni kai na, jami'in sirri."
da mamaki na ke duban sa cikin kuma rashin fahimta nace "Jami'in sirri?."
kai ya gyaɗa yana murmushi tare da ruko hannuna yace
"Eh ni SS ne kece mutum na huɗu da kukan koni waye Daddy na da Mommy na da kuma Kawa."
cikin matukar mamaki nake duban sa, ban taɓa zato ko sammani ba, ban taɓa ganin wata alama a tare da shi ba, lallai kuwa waɗan nan jami'an sun san ai kin su, in ba wai sun so ka san ko su waye bane ko shekara dubu zakayi da su baza ka taɓa sani ba,
tunanin hirar da Bappa ya taɓa min akan sa na lokacin da yaje rugar su ya kama ɗaya da gacikin makiyayin su, wan da basu san cewa shi ɗan fashi bane, ashe dai dama aikin sa ce ya kai shi can.
maganar sa ce ta katse min tunanin da nake
"Kiyi min alkawarin ko bayan raina Ahmad zai gaje ni."
da sauri na dube shi jin abin da ya faɗa mai haɗe da kalmar ko bayan ransa.
murmushi ya yi tare da kawar da maganar da wata zancen da ban.....





*Bayan wata biyar*

Zaune muke a parlour dukan mu cike da walwala da jin daɗi,
sai dai tun waye war garin yau na sinci kaina cikin matsanan ciyar faɗuwar gaba da son yin kuka.
haka nayi ta daure wa ina ta son gusar da fargabar da bansan dalilin yin sa ba. Ahmad karami da yanzu yafara tafiya sai gujegujen su suke a sakiyar parlour shi da su Naseem,
ina kwance jikin Ahmad sai binsu da dariya muke cike da shauki.
ɗan muskutawa nayi na ɗago kaina ina duban fuskar sa nace
"My last month ɗin nan zan yaye yaron nan."
yace
"A'a kam gaskiya ba yanzu ba ki bari ya kara wata biyar nan gaba sai a yaye shi."
ido na waro nace "Cap wata biyar wannan katon yaron da kowa yagan sa yake cewa har yanzu ban yaye shi ba, wani irin girma kake so yayi kafin a yaye shi, ni dai Allah ya ishe ni da tsotso."
"To masu faɗan ai basu san watannin sa bane dun sun gansa da girman jiki wannan ɗan jaririn suke cewa a yaye shi,
wani shan nono ma yake yaron da zai wuni yana wasan sa bai zo in da kike ba."
baki na turo tare da bubbuga kafafuna kan kujera nace "Ni dai kam watan nan na kare wa zan kai wa Aunty Rasheedat shi ta yaye shi."
yace "To ya isa ba sai anyi min rigima ba zan yi tunani amma dai kafin nan taso muje kiji wani magana."
kafaɗa na make ina dariya nace
"A'a faɗa a nan basai mun shiga ciki ba naki wayon, ina dai yanzu muka fito."
a hankali ya raɗa min "Kari zanyi."
dariya nayi ina make kafaɗa..
wayar sa ce tayi kara ya ɗaga.
bayan yagama magana ya sauke wayar kana ya dube ni da murmushi yana faɗin
"Alhamdulillah wasu kuɗaɗen da Daddy ya bada kwangilar wasu kamfanoni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login