Showing 84001 words to 87000 words out of 125808 words

Chapter 29 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

462

ɗaya ɗakin da ke kusa dana su Naseem..
har na kammala cikin abincin bai dawo da shi,
Inna Wiro ta fita tace bari taje tayi wanka, niko na gyara na kwanta har bacci yafaraɗa ɗauka ta kafin ya shigo.
a hankali ya hayo gadon yace
"Yi hakuri kyakkyawa ta tashi ki bashi nono kin ji, Allah yunwa yake ji kiga fa sai latse baki yake."
na mike zaune tare da karɓar sa dan nasan yanzu kam yana bukatar nonon sosai.
kiciniyar janye rigata sama na shiga yi, sai ya maso ya taimaka min yaja rigar sama, yasaka hannun sa cikin bra ta ya ciro nonon da kansa ya saka masa shi cikin baki niko naɗan tallafe masa saboda kada yayi masa nauyi a baki.
ya sunyar da kansa ya sumbaci saman nonon, kana ya ɗago ya saka hannu ya ciro ɗayan, a hankali ya manna bakin sa ya sumbace sa shima,
yace "Nayi missing ɗin ku." sai ya saka hannu yarika shafa nonon,
a sannu ya leko fuskar yaron yayin da hannunsa ke manne kan ɗaya nonon yace
"Yau wa sha sosai ka kara kato."
murmushi nayi tare da duban sa nace
"Wani suna ka saka masa ne?." baki ya washe yace "AHMAD." ido na waro nace "Wane Ahmad fa kace Ahmad kuma."
yace "Eh Ahmad sunan da yanzu nayi masa huɗuba da shi kenan."
kai na jinjina nace "To me za'a rika ce masa kenan?." yace "Babu wani sunan da za'a rika kiran sa dashi face sunan sa Ahmad Ahmad Tijjani Sabil."
baki na rike nace "Taya za'a rika kiran sa da Ahmad bayan sunan ka kenan ai sai a nemo wani sunan da za'a rika kiran sa da shi."
yace "A'a kyakkyawa ta sunan da za'a kira sa da shi kenan asalin sunan sa Ahmad."
baki na turo gaba nace "To har yara ma haka zasu rika kiran sa da shi?."
murmushi mai sauti yayi kana yaja kumatu na yace
"To ai su yara basu ma san sunana ba kuma ko da ace sun sani ma nasa daban ne nawa daban, bare ma basu sani ba Daddy kaɗai suka sani, sai dai idan kece zaki faɗa musu."
da sauri nace "Yaushe." kumatu na yakuma ja yace "Duk san da kika cigaba da kira na da sunan."
nace "To ba sunan ka ba kenan Ahmad."
ido ya waro tare da yin dariya yace faɗar sa bai miki nauyi a baki ba, ko da Ahmad karami kike?."
kai na sunkuyar ba shakka sunan tayi min mugun nauyi, yauce rana ta farko tun farkon haɗuwar mu da shi har rana mai kamar tayau ban taɓa kiran sunan sa kai tsaye ba sai dai narika yin komai a dungu, bana taɓa iya kiran sunan sa.
hannu ya saka ya ɗago haɓa ta yace
"Me kika ce sake faɗa naji ni Ahmad ɗin?."
kai na daɗa sunkuyar wa ina murmushi, ai ko ba komai shi babba ne, hakan baya rasa nasaba da rashin iya kiran sunan sa da nake kai tsaye, ko ba komai ya girme min nesa ba kusa ba, ga wata babban girman wato da yake a matsayin miji na.
fuska ta ya leko yace "To in ba so kike ki sanar musu da sunan nawa ba, to a canza min suna yanzun nan adai na yimin abu kamar bani da suna arika kirana da sunan babu."
ban yi magana ba sai zare nonon da nayi abakin yaron ganin yayi bacci, na gyara na shinfiɗa shi, sai na yunkura ina kokarin mike wa,
cikin hanzari ya janyo ni na faɗo jikin sa, sai ya rungume ni yashiga ai kamin da zafafan sakwannin sa, masu birkita min lissafi, yashi nuna min yan da yayi missing ɗi na na wanaki uku.
duk kanin mu numfashi muke sauke wa a hankali ya kawo bakin sa saitin kunne na cikin yin kasa da murya yace
"Kyakkyawa ta wani suna aka bani? oya faɗa min naji."
a hankali cikin yanayin da yagama saukar min da kasala nafurta
"My."
wani irin runguma yayi min kamar zai cusa ni cikin kijin sa yace
"Wlh yayi kai amma gaskiya ni mai sana ne komai kin iya kamar yan da kika iya haifo min wannan kyakkyawan santalenen yaron nan haka kika iya zaɓar min sunan da ya dace da ni, ina son ki HAMDAH
ina yimi ki son da banayi wa kaina."
bakin sa ya dadaɗa mayar wa cikin nawa, nan ma yashi sau ke min wata sabuwar kasalar, tuni idanunsa ya gama sauya wa sai fidda numfashi yake.
gaba ɗaya ya birkice yakuma birkita ni, joystick ɗin sa ya damke da hannun sa da karfi a hankali cikin fizgar numfashi yace
"Zafi yake min ki tai maka min."
ido na waro nace "Ta ina ko ka mance akwai jini kuma akwai ciwo agurin."
kai ya girgiza yace "Na sani bata nan ba."
sai ya cusa hannunsa cikin wando yazaro sa, yana tsaye kem sai zillo yake.
hannuna ya kamo duka biyu ya saka kansa yaɗan matse, fahimtar me yake nufi da sauri nace
"Inna Wuro zata shigo fa." yace "Bazata shigo yanzu ba." a hankali na gyara na shiga kokarin taimaka masa ta hanyar sarrafa shi da hannu da kuma baki na, dan nasan yana buƙatar taimako na a wannan lokacin duba da yanda yake ta matse ido.
sai da na tabbatar da nasama masa nutsuwa kana na zare bakina kan abar tasa, nayi amfani da toilet paper wajen kawar da madarar sa.
sumbatar goshi na yayi tare da faɗin
"Nagode sosai kyakkyawa ta."
idanuna na lumshe tare da kuma buɗe
wa...

Ya juya yana faɗin "Bari naje nayi wanka."
bayan sa nabi da kallo har ya fita, sai na sauke numfashi tare da mai da bayana na jingina da jikin gado a hankali na lumshe idanuna.
fitar sa da kamar minti 30 Inna Wuro ta shigo, ta leko fuskar yaron tace "Bacci yake ne?." nace "Eh."
kofin da ta shigo dashi rike a hannun ta ta mika min tana taɗin
"Gashi kisha maganin da Malam yace a dafa miki ne."
nace To tare da karɓa, nace "Inna Wuro kinji sunan da ya sa wa yaron nan wai Ahmad."
Inna Wuro tayi dariya tace "Ai yanzu yake faɗa min a hanya ta tazuwa nan, nace to kaji Ahmad baban Ahmad, Allah ya raya shi da imani yaɗau ko halin uban sa da kakasan sa."
nace "Wai fa haka za'a rika kiran sa nace a canza masa yace a'a taya za'ayi a rika kiran sa da sunan."
tace "To shi haka yaga yafi tun da shi yace sai a rika kiran sa da hakan kawai."
kai kawai na girgiza kana nashiga shan maganin..



Washegari da sassafe Hajiya Karima tazo lokacin ana shirin yiwa Ahmad karami wanka, a parlour'n sama ta zauna, sai da Inna Wuro tayi masa wanka ta shirya shi kafin ta mika wa Faty da ke zaune tana zaman jiran a gama masa wankan a bata shi.
Inna Wuro tace ta kai wa kakar sa shi a parlour.
sai a lokacin nima na mike na fita parlour'n, Faty tazo daf da ita zata mika mata ɗan mukajiyo maganar Ahmad a sama.
"Da kata Faty!." cak Faty ta tsaya batare da ta mika mata ɗan ba,
ɗan razana Hajiya Karima tayi a ɗan daburce ta ɗago kanta.
ya karaso cikin parlour'n yayin da idanunsa ke kan hannun Hajiya Karima, Rasheedat na biye da shi..........!






29






Da sauri cikin dabara Hajiya Karima ta mai da hannun ta cikin mayafin ta.
murmushi Ahmad yayi ya mika hannu ya karɓi Ahmad karami yana faɗin
"Ke Faty haka ake rukon yaro a garin ku? ya zaki fito da shi a sanyin nan babu wani isasshen kaya a jikin sa, bani shi nan budurwar kauye kawai."
Faty tace "Kai Yaya Ahmad ba ga kaya ajikin sa ba."
yace "Ke yaushe kika san yan da ake rainon ɗa haka zakije gidan ustaz ɗin nan kina fidda masa ɗa babu kaya a sanyi ko."
dariya tayi tana rufe fuskarta.
baki na buɗe nace "Wani Ustaz ɗin?." yace
"Ita ta sanshi ai."
da sauri tayi waje tana faɗin "Ni babu ruwa na."
ya dubi Hajiya Karima yana daɗa faɗaɗa murmushin sa yace
"Hajiya so take tasa angon ki ya kamu da mura wannan kayan ai baiyi a fito da shi ba."
baki Hajiya Karima ta washe cikin ɗan kame-kame tace "Eh haka..haka ne."
wani murmushin yakuma sake wa kana ya juya ya shige cikin bedroom ɗina.
zuwa can yafoto da shi cikin wani katon towel ya karaso inda take ya mika mata shi yana faɗin
"Hajiya ga angon naki."
baki ta washe tace "A'a kaga Ahmad ɗan Ahmad jika ga Tijjani sabil, kaman kai lokacin kana jariri."
baki ya washe yana zama kan kujerar da ke fuskantar ta yace
"Hajiya da gaske haka nake lokacin ina jariri anya nakai sa kyau lokacin kuwa?."
tace "Sosai yan da ka ganshi haka kake kai da gashi har yanzu kyan naka na nan bai gushe ba."
kallo na yayi tare da ɗaga min gira.
niko baki na taɓe a ɓangaren Aunty Rasheedat ma haka a bin yake itama bakin ta taɓe sannan tace
"Hajiya kice kun sha kallo lokacin can."
fuska Hajiya Karima ta ɗan suke tana yimata kallon kasa-kasa.
itako Rasheedat wani murmushi ta sake tare da jijjiga kai.
Ahmad kuwa idanunsa a kan ɗan da kuma hannun Hajiya Karima. tana kokarin mike wa da sauri shima ya mike yana faɗin
"Hajiya badai tafiya zakiyi ba?."
dariyar yake tayi tace "Gidan wani biki nake son zuwa direba ma yana waje ya zaman jira na, dama nazo ne naga jikar nawa gashi nan sai baccin sa yake Allah ya raya mana shi muga girman sa."
karɓar ɗan yayi a hannun ta yace "Amin amin gun gode Hajiya."
yayi mata sallama ta fita. tana fita ya matso in da Rasheedat take ya zauna tare da jan towel ɗin da ya naɗe yaron ciki yace
"Ɗau ke shi ban da towel ɗin."
ta ɗago shi da iya abin ɗaukar sa da ɗazu aka fito da shi ta rungume shi a jikin ta tana sumbatar goshin sa.
shiko Ahmad mike wa yayi rike da towel ɗin a hannunsa yanufi kasa..
numfashi Rasheedat ta sauke dan tasan komai akayi akwai wani abun.
ta dubeni da murmushi ganin yaron ya farka yana mutsumutsu tace
"HAMDAH bashi nono kin ga ya farka."
nace "Allah Aunty Rasheedat yaron nan yafiye tsotso Allah ni bacci ma nake ji kuzau na da shi kawai ki bashi madara ya sha."
na mike tsaye na nufi bedroom ɗina. dariya tayi tace
"Madara kuma ah da sauran sa tukun kidai tai maka ki bashi ɗin."
ta biyo nita cigaba da faɗin
"HAMDAH karɓe shi kibashi kin ga zai yi kuka."
Inna Wuro da take cikin ɗakin tana gyara, ta karɓe shi ta miko min shi...

Rasheedat na fita daga ɗakin lokacin Ahmad ya hauro, da fuakar tambaya ta dube sa, sai ya ruko hannun ta ya janyo ta cikin bedroom din da suke kusa da shi.
suna shiga tace "Aboki me ke faruwa ne ina kakai towel ɗin?."
numfashi ya sauke yace "Nasa aje a yar da shi ne, tazo da wani irin guba mai amfani da fatar jiki yana saurin yiwa yara musamman jarirai illa acikin mintuna kalilan, shine a hannunta duk da yana cikin kwalba
amma yana da hatsarin gaske, taso yin amfani da shi wajen sakawa yaron a jikin sa, bayan ƴan mintina kuma zai shige cikin jikin sa daga nan kuma sheke nan, fatan jariri bashi da karfi koda kwalbar kaɗai ya taɓa jikin sa za'a iya samin matsala, shiyasa na saka masa towel ɗin nan ta in da koda kwalbar ya taɓa shi ma zai tsaya a iya jikin towel ɗin ne."
Ido Rasheedat ta waro cike da tsananin tsoro tace
"Aboki ya kamata kayi wani abu fa, matar nan babu ɗigon imani tare da ita, zata iya bin tawata hanyar tun da taga yanzu bukatar ta bai biya ba, nikam nafara jin tsoro."
murmushi yayi yace "Babu abin da zata iya yi."
tace "To amma dai zaka faɗa wa HAMDAH ko dan tasan me ake ciki tadaɗa sanya ido sosai, kada ranar da baka nan kuma tazo."
yace "A'a baza'a faɗa mata ba idan aka sanar mata hankalin ta zai tashi dan ba ni da ɗan kaɗai take hari ba har da ita, idan taji kuma hankalin zai tashi za'a iya samin matsala."
cikin kaɗuwa tace "Har da ita?."
kai ya jinjina kana yace
"Muje babu komai."


Ana gobe suna da daddare Ahmad ya shigo, Inna Wuro na ganin sa ta fita, ɗan madaidaicin akwatin da ya shigo da shi ya aje kan table,
sai da ya sumbaci goshina sannan ya sumbaci Ahmad karami dake bacci.
yaɗa go kana ya zuge zip ɗip ɗin akwatin wasu kaya ne na alfarma a ciki, dogayen riguna ce irin na amare haɗe da jaka da takalmi da sarka da ƴankunne da abun hannu na gold,
tsayuwa kwatan ta muku kalar tsaruwan kayan ma ɓata lokaci ne, ya haɗu yayi kyau ya tsaru iya tsaru wa.
da sauri na mike na ɗago ɗaya daga cikin rigunar na manna shi a jikina nace "Wannan fa kai gaskiya sunyi min kyau sosai."
murmushi yayi yace "Yanzu naje na amso su a airport jiya nasa a siya
yau aka saka a jirgi."
murna yahani tsayuwa naji daga wata kasa yasa asiya, naɗago sarkar da sai wal-wal yake yana ɗauke ido nace
"Kai gaskiya wlh duk sun yi kyau sosai fa."
dariya yayi yace "Ashe nima na iya zaɓe kenan."
nima dariyar nace "Gaskiya yayi kyau sosai ka iya zaɓe kam."
wayar sa ya ɗauka ya daddanna yace
"Zo ki gani." gefen sa na zauna ina leko cikin wayar.
hotunan wani katon hall ne wan da tsaruwan sa yakai ya kawo yace
"Anan za'ayi toron bikin mu dana suna gobe da karfe sha ɗaya na rana za'a fara za'a tashi karfe 11 na dare."
da mamaki nace "Ina a gida za'ayi taron."
yace "Ina ai ba iya taron suna ba ne kaɗai har da taron bikin mu, yanzu haka ina da ba'ki waɗan da suka zo daga kasashe masu nisa sosai suna masaukin da a ka tanadar musu wasu kuma zasu iso cikin dare wasu gobe da safe."
kai na jinjina jin da faske yake nace "Allah ya kaimu, Ukhtee ma ta kusa iso wa wata kila jirgin su ya sauko karfe 9."
yace "To bari a sa direba ya shirya zuwa taro ta, ya kamata ya isa airport kafin saukowar su."
kira ne yashigo wayar sa ya mike yana faɗin
"Wani abokin Daddy na ne daga ɗan Nigeria ne mazaunin Ingila, jirgin su ya iso kenan bari naje nasa a taro shi, bani number Ukhtee na baiwa direba ya tafi yanzu time zai yi."
nace to. ina bashi yafita da sauri.
da misalin karfe 9 kuwa jirgin su Ukhtee ya sauko, direba ya ɗauko ta zuwa gida, har farfajiyar gida naje na taro ta, muka rungume juna muna ihun murna.
ranar kusan kwana muka yi muna hira...

Washegari tun sassafe Hajiya Rahama tazo da me makeup dan jiya mun yi waya da ita, bayan nayi wanka na zauna a ka shiga tsantsara min kwalliya,
ana gamawa nasa Ukhtee ta zaɓo min ɗaya saga cin kayan da jiya Ahmad ya kawo min, na saka na zauna me kwalliyar tashiga naɗe min ɗankwalin kayan a kai tana gama ɗaurin, aka miko min takalli da ɗan madaidaicin pos wan da suma acikin akwatin aka ciro su, nasaka takalmin narike pos ɗin a hannu sai ɗan karamin gyale wan da aka rataya min shi a hannu,
karfe 11 da minti goma a ka gama yimin komai, kowa ya tsaya kallo na kamar basu taɓa ganina ba, sai faɗi suke Masha Allah. Aunty Nasiba da Faty da Ukhtee sai hotuna suke ta yimin.
hannu na wacce tayi min makeup ɗin ta ruko muka tako gaban mirror mirror'n tayi min nuni da shi tare da faɗin
"Bismilla." ina sauke idanuna kan mirror sai da naɗan girgiza, sosai na kure kaina da kallo ta cikin mirror.
sai nake gani kamar ba ni bace, "Masha Allah." nafaɗa a kasan raina, ni kai na nasan nayi kyau ba na wasa ba.
kiran Ahmad ne ya shigo waya ta na ɗaga yace
"Ki fito gani a waje time yayi fa har yaɗan go mun bar mutane acan."
nace to, nayi wa Ukhtee magana da larabci kan ta karɓi Ahmad karami dake nannun Hajiya Rahama wan da shima aka shirya sa cikin kayan alfarma wan da ɗazu Aunty Rasheedat ta aiko dashi tace a sa masa.
muka fito gaba ɗayan mu, tsayuwa nayi ina kallon kayan dake tare cikin parlour Inna Wuro da wasu ba'ki suna zaune suna kallon kayan, nan Inna Wuro take faɗa min dangin Ahmad ne suka kawo.
nace mata zamu tafi gurin taron ne ko zata je, tace min a'a ita kam tana gida.
wasu daga cikin mutanen cikin parlour'n suka mike suka ce suma zasu.
a parlour'n kasa na iske mutane tam wasu ma ban san su ba.
nan muka ɗunguma mukayi waje.
motoci ne ajere a tsakar gidan da suka kai guda goma,
motar sakiya an bita da wani kalliyan furanni ta sama da gefe-gefen ta, kuma kaf cikin su rafi kowani mota kyau.
da sauri wani soja dake tsaye jikin motar ya buɗe marfin gidan baya, can na hango Ahmad yana leko ni.
a hankali na karaso jikin motar, da sauri sojan yayi baya ya daɗa buɗe marfin motar, a sannu na shiga nayi wa Ukhtee magana nace ta shi gaba.
sojan ya mai da marfin ya rufe.
kana ya buɗe mata itama ta shiga,
acikin motar na tadda su Naseem sun sha wanka na alfarma kayan su iri ɗaya Nasmah har da makeup a fuskar ta, sun yi kyau sosai.
shima Ahmad ɗin wani kaya ne a jikin sa na alfarma agogo da takalmin kafar sa sai sheki suke.
ido Ahmad ya kura min babu ko kiftawa yabuɗe baki da hanci gaba ɗaya yana kallo na.
iska na hura masa a fuska nace
"Ya dai?." firgigit yayi sai yapl damko hannuna yace
"Kyakkyawa ta kin gan ki kuwa kin ga yan da kika daɗa kara kyau."
murmushi nayi nace "To ai kai ma kayi kyau."
baki su Naseem suka shiga washe wa suna faɗin
"Mommy tayi kyau." nace "Kuma kun yi kyau."
Ahmad suka gaisa da Ukhtee yana yi mata ya gajiyar hanya.
jama'a kowa ya shishiga mota a ka ja motocin a jere aka ɗau hanyar hall ɗin.
tun daga farkon shiga layin da zai sadaka da hall ɗin jami'an tsaro ne ke tsaitsaye har bakin get ɗin,
baka jin komai sai tashin sautin kiɗa,
a hankali aka wangale get ɗin motoci suka kusa ciki,
cikin katon farfajiyar gurin cike yake da motoci, a haka aka rika faka motoci layi-layi.
sauran motocin da muka zo da su duk mutanen ciki suka fita suka nufi cikin hall ɗin, muna zaune cikin motar har waɗan da suka zo daga bayan mu suka shige ciki.
zuwa can Rasheedat ta fito daga cikin hall ɗin, cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login