Showing 27001 words to 30000 words out of 125808 words
ta kokarin gina shi domin yayi karko to kuwa zai iya rusa min shi, tabbas zan ɗauki mataki kansa, "Amma mene ne mafita?. nayi wa kai na tambayar ina gyara zama ta,
"Mafitar kenan kawai ki canza musu makaranta."
zuciya ta ta bani amsa, kai na jinjina da gaskata abun da zuciya ta ta faɗa min, hakanne kawai mafita ta yadda zasuyi nesa da shi, idan kuma ba haka ba to kuwa abun da nake ta kokarin cire masu kwaɗai tar sa a zukatan su shine zai faru, dan kuwa in har hakan yaci gaba da faruwa zasu tashi da sanin wani mahaifi a ransu wan da bana son su san haka, nice nan uwa kuma uba a rayuwar su, sam bana son su tashi da jin cewa zasu sa mi uba ni zasu cigaba da jina uwa kuma uba a rayuwar su.
bana so su sanyawa ransu abun da baza su samu ba a rayuwar su, to mene ne amfanin sanya wa ransu hakan,
gara kawai su san cewa ba su da uba, su ji a ransu ni ce uban nasu kuma ni ce uwan su.
wannan kaɗai shine mafita in sauya musu makaranta in nesan tar da su daga gare shi, in ma koyarwa yake a makarantar imma mene ne baya sake ganin su bare ya cigaba da cusa musu wani ra'ayin, ai dai sun rabu bashi basu, bazai sake ganin suba suma haka bare su sake kiran shi da wani Daddy,
"Ɗan rainin wayo har da cewa surika ce masa wani Daddy, sai kace wani uban su ko meye gamin sa da su oho."
naja dogon tsaki tare da yin kwafa kana na mike, nashiga tuɓe musu uniform ɗin su, ina faɗin
"Ku da shi ɗin duk zanyi maganin ku."
bathroom na jasu da kai na nayi musu wanka yau, muka fito na saka musu wasu daga cikin kayan su da yake bedroom ɗina, sai da na nagabatar da sallar azahar kana na janyo su muka sauka kasa.
dinning area muka zarce bayan munci abinci najasu muka tafi part ɗin su Inna wuro, nan muka tarar da Faty ita ma dawowar ta daga school kenan, nan muka yada zango mukata hira...
da yammacin ranar zaune nake a parlour'n sama na ɗago wayata na laluɓo number shugaban makarantar su Naseem.....!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:54 - Ummi Tandama😇: Yan da idanun sa yasarkafu cikin nawa haka babu zato ko sammani shi yasani shiga yanayin,
sai kuma na gyara tsayuwa ta da kyau, wani kallo yake bina da shi daga sama har kasa kana yace
"Na ɗauka kafin kiran hukuma ihu zaki yi ta yi kitara jama'a kice ga ɓarawo yazo satar yara, ke ba'a yi miki ihu ba har ke zaki wa wani ihu? karfe nawa ne yanzu wai wannan lokacin ne lokacin zuwa ɗaukar yara a makaranta,abar yara can kowa ya watse sai su kaɗai a cikin makaranta, sabo da baki san abun da kike yi ba an turaki ɗaukar su kin tsaya kin ɓata lokaci a hanya kina damuwar ki wata kila ma kinbi gidan kawayen ki kin gama sharholiyar ki,
kafin nan kika zo wai ke a hakan kinzo ɗaukar su a makaranta, karfe nawa yanzu?. karfe nawa ne yanzu?!".
yakuma nanata tambayar, yana maganar ne ida nunsa a kaina da kuma alamun jaddada tambayon da yake jefa min,
gashi dai maganar cikin faɗa yake yin sa amma lamɓansa a hankali suke motsawa.
dogone yana da faffaɗar kirji da zubin kakkarfan maza, fuskarsa na ɗauke da ɗan siririn saje wan da ya zagaye fuskar nasa har zuwa ɗan gemun sa da bai wuce rabin kamu ba, irin gemun da gayu suke bare.
baza a kirasa da fari soll ba sanna kuma ba baki bane, hasken sa dai-dai.
kwantaccen gashin kansa baki sitif yasha gyara mai tsamtsi da tsulɓi sai wani yal-yal yake, sabo da iskar dake kaɗawa.
Kaina nakawar gefe tare da murguɗa baki nashi a wanne zai zauna yana wani masifa to ina ruwan shi ne ma.
ɗan rutsunawa yayi yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran kana ya dubi ko wannen su yace
"Idan kunje gida kuce wa Mommyn ku kada a sake turo Aunty ku ta ɗauko a School a rika ai ko me wayo yarika ɗauko ku, wan da bazai barku kuyi ta shan wahala a nan ba, kunji ko?."
kai suka gyaɗa suna ta faman shan chocolate "Yauwa to kuje gida sai gobe zan kawo muku wani chocolate ɗin, kada ku man ta in kunje gida kufaɗa wa Mommy kada a kuma turo wannan Aunty'n naku ɗaukar ku a School a aiko mai wayo."
yayi maganar yana yi musu alama da suje in da nake yana binsu da murmushi,
ido na waro cikin masifa nabuɗi baki zanyi magana, dai-dai lokacin mota ta faka gefen mu, da mugun gudu, Yakubu direba yafito da sauri ya iso in da muka yana faɗin
"Ranki shi daɗe Hajiya wlh gosulo ne yatsare ni tun ɗazu babu ta yan da zanbi na koma da baya na canza wata hanyar, gaba da baya motoci suka sani a tsakiya,jibi kumatu na har mari nasha dana nimi in juya dan na canza hanya, Hajiya a gafarce ni, wlh gosulo ne, ita kuma wayar sam na mance jiya da zankwanta bacci nacire ta a kara yau har gari yawaye kuma ban mai da kararta ba, Hajiya ayi hakuri da Allah."
maganar yake tamkar zai zuba guiwowin sa a kasa yana tafa bayan hannun sa a cikin ɗaya tafin hannunsa alamun roko,
banyi magana sai juya wa nayi nanufi gun motar dana zo da ita, dan wannan mutumin yakure ɓata min rai.
Muryar Yakubu naji yana faɗin
"A'a ranka shidaɗe ina wuni barka da warhaka."
bude motar nayi nashige ciki batare da naji amsa gaisuwar da yake yi masa ba.
sai juyawar sa nagani yamatsa jikin motar sa yana kokarin bude marfin gidan baya, da sauri a ka buɗe gidan gaba wani ya fito cikin hanzari yarigasa kai hannu jikin kofar yabuɗe, kana yaɗan ja dabaya ya bashi hanya yashige motar ya mai da murfin ya rufe, kana shi kuma yakoma mazaunin direba yaja motar sukayi gaba.
Yakubu yakamo hannun su Naseem ya kawo su motar da nake yabuɗe gidan baya yasaka su, yace
"Hajiya bari na rufe wancan motar sai na kaiku gida a wannan na hau abun hawa na dawo na ɗauki wanca ɗin."
yajuya da sauri ya nufi in da motar da yazo da ita yake, fita nayi nakoma baya in da su Nasmah suke, yana kulle motar yadawo yashiga mazaunin direba yaja motar.
Munbar harabar makarantar da ɗan nisa kana na juyo na dubi su Nasmah dasuka gama kwaɓe jikin su da chocolate, ganin ina kallon su sai Nasmah ta miko min na hannuta tace
"Mommy akici". cikin masifa nace "Ai sai kun sha duka ba kun iya kwaɗayi ba bakusan mutum ba kuka ma binsa, waya sani ma ko mai satar mutane ne yayi gaba da ku wata kila ma badun na iso da wuri ba da yanzu yayi gaba da ku, yaje yayi kuɗi da kanku,
idan kuka kara ganin mutum baku sanshi ba kuka bishi sai na zane ku, bare har ya baku abu ku karɓa sai na yanke hannun ku, yajaku mota zaiyi gaba da ku Allah ya so ku ai da kuna can Allah kaɗai yasan halin da kuke ciki, badun na iso da wuri ba, ɗan rainin hankali wai arika ai ko mai wayo yarika ɗaukar ku to ina ruwan sa ma daku tukun, mttsss." nayi maganar tare da jan tsaki.
baki Naseem yawashe cikin ɗan sallen murna daga zaunen da yake yace
"Ai Daddy yace dai caya mana mota."
wani irin faɗuwar gaba naji da ya ambaci sunan Daddy da sauri nace "Kai Naseem waye kuma Daddy?." Nasmah ce ta caɓe zancen da faɗin
"Daddy daya bamu chocolate yace dai cayamin jigi haida mota da chocolate da yawa."
da karfi jin yan da zuciyata ke tafarfasa kai na ke sara min nace
"Kai ya isa! idan na kara jin kalmar wani Daddy a bakin ku sai na fasashi, ku bani chocolate ɗin nan."
nafaɗa ina karɓe chocolate ɗin hannun su na zuge glaas ɗin motar nayi wurgi dashi.
maganar Yakubu najiyo wan da tashin hankalin da nashiga ciki yanzu sama-sama nake jiyo shi yana faɗi
"Hajiya ai shi wannan mutumin bamai satar yara bane mutumin kirki ne, shine Ahmad Tijjani Sabil mai kamfanonin nan wan da ake nuna shi agidajen talabijin, ai ko ɗazu dana kawo su makaranta na tarar da motar kamfanin shi tana sauke kujeru dawasu kayan amfani na makaranta,ai kin sa kenan yana da yawan taimako kuma taimakon sa yafi yawa a inda yara suke."
"Ahmad Tijjani Sabil."
na mai-mai ta sunan a raina ina ta son tuna in da nasan sunan, sai a lokacin na tuna ɗazu da safe ake labarai a kansa a gidan tv anan nataɓa jin sunan.
Naseem yace "Ai nima Daddy yace dai taya min mota in tuka akaina."
cikin tsawa nace "Ban ce kada naji wani ya kara min maganar wani Daddy anan ba?, rufamin baki idan ka kara sai na fasa ma baki bari ka gani."
Yakubu kuwa ci gaba da zuba yake wan da ma gaba ɗaya hankali na baya cikin motar da jikina gaba ɗaya.
Muna komawa gida nakira *HAM'NAS* Store Complex nace a kawo min motar wasan yara guda biyu da wasu kayan wasa, batare da ɓata lokaci ba motar ShopRite ɗin ya iso, a ɗakin kayan wasan su aka jibge musu,
ihun murna suka sake ganin motocin cikin tsallen murna Naseem yace
"La iyin motan da Daddy yace dai taya mana babba."
da sauri na mike daga kan kujerar da nake zaune cikin ɗakin kayan wasan su, hannayen su duka na riko nadawo na zauna, inajin zuciya ta na min mugun ɗaci da kuna a duk san da naji sun furta kalmar Daddy a bakin su,
duban su nayi dukan su nace
"Kuna ji ko Naseem Nasmah?, shi wancan mutumin ba Daddy'n ku bane baku sanshi ba kuma ku bakuda Daddy, nice Mommy'n ku kuma nice Daddu'n ku bakuga na siya muku mota ba, idan kuka sake faɗar Daddy bazan sake siya muku mota ba, kuma zan sa akwashi waɗan nan ma a tafi dasu, baku da Daddy nice Daddyn ku kunji ko?."
kai suka gyaɗa nace "To maza kuje kushiga motar ku." ai ko da sauri suka ruga in da motar suke suka shiga,
ina tare da su a ɗakin sai zaga ɗakin suke a cikin motar, suna dariya.
numfashi nasauke ganin suna cikin farinci sosai, Nasmah ta danna motar ta motar tatafi tsuu zata garu da jikin garu-bango da sauri na mike na tafi da gudu na taro ta, na ciro ta ciki ina faɗin
"To ya isa haka muje kuyi wanka kuci abinci sai kuma anjima zan sa afito muku da shi can tsakar gida kuyi wasan acan."
nayi waje da su.
Yau Juma'a da wuri Talatu tagama yi musu shirin makaranta, narako su har sai da motar kaisu makaranta yafita kafin na juya a hankali, gaba ɗaya yau jikina baya min daɗe a hankali na isa bakin swimming pool na cire takalmata gefe na zauna bakin swimming pool ɗin na zura kafafu na ciki, a hankali nake motsa ruwan da kafata ina ɗan lilashi ciki, wasu hawaye ne masu ɗumi suka zubo kan fuskata banyi kokarin sai da su ko danne zuciya ta daga abun da take jiba, tun jiya nake jin kai na cikin yanayin ina so nayi kuka ko zanji sassaucin abun da nake ji cikin zuciya ta, sai dai ban sami damar yin kukan ba saboda su Naseem, sam bana so nasaka musu rauni cikin zuciyar su, dan aduk san da irin wannan damuwar ta taso cikin zuciya ta zama nake a ɗaki nayita kuka, aduk san da sukaga ina kuka sun rika tambaya ta me ya same ni idan nayi shiru ban basu amsa ba ko nace musu babu komai suma sai su fashe da kukan su rungume ni muyita kukan.
tabbas ina ganin rauni da damuwa aduk san da hakan tafaru agare su, duk da kuwa kasan cewar su yara wan da basu san komai ba, amma nasan akwan atashi idan hakan yaci gaba da faru zasu tashi da abun a ransu,
nasan ɗaci da kunar dake tattare da kuncin ganin UWA cikin damuwa game da ɗan ta, dan kuwa shike hanani sukuni a koda yaushe.
wasu hawaye ne masu zafi da kuna suka cigaba da wanke min fuska cikin jan sheshsheka nashiga faɗin
"Ummi na kizauna gidan Abba Ummi bazan taɓa yafewa kai na ba har idan nayi sana diyyar barin ki gidan Abba, Ummi na zancigaba da yin nesa dake har idan hakan zai sa ki cigaba da zama gidan Abba."
kuka sosai ya kwace min cikin muryar kukan nacigaba da faɗin
"Abba wlh ban ai kata zina ba ban taɓa ai kata zina ba, Abba zan cigaba da yin nesa daku har idan hakan zaisa Ummi na tacigaba da zama agidan mu, bana so nayi maraicin uwa batare da tabar duniya ba,
Abbu Mamie Ya Masa'ud Auny Rafee'at Aunty Jaleela Nusaiba Fauzaun, kewan ku da begen ku yana hanani sukuni,kullum da ku nake kwana cikin raina, shin haka kuma kuke kewata ina son ku ko da yaushe ina tare da ku a cikin zuciya ta,
ku yar da dani wlh ƴaƴana ba shegu bane, wlh Allah ban taɓa zina ba,
Allah sarki Inna ta da kina nan da kin faɗa musu kalar tarbiyyar da kikayi min wan da ko da agidan karuwai zan zauna bazan yi iskanci ba, bazan yi ba, bazanyi ba,
Ya SALEEM Ya SALEEM Ya SALEEM me na tare muku kai da matar ka meyasa zaka rabari da *MAHAIFIYA TA* karabani da ahalina me nayi muku, me yasa zaka sheganta min ƴaƴana tsaftatattu ka dan ganta su da wani uba wan da bansan ko waye shiba,
duk hakan na menene da har sai ka kazanta min ƴaƴa? ƴaƴa na ba kazan ta bane kamar yadda ka faɗa ƴaƴana tsaftatattu ne bazan taɓa yafe maka Ya SALEEM bazan yafe maka b...."
Kuka ne yaci karfi na nakifa kaina da guiwa na nayi ta kuka kamar raina zai fita.
najima sosai zaune a gurin ina ai kin kuka, mai cike da kuna da bakin ciki. da kanshi hawayen ya tsaya badun na tsai da shi ba, sai dai kukan zuci danake, a hankali na mike cikin matsananciyar ciwon kai wan da dakyar nake iya buɗe idona duka sabo da zafin ciwon kan, na nufi ciki.
direct bedroom na shige kana shiga bathroom wanka nayi nafito na sauya kaya na zo na kwanta bakin gado,
karatun Alkur'ani na kunna cikin wayata a hankali nake bin karatun, a sannu narika jin zuciya ta tana samin salama da nutsuwa, a hankali narika jin bacci na fizgata ta, na lumshe idanuna.
can cikin baccin da ya ɗauke ni da nisan ta baifi na minti 20 ba.
najiyo muryar su Nasmah, da gudu suka haye gadon suna faɗin
"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."
ida nuna na rumtse da ɗan karfi dan har lokacin kai na bai bar yimin ciwo ba,
mike wa zaune nayi jin sun zube a jikina na ɗago su ina faɗin
"Wai har kun dawo? amma dai ba'a tashi ba ko."
nayi maganar ina duban agogo, karfe 12 har da rabi,nayi mamakin gani in da lokaci yatafi har haka, ranar yau karfe 12 saura suke dawowa har sun dawo anyi musu wanka an sauya musu kaya.
lallai najima ina kuka har ban san lokaci yatafi har haka ba, tausayin kaina ya kamani, ɗan guntun kwallar da ke kokarin sauka a idona ɗaya nayi saurin kai yatsata na tare shi kana na gyara zama ta ina faɗin
"Ashe dai lokacin tashin naku yayi, to yaya karatu yau ansha wasa ko."
nayi maganar ina shafa kansu.
baki Nasmah ta washe ta mike tsaye a kangadon tace
"Mommy yau Aunty'n mu tayi mana haka."
tarike kugu tare da girgizawa, dariya nayi ina faɗin
"Au kice yau Aunty rawa tayi muku."
"Ba haka bane haka ne".
Naseem yafaɗa tare da mike wa yarike kugu yasoma tsalle.
ido na ware nace "Kai kuce yau kunsha rawa." cikin tsallen yace "Eh ai hadda chocolate ma."
tsai da tsallen da yake yayi sai kuma ya dira a godon da gudu yafita sai gashi ya dawo da School bag ɗin sa, a tsakiyar gadon ya zazzage School bag ɗin sai ga Chocolate masu yawa haɗe da littattafan sa sun zubo,
da mamaki nace
"Yau kuma Talatu kayan zaki tacika muku a jakar."
nakai hannu na ɗibo chocolate dasuka kai guda biyar kala daban daban, ga kuma wasu a gaban sa, da ɗan mamaki nake kallon su dan asanina babu kalar waɗannan chocolate ɗin acikin kayan cime-cimen su kalar nasu ba irin wannan bane.
"Kai Naseem a ina ka samo waɗan nan chocolate ɗin?."
nayi maganar ina duban sa, da sauri Nasmah tace
"Nima akwai nawa." ta dira agadon da gudu tayi waje, Naseem ko bai bani amsa ba sai kokawar buɗe laidar chocolate ɗin yake.
ta shigo da school bag ɗin ta itama ta zazzage, nace
"Kai wai waya baku wannan abun haka, Talatu Talatu."
nashiga kwaɗawa Talatu kira dan na fara tunanin ko rikici sukayi mata gun shirya su tabuɗe wani katon ɗin chocolate ɗin daban.
Naseem da yakai Chocolate ɗin baki ya kutsura yana ɗaga kafaɗa alamun yana jin daɗin abun yace
"Daddy yace mucinye wannan duka dai kaya mana wani."
"Ai yace idan ka kaiɓa min baye kaya maka ba ni de bani da yawa."
cewar Nasmah tana kai wan da ta ɓare baki.
Ido da baki na waro da mamaki tuno wan da suka taɓa kiran sa da Daddy a makarantar su nace "Wani Daddy mutumin nan ko?, a ina kuka san shi dan gidan ku da har zaku rika ce masa wani Daddy."
Naseem daya cika chocolate a bakin sa yace
"Ai Daddy yace kuma dai jo ya auke mu ya kai mu can guyin kifi babba."
cikin tsawa nace "Bana ce muku kada wani yasake baku abu ku karɓa ba? ashe bakuji ba so kuke nazane ku ko?, bana ce muku nice Daddyn ku nice Mommy'n ku ba, shi ba Daddy'n ku bane, baku san shiba shima bai sanku ba, bakuda Daddy nice Daddy'n ku, kuna jina dai ko?."
nariko kunnuwan su ina jijjigawa a hankali, suka gyaɗa kai.
shiru nayi tare da komawa na jingina bayana da jikin gado jiki a sanyaye nashiga maganar zuci
"Kuhi hakuri ƴaƴana ni zan cigaba da zame muku uwa kuma uba a duniyar na."
jin kwalla nakokarin zubomin nayi saurin dakatar dashi...
A ranar nasa aka kawo musu chocolate dawsu kayan makulashe aka kara kan wan da yake gida.
washegari ranar