Showing 51001 words to 54000 words out of 125808 words
yace
"HAMDAH fito kuje asibiti ga Ahmad na jiran ki, kinsan yanzu ba ayin aure sai da gwajin lafiya kuje ku gwada lafiyar ku sabo da sai da shi
yanzu ake yin aure, kafin a ɗaura aure gobe dole sai an bukaci takardar shaidar ingancin lafiyar ku wan da yafito daga hannun likita."
nace "Bappa lalle ake min kuma yanzu akayi bai bushe ba."
yace "To bari ace yatafi in yaso anjima sai ya dawo."
To na amsa da shi a takaice...
Sai bayan sallar la'asar kafin lallen yabushe aka wanke, duk nabi na gaji, a gabiye na faɗa cikin bedroom ɗina, nashige cikin bayi domin yin wanka nakuma gyara jiki na, dan naji alamar zuwan al'ada ta. shi yasa nace wa Hajiya Lubabatu zanje ɗaki na na ɗan watsa ruwa acan na huta dan nagaji da yawa,
ina gama kimsa jikina nafito, gaban mirror na zauna nasoma shafa haɗin mayuka masu daɗin kamshi data haɗa min.
waya ta ce tashiga ruri ganin mai kiran yasa nayi banza, yayi ta kira yafi a kirga ban ɗaga ba.
knocking akayi tare da yin
sallama daga bakin kofa, jin muryar Faty ce yasa nace tashigo.
tace "Adda HAMDAH wai kizo inji Yaya Ahmad."
fuska na ɓata nace "Kice bazan zo ba."
har takai bakin kofa nace "Bappa na gida ne?." tace "Eh." nace "Kice masa ina zuwa."
ta amsa da to tayi waje.
tsaki naja a fili nace
"Wlh badun kada Bappa yace naraina sa ba Allah da ba abin da zaisa naje."
sai da nagama iya yanga ta kafin nasaka kaya nafito ina gyara mayafin kaina, su Nasmah na ganina suka biyo ni da gudu suna faɗin "Mommy damu biki." Aunty Nasiba dake parlour'n kasa tana tare da masu aiki suna ta shirya abinci, nace mata zamuje asibiti tace "A dawo lafiya Allah ya tsare."
nace "Amin." nayi waje su Naseem suka biyo ni suna cigaba da faɗin zasu bini..
Yana zaune a mota yana ganin mu tun kan mukaro ya fito acikin motar.
ihun murna yaran suka sake sukayi gurin sa a guje suna faɗin
"Laa Daddy yazo oyoyo Daddy." ya buɗe hannun sa suka faɗo jikin sa ya rungume su yana dariya tare da bin ko wannen su da sumbata.
na karaso gurin fuska ta ɗaure tamau, yasake yaran yana faɗin
"Kuzo mu buɗe wa Madam mota kada ta gaji da tsayu." yazaga ɗaya barin ya buɗe yadube ni dakyau sannan yace
"Kyakkyawa ta bismilla taho ki shiga." yayi maganar tare da nuna min hanya da hannu yayin da ɗaya hannun sa ke rike da marfin motar.
fuska na yamutsa namatso jikin marfin motar, ganin yana tsaye daf da in da zanbi nashiga cikin motar, sai na ja natsaya tare da naɗe hannaye na a kirji.
murmushi ya yi kana yaɗan ja da baya kaɗan tare da faɗin "Bismillah Madam." baki na taɓe nashige cikin motar da bismilla. yamai da marfin ya rufe.
tuni su Naseem sun shige gidan baya sai tsalle-tsalle suke. yazaga gefen direba ya shiga ya ja motar a hankali yayi hon mai gadi ya buɗe get yasa kai yafita a hankali.
A hankali yake tukin kamar mai tautsayin kasa, yayin da su Nasmah keta zuba masa surutu yana biye musu, lokaci zuwa sai ya juyo ya kalle ni, niko na ɓata rai nayi kamar bana cikin motar.
sai da naji ya gyara parking kafin na ɗago, *HAM'NAS* International Hospital na ganmu ciki.
maganar sa najiyo yana faɗin
"Mushiga kyakkyawa ta ko na sauko na buɗe miki ne?."
tun kan yarufe baki nayi saurin ɓalle marfin motar nafita ina jan karamar tsaki........!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama😇: *HMDH*
*WASA FARIN GIRKI*
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR
17
Yace "Hajiya za'a ɗauko ta amma ba yauba sai bayan ɗan wani lokaci."
Hajiyar takarkata baki tana faɗin
"Aure jibge kayi ne? yo in ba haka ba ace duk girman gidan nan ba rashin ɗaki ba ba komai ba, kayi aure kabar matar ka wani waje bazaka haɗa kan iyalen ka guri guda ba, ko gimbiyar taka ta hanaka kawota gidan ne?."
yace "Hajiya ita kuma meye nata a ciki, ai in da wan da yake son auren nan ma to bayan ta ne, wani ɗan karamin dalili ne kawai yasa yau baza a ɗauko ta ba."
tace "Eh ai dama ita bata laifi badai ta yi sake an yi auren ba ai wayon ta ya kare."
Murmushi Rasheedat data sako kanta cikin ɗakin ta sake dan duk abin da suke a kan kunnen ta,ba farau bane hakan gun Hajiya da dangin ta, a koda yaushe gani suke ta mallake shi sai abin da tace zaiyi, ko wannan auren ma dasuka jishi lokaci guda sunyi matukar murna acewar su yanzu ne zai auri mata ita kam itace mijin shine matar,duk da dai bahaka suka so ba sai dai babu in da suka iya haushi da sanar Rasheedat shi yasa su yin murnar auren nasa. gani suke ta gama mallake sa sai abin da ta ce tahana wasu shigowa suci arziki, ita ba haihuwa ba, Hajiya Karima itace Uwar gidan Alhaji Tijjani Sabil wato mahaifin Ahmad, wacce yanzu yake kallon ta a matsayin uwa,
tun kafin ya auri Rasheedat Hajiya Karima taso haɗa shi da ɗiyar kanin ta wacce take hannun ta suna tare duka da Rasheedat ɗin a gidan mai suna Sakeenat, yaki amin cewa yace sai ƴar uwar sa ta jini,
duk yan da Hajiya Karima takai ga shiga da fitan ta haka Ahmad yaki sam yake kuma Allah bai bata ikon juya shi ba.
karshe dai haka ta hakura badun taso ba, a ɓangaren Sakeenat ma kuwa tana son Ahmad kamar tayi yaya har kuma gobe tana son sa, sabo da shi taki zaman auren da aka mata ko yanzu da take zawarci tana fata da burin mallakar Ahmad, sai dai abune mai wuya dan ko gaisuwar ta baya amsawa...
Rasheedat
ta karaso cikin ɗakin ta dire babban tray da aka shirya musu abincin su ciki, kana tayi musu barka da warhaka, a yatsine hajiya Karima ta amsa bai dame ta ba tana dago wa suka haɗa ido da Ahmad suka sakarwa junan su murmushi.
kana tayi waje.
wayar sa ce tayi kara ya ɗaga kiran sannan ya mike yafita.
Da sauri ya bi bayan Rasheedat dake kokarin shiga corridor dazai sadata da side ɗin ta, ya ruko hannun ta ya janyo ta sukayi gefen sa suka shige cikin bedroom ɗin sa, suna shiga ɗakin ya janyo ta jikin sa ya rungume tare da marairaice murya ya ce
"Wash Kawa nagaji." gemun sa ta ja tace "To yau dai bazan ce ma sannu ba dan yau rana ce ta musamman gajiya dole."
fuska ya marairaice yace "Haka zakice?." tace "Haka na faɗa, muje na tayaka wanka kanwata nazaman jiran ka, dan kasan dai kai zakaje ba dai ita tazo ba."
murmushi yayi tare da shafo gefen fuskanta yace
"Hukuncin da aka yanke min kenan?."
tace "Har ya zartu ma kuwa."
a tare suka saki dariya, nan tashiga taimaka masa yarage kayan jikin sa kana suka faɗa bayi, ta taimaka masa yayi wanka kana suka fito, nan ma ta tayashi sa kaya sannan ta bisa da turaruka masu daɗin kamshi.
gaban wardrobe ta isa ta buɗe ta ciro jaka mai ɗan girma sannan ta rufe ta buɗe ɗaya gefen tashiga ciro kaya tana zubawa cikin jakar,
ido ya zuba mata ganin yan da take aikin zuba kaya cikin jakar yace
"Kawa ina za'a kai kayan kuma?."
bata bashi amsa ba har sai da ta cika jakar tam da kaya kafin ta juyo ta dube shi tace
"Ina zuwa." ta fita jim kaɗan ta dawo da mayafi a kanta
ta ruko hannun sa tare da faɗin
"Taso muje na raka ka duba kagani har karfe 11 saura."
yace "Kawa ina kuma?." tace "Ina kuwa in ba gidan HAMDAH ba ko kasan cewa lokacin ta kake shiga, yanzu haka tana can tana zaman jiran ka."
ido yaɗan waro yace "Shine da wannan katuwar jakar kamar wan da ake kori na."
tace "Eh ayau kam kusan haka din ne."
Ta janyo hannun sa tare da ɗaukar jakar sukabi ta kofar baya,ɗaya daga cikin motacin sa suka shiga ya jasu a hankali suka fita.
a hanya ta sashi ya tsaya ya siya gasassun kaji kafin suka wuce.
suna isa bakin get din gidan yayi hon masu gadi suka buɗe masa, yakusa hancin motar ciki yana dai-dai ta parking suka fito a tare, tana rike da jakarsa inda shi ke rike da laidar gasassun kajin da suka tsiya, suka nufi side ɗin.
Sauko wata kenan daga sama yunwa ta dame ni dan wunin ranar yau bansa komai a ciki na ba,
na shige kitchen nashiga bude buɗe ko zan ga abin da zan sawa cikina,
wani kula na buɗe mai ɗauke da tuwon farar shinkafa mai ɗume, na ɗau plt na saka laida ɗaya, kana na buɗe ɗaya kular dana gani a kusa dashi, miyar agushi ne daya ji busashshen kifi da hanta na zuba akai kana nafito parlour na zauna nasoma ciki.
knocking ɗin kofa akayi har sau uku akai-akai, ido naɗa zubawa kofar da tunanin mai buka kofar da daddaren nan, nai tunanin ko su Talatu ne, na mike a sannu na isa jikin kofar na murza key ɗin tare da buɗo kofar.
da ɗan mamaki na kalli waɗan da ke bakin kofar, Rasheedat ta saki murmushi da faɗin
"Kada ace bacci kike muka taso ki?."
murmushin yake namayar mata ganin yanda take ta yimin magana cikin fara'a.
shiko na tsaye bai yi magana ba amma idanunsa a kaina, ganin yan da ya kafe ni da mayatattun idanun nan nasa sai na saki kofar najuya na koma ciki.
suka biyo bayana, zama sukayi kan kujera in da nikuma na zauna kan hannun kujerar da ke can karshe ina zaman jiran jin abin da ya kawo su da daddaren nan.
Rasheedat ta dube ni fuska ɗauke da annuri tace
"Narako sa ne da kaina na baki hakurin rashin zuwan sa da wuri wlh ba'i ne sukayi yawa sai a hankali, gashi nan na kawo miki shi da fatan za'a kula da shi yanda ya kamata,
to ni bari naje dare yana daɗe yi sai da safen ku Allah ya tashe mu lafiya."
ta mike tare da duban Ahmad tace
"Aboki bani makullin motar na koma."
ido ya waro yace "A daren nan zaki fita ke kaɗai? bazai yuwu ba bari nasa a maida ki."
murmushi tayi tana karɓar key ɗin a hannun sa tace "Babu abin da zai faru da yardar Allah Allah zai tsare, ka mai da ni karamar yarin yace nifa yanzu na girma."
ta kashe masa ido tana kokarin juyawa ta tafi.
nayi saurin mikewa tare da dakatar da ita ta hanyar faɗin
"Da kin tsaya kin koma da shi da zai fi muku."
ina kaiwa nan na juya na haye sama...
Rasheedat tayi murmushi tare da dafa kafaɗan sa tace "Aboki katashi ka bita ka shawo kanta, kasan amarya sai da lallami."
kai ya jinjina yaruko hannayen ta duka biyu yayi kiss ɗin su, kana ya lumshe idanun sa tare da buɗe su a lokaci guda,
ya mike tsaye yace
"Muje a maida ki gida hankali na zaifi kwanciya."
koda suka fita ɗaya daga cikin security gidan ya umurce sa daya mai da ita gida, yana tsaye saida yaga fitar su kafin ya koma ciki.
yana shiga ya rufe kofar side ɗin kana ya haura sama. yana kusa kansa cikin parlour'n sama,
idanunsa ya lumshe tare da jan numfashi ya shaki daddaɗan kamshi mai sanyi da rasa zuciya, a hankali ya buɗe idon nasa cikin kayataccen parlour'n a fili ya furta "Masha Allah."
a sannu yafara taka kafafun sa cikin parlour'n yayin da yake rarraba idanunsa ga kofofin bedroom's ɗin da ke cikin parlour'n,
a sannu ya nufi wasu kofafin bedroom's
guda biyu wan da suke a jere, yasaka hannun sa jikin ɗaya kofar ya murɗa a hankali ya tura kofar, ya kusa kansa ciki.
can ya hangi su Naseem kan gado suna baccin su cikin kwanciyar hankali,
murmushi ya sake a hankali ya karasa shiga cikin ɗakin a bakin gado ya zauna yashafi gefen fuskar ko wannen su yana binsu da murmushi kamar waɗan da idanun su biya, kana ya mike ya daɗa jan bargo ya rufe musu jiki, yafita ya ja musu kofar.
numfashi ya sauke lokacin da yamaso jikin ɗaya kofar da ke kusa da bedroom ɗin su ya tura kofar ya leko kansa ciki,
babu kowa cikin ɗakin sai dai a gyare yake tsaf-tsaf gadon cikin ɗakin yasha shinfi ɗakin sai kamshi yake tashi, shakar kamshin yayi yana mai jin daɗin kalar kamshin da side ɗin gaba ɗaya yakeyi, kuma ko wani bedroom da kalar kamshin da yake tashi.
mai da kofar yayi ya rufe ya juyo ya zuba wa ɗaya kofar dake can gefe ita kaɗai ido.
a sannu ya taka izuwa jikin kofar, sai kuma ya ja ya tsaya na ƴan dakiku kana a hankali ya kai hannun sa jikin handle ɗin kofar a hankali ya murɗa ya tura kofar a sannu ya kusa kansa ciki.
wani irin dogon numfashi yaja yana mai shakar daddaɗan kamshin daya bigi hancin sa...
firgit na mike zaune jin an turo kofa, cike da mamaki nake kallon sa yana tsaye idanun sa a lumshe a sannu yaware idanun nasa a kaina.
A hankali ya soma takowa cikin ɗakin, ina ganin haka na yi saurin zamowa bakin gadon ina binsa da kallon tuhuma, gani ya dumfaroni gadan-gadan yasani mikewa da sauri nace
"Meya kawo ka cikin ɗaki na?, ka ketare tun daga kasa ka hauro sama kashigo min har cikin ɗaki?."
sai da ya matso daf dani kafin yasoma magana
"Hurimi iko mallaki, duk na haɗa yau, babu wani shamaki sakani na da ke meye nayi min wannan tambayar kyakkyawa ta."
yayi maganar yana kokarin ruko hannuna, nayi baya da sauri cikin ɗan ɗaga murya nace
"Kafita min a ɗaki Malam."
ido ya zuba min babu ko kakkauta wa yana bin jikina dawani irin kallo, da sauri na kalli jikina, riga da wando na bacci ne a jikina rigar mai tsiririn hannu irin mai gidan bra ɗin nan, mai tsamtsi ne sosai ya bi jikina ya lafe.
kan na an kara har ya matso daf dani har jikin mu na gogan juna, baya nayi da sauri na matsa baya kasan cewar ina tsaye daf da bakin godo ne sai ji na nayi na zube kan gadon.
da sauri na mike zumbur na saka hannaye na bibbiyu na ture kirjin sa na bi gafen sa nasa kai zan wuce,
sai ji nayi ya cafko hannuna ya janyo ni jikin sa har sai da na garu da jikin sa,
"Ka sake ni idan ba haka ba wlh sai nayi maka abin da baka taɓa tunani ba."
ɗan rankwafowa yayi saitin fuskata a hankali ya furta
"Za ki sa a zo a fitar dani ko? wani sam bazai iya ba kin taɓa ganin in da aka fidda miki ɗakin matar sa."
sai kuma ya saki murmushi mai sauti a sannu ya sauke yatsar sa kan baki na yana ɗan zagaye lip ɗina, sai ya lumshe idanun sa a lokaci guda ya buɗe yace
"Suna da kyau sosai gwanin ban sha'awa."
yayi maganar tare da ɗan matsa laɓɓana,
da sauri na bige hannun sa, ina wasa masa harara.
na fizge jikina da sauri na nufi kofa na buɗe nafita,
ɗakin su Nasmah na shige na maida kofar na rufe tare da murza key, nahaye tsakiyar su nayi kwanciya ta.
A ɓangaren Ahmad kuwa bayan ta yabi da kallo har ta fita, kana ya sauke numfashi a sannu ya masa bakin gadon ya zauna yakai tsawon minti 20 kafin ya mike yafita a ɗakin, kasa ya sauka ya ɗau jakar kayan sa ya dawo dakin,
yabuɗe jakar ya ciro jallabiya mara nauyi ya tuɓe kayan kijin sa ya saka sannan ya haye gadon ya kwanta tare da janyo pillow ya rungume a jikin sa yana mai shakar daddaɗan kamshin dake tashi daga jikin pillow'n zuwa gadon gaba ɗaya
a fili ya furta
"Yarin yar akwai son kamshi."
sai kuma yasaki murmushi yana daɗa rungumar pillow'n, ya ɓata tsawon lokuta masu tsawo kafin bacci yasami nasarar ɗaukar sa.
Washegari kiran sallar asuba a kunnen sa ya mike yashiga bayi yayi al'wala yafito da ɗan sauri ya fita dan lokacin ana kokarin tada ikama, har zai wuce yadawo kofar su Naseem ya bubbuga, kamar a mafarkk najiyo buga kofar da ake na mirgina cikin magagin bacci na ɗan ɗaga murya nace
"Waye?."
yace "Kitashi kiyi sallah lokacin salla yayi."
tsaki naja jin muryar sa dan ni nagama mance wa ma da wani cikin gidan, najuya na gyara kwanciyata na mai da kaina na cigaba da bacci na, dan ina fashin sallah...
Bayan an idar da salla Ahmad ya iso gurin Bappa dake zaune sakiyar masallacin yana koyawa masu aiki da security karatu, shima yaɗau Kur'ani akaci gaba da yi da shi, sai da guri yayi haske sosai kafin Bappa ya tashe su, kowa yafita zuwa gurin aikin sa.
Ahmad ya gyara zaman sa yashiga gai da Bappa ya amsa kicin kula da sakin fuska sannan ya ɗaura da faɗin
"Ashe dai anan ka kwana." kai Ahmad ya sunkuyar yace "Eh." Bappa yace "Masha Allah to ya cikin gidan?."
yace "Lafiya lau alhmdllh."
ɗan shiru Ahmad yayi kansa a kasa, Bappa ko farin ciki ne fal cikin zuciyarsa da yau HAMDAH ta kasance matar aure yana da tabbacin daɗa samin nutsuwa cikin rayuwar ta, kuma yana hasashe da sa ran mijin datake aure bazai hofantar da ita ba.
Ahmad yaɗan muskuta har lau kansa a kasa yace
"Da jiya naso mutafi can gida na da ita amma sai nayi tunanin hakan ba mai yiwuwa bane."
Bappa yace
"Gaskiya kam yiwuwar hakan abune mai wuya dan nasan HAMDAH bazata yarda ba, sai dai kawai karika zuwa nan ɗin, a hankali idan ka shawo kanta sai ku koma can ɗin."
kai ya jinjina shi kansa yasan hakan shiya sa ma bai fara tinkatar ta da wannan batun ba.
ganin yayi shiru bai kuma cewa komai ba sai duba agogo yake, yasa Bappa cemasa ya tashi yaje dan ya fuskanci nauyin sa yake ji.
Bappa ya daɗa jinjina girman soyayya da aure, duba da babban mutum kamar Ahmad Tijja Sabil dayafi karfin komai sai gashi yana rusunar da kai da kuma girman sa akan mace.
A hankali nayi mika tare da yin salati na mike zaune ina mussuke ido,
kallon gefe da gefe na nayi, su Naseem sai sharar baccin su suke.
a hankali na zamo bakin gadon na mike nashiga bayi, wanka nayi sosai kana na janyo towel daga cikin towel ɗin wankan su, buɗe towel ɗin nayi ina binsa da kallo, bashida wani girma sosai kuma a hakan duk shine babba cikin sauran towel ɗin da suke jere a