Showing 18001 words to 21000 words out of 125808 words
kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka ɗunguma.
yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa daɗan rata da gidan da muke ciki, sannan muka wuce wasu unguwanni biyu duk kanin su da gidaje ɗai-ɗai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa.
daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga can nahango ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi ɓaro-ɓaro.
idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na buɗe,
Mun zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,
daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu ɗauke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu ɗauke da sunan ( *HAM'NAS International HOSPITAL* )
suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.
daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.
Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faɗa min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..
Damin Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,
yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,
haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije ɗauko su nace yace musu kada suzo da komai, dan cikin side ɗin dana matsawa Bappa sai ya zabi ɗaya daga cikin side ɗin gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side ɗin.
hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika ɗaukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.
a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa.
nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daɗi matuka, sai narika jin su tamkar wani ɓari ga ahalina,
ganin su yaɗan rage min kewa da begen family na.
Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka ɗauki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai ɗaya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, ɗaya motar kuma mutane huɗu ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.
mun isa cikin garin Kano da misalin ƙarfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,
gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.
bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka ɗau hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina.
Sati biyu muka ɗauka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karɓa mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,
lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin ɓari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,
cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar ƙwaƙwalwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faɗin
"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na".
kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.
cikin ɗaga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace
"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!".
gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki ɗaya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,
Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba ɗaya.
A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe.
numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faɗin
"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".
yadubeni da kula yace
"Sannu ko HAMDAH".
kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.
"Zai bari insha Allahu".
yayi maganar tare da buɗe tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya goma na farkon surar haɗe da ayatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka.
Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno da Mama mai awara, da sauri nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba ɗaya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma wata maganar naji na kasa, har kuma yanzu ina jin yanayin...
da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki.
Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin ta yayi masifar tashi, yace ta taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da ɗan karamin ƙwarya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace
"Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da shi sun mance cewa Allah baya bacci".
Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji".
ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci yaɗauke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a ɗaya ɗakin dake kusa da nawa.
washegari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau...
muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side ɗin suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da faɗin
"Allah Inna wuro bakuga abubuwan yan da sukayi kyau ba kai har da garin da ban taɓa zuwa ba".
nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan
Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira....
bayan kwana biyu
Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka zo su da wasu mata guda biyar sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki,
mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin waɗan da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan ɗauke su ai ki irin gidajen masu kuɗi ɗin nan, a cikin su na zaɓi guda uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su.
ɗaya na ɗauke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side ɗin,
na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma ɗayar na turawasu Inna wuro ita zata rika kula da tsaftar side ɗin su dakuma girkin su.
nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba ɗaya.
mun zauna da su na ɗan wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana.
Haka rayuwa tacigaba da tafi, tuni akayi bikin buɗe masana'antu da masallatan nan manyan shuwagabannin Nigeria sun halacci torurrukan sun kuma bada gudummawar su kwarai da gaske wajen ganin an ɗibi ma'aikata masu inganci.
Bayan wani lokaci
Tuni aka damkamin ragamar duk wasu kaddarori na ni nake bada umurnin ayi da kuma kar ayi, har kuma yanzu muna tare da jagororin nan su suke sanya ido kan ganin komai yatafi dai-dai.
tuni nasa aka baiwa Fatu uniform a ɗaya daga cikin makarantu na, dan dama acan rugar ma tana karatun ta tacigaba a nan.
Zaune nake a parlour ina dudduba jerin sunayen mata da matasan da nasa a ɗiba, a karkashin paudasion ɗina domin basu tallafin wasu kuɗaɗen da zai jamusu jari domin dogaro da kai na tura da kuɗaɗen tallafin izuwa asusun *HAM'NAS* paudasion.
a hankali na mike tsaye tare da yin mika haɗe da salati, wayoyina na tattara haɗe da sabuwar system ɗina, na haura sama,
kan bedside na ajiye su kana na haye gado dan bacci nake ji, ina so nayi baccin kafin su Naseem su shigo dan suna can side ɗin su Bappa.
har na kwanta na tuna da akwai maganar da nake so muyi da Bappa kan wani Company na murza karfe da ake gina shi a Lagos,
mikewa nayi na fita dan ina so muje ziyarar gani da ido acikin satin nan.
da gudu Nasmah ta shigo tana faɗin
"Mommy kin ga Naseem ko jai camin jiji".
Naseem shima dagudun yashigo yana binta da abun yana dariya, Fatu na biye da su tana dariya da faɗin "Naseem kabari kar ka sa mata".
da sauri nakarasa sauka kan step na rungumo Nasmah dake falfala gudu kamar zata kife kasa nace "K.......!�?
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:54 - Ummi Tandama😇: "Kai Naseem me zaka sa mata kai ka bari zata faɗi fa kabari."
nayi maganar ina ɗago Nasmah cak na rungume ta a jikina, shiko dariyar yake yana matsowa in da muke ya ɗaga hannun sa sama tare da yin ɗagelgel da kafa, yana washe baki,
na ce "Idan ka zo nan sai na mare ka, zo kagani zo ka samata kagani,
dariya sosai yarika yana faɗin
"Mommy dan tamata ne dan ta mata wannan."
"To ka samata kagani sai na maka bulala."
kiran Talatu mai kula dasu nashiga yi ina faɗin
"Talatu zo ki kaishi wa ɗawisu ta cakwaɗe shi tun da dai shima sa mata jiji zaiyi."
Talatu ta iso da sauri tana faɗin
"Ayi hakuri Hajiya kar a kaishi wa ɗawisu zata cake shi, zo nan Naseem kada kasa mata ko, so kake a kaika wa ɗawisu ta cake ka,zo ko ɗan lele na mene ne zaka sawa Nasmah ɗin?."
ɗan karamin tafin hannunsa da ya dunkule ya buɗe kaɗan ya nuna mata kana ya kuma dun kulewa yana cigaba da dariya, "Lalala shine zaka sa mata?."
cewar Talatu tayi maganar haɗe da dariya, kai ya gyaɗa yana washe baki, duban Fatu nayi ina faɗin
"Wato Fatu keda Naseem kuke sawa Nasmah ta abin tsoro ko? to bazata sake wasa da ku ba."
dariya Fatu tayi tare da faɗin
"Allah Adda HAMDAH kin ga bansan in da yasamo ba kawai ganin sa nayi ya shigo da shi a hannunsa,malam buɗe takarda ne fa."
"Au malam buɗe takarda ne ya ɗauko shine yake so ya sa mata to bari yagani sai an kaishi wa ɗawisu shima, shine baki karɓa ba ko Fatu kika tayashi tsoratar da ita."
"Allah Adda HAMDAH binshi nake na karɓa shine yagudu."
Talatu ta ɗauke shi tabuɗe hannunsa taciro abun tana faɗin
"Kawo shi nan a yasar da shi kada ka saka mata kaga tana jin tsoro, kaima kada ka sake ɗauka a hannun ka."
tana rike da hannunsa tafita waje ta yasar da shi kana suka dawo ciki.
karaso wa cikin parlour nayi na zauna kan kujera tare da zaunar da Nasmah kan cinya ta, na dubi Fatu nace
"Fatu Bappa na ciki ne?."
tace "A'a yafita". sai kuma ta turo baki gaba tare da faɗin
"Adda HAMDAH nifa wannan sunan Fatun nace ki dai na faɗin shi, Fatun nan fa a can Ruga ne fa ake kiran Fatun nan tun da yanzu mutum yazo birni har yanzu ayi ta ce mishi wani Fatu, gaskiya Adda HAMDAH ni wlh na canza suna Fatu ai duk su Inna wuro ne suka wani lankwasa min suna yaya Mahmoud dake shi a birni yake ai Fatima yake cemin,haka jiya wata ƴar ajin mu tana ta min dariya wai ni Fatu, aradun Allah na canza suna ko a ajin mu ma na faɗa na canza suna".
dariya muka tuntsire da shi, Talatu tace
"To Fatu man yan gari me kike so ace miki kenan?".
"Ai sunana da yawa masu daɗi ma, Nana, Fatima, Faɗimatu, Faty Zarah duka gasunan masu daɗi sai a rika cewa mutum wani Fatu kamar rugo".
nace "To lallai kam kamar kin sani da ma kam wannan sunan bai dace da ke ba yanzu dai kawai Faty za'a rika ce miki."
tace "Yauwaaa Adda HAMDAH Faty wlh yama fi amma kuna ta cemin wani Fatu kamar rogo".
"Hhhhh Faty kenan Allah bakida dama".
tace "Yauwa Adda HAMDAH gashi kin iya faɗin sunan dai-dai mai daɗi".
kai kawai na girgiza ina dariyar ta.
tace "Zo muje muyi wasan mu o Nasmah."
nace "O'o kuje bazata biku ba kuje kusata kuka bazata biku ba kam kutafi ku."
"Allah bazan barshi yasa mata ba". fuskata na kawo dai-dai fuskar Nasmah nace
"Zaki bisu?". kai ta gyaɗa "To muje daga gun na duba ko Bappa ya dawo".
nafaɗa ina mikewa na direta kasa tare da ruko hannunta muka nufi side ɗin su Inna wuro.
a parlour muka tadda Inna wuro Bappa bai dawo ba sai na zauna muna ɗan taɓa hira da ita.
muna nan zaune har Bappa ya shigo yazauna muka cigaba da hirar da shi, acikin hirar nake yi masa maganar yace kwarai kuwa ya dace kam aje domin a ganewa ido, in yaso satin sama sai a je, duk da akwai idanu da yawa akan lamarin. nace "Toh Allah yakai mu."
muna zaune sai ganin Naseem mukayi ya kin kimo school bag ɗin Faty, a tsakiyar parlour'n ya zauna ya tuttuɗe littatafan cikin jakar kasa ya ɗauki littafi guda ya buɗe yana ta gwalaɓe wai shi yana karatu.
dariya duka muka saka, Faty ko da gudu ta mike taje ta tattari litattafan ta tana ta faɗin
"Kai kasan meye a ciki ka iya karatu ne".
Inna woro tace "To ai karatun yake baki gani ba".
cikin muryar dariya nace "Um karatu yake ko gwalaɓe har da wani mike kafa kamar mai karatun gaskiya."
"Ah to gaskiya za'a saku a makaran ta tun da har ka iya ɗauko littafi kazauna ka buɗe kana karatu".
cewar Bappa yana yi masa dariya.
"Wlh Bappa nima dama ina so a turasu makaranta amma a sona sai sun cika shekara uku da rabi, amma gashi nan bakin su ya buɗe kawai sutafi yanzu."
Bappa ya jinjina kai kana yace
"Kwarai kuwa ya kama ta kam tun yanzu, tun da ga bakin su nata kan buɗe wa a kai su makaranta yakarasa buɗewar a can"....
A cikin satin akayi musu komai da komai nashiga makaranta, sai dai wata makarantar daban badaga cikin nawa ba, dan *HAM'NAS* International School Of Science Of Technology. suna da nisa saka nin mu, duk da dai shima makarantar da aka sasun yana da ɗan nisa sai dai baikai su nisa ba,
Islamiyar da a kasasu kuma anan unguwar tamu yake.
ranar da zasu fara zuwa kuwa zo kaga murna wajen su, da misalin karfe 7 na safiya Talatu taga ma shirya su tsaf, Zulai kuma ta shirya musu lafiyayyen breakfast ɗin su.
ina rike da hannun su muka fito in da Talatu ke biye da mu rike da school bag ɗin su da baske, parking lot muka nufa, tun kan mukaraso Yakubu direba dake goge mota yayi hanzarin buɗe marfin motar, cike da ladabi yaɗan duka yana faɗin
"Barka da safiya Hajiya."
"Yauwa barka." nafaɗa cikin ɗan jin nauyin yan da suke yimin idan zasu gaida ni, duk kanin ma'aikatan gidan sun girme min nesa ba kusa ba wasu ma sun haife ni sun juya,nakan ji nauyi a duk san da sukayi min irin wannan gaisuwar.
Nasmah naɗaga nasaka ta cikin motar, Naseem kam cemin yayi shi da kan sa zai shi, Talatu tayi dariya tana saka musu school bag ɗin cikin mota tace
"Naseem iyayen rigima kai bazaka bari a saka ka ba da kan ka zaka shi ka girma ashe".
kai ya gyaɗa yana gyara zama tare da faɗin
"Eh nagima da kaina naciga."
tace "To babban zance ke kuma Nasmah yaushe zaki girma?". Nasmah ta cuno ɗan karamin bakin ta gaba tace "Gobe dan gima ai".
murmushi nayi tare da shafa gefen suskar ta nace
"Au ke sai gobe zakiyi girman naki?". kai ta gyaɗa tana murmushi, kansu na shafa dukansu nace
"To sai an dawo ayi karatu sosai kunji".
sukace to. direba yaja mota ina ɗaga musu hannu suma suna daga min
mai gadi yawangale get suka fita..
Kwana uku kullum cikin ɗoki suke zuwa makarantar ranar na huɗu kuwa ɗoki tafara kare wa, ina kwance sai ga Nasmah ta shigo da gudu ɗaure da ɗan karamin towel ɗin wankan su tahaye gado ta ɓoye a baya na tana faɗin
"Ni bajan je school in ba."
zanyi magana sai ga Naseem shima da wandon uniform ajikin sa babu riga, sai muryar Talatu daga bakin kofa tana faɗin
"Kai Naseem kazo nakarasa saka maka kayan".
mikewa nayi zaune ina faɗin
"A'a yaya ne tsaya mana". ai kan kace me shima ya ɗale gadon
cikin cuno baki gaba Nasmah ta daɗa laɓewa jikina tana faɗin
"Ni Mommy bajan je School in ba".
ido na waro ina duban Naseem shima da yake faɗin
"Nima bayan jeba".
kai na langwaɓar gefe nace
"Oh yanzu wa School ɗin kuke gudu ne, bazaku je ba kuma, yaushe ne kuka fara zuwan da har zaku fara fashin sa?, kuna