Showing 78001 words to 81000 words out of 125808 words

Chapter 27 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

456

hango ƴar karamar ramar da yayi, ta dube shi da kyau sannan tace
"SALEEM baka da lafiya ne kam?."
kai ya girgiza batare da yayi magana ba.
tace "Ai ho nazaci baka da lafiya ne dan naga kaɗan faɗa kaɗan."
Abba yace
"Wata kila hidimar office ce ta sashi a gaba kin san shima yana sa haka idan ka rasa nitsuwar ka."
Ummi tace "Haka ne Allah yasa mu dace."
suna nan tsaye motar Abbu yashi gidan, koda ya gyara parking yafito duk kanin su gaishe sa sukayi ya amsa, in da ya amsa gaisuwar SALEEM a sama-sama kana yayi gaba Abba ya bi bayan sa.
SALEEM kuwa motar sa ya shige yabar idan, Ummi kuma ta wuce side ɗin ta.

Parlour'n da su Abbu suke zama suɗan tattauna nan suka wuce, suka zauna suna ɗan tattauna lamuran su.
Abbu ne yamai da hankalinsa kan TV yana sauraran labaran almuru da ake gudanar wa a wannan lokacin, in da ake sanar wa kan manyan masu kuɗi da suke bada taimako da tallafi ga marasa karfi, jinjina kai yayi jin ta in da taimakon ya fito yace
"Kai wannan matar Allah dai ya saka mata wlh tana da kokari sosai, ko wancan satin ma naji kalar taimakon da tayi na dubban nin ɗarurruwan kuɗi ga mara sa karfi,
in dai za'a cigaba da samin irin su a Nigeria ai kasar mu zata cigaba ba ɗan kaɗan ba,
dubi yan da take ta bada mai kamar kyau ta a cikin gari Allah dai ya kara mata buɗi."
Abba ya amsa da "Amin amin ai Yaya ko yanzu ma bakaga layin da ake yi a gidajen manta ba irin su kuma kullum buɗe suke gani ba ci baya ba."
Abbu yace
"Kwarai da gaske Allah ya daɗa buɗa mata."
hirar suka cigaba da yi har sai da aka kira magriba kafin suka nufi masallaci.
bayan sallar isha da Abbu ya tafi side ɗin Mamie hirar matar yayi ta mata da irin kokarin da take,
sukayi ta sanya mata albarka da dukiyar ta.....)





Abuja


Zaune muke a parlour ni da su Naseem Aunty Rasheedat tayi sallama da kaya niki niki a hannun ta, Zulai da Talatu na biye da ita ɗauke da wasu kayan,
ta Suka dire shi sakiyar parlour,
na dube ta daɗan mamakin ganin ta da manyan laidadi nace
"Sannu da zuwa Aunty Rasheedat."
tace "Yauwa HAMDAH ya nauyin jiki?."
murmushi kawai nayi dan nidai bana jin wani nauyin jiki cikin da bai girma ba ake tambayar nauyin sa.
zama tayi gaban kayan kana ta shiga ciro su cikin manyan laidodin kayan baby ne kala-kala a ciki haɗe da kayan wasa,
da gudu su Nasmah suka je in da take Naseem daya ɗago wani abin wasan baby yace
"Mamy kin kawo mana ne?."
Kuma tun sa ta ja tace
"A'a zan kawo muku naku wannan na baby'n ciki ne, baku san Mommy zata samo mana yaro ko yarin ya ba."
tsalle sukayi cike da murna suna faɗin
"Yeee Mommy zata samo mana yaro."
Nasmah ta dubi Aunty Rasheedat ta dafa kafa ɗar ta tace
"Mamy yaushe Mommy zata samo mana?."
yatsun ta shida ta nuna mata tace
"Saura wata haka ta samo nama."
tsallen murna tayi tazo in da nake da gudu tace
"Mommy guda haka zaki samo mana yaro."
ido na waro ganin ta ɗaga yatsun ta biyar tana yimin nuni da su nace
"Akuya ce ni."
dariya Aunty Rasheedat da Talatu da Zulai sukayi, Talatu tace
"Ai ba akuya kaɗai suke haifan biyar ba idan Allah ya nufa sai kiga an haifo biyar ɗin."
kai na girgiza nace "Ba amin ba wlh."
dariyar suka kuma.
Aunty Rasheedat tace "Muna so ko goma ne ma Allah yakawo su masu albarka."
ido na kuma waro wa ina faɗin
"Lallai ma."

Ɗakin kayan wasan su Naseem tasa su Sulai suka kwashe kayan da tazo dashi, suka kai cikin ɗakin suka jibge shi a gefe.


Bayan wata ɗaya.........!






Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: 27





Tun daga ranar da Ahmad yasami labarin ina da ciki, bai sake barina nayi wani abu da kaina ba.
ko wan ka baya bari na nayi shi yake yi min da kansa, ko naki nace ya bar ni nayi da kai na sai ya ce
bai isa na janyo masa a sara ba, shi da kan sa zai min.
koda six yake da ni a hankali yake bi da ni.
tun da Dr ya bashi shawarwari game da cikin kan abincin da zan rika ci,sabi da lafiya ta da ta abin da ke cikin. shike nan ya hana ni sakat da cin abinci.
a rana sai yabani naci abinci kusan sau goma, dan yanzu idan ya bani naci anjima kaɗan zai kuma kara min.
yanzu kullum muna tare da shi ko yana gida na ko baya gida na,
idan yana gidan sa da sassafe zai zo bazai koma ba kuma sai dare.
washegari kuwa zai kuma dawowa da sassafen...


Kwance nake a kan dago na tasa ɗan karamin ciki na gaba wan da yanzu watan sa huɗu kenan.
idan bama kasan da cikin ba, bazaka ce da wani halitta cikin cikina ba, dan bai wani fito sosai ba, bakamar irin cikin su Naseem lokacin da ya kai watanni huɗu ya fi sosai kamar wan da yafi watan nin sa ba.
Ahmad ne ya shigo ɗauke da plt a hannunsa, perpesun kayan ciki ne haɗe da ganyen ogu da dafeffen kwai a gefe, wanda yasha kayan kamshi da na yaji sai tashi da kam shi yake,
ya dire plt ɗin saman table kana ya hayo gadon ya zauna ya tankwashe kafafun sa a gaba na yashafo fuskata yace
"Kyakkyawa ta taso kici perperun gashi na ɗebo miki."
fuska na ɓata nace
"Ni na koshi ba ɗazun nan ci ba, ni bana jin yunwa yanzu."
ido ya waro yace
"To ai ba sai kinji yunwa ba, bakiji abin da Dr yace ba kirika cin abinda zai kara miki jini da kuzari da lafiyar baby na ba ga perpesun can cikin tukunya ko kwata baki ciba, kuma yanzu nasa Zulai ta kuma girka miki gwaten wake da hanta."
ido na waro nace "Nayi yaya da shi sauran perpesun ma kaje ka basu su ci ni nagaji da ci, kullum-kullum kawai mutum yayi ta ci."
yace
"Dan Allah ki taimake ni kitashi ki ci,cin waɗan nan abubuwan fa sune samin lafiyar ki data baby na, so kike a sami wata matsala? dan Allah ki tashi ki ci kada yayi sanyi."
ya saka hannu ya ɗago ni, ya tallafo ni ya ware kafafun sa ya sani sakiyar cinyar sa, kana ya mika hannu ya ɗau plt ɗin yasaka shi gabana, ya ɗibo perpesun a cokali zai kai bakina.
karɓi cokalin nace
"Ni zan ci da kaina." yace "To ci
maza dan Allah ki cinye duka."
nace "To Allah kaɗan zan ci dan bana jin yunwa."
yace "To ci dai."
a hankali nasoma ci, ganin na fara ci sai ya daɗa gyara zaman sa da kyau, a sannu ya tura hannunsa cikin riga ta ya kife hannunsa kan ciki na, wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a hankali yashiga shafa cikin.
bai fi cokali biyar na ciki ba nace nakoshi.
da sauri yace "Please kyakkyawa ta kiɗan kara kaɗan."
nace "Allah nifa na koshi."
duk yan da ya matsa kan na kara ko kaɗan ne naki daya masa sai na sa masa kuka, ai da sauri ya rungume ni yashiga rarrashi na..

Washegari tun da sassafe ya ɗaga ni da kyar na buɗe idanuna dan bacci ne fal a ciki,
yace "Tashi muje kiyi wanka mutafi asibiti yau zaki fara awu, dan likita yace cikin na cika wata huɗu yakamata ki fara yin awu kin ga yau Monday dai-dai kenan."
fuska na ɓata nace
"Ni bacci nake ji kabari ba yau ba."
da sauri yace "A'a ina, duk da dai baccin da awun duk suna da amfani amma dai muje a duba lafiyar baby in mun dawo sai ki cigaba da baccin kinju kyakkyawa ta."
ya karashe maganar da tsi
gar rarrashi.
kai na gyaɗa masa a hankali.
murmushin nan nasa mai narka zuciya ya sakar min kana ya sauke bakin sa kan goshi na ya manna min kiss,
idanuna na lumshi tare da kuma buɗe su, ya ɗago yana kallon fuska ta a hankali ya furta
"Ina son ki kyakkyawa ta."
idanuna na kuma lumshe wa a lokaci guda na buɗe, tabbas na gama yarda da son da yake yimin a koda yaushe ina hango sona acikin kwayar idanunsa.
idanunsa cikin nawa cikin sanyin murya yace
"Yaushe zaki faɗa min kema kina so na da bakin ki?."
kasa nayi da nawa idon batare da nace komai ba.
murmushi yayi yace "Ko a iya haka ma na gode."
duban sa nayi da fuskar tambaya jin ya faɗin haka.
murmushi ya kuma tare da ɗaga min gira kana yace
"A faɗa min ɗin ne dai ajin ya hana amma gashi nan ina hango shi."
yasa yatsar sa karkashin idanuna.
kai na nayi saurin kawar wa tare da yunkurin mike wa, ƴar karamar dariya yayi ya taimaka min na mike tsaye yayin da ya soma zolaya ta.
"Ajin nan ya ishe ni haka a ajiye shi a gefe a fito fili a faɗa min ana sona, tun kafin ajin ya tsinke dan wata jiya ta tare ni a hanya tace tana sona, nace ta bari tukun da wan da nake so idan bata ce tana sona ba zan zo na amshi soyayyar ta."
baki na taɓe dan yanzu na gama karantar kalar zolayar sa nace
"Ayya ai da ka amince mata kawai."
da sauri ya leko fuska ta yace
"To ai ke nake jira ƴammata idan baki faɗan kina sona ba sai na koma gurin ta."
"Yi maza kaje ka sanar mata kada ka maka anan."
nafaɗa ina kokarin wuce sa, da sauri ya ruko ni yace
"Bari dai na ɗan kara jira tukun."
ya janyo hannuna muka shiga bayi.
bathtub ya cika da ruwa mai ɗumi,
kana ya tuɓe min kayan jikina, na shige ciki na zauna ina mai jin daɗin ruwan, na lumahe idanuna.
da sauri na buɗe idanuna jin motsin sa cikin ruwan sai ganin sa nayi shima a tuɓe,
ya ɗau sosa da sabula yashiga wanke ni shima yana wanke jikin sa a haka akayi wanka,
kana ya ruko ni muka fito bedroom,
koda nazo sa kaya hana ni yayi sai da yagama sumbatar ciki na kafin ya saka min da kan sa.
muna gama shiri muka fito muka dadda an gama wa su Naseem shirin School.
a saman dinning duk muka yada zangon mu, sai da ya haɗa musu abincin da duk sukace suna so kafin ya juyo kai na.
perpesun naman zabbi ya zuba min haɗe da tea mai kauri yana kokarin zubo wani abun nace masa
ya isa wannan ɗin ma ba iya cenyewa zan yi ba. ciki na ya shafo
yace "Yanzu fa zaki fara kamata yayi ki fara da mai yawa."
duban su Naseem yayi yakamo kumatun su yace
"Kanin ku yakusa isowa Yaya Naseem da Aunty Nasmah."
washe baki sukayi cike da jin daɗi Naseem yace
"Daddy ina kanin?."
ciki na ya shafa yace "Ya na nan yakusa fito wa."
da sauri Nasmah ta mike tazo kusa da ni tana kokarin jan riga ta sama.
hannunta na bige nace
"Ke meye haka?."
tace "Mommy danga kanin ne fa."
fuska na ɓata nace "Ka dani ko."
dariya yayi sosai kana yaɗan sakaita dariyar, ya dafa kanta yace
"Zaki gan shi?." kai ta gyaɗa tana washe baki.
yace "To ba ri ki ganshi."
juya kujerar da nake yayi yadurkusa kana ya saka hannu yana kokarin jan rigata sama, nayi saurin rike hannunsa nace
"Me ye haka?." juya hannun nawa yayi yarike cikin nasa kana yajan je rigar da ɗaya hannunsa, yace
"Kibar yara suga ɗan uwan su."
tafin hannunsa ya kife kan cikin yana ɗan shafawa yace
"Nasmah zo ki gani ga kaninku a nan yaron yana nan a nan."
dariya sukayi har suna rige-rigen
taɓa cikin.
Naseem yace
"Daddy ni ban ganci ba."
yace "Yana cikin ciki yakusa fita ku ganshi."
sallen murna suka yi suna faɗin
"Ye damuga yaro, Mommy data samo mana yaro."
kafa na shiga bubbugawa a kasa nace
"Kuma na fasa cikin abincin."
da sauri ya saki rigar yace
"Yi hakuri kyakkyawa ta ci mu tafi o."
sai da yayi ta lallami na kafin na soma ci.
hannu ya saka muka ci tare muna ci yana karawa da dabara yayin da yake ta jana da wasa har naci da yawa sosai.
bayan mun gama muka fito waje in da Talatu ke biye da mu rike da school bag ɗin su.
ko da akazo shiga mota dirjewa yaran sukayi suka ce sam moton Daddy'n su zasu shiga, fuska na ɗaure nayi musu tsawa nace
"Maza ku shige kusha mota kutafi so kuke kuyi latti."
da sauri yace
"A'a a'a kyale su kushiga muje, Talatu sa musu jakar su cikin mota."
da sauri tace to.
ya buɗe musu motar suka shiga, Talatu saka musu jakar su cikin motar,
kana ya buɗe min nima na shiga, ya zaga gefen direba ya shiga ya ja motar, mai gadi ya buɗe get muka fice a gidan..
sai da yafara bi ta makarantar su da kansa ya sauka ya ruko hannunsu ya shiga da su cikin makarantar kafin ya fito muka nufi asibiti.

Muna shiga cikin asibitin batare da ɓata lokaci ba aka gama kimsa mana komai,
koda nazo shiga ɗakin awu tare da shi muka shiga, yana tsaye yana kallon komai, idan yaga nurse ɗin taɗan danna cikin sai yace wai tayi a hankali kada a sami matsala, a haka a ka gama muka fito muka nufo gida.

Tun daga lokacin idan wata ta zagayo lokacin zuwa awu yayi da shi muke zuwa kuma yana tsaye za'ayi komai....


Haka rayuwa yaci gaba da tafiya,
sosai Ahmad ke kula da ni baya kaunar yaga wani damuwa ko ɓacin rai tare da ni, bazai taɓa samin sukuni ba har sai yaga ya gusar min da damuwa ya sanyani farin ciki....
a yanzu cikina watan sa 7 yafito ɗas da shi, haka zai tasani gaba ya tuɓe min riga yayi ta kallon cikin, yana ganin in da yake motsa wa, yayi ta sumbatar sa, idan nace ni na gaji ya kyale ni.
sai yace ai ba da ni yake ba da babyn sa yake, wai yana mika masa gaisuwa....

Zaune nake a parlour Inna Wuro tashigo rike da manyan kofuna guda biyu, ta iso ta dire su a gaba na tazau na nata faɗin
"Sannu HAMDAH ya nauyin jiki." murmushi kawai nayi. ɗaya kofin ta buɗe ta miko min tace
"Karɓi kisha maganin zaki ne dana bayamma zai taimaka miki sosai."
nace to na amsa nasha da ɗan yawa ta karɓa sauran ta mika min ɗayan shima na sha.
ganin Ahmad ya shigo yasa ta mike wa tana faɗin
"Anjima ki kara sha shi zai zamo ruwan shanki za'a kawo miki wani anjima."
nace to
ya karaso ya gaishe ta ta amsa tana fita daga parlour'n.
ya zauna gefe na tare da ɗaga riga ta sama ya sumbaci cikin kana ya ɗago yana faɗin
"Mene ne Innar ta kawo miki shine ba tayi."
nace "Ɗauka ka sha." buɗe marfin kofin yayi yaɗan kai bakin sa ya ɗan ɗana yayi saurin aje kofin yana yamutsu fuska.
dariya na yi nace "Ka kara mana."
yace "A'a ya ishe ni, amma meye wannan ɗin?."
nace "Maganin zaki ne da na bayamma."
yace "Meye su ɗin."
nayi masa bayani ta yanda zai fahimta.
yace "Oh to karɓa ki kara sha, ai naji tana cewa anjima ki kara sha shine ruwan shan ki."
fuska na ɓata tare da make kafaɗa nace
"Ba yanzu nasha ba."
yace "To an jima kaɗan zaki kara."
nace "To kabari anjiman yayi mana."
yace "To ai gara dai na tuna miki tun yan zu kar anjiman yayi kice da saura."
dariya nayi ina faɗin
"Ai irin anjiman ka ne yanzu sai kace yayi."
shima dariyar yayi yace
"To shike nan a saka time kada lokaci yayi kice bai yi ba."
nace "Eh a saka." yace "Bayan minti 5."
"Tab banyar da ba yayi kaɗan."
"To na kara biyar a kai."
nace "Naki wayon." yace "To ashirin yanzu kam ba kankari."

Ai kuwa duk bayan minti 20 zai sani na sha, ganin ya matsa min sai na gudu sashin su Inna Wuro.
har can ɗin ya bini da kofunan yace wa Inna Wuro ta kara maganin wannan ya kusa kare wa.
nace
"Allah Inna Wuro kar ki kara ni nagaji da sha tun ɗazu yake ta bani."
yace "Ina ance yazama ruwan shan ki ne."
"Shike nan shan ruwan babu adadi ni ciki na zai fashe."
Inna Wuro tayi dariya tace
"Idan ta shanye wannan da rana sai dare kuma sai a kawo mata wan da zata sha har gari ya waye."
nan ne ya kyale ni amma yace mutafi na karasa shanye sauran.
nace ya tafi zan zo anjima, fir yaki sai da ya tasani gaba muka koma...
tun daga ranar kullum shi yake zuwa da kansa ya karɓo min ruwan maganin, yakuma tasa ni gaba sai na sha...


A bangaren Hajiya Karima kuwa
tsaye take ita da wasu maza guda hiyu, a cikin bedroom ɗin ta, sunyi jungum-jungum kamar waɗan da aka aiko wa da bakin labari,
ɗaya daga cikin mutanen yace
"Hajiya shima kawai a kunce masa tayar mota yabi uban sa inda yaje."
Hajiya Karima tace "Ai matsalar ba daga nan take ba, yanzu fa duk wata shirin mu ya kwaɓe idan aka kashe Ahmad tofa anyi ba'ayi bane, dan kuwa yanzu yasami magaji dole a mufara bi ta kan ita matar tasa mai cikin kafin shi."
ɗayan yace "To Hajiya me kike ganin za'ayi mushiga cikin dare mu harbe banza kawai."
tace "Ina ai bazai yiwu ba dan gidan ta da matakan tsaro iri-iri, akwai jami'an tsaro da masu gadi kuma ko wannen su yana da bindiga, shigan gidan zai bada wuya, dole dai mubi ta wata hanyar, ni a tuanani na kawai mu jira ta haifi cikin sai mu kawar da shi,in yaso duk mu haɗa har da ita mai azarɓaɓin yin cikin kafin shi Ahmad ɗin.
suka ce haka za'ayi,
nan suka cigaba da tattauna in da lamarin zai tafi musu batare da wata matsala ba.....




A gurguje Please 👌🏻


Bayan wata biyu

Yau tun da gari ya waye nake jina wani iri, sai dai narika daure wa ban nuna masa komai ba.
har wajen karfi sha ɗaya, zuwa lokacin kam nafahim ci nakuda ce kuma sosai nake jin sa.
har kuma lokacin ban nuna masa wani abun na dami na ba na rika daure wa har mukayi wanka yafita, kafin yafita kuwa yayi ta tambaya ta, babu abin da yake damu na me kuma na ke so. nace masa babu komai...
ina zaune a bakin gado nayi nayi na iya mike wa na kasa, sai na zame kasa nasaka goiwowi na a kasa na kife kaina jikin gado, ina juya kai cikin mawuyacin hali.
"Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un wayyo Allah na."
nafaɗa da karfi ina juya kai.
sallamar Faty naji daga bakin kofa, da karfi na ɗaga murya na kira ta, da sauri ta shigo nace
"Je ki kira min Inna Wuro da sauri."
hankali tashe ganin halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login