Showing 105001 words to 108000 words out of 125808 words

Chapter 36 - Hamdah Book Four Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

460

guda uku kafin ya rasu, ba a fara aikin ba ya rasu sai a ka dakatar da aikin, waɗan da a ka basu kuɗin basu dawo da shi ba sai yau, lauyan sa ne ya kirani yanzu nazo na karɓi kuɗin."
mike wa zaune nayi ina faɗin
"Masha Allah an godewa Allah."
ya mike yana faɗin "Bari naje yanzu wai ni a ke jira."
nace "To a dawo lafiya."
har yakai bakin kofa ya jiyo ya kuma dawowa cikin parlour'n, in da su Naseem suke ya isa ya sunkuya dai-dai tsawon su, ya shafa kan ko wannen su yace
"Allah yayi muku albarka kuyi rayuwa mai kyau da inganci, kowa ya bani sallamar sa anan fita zanyi."
yanuna musu gefe da gefen kumatun sa.
cikin washe baki Nasmah ta sumbaci gefen kumatun sa na dama Naseem kuma ɗaya gefen, ganin abun da suka yi Ahmad karami shima ya maso ai kuwa ya yanka masa cizo a kuma tu.
dariya dukkan mu muka yi,
kumatun ya shafa yana faɗin
"Ash Ahmad sallamar taka kenan?."
karaso wa in da suke nayi ina dariya nace
"Oh Ahmad haka aka ce maka suka yi ne." yaɗa ga shi sama ya na juyi da shi sai washe baki yake, daga bisani ya dire shi kasa.
yayi ta biye wa yaran suna ta wasa sai da nace masa, ya tafi ko ya mance a na jiran sa.
nan ma har ya kai kofa yakuma juyowa, ya kira yaran tare da buɗe hannayen sa suka so da gudu ya haɗa su duka ya rungume su.
ido na ɗan kura musu yayin da fargaba mai haɗe da faɗuwar gaban nan ke daɗa taso min.
maganar sa naji yasani saurin mai da hawayen da naji suna kokarin zubo min.
"Zo mana kyakkyawa ta." yafaɗa yana min alamar nazo kusa da shi, jiki a sanyaye na taka zuwa in da suke, sai ya janyo ni duk ya haɗa ya rungume mu, a tare muka sauke ajiyar zuciya ni da shi.
duk kanin mu shiru mukayi muna cikin jikin sa, yayin da zuciya ta ke wani irin bugawa.
jin yanayin nason firgita ni sai na ɗan mosa, a hankali ya sake mu yana binmu da murmushi.
da sauri na maso jikin sa na ruko hannunsa na kankame shi gam, murya na rawa tuni hawaye yafara zubo min nace
"My tsoro nake ji." Naseem da Nasmah ya kalla yace
"Kuje kasa kujira ni gani zuwa yanzu."
suka amsa da sauri suka nufi parkour'n kasa, da sauri ya janyo ni ya rungume ni tare da haɗe bakin mu, da karfe na daɗa rungume shi ina daɗa cusa baki na cikin nashi. yayin da nake jin numfashi na ke yin sama-sama, da sauri na janye bakina sai kawai na saki kuka ina jujjuya kaina.
da sauri ya rirrike ni cikin muryar dariya yake faɗin
"Ke lafiyar ki kyakkyawa ta meye kuma na kukan kuka baya baki wuya ke, to ya isa faɗa min me ya saki kukan."
baki na turo ina jan shesshe ka.
"Mene ne me ya same ki?."
kai na girgiza dan nima ban san dalilin kukan nawa ba.
hawayen yashiga share min yana faɗin
"To bana son wannan kukan ko nan gaba dan Allah kiyi min alkawarin zaki daure, addu'a yafi komai tasiri a kan koma me, aduk san da kika ji tsoro ko fargaba ko faɗuwar gaba ko wannan kukan kiyi kokarin danne su ta hanyar faɗin
Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un,
wannan kalmar yana samar wa zuciya nutsuwa,shagwaɓaɓɓiya ta."
ya karashe maganar cikin sigar zolaya tare da jan kumatu na.
yaci gaba da faɗin
"Ni bari naje kar su gaji da jira na, kiyi min shiri mai kyau anjima yau ina sa ran da zaran na jefa kwallo na ya isa raga, Ahmad nason kani ko kanwa."
yayi maganar yana kashe min ido,
baki na kuma turo wa cikin muryar shagwaɓa nace
"Ka mance gun Aunty Rasheedat kake."
kai ya dafe yace "Oh wlh gaba ɗaya na mance amma dai zan dawo kafin dare ayi min shiri kawai."
haka yayi ta jana da wasa da kuma salon zolayar sa mai sani nishaɗi har sai da yaga na ware har da dariya ta kafin ya sake ni, ya juya zai fita Ahmad karami dake wasa gefen mu ya saki wani irin kuka, yana mika masa hannu.
da sauri ya dawo ya ɗauke sa yashi rarrashin sa, sai da yayi shiru kafin ya mika min shi yana faɗin
"Je ka gurin Mommy kada ka sake kuka, kada ki barshi ya sake yin kuka ki tsaya masa ya kasan ce cikin farin ciki, mu je ayi min rakiya ko."
na bi bayan sa muka sauka kasa, nan muka tadda su Naseem duk mukayi waje tare.
ko da muka isa parking lot ya karɓi Ahmad karami yayi ta masa wasa yana kyalkyale dariya su Nasmah ma haka, sai da ya gama yiwa yaran wasa kana ya mika min Ahmad yace bari yaje ya sanar wa Bappa Yakamata ya sami labarin da wuri.
muna tsaye a parking space yaje ya dawo,yake sanar min Bappa ya taya sa murnar fitowar makudan kuɗa ɗen sa.
yashige mota muna ɗaga wa juna hannu har ya fita,
numfashi mai karfi na sauke san da motar sa ta ɓace wa gani na, jiki a sanyaye na juya muka koma ciki....



Da misalin karfi 6 da yanma,
har zuwa wannan lokacin ina dai nan ne amma gaba ɗaya yanayin baya min daɗi,
kiran Ahmad ne ya shigo waya ta da sauri na ɗaga tare da yin sallama.
ya amsa yana faɗin "Kyakkyawa ta mun gama komai na karɓo kuɗin gasu a mota, sai dai banki yanzu sun tashi zan kai su gida gobe zan sa a kaisu banki."
"Masha Allah mun gode wa Allah, amma My kai kaɗai kake tafi babu security?."
yace "Tare da su muke, ina zuwa."
ya faɗa tare da ɗan yin shiru,
jin abun da yake faɗawa security yasani faɗin,
"My mene ne?." yace "Wasu mota ne guda biyu suke bayan mu tun ɗazu na lura kamar biyo mu suke, ina son sanin ko su waye ne."
jin yana kokarin kashe wayar da sauri nace
"My kada ka ci gaba da tafiya da su ku canza hanya ni dai hankali na bai kwanta ba kaji dan Allah."
yace "To yan da kika ce haka za'ayi kyakkyawa ta."
ina tsaye cikin ɗaki rike da waya sai kaiwa da komo wa nake da kyar na samu na iya zama, tafiya da kuɗi masu yawa a mota irin haka a kwai hatsari sai dai saukin ma ɗaya yana tare da jami'an tsaro.
da sauri na ɗaga waya shigo war kiran sa yace
"Kyakkyawa ta na iso gida ta hanyar canza hanya kamar yadda kika faɗa."
numfashi mai karfi na sauke nace "Kai alhmdllh amma wlh duk a tsorace nake har naji hankali na ya kwanta."
yace "To je kiyi salla kiyi mana addu'ar dace wa da rahamar Allah nima masallaci zan tafi yanzu."
nace to...

Da misalin ƙarfe goma na dare ina kwance sakiyar yara na yayin da waya ke kare a kunnena kamar kullum, a duk san da Ahmad baya gida na to muna tare da shi a waya, ko yanzu hira da shi muke ta waya.
hamma nayi haɗe da mika tare da yin salati nace "My bacci." yace "To sai da safe kiyi baccin ki mai daɗi."
murmushi mai sauti nayi nace "Kai ma haka."
na kashe wayar,na bi yaran da addu'a nima na shafa na gyara kwanciya ta, wani irin faɗuwar gaba naji da sauri na dafe kirji na, a hankali na fara nanata kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un³.
gaba ɗaya bacci ya kairace a idona ina dai kwance shiru.
can wajen karfe 2 na dare har lokacin ina kwance idanuna kuma biyu,
da sauri na janyo waya ta dake tsuwa karkashin pillow, ganin mai kiran nawa yasa ni saurin mike wa zaune na kai wayan kunne na tare da faɗin
"My." yace "Baki bacci ba kyakkyawa ta?." nace "Na kasa nakasa yi My."
numfashi ya ɗan sauke tare da faɗin "Ko na zo ne." kai na girgiza da sauri nace "A'a dare yayi sosai."
yace "To ki tashi kije kiyi al'wala kiyi nafila ko da raka'a biyu ne kiyi addu'a zakiyi Baccin."
nace to. yace "Ina su Naseem?."
"Ga sunan suna bacci."
"Shafa min kansu duka ki sakawa Ahmad wayar a kunne."
nace "Yana bacci ai." yace "Eh sa masa."
a hankali nayi yanda yace na saka masa wayar a kunnen sa, magana ya soma yi a hankali yace
"Ahmad Ahmad Tijjani Sabil, kada ka bari wannan sunan ya mutu, kada ka sake duniya ta mance da wannan sunan duniya ta cigaba da faɗar waɗan nan sunayen, kamar yadda nayi tsayuwar daka domin ci gaba da ɗaukaka sunan Tijjani Sabil da har yau duniya basu mance da shi ba,suna kuma yi masa addu'a a koda yaushe,
Allah ya dauwamar da albarka cikin rayuwar ka kai da ƴan uwan ka."
da sauri na ɗago wayar a kunnen sa ganin yana motsi, nace
"My me kuma ya kawo wannan maganar a daren nan?."
murmushi mai sauti yayi yace
"Kiyi hakuri kyakkyawa ta."
nace "Na me fa?." yace "Ba komai rayuwar ce dai dole sai da hakuri, Ahmad yana son ki da kaunar ki."
numfashi na sauke zuwa yanzu maganganun sa na tun waye war garin yau da kuma yanzu sun fara da mi na, suna son su haɗe su cunkushe da yanayin fargaba da faɗuwar gaban da na ke ji.
nace "My nima ina son ka da kaunar ka."
yace "Nagode kyakkyawa ta, kin san me?."
nace "Sai ka faɗa." yace "Ɗazu ban zo da kuɗin nan gida ba a hanya na kira manajan banki yazo sai mukayi canjen mota na bashi nawa wan da kuɗin yake ciki na karɓi nashi, shi ya tafi da nawa gidan sa gobe zai shige da shi banki."
nace "Ai ma hakan yafi gara da ka bashi kaga idan zai tafi ban kin sai ya tafi da shi yafi sauki ma."
jin ya ɗanyi shiru baiyi magana ba nace
"My kai ma bacci kake ji ka kwanta sai da safe."
yace "A'a naji karan buɗe get ne."
nace "A cikin daren nan?." "Ai nima shine na gani bari naje na ga ko waye mai gadi ke buɗe wa get da daren nan ina zuwa."
ya kashe wayar tare da duban qRasheedat dake kwance a gefen sa, ya mike ya sauko a gadon ya fito.
a hankali yake tafi ya har ya fito, ga mamakin sa sai yaga an kakkashe wutan gefe da gefen gidan har zuwa lungunar dake cikin gidan duk wutan a karkashe, iya wutan dake can bakin get da kuma na hanyar shiga side ɗin sa da na Rasheedat ne kawai a kunne.
can ya hangi security kwakkwance a gurin zaman su duk suna bacci ko wannen su ya yada bindigan shi gefe suna ta sharar bacci.
gefe can kuma karnukan gadi ne suna zazzaune sai fidda harshe da ciccire ido suke.
motsi yaji a ta gefen sa in da babu hasken wuta a gurin, a hankali ya mai da duban sa gurin ya kurawa gurin ido sosai, inuwar mutum ya hango tsaye a gurin. da sauri ya waiga ɗaya gefen sa nan ma yakuma hango inuwar mutum, a hankali yayi baya yarika tafiya da baya da baya cikin hanzari ya koma ciki, da sauri ya shige bedroom ɗin sa,
ya isa jikin gado ya saka hannu sa kasan gado yaja sai ga drower ya bayyana yaciro bindiga ciki ya mai da drower ya ɗago yana gyara rukon bindigan a hannunsa.
Rasheedat ce tayi juyi tare da ware idanun ta a kansa, da sauri ta mike zaune tana faɗin
"Aboki lafiya?." yace
"Ɓarayi sun shigo gidan nan." ido ta waro da sauri ta duro a gadon tana faɗin
"Ina security suke har ɓarayi suka sami damar shigowa gidan nan?."
yace "Akwai matsala suna nan abin mamaki duk kanin su bacci suke."
ya juya da sauri yana kokarin fita tasha gaban sa da sauri tace
"Aboki ina kuma zaka je?, a'a kada ka fita, kayi waya wasu jami'an suzo, kasan da abin da suka zo,
hakika da abin da suka taka tun da har kaga suka iya samin karfin guiwar shigo wa gidan nan duk tulin tsaron da ke gidan nan."
yace "Nasan abun da ya kawo su kuɗin nan ne kuma baya gidan nan ma zan je naji da su."
ya juya da sauri.
da gudu ta bi bayan sa ta rungume shi ta baya tana faɗin
"Aboki kada ka fita ka tsaya na buɗe maka kofar baya ka fita ta can dan Allah kada kaje."
juyo wa yayi ya rungume ta yace
"Kawa ki zauna duk abunda zakiji kada ki fito, kiyi min addu'a kinji."
kai ta shiga girgiza wa tare da sakin kuka tana faɗin
"Aboki kada ka je na roke ka ka fita ta kofar baya."
jikin sa ya zare daga nata, lokacin da aka fara harbi cikin gidan, ya tallafo fuskarta yace
"Kiyi min alkawarin ba zaki fito ba duk abun da kika ji, kizauna cikin ɗakin nan ki kulle kanki bazan taɓa barin su sushigo ciki ba zan kare ki da yardar Allah,sannan kuma bulet bazai iya ɓula ginin gidan nan ba ko da ace sun yi yunkurin yin harbi cikin nan, kada ki fita kizauna a nan."
harbi aka cigaba dayi cikin gidan ta ko ta ina, Rasheedat ta daɗa kankame shi tana faɗin kada ya fita.
da sauri ya sake ta ya fita.
ita ko kuka ta kuma sake wa ta durkushe a gurin, sai kuma ta mike da sauri ta isa ta kulle kofar, ta koma bakin gado tana cigaba da kukan..

A hankali cikin sanɗa Ahmad ya fito
yayin da ya gyara rukon bindigan sa da kyau.
harbin yashiga mai da musu daga inda yake laɓe suka rika musanyar wuta sakanin sa da ɓarayin.
kara ɗaya daga cikin ɓarayin yayi lokacin da harbin Ahmad ya same shi, ya zube a gurin,
kaimi ɓarayin suka kara akan harbin da suke, cike da tafasar zuciya cikin hanzari Ahmad yafito daga in da yake laɓe, yana fita daga gurin kuwa wani yayi saitin sa ya sake masa harbi a gefen kirji.
dafe gurin yayi cikin jin azaba da raɗaɗin shigan bulet jikin sa,
cikin tsananin tafasar zuciya da kunar rai yayi gaba da gaba da su in da yakuma samin nasarar harbin mutum biyu a kafa,
cike da tsananin mamaki ya tsaida harbin da yake ganin amintaccen mai gadin sa, yana nuna shi wa wasu ɓarayi huɗu da suke tsaye da hannu,suka juyo tare da saita shi da bindiga.
kafin ya dawo da ga mamaki mai haɗe da tunanin daya tafi, sai ji kake tau-tau saukan harbi a cikin sa har sau biyu, kara yayi tare da damke cikin sa da jini ke tsiyaya, yayi tangal-tangal kafin ya isa kasa ya harbe su gaba ɗayan su su huɗun nan har da mai gadi cikon na biyar, a tare suka zube kasa mutattu.
yana kwance a kasa yana sakin wani irin numfashin wahala wan da yafi kama da na fitar rai...


Ina zaune a kan sallaya bayan na idar da nafila kamar yadda Ahmad yace min nayi zan sami bacci,
gaba ɗaya ilahirin jiki na babu karfi tamkar an zare min laka.
na janyo wayata lokacin karfi biyu da rabi,
na danna number Ahmad tare da kara wayar a kunne na, yayi ta ringing har ya yanke bai ɗaga ba, kuma mai da kiran nayi shima har na cire rai da ɗaukar nasa dan nafara tunanin bacci yayi.
wani irin razana da zabura nayi jin muryar sa yana faɗin
"Kyakkyawa ta sun harbe ni sun harbe ni......!




Mommyn Twins
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 34







Bappa yace "Allah mai girma da
ɗaukaka ashe dai jikata ce HAMDAH, a she dai jika ta ce nake zaune da ita cikin rashin sani, alhamdulillah masha Allah, hakika ɗan adam baya fidda rai da rahamar Allah, ashe wata rana zan haɗu da jinina ga jiko ki na ga ƴaƴa na, kuzo nan ƴaƴa na Allah yayi muku albarka."
ya janyo su Abbu jikin sa yana ta sanya mu
su albarka,
Abba ya nuna goggo Hauwa yace "Wannan ita ce kanwar mu."
Bappa yace "Taho nan kema."
Goggo Hauwa ta mike tana sharar kwalla taje in da yake su Abbu suka ce tabbas Inna tana faɗin tana da kani amma bata san in yake ba sun rabu tun suna kana na.
tabbas nima Inna tasha faɗa min tana da ɗan'uwa sai dai tun suna kana na aka raba su yanzu bata san in da yake ba..
Uncle Mahmood farin ciki ya gama lulluɓe shi yau shima gashi cikin ahlinsa.
haka akayi ta farin ciki yayin da farin cikin ya gusar da alhinin da Na'ima ta sakawa mutane...
Ahmad ya dube ni kasan cewar yanzu a kusa da shi na zauna, yace
"Ina taya ki murna na karuwar ahlinki, sai naji ina ma ace nine iyayena da ƴam'uwa na suke zagaye da ni haka."
kai na rausayar ina mai jin tausayin sa, na sauke hannuna kan nashi dake saman hannun kujera nace
"Allah ya haɗa ka da su a jannatir firdausi."
murmushi yayi tare da faɗin amin amin....


A ɓangaren Na'ima kuwa tana fita a gidan, a hargitse cikin matsanancin tashin hankali ta tsari mai napep.
tayi gidan bokan ta,
tana zuwa ta shaida masa abun da ke faruwa.
bokan yace taje ta kawo cikiton kuɗin aiki yanzu ta dawo a rufawa kowa baki su mance da abunda ya faru, a kuma kashe HAMDAH.
tace to ta fita abujajan ta dawo gida,
domin ɗaukar kuɗin da Raliya ta bata aro ta kaiwa boka.
tana shiga gida ta dadda SALEEM a parlour da magunguna da gorar ruwa a gaban sa da alama yanzu yagama shan maganin.
tana kokarin wuce sa tashiga ɗaki, ya dakar da ita ta hanyar kiran sunan ta
"Na'ima." ya kira sunan ta batare da ya dubi in da take ba.
sai da hantar cikin ta ya kaɗa, jin yan da ya kira sunan nata a sama,da jin amon sautin sa da babu wasa ciki.
a fusace ya mike tamkar fusataccen zaki yayi kanta,
tana ganin haka ta shiga ja da baya tana kokarin gudu,
da sauri ya cakfo ta tare da shako wuyan ta har saida idananun ta suka fiffito waje,yayin da numfashin ta yake kokarin barin jikin ta.
wasu tagyayen maruka yashiga shinfiɗa mata nan da nan fuskarta ya canza kala.
sai kuma ya sake ta da sauri tare da dafe kirjin sa da hannayen sa biyu, yashiga yin tari a hankali ya durkusa kasa.
Na'ima ko yana sakin ta da sauri tayi baya tana maida numfashi tare da shafa wuyan ta da fuskar ta daya sauya masa kamanni...
hannun sa ya ɗaga yayin da taren ke ci gaba da zuwar masa ya nuna ta tare da faɗin
"Fita tafi na daina ganin ki, ki sani har aba na haramta kaina gare ki, fita min a gida tafi na daina ganin ki,
kije Allah ya haɗa ki da hukubar duniya dana kiyama."
numfashin sa ne ya soma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login