Showing 99001 words to 102000 words out of 125808 words
Fauzan.
Naseem da Nasmah suna like a jikin Ya Masa'ud wai har sun gane shi kenan sai surutu suke zuba masa, wannan yace Uncle kaza wannan yace Uncle.
Ahmad karami kuwa yana hannun Mamie tana yi masa wasa yana dariya.
ana ta hira cike da jin daɗi da nishaɗi.
nan suka yi ta yiwa Mama mai awara godiya da irin kokarin da tayi a kaina...
Acan gidan SALEEM kuwa labarin zuwan su HAMDAH ne ya iske Na'ima,
a bujajan ta taso dan gane wa idon ta karya ne ko gaskiya, dan yau tayiwa boka alkawarin kawo masa cikon kuɗin sa, dan wan da suka shirya zai sace Ameer baya nan shine aminiyar ta Raliya ta bata aron cikiton kuɗin da zata bawa boka, idan aka karɓi kuɗin fansar Ameer ta biya ta,
shikuma yayi mata alkawarin yau ɗannan da daddare zai tura aljanu su kashe HAMDAH...
Sallama muka jiyo daga sama, duk kanin mu muka mai da hankali bakin kofa,
kamar an jefo ta haka ta faɗo cikin parlour'n, wani irin kallon-kallo muke yi da Na'ima da tayi mutuwar tsaye bakin kofa.
dogon tsaki Aunty Rafee'at ta ja kana tace
"HAMDAH kalli wannan hoton ki gani."
tayi maganar tana nuna min hotunan mu da ta sa Fauzan ya ɗibo a side ɗin Ummi.
dariya nayi ganin hoton tun ina Dass wani lokaci Inna ta bani kuɗi naje na ɗau hoton,
kai na girgiza tare da faɗin
"Allah sarki Inna ta."
Ahmad da hankalin sa ke kanmu yana binmu kallon cike da sha'awa da burge wa ganin yan da muke da junan mu yace
"Madam muga hoton."
ɓoye sa nayi a baya na ina dariya, Aunty Jaleela ne ta fizge hoton tana faɗin
"Bashi yaga munin kawai." ta mika masa hoton.
nace "Allah Aunty Jaleela ko a da ma na fiki kyau."
Ya Masa'ud yace "Bare kuma yanzu har girma kin fita ƴar gidan Inna."
dariya na fashe da shi nace "Yau wa Ya Masa'ud faɗa mata dai."
Aunty Rafee'at tace
"Oh Masa'ud zaka fara haɗin naka ko."
tayi maganar tana dariya cike da kewar faɗar mu da Aunty Jaleela da muka saba.
Aunty Jaleela kuwa hararar sa tayi tace "Ni sa'ar ka ce Masa'ud?."
Ya Masa'ud yace
"Aunty Rafee'at matsa na mari bakin yarin yar nan."
dariya muka yi dukan mu har da Ahmad da hankalin sa ke kanmu,
yana kallon hoton yana dariya, idan muka haɗa ido da shi sai ya nuna min hoton yayi dariya,
baki na rika murguɗa masa nima ina dariyar...
Na'ima tana tsaye kamar wacce a ka kafata idanunta a kaina, kamar a mafarki haka take ganin komao.
Ummi ce ta dube ta tace
"Shigo mana Na'ima ya kika tsaya a gurin."
ta janyo ɗan da ke rike a hannunta suka karaso cikin parlour'n hankali a mugun hargitse....
Hospital
Dr Mukhtar ne zauna cikin offece ɗin sa, kamar daga sama yake jiyo hayaniya cikin asibitin,
da sauri ya mike ya fito, sai ganin ƴan sara suka yayi cike a cikin parlour'n asibitin shi, ko wannen su daga mai wuka sai mai adda sai walkiya suke, suna faɗin
"Ina likitan yake."
ido ya wawwaro cike da tsoro yace
"Bayin Allah lafiya?."
wani bakware ne yayi kansa da adda yace "Na sassare ka idan ka kuma mana tambayar da bata gamshe mu ba, kai ne likitan?."
kai ya gyaɗa jikin sa na ɓari.
yarinyar da suke tare da ita ya janyo ta yace
"Kasan wannan?." Ido Dr Mukhtar ya kura mata yana ta son tuno in da ya taɓa sanin ta.
mari ɗan saran yayi masa da adda a fuska da karfi yace
"Ka gane ta?."
a gigice yashiga gyaɗa masa kai dan marin yasa shi tuno ta da sauri.
yace "Eh..Eh.. na gane ta."
murmushi bakwaren yayi yace
"Ai da har na soma tunanin nasa yara su ankarar da kai su tsastsaga min kai."
fuska bakwaren ya murtuke yace
"Ina ɗana da ta zo ta siyar muku da shi anan, sabo da ku kananun ƴan isaka ne shine zaku karɓi ɗana ku bata kuɗi, zan nuna muku naku iskancin kaɗan ne idan ɗana bai fito ba duk wan da yake da hannu kan lamarin sai na bubburma masa wuya."
da sauri Dr Mukhtar yace "Wlh billahil lazi baya gurina yana gurin wata ne."
kwashe sa wani yayi yakaɗa keyar sa yace
"Wuce muje ka nuna mana in da take."
suka tasa shi gaba suka ɗaura shi kan mashinan da suka zo da shi,
gidan su Raliya suka fara zuwa kasan cewar bai san gidan Na'ima ba.
suka raki sa'a Raliya tana gida, yace musu da tare suka zo suka karɓi yaron shi bai san gidan ta ba ita tasan gidan ta.
nan suka saka Raliya ita ma gaba bayan sun gama gwaza mata mari.
suna zuwa gidan Na'ima mai gadi ya shaida musu ba ta nan,
Raliya ta kira ta a waya tace mata tana cikin gidan su SALEEM, nan suka ɗau hanyar gidan...
koda suka zo shiga gidan ganin su da makamai sai security suka hana su shiga gidan...
jin bayani ya a waje da karar wasa wukake da adduna yasa muka fito dan ganin me ke faruwa,
jin abun da ɗan saran nan yake faɗin
"Wlh sai ya sassare ta idan bata fito masa da ɗan sa ba."
yasa Abbu cikin rashin fahimta yace wa security su bar sa shi ya shigo yaji gurin wa yazo."
tare suka shigo da Raliya da yarinyar da yake ta janta, da kuma Dr Mukhtar.
ido Na'ima ta cicciro cikin tsananin tsoro da firgicin ganin yarin yar da ta karɓi yaro a gurin ta tayi karyar cewa ita ta haife sa,
ga kuma Raliya da Dr Mukhtar..
Abbu yace
"Gurin wa kuka zo a gidan nan."
bakwaren ya dubi yarinyar cikin muryar ƴan iska da suka gama holewa da kayan maye yace
"Bazaki nuna ta ba sai na daddatsa ki."
da sauri yarin yar ta ɗago hannunta na rawa tashi nuna Na'ima tana faɗin
"Gata nan ita ce wannan."
baki ya karkata cike da rashin mutumci yace
"Okay ɗan nawa kenan wannan dan tsabar rashin daraja da kika san bazaki iya haifa ki rike ba shine bazaki kawo min shi ha, ance miki ni abin kunya dami na yayi zan kaiwa tsohuwa ta ta rike min shi, taho nan yaro nine ubanka."
ya miko hannu zai ruko hannun ɗan da ke hannunta.
cikin rashin fahimta kowa ke kallon su Abbu yace
"Me kake nufi kana nufin kace shi wannan ɗan naka ne?.�?
yace "Eh mana ɗana ne mana."
Abbu ya jinjina kai cike da al'ajabi yace
"To ɗan dakata kaɗan." wayar sa ya daddan na yakira lambar Ya SALEEM yana ɗagawa Abbu yace
"Duk in da kake duk abun da kake kabari yanzu yanzun nan kazo ina neman ka."
daga cikin wayar Ya SALEEM yace
"Gani nan kusa da gidan ma."
yana kashe wayar mutar sa tana karaso wa nakin kofar gidan,
ganin cincirindon kwarawa ƴan tsara suka haɗe da hukuma a kofar gidan su, yasa shi fita cikin motar da sauri yanufi cikin gidan.
yana sa kafa cikin gidan muka haɗa ido da shi.
cak ya ja ya tsaya yayin da zuciyar sa tayi wani irin tsalle har sai da yakai hannunsa ya dafe kirjin sa da sauri.
niko cikin hanzari na janye idanuna a kansa, yayin da naji kirji na yayi wani irin bugawa..
Abbu yace "Ka tsaya kuma ka karaso mana kai muke jira."
a sannu ya shiga ɗaga kafar sa har ya karaso gurin.
Abbu ya dubi Ya SALEEM da kyau yace
"Kasan wannan?." ya nuna ɗan saran
kai ya girgiza batare da yace komai ba.
ɗan saran cikin yanayin Muryar maye yace "Ai da ma bai Sanni ba, kamar yadda nima ban san shi ba, kamar dai yadda ban san wannan matar da ta siya ɗana ba."
ya karashe maganar yana tangaɗe da ɗaga addan da ke hannunsa sama yana nuna Na'ima da shi.
Abbu ya girgiza kai kana yace
"To kaji wai ɗan ka ɗan shi ne, dama nace kazo ya faɗa a kunnen ka bazai bamu sako mu faɗa maka ba."
sai a lokacin Bappa yayi magana dan sai yanzu ya fahimci in da batun ya dosa, yace
"Kai yaro kace ɗan ka ne wannan ta ya aka yi ya zamo ɗan ka bayan ga uba da uwan yaron anan?."
mari ya kai wa yarin yar yace
"Faɗa musu yan da kika yi kika siyar min da ɗana, a miko min shi na tafi ina da shara yau."
duban ta Bappa yayi yace "Ke yarin ya ya akayi haka, da gaske ɗan sane?."
hawaye ta shiga share wa tana jan hanci tace
"Eh ɗan sa ne, dama..dama..dama lokacin ina da ciki ne da zan haihu shine iyaye na suka kore ni suka ce ba a gidan su ba, shine naje asibitin wannan."
ta nuna Dr Mukhtar dayake ta tsilli-tsilli da ido,
kana ta cigaba da faɗin "Shine na haihu sai waɗan nan suka kirani."
ta nuna Na'ima da Raliya sannan ta cigaba
"Shine suka ce suna son ɗan in dai yadda shi zan yi, shine wannan ta bani kuɗi ta karɓe sa."
ta karasa maganar da nuna Na'ima.
Bappa ya dubi Dr Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa yace
"Abun da ta faɗa haka ne shin a asibitin ka akayi haka?."
Dr Mukhtar ya shafa gefen fuskar sa daya kunbura in da bakwaren ya ya mare sa da adda, ya gyaɗa kai tare da faɗin
"Eh haka ne a asibiti na ta haihu kuma ni na karɓi haihuwar, kuma wannan shine ɗan."
ya nuna ɗan dake rike hannun Na'ima.
salati kowa ya sake cike da ɗinbin mamaki, masu tafa hannu suna tafa wa masu salati suna yi.
Abbu ya dubi Na'ima yace "Mika musu ɗan su."
jiki a sanyaye cike da taren jin kunya ta tura musu ɗan.
bakwaren ya ja hannun ɗan yana faɗin
"Taho nine nan uban ka, ke kuma wuce muje ko na tsastsaga ki anan."
ya kaɗa keyar yarin yar suka fita,
yaja ƴan uwan sa ƴan sara suka yi gaba.
Dr Mukhtar ma yaja kafa ya fita tsimi-tsimi Raliya ta bi bayan sa...
Baya Ya SALEEM yayi yayin da hannunsa ke dafe da kirjin sa.
a hankali ya shige cikin ɗakin Ya Masa'ud.
Mamie ta dubi Na'ima da take jin wani irin tsanar ta rai ɓace tace
"Shi yasa ko dai-dai da rana ɗaya ban taɓa jin son ɗan nan ba ashe sabo da ɗan shege ne ba jinina bane."
Mamie ta juya ta nufi side ɗin ta rai ɓace.
shewa Aunty Rafee'at tayi tashiga tafa hannu, ta zo gaba Na'ima tana yi mata wani irin kallon sama da kasa
tace "Ai dama karshen muna fuki jin kunya, duk wanda yace ruwan wani bazai tausa ba nasa ko lum-lum bazai yi ba, zakaran da Allah ya nufa da cara kuwa ko ana ga muzuro ga shawo sai ya yi,
wacce kika lankaya wa tayi ciki da auren ta kika kazan ta mata ciki, gata a gaban ki ta zame miki abun kallon abin kwatance,
ɗan shege zaki kawo mana cikin family bama bukatan bare a cikin mu,
fita mana agida makira algunguma kaɗan kika fara gani,
sai duniya tayi juyin masa da ke."
Aunty Jaleela tace "Kamar yanzu kuwa zaki fara ganin aya, sai kin gwammaci mutuwa da rayuwar ki, fita a kace fita mana agida."
suka kaɗa ta har waje.
niko ina taaye ina kallon abin kamar a Film,
Bappa ya girgiza kai yace
"Duk wan da ya nufi wani da sharri a kwan a tashi kan sa yake koma wa, Allah ka tsare mana imanin mu."
aka amsa da amin kana muka juya muka koma ciki.
kowa yana jinjina lamarin.
har muka zazzauna ana alhenin abun.
Bappa yana ɗago kansa idanunsa sukayi arba da wasu hotunan Inna guda biyu acikin glass ɗaya, dake like jikin garun parlour'n,
huf ya mike tare da nuna hoton da yatsa yana tafiya in da yake, cikin rawar murya Bappa yace
"Adda A'i."
da mamaki kowa ke kallon sa su Abbu suka mimmike tsaye,
ya juyo da sauri yana faɗin
"Wannan hoton a ina kuka samu?."
Abba suka haɗa baki wajen cewa
"Innar mu ce ka santa ne?."
da sauri Bappa ya fita gurin mota yaje ya buɗe kana yabuɗe jakarsa dake cikin motar ya ciro wani hoto kana ya dawo cikin parlour da sauri,
ya mika musu hoton wan da yake iri ɗaya da ɗaya daga cikin hotunan,
da mamaki su Abbu suke kallon hoton iri ɗaya da wan da yake jikin garun parlour,
Bappa yace "Dai-dai da rana ɗaya ban taɓa ajiye hoton a wani guri daban ba ko da yaushe yana cikin jakata sabo da girma da matsayin wacce take cikin hoton a guri na,
Adda ta ce ita ta sha nono ta bar min,
lokacin da Bappan mu ya rasu ina ɗan kara mi, sai ƴan uwan Baban mu suka ɗauke ni suka tafini, kasanceaar ni na miji ne, suka barwa Maman mu Adda A'i,
kamar yadda kuka sani mu fulani bamu fiye zama guri guda ba, musamman fulani makiyaya, haka mukayi ta yin nesa da in da mamar mu take,har muka sallaka Nigeria,
tun da aka tafi da ni bansake haɗuwa da Maman mu da Adda A'i ba,
bayan wasu shekaru masu dama aka zo ma na da sakon rasuwan maman mu da kuma wannan hoton, aka bani duk da lokacin da muka rabu da ita ina yaro ne sosai amma bai hanani gane ƴar uwa ta ba,
lokacin da girma ya same ni na dawo Nigeria da kaina ban san kowa ba hansan ta inda zan fara neman ƴar'uwa ta ba, rugar mu da na rike sunan sa nayi ta bincike a kansa har naje rugar, duk wanda na tambaya sai ya cemin baima santa ba,
a haka na fauwalawa Allah komai nacigaba da addu'a Allah ya haɗu mu da ita, haka na rika ajiyar hoton nan harrrana mai kamar tayau,
ashe dai da rabon mugana ina Adda A'i take tana ina?."
Abbu yace "Allah yayi mata rasuwa."
salati Bappa yayi sai ga hawaye a idon sa, kowa sai da yayi kuka tuno da Inna..........!
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 32
Ummi ta rika bubbuga baya na tana faɗin nayi hakuri, yayin da hawaye ke cigaba da zuba a idanunta.
da sauri na saki Ummi na juyo hawaye na zuba a ido na, na saki murmushi hawaye na zuba cikin matukar farin cikin ganin yau gani ga mahaifiya ta, na dubi Ahmad nace
"My ga Ummi yau gani ga Ummi na, Bappa Ummi na ne Ummi na ne."
sai na kuma rungumar ta ina hawaye haɗe da murmushi.
wani irin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyoyin su Ahmad yace "Barka da zuwa Ummi hakika mun yi farin ciki da zuwan ki."
Bappa ko Masha alhmdllh alhmdllh yake ta faɗa yayin da fuskarsa ke bayyana jin daɗi.
security kuwa gaba ɗayan su kowa yayi zuruu.
Ummi ta share hawaye da gefen mayafin ta tace
"Duk da sun kore ni na ayyana a raina bazan yi nisa da nan ba sai na ga HAMDAH da take cikin gidan nan dan jiki na na bani kece kiyi hakuri HAMDAH."
na sake ta tare da faɗin "Ummi kiyi hakuri."
sai kuma na juyo in da security suke nace
"Uwa ta kuka yi wa wulakanci kuka hana ta shiga gidan duniya bana kiyama ba."
Ahmad ya ɗaga murya cikin tsawa yake ce da su,
"A wani dalilin zaku hata ta shiga bayan ta sanar da ku ko wacw ce ita!?."
suka haɗa baki wajen cewa "I'm sorry sir sabo da ba'a sanar mana da zuwan nata bane, kuma bayi zaton mamar Madam bace da gaske mun ɗauka waɗan da suke alakanta kansu da ita ne kawai dan a barsu su shiga."
Ahmad yace "Sai kuma baza ku iya kira ko zuwa ku sanar a kwai bako a waje ko ansan da zuwan sa ba? wani irin banzar aiki kuke ne!,
an ajiye ku kurika wulakanta mutane ne a bakin get."
Bappa yace "Sam bai dace ba ya kama ta idan irin haka ta faru, har idan ba'a sanar muku da zuwan bako ba, to idan yazo ba ku kore sa ba, ku nimi masaniya kan cewa an san da zuwan nasa ne sabo da wata rana zaku iya korin ɗan gidan abun kuma ba zai yi kyau ba,
to ba gashi yanzu kunyi a kan uwar mai gidan ba."
Ummi tayi murmushi cike da Dattaku tace
"A'a babu komai wlh, ai abakin ai kin su suke, kuma hakanne zai nuna tabbacin jajircewa kan aikin nasu, basu yi laifi ba sai dai kawai a kiyaye gaba."
security suka shiga bawa Ummi hakuri kamar zasu zuba goiwowin su kasa, tace wlh har cikin ranta babu komai kuma bataji haushi ba dan a bakin ai kin su suke.
na ja hannun Ummi cikin farin ciki muka yi ciki in da na karɓi jakarta na rike a ɗaya hannuna.
da sauri Inna Wuro ta fito dan Faty taje ta sanar mata Ummi na ta zo, a tare duk muka ɗunguma mukayi cikin parlour,
Bappa yace shi zai shiga Masallaci bari su yi salla zai shigo su gaisa,
a parlour Ahmad ya mika min Ahmad karami yace shima bari ya je yayi salla.
gaba ɗaya baki na yaki rufuwa farin cikin da nake jin kaina ciki tamkar anyi min albashir da aljanna.
a kan kafar Ummi na dire Ahmad karami, Ummi ta rike sa ta na faɗin "Yaya sunan sa?." nace Ahmad.
tace Masha Allah Allah ya raya da imani."
su Talatu suka shigo parlour'n suna kwasar gaisuwa da tayani farin cikin zuwan Ummi na.
Ummi ta kurawa Naseem da Nasmah ido da suke ta tsalle gefen ta sunayi wa Ahmad karami kawa, ta dube su da murmushi tace
"Yaya sunan ku?." kusa da ni Naseem ya zo ya kawo bakin sa kunne na yace "Mommy ita yaya sunan ta."
ido na waro tare da saurin toshe kunne na wai shi a dole magana a hankali zai yi kada kowa yaji amma kamar ihu yayi min cikin kunne.
dariya duka parlour'n a ɗauka, nace
"Mama na ne fa kun gaishe ta kuwa, sunan ta Ummi."
murmushi Ummi tayi yayin da ta kasa janye idanunta kan yaran, ta janyo hannunsu tana faɗin
"Bari na faɗa muku sunana kuma sai ku faɗa min naku, suna na Ummi ku ya sunan ku?."
Naseem ya washe baki yace sunan sa Naseem ita kuma sunan ta Nasmah.
ai ko Nasmah ta shiga bubbuga kafa kasa wai ita zata faɗi sunan ta da kanta.
Ummi tace "To faɗa min naji ban ji nashi ba."
ta washe baki tace Nasmah.
ai ko surutun su suka shiga cike ta da shi, suka rika bata rabaran da bata san tushin sa ba, har da labarin gobe Dadday'n su yace zai ɗauke su da kanin su ya kai su ya kara siyo musu lilon doki.
Nasmah ta wawwaro ido tace
"Kuma muna da wani har guda haka kuma Daddy'n mu yace zai kara mana guda haka."
tayi mata nuni da yatsun ta huɗu da kuma biyu wan da za'a kara musu.
Naseem yace "Zo kiga lilon dokin mu yana kusa da ɗakin ɗawisu ne fa."
yayi maganar shima yana wawwaro idanu
Ummi tace "To sai gobe