Showing 87001 words to 90000 words out of 125808 words
shigar ta na burge wa irin shigar manyan mata matan manyan mutane.
ta karaso jikin motar in da wasu sojoji guda huɗu suka mara mata baya,
ta buɗe gefen da nake fuska ɗauke da murmushi tace
"Ku sauko ku ake jira."
a hankali na zuro kafafu na waje na mike tsaye,
ɗaya daga cikin sojojin ya zaga da sauri ya buɗe gefen da Ahmad yake, shima ya fito, sannan a ka buɗe wa Ukhtee tafito rungume da Ahmad karami.
Naseem da Nasmah ma suka fito.
cikin harshen turanci Rasheedat tace wa Ukhtee ta bata ɗan bayan sun gaisa tayi mata maraba da zuwa kasar mu...
Naseem da Nasmah suna gaba ni da Ahmad muna biye da su, in da Rasheedat da Ukhtee ke bayan mu, Rasheedat nata gefen Ahmad Ukhtee kuma tana ta gefe na.
haka Rasheedat ta tsara yan da zamu tafi a jere,
takuma bawa Naseem da Nasmah wasu fulawa masu kyan gaske suka rike a hannun su.
a hankali muka fata takawa a sannu har muka isa bakin kofar da zai sada mu da ai nahin cikin hall ɗin.
a sannu muka kusa ciki, wani irin wal-wal haka hasken camara ke haska mu, a take aka saiya kiɗa aka saki wani zazzakar waka mai kwankwasa zuciyar masoya, ga mamaki na sai naji sunan mu ake ambata cikin wakar,
gaba ɗaya cikin hall ɗin yaɗau ki tafi raf-raf-raf, yayin da MC yashiga zuba kirari.
"Gafa taurarin sun danno farin wata sha kallo an gai da ango da amarya."
sai ya shiga bin wakar da ke tashin yana faɗin
"Ga HAMDAH sarauniya mata ga Ahmad sabil uwa ga Ahmad kaga mai farar aniya."
a hankali nake ɗaga kafata da naji tana yi min nauyi dan jama'ar da na gani cike a gun.
yayin da aka cigaba da haska mu da camara.
har muka isa mazaunin da aka tanadar mana,
kuje rune guda huɗu a jere sai wasu biyu ƴan madaidai ta a ta kasa da namu wato step ɗin dake kasa da mu.
a biyun tsakiya muka zauna ni da Ahmad Rasheedat ta zauna a gefen sa in da Ukhtee kuma ta zauna a gefe na,
Naseem da Nasmah kuma a biyun da ke kasan mu.
muna zama kuwa camara suka cigaba da haska mu,
ƴan jaridu ma aikatan gidajen TV ne ta ko ta ina a gurin sai ɗauka suke.
nan da nan akafara gudanar da biki, yayin sa ƴan wasan hausa da mawaka kowa ya fito yana nuna bajin tar sa.
taro yayi taro anyi ɓarin kuɗi,
ma'aikatan hotel da akayi odar su hotel daban-daban da suka girka kalolin abinci kala-kala. sai zubawa ake ana kaiwa tebur-tebur.
MC yace ana bukatar ango da amar ya su fito,
Rasheedat ta ɗan karkato in da yake tayi masa maga, sai ya riko hannuna ya mike kana ya mikar da ni, a hankali muka sauka muka shigo cikin filin.
wani kiɗan aka kuma sakewa shima da sunan mu cikin wakar.
yana rike da hannuna dukan mu muna tsaye, kai na na sunkuye,
yaɗan sunkuyo da kansa dai-dai fuskata yace
"Bazaki yi rawa ba."
kafaɗa na make cike da jin kunya nace
"Ban iya ba." yanayin yan da muke maganar da shi hakan yabada wani irin kala, ai ko hall ɗin ya kaure da ihu da tafe.
cike da jin kunya na kife kaina jikin kafaɗar sa.
hannu ya zura cikin aljuhu yaciro ɗaurin kuɗi ƴan 1-1k sababbi katakar yashiga lika min, yana murmushi ban ɗago ba kai na najikin kafaɗar sa,
sai da naji maganar Rasheedat daf da ni tana faɗin,
"Ba zakuyi rawa ba." sai na ɗago tare da girgiza mata kai ina murmushi.
liki tashiga yi mana tarika ciro kuɗi cikin jakarta tana wasa mana, ta dage tarika tika rawa.
nan manya manyan mutanen dasuka taho daga kasashe daban-daban suka rika shigowa filin suna lika mana kuɗi, wasu kuɗin kasar mu wasu kuma na kasashen da suke...
kai tsaye ake nuna shagalin bikin dan daga can jikin bangon hall ɗin katuwar majiki ne ke haska duk abin da ke faruwa..
biki yayi biki
naira tayi kuka agurin....
A can cikin garin Bauchi Masa'ud ne kwance cikin ɗakin sa da waya rike a hannunsa, yana kalle-kalle a yana gizo,
ido ya kurawa wani bikin da yaga ake gudanar wa,gani har ya shari kusan minti 5 bai ga shigowar ango da amarya ba sai ya wuce.
yana yin gaba kuwa yakuma cin karo da wannan bikin da ake hasko sa kai tsaye.
da mamaki yakurawa amaryar ido tare da maimaita sunan da yaji MC yana kira "HAMDAH!."
yafurta da karfi, yayin da hannunsa yashiga ɓari idanunsa a kan fuskarta, duk da ta kara girma da kuma kwalliyar dake fuskarta tabbas bazai taɓa iya mance fuskar nan ba.
da sauri ya mike yayi waje har yana cin karo.
tun daga bakin kofar side ɗin Mamie yashiga kwaɗa mata kira
"Mamie Mamie Mamie."
kasan cewar yau weekend ne su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleeta sun zo gida dukan su da ƴaƴan su,
Na'ima ma tazo da nata ɗan, duk suna hallare a sashin Mamie har da Ummi.
da sauri Mamie ta ɗago jin irin kiran da yake kwaza mata sai kuma gashi ya faɗo cikin parlour'n kamar an jefo sa, ko gaban sa baya gani.
tace
"Kai Masa'ud wani irin hauka ne haka, bazaka shigo ba tun daga waje kake lafta min kira irin haka kamar wani sabon makaho."
da sauri ya karaso in da take kamar zai faɗi a kan ta hannunsa na ɓari yace
"Mamie kigani Mamie HAMDAH HAMDAH ce."
sai kuma ya sake wa Mamie wayar da sauri ya juya ya fizge rimut ɗin da ke hannun Nusaiba ya daddan na sai gashi ya kamo ɗaya daga cikin tashoshin da ake haska bikin kai tsaye..............!
Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:58 - Ummi Tandama😇: 30
Masa'ud da gaba ki ɗaya ya jikin sa ya kama suma kamar zai tashi sama yace
"Mamie kun ganta wlh itace HAMDAH ce ga ta nan itace wannan."
yakai hannu yana taɓa jikin TV dai-dai fuskar ta.
gaba ɗaya cikin parlour'n suka mai da hankalin su kan TV. Aunty Rafee'at ta mike da sauri tazo jikin TV tana karewa wanda Masa'ud ke nunawa kallo, da karfi ta furta
"Wlh ita ce wlh HAMDAH ce wannan, masa musu su gani Masa'ud masa su ganta."
tayi maganar tana ture shi gefe.
Ummi da tayi mutuwar zaune tana kallon abin mamaki, sai ga hawayen farin ciki yana fitowa daga idon ta.
yayin da bakin ta ke ta furta kalmar
"Alhamdulillah³."
Mamie kuwa abun kamar a mafarki take ganin sa yayin da zuciyar ta ke ta son tunano mata abubuwan da suka faru abaya, yayin da wani abu ya taso yake ta son danni hakan.
kokawa tashiga yi sakanin zuciyar da wannan abun da ke ta faman son danne hakan, lallai ba shakka wannan HAMDAH ce, duk da girma da cika da sauyin da ke tattare da ita, koda shekaru ɗari tayi basa tare bazasu kasa gane jinin su ba.
wasu zafafan kwalla ne masu ɗumi suka zubo mata, takasa iya furta komai kamar yadda ta kasa janye idanunta daga kan TV.
hannunta na rawa ta shiga nuna TV da yatsa yayin da bakin ta yakasa iya furta komai, sai zafafan hawayen da suka cigaba da wanke mata fuska.
Da gudu Aunty Jaleela taje ta rungume Aunty Rafee'at tana faɗin
"Wlh ita ce HAMDAH ce Aunty Rafee'at da gaske ita ce."
Nusaiba da Fauzan ma suka mike suka rungume suna faɗin
"Aunty HAMDAH ce wlh ita ce."
parlour'n ya kaure da hayaniya da ihun murnar da su Aunty Rafee'at suke..
A ɓangaren Na'ima kuwa tun san da ta sanya idanunta kan HAMDAH dake cikin TV, tayi wani irin daskarewa
a zaune a gurin, wani irin bugawa kirjin ta yayi da mugun karfi har sai da takai hannu ta dafe kirjin nata.
su Abbu da suke zaune cikin parlour'n da suke zama shi da Abba, jin hayaniyar dake fita daga cikin side ɗin Mamie yayi yawa sai suka mike da sauri suka fito.
dai-dai lokacin motar SALEEM yashigo gidan, daga cikin mota ya hangi yan da su Abbu suke sauri suka nufi side ɗin Mamie.
cikin hanzari ya faka motar yafito yarufa musu baya.
a kusan tare suka shiga parlour'n Mamie Abbu ya buɗi baki da zumbar tambayar abin da kefaru idanunsa ya sauka kan TV dai-dai lokacin da aka hasko katon hoton HAMDAH wan da ya maimaye fuskar TV gaba ɗaya,
inda ɗan jarida yake faɗin
"HAMDAH kenan shahararriyar ƴar kasuwan nan wacce aka fi sani da *HAM'NAS CO PETROLEUM NIGERIA LIMITED*
ayau ne ake gudanar da shagalin bikin su da kuma murnar samun karuwan ɗa da sukayi, ita da mijinta shahararren attajin nan shahararren ɗan kasuwan nan wacce duniya ta sanshi wato *AHMAD TIJJANI SABIL* ."
sai a ka ɗauke hoton ta kana aka kuma sakin wani katon hoto, tana tsaye rike da jariri Ahmad na tsaye a gefen ta ta dama yaɗan leko fuskar ta suna yi wa juna murmushi, in da Rasheedat ke tsaye gefen ta na hagu, Naseem da Nasmah suna tsaye a gaban su suna dariya,
ɗan jaridar yaci gaba da faɗin
"Kai tsaye ake gudanar da shagalin bikin, gamu nan a filin taron, biki yayi biki jigajigan shararrun ƴan kasun nan kuma ma'aurata Ahmad Tijjani Sabil da amaryar sa HAMDAH wacce akafi sani da *HAM'NAS* Co petroleum Nigeria limited,suna cike da murna da farin cikin kuma samin karuwa da farin cikin karuwan family'n su, muna nan zamu cigaba da kawo muku yan da bikin take kasan cewa a filin taron kai tsaye kucigaba da biyo mu."
shagalin bikin aka cigaba da nunawa...
Kamar a mafarki kamar abun almara haka dukkanin su suke kallon.
yanayin da Mamie ta shiga shi Abbu ya shiga, sai nuna TV yake da yatsa, Abba kam baya yayi ya jingina da jikin garu yayin da idanunsa shima ke kan TV.
a ɓangaren SALEEM kuwa wani irin wawan burki yaja yatsaya cak daga bakin kofa, yayin da zuciyar sa tayi wani irin tsalle tamkar zata faso kirjin sa ta fito,
wani irin rumtse idanunsa yayi da mugun karfi yakuma ware sa a kan TV,
dai-dai lokacin da Ahmad ya rungumo ta ita da baby'n su suna dariya, yayin da wani bature yake yi musu liki.
da karfi ya kai hannunsa ya dafe kahon zuciyar sa,da yake wani irin tafarfasa, wani tari ne ya suɓuce masa yashiga yin sa babu ko kakkautawa yana mai cigaba da damke kirjin sa,
baya yashiga yi hannunsa na dafe a kirjin sa.
Masa'ud ne yalura da halin da yake ciki da sauri ya isa in da yake, ya yana faɗin
"Ya SALEEM sannu ka shake ne bari na kawo maka ruwa."
hannu ya ɗaga masa kana yayi waje dafe da kirjin sa yana mai cigaba da tarin...
zumbur Na'ima da zufa yashiga keto mata ta mike tsaye ta tsaɓe ɗan ta tayi waje da sauri, mai adaidaita ta tsare yakai ta gida, tana shiga gida hankali tashe takira kawar ta Raliya a waya tana ɗagawa tace
"Raliya kina ina." jin yan da tayi maganar hankali tashe yasa Raliya faɗin
"Aminiya me ya faru? ina gida yanzu dai nake shirin fita."
tace "Kizo gida yanzu-yanzu akwai matsala."
Raliya tace "Wacce irin matsala kin tsinkar min da gaba."
cikin tsananin tashin hankalin da take ciki tace
"Ashe yarinyar nan bata mutu ba tana nan a raye, ashe ita ce mai kamfanin *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Co Petroleum Nigeria Limited."
Raliya tace
"Wai wa kike magana ne kam ban gane ba."
tace "HAMDAH HAMDAH nake faɗa."
da karfi Raliya tace "Wacce HAMDAH ke bari gani nan zuwa."
tana kashe wayar ta zari makullin mota tayi waje,
tarika kai wa da kawowa a parking space har Raliya ta iso. Raliya
tace "Wai me kike faɗa min ne kina nufin kice min HAMDAH bata mutu ba tana raye kuma anan kusa?."
da sauri Na'ima tashiga mota tana faɗin "Shiga shiga zakiji komai a hanya kada mu ɓata lokaci."
Raliya na shiga ta figi motar da mugun gudu suna fita a gidan Na'ima
ta dubi Raliya hankali a mugun tashe tace "Aminiya HAMDAH na da rai ko kin san ita ce me kamfanin *HAM'NAS* sai gata ɗazu ana nuna ta a TV ita da wannan mai kuɗin Ahmad Tijjani Sabil amatsayin miji da mata, Raliya ina cikin muguwar tashin hankali gurin boka zamu je yanzun nan, shi da yace baza a sake jin ɗuriyar ta ba kwasam sai na ganta cikin daula, dole na sake sabon shiri ya daɗa jefa ta can da nisa taya ne ma ta kasan ce haka ina wlh da sake wai HAMDAH ce tazamo mai kuɗi kuma wai har ta auri hamshakin attajiri, wani bokan ne yabata sa a haka."
kirji Raliya ta buga tace
"Wai da gaske HAMDAH ce mai kamfanin *HAM'NAS* amma taya akayi haka? kai amma ni ina da kokon to kan lamarin."
Na'ima tace "Ga abu a fili a TV naganta da idanuna ba faɗa min akayi ba mu gurin boka bamuyi haka da shi ba maza-maza yakashe ta kawai idan ba mutuwa tayi ba bazan taɓa samin sukuni ba."
gudu Na'ima take shararawa har suka iso dajin da bokan yake,
a gindin bishiyar da suke faka motar su a duk san da suka zo gurin bokan a nan suka faka motar suka fito.
da sauri nufi in da bukkan bokan yake, tun kan su haura kan tudun da zai sada su da bukkan suka rika jiyo gurnani da wani irin kala mai firgitar wa,cike da fargaba Raliya ta dubi Na'ima tace
"Ko kinji abin da nake ji?."
cikin bushewar zuciya
Na'ima tace "Naji yanzu haka wani gagarumin ai ki yake muje a shigar da namu gaba ɗaya ayi akashe ta na huta."
suna haurawa saman tudun babu shiri suka ja wani wawan burki, gaba ɗayan su jikin su ya ɗau ɓari.
bakon suka hango kwarkwasa sun maye jikin sa tun daga saman sa har kasa ko fuskar sa ba'a iya ganin, sun cike ko ina a jikin sa, kunne ido baki hanci ta ko ta ina sun baibaye sun rufu a jikin yam-yam.
shiko sai wani irin kara da gurnani yake, sai ya yanki jiki ya faɗi akasa ya goga fuskar sa a kan duwatsun da suke gurin yayi ta goga wa jini yana fita, yakuma mike wa yakuma faɗuwa kamar wan da ake ɗaga shi ana buga shi da fuska, kwarkwasar nan kuma suna nan a jikin sa.
da mugun gudu suka juya ganin wasu kwarkwasa suna gangaro wa in da suke, nan take bokan nan yakuma yin sama kamar wan da aka ɗaga shi sai gashi cikin wutar da yake hurawa domin yin wani asirin sa ko shan ɗumi.
yayi ta birgima yana bige-bige da kara haɗa da gurnani mai firgitar wa cikin wutar.
Raliya da Na'ima har suna rige-rigen shiga motar har gindin motar kwarkwasar na suka biyo su Na'ima ta ja motar a guje suna waigen bayan su da duba kasan kafar su ko kwarkwasan sun biyo su..
sai da sukayi nisa sosai kafin Na'ima ta dubi Raliya tana haki tace
"Raliya boka ya mutu yanzu meye mafita?."
Raliya tace "Gurin wani bokan zamu je ai basu kare ba."
daga nan suka nufi gurin wani bokan
da Raliya ta faɗa mata ita ma wata kawar tace ta nuna masa gurin sa.
suna zuwa bayan sun gama zayyane abun da ya kawo su, bokan yace
ta ajiye miliyan 10 wan da za'a fara ai ki da shi, dan ai kin nata babba ne.
babu wani dogon nazari ko tunani ta ajiye masa check ɗin miliyan 10.
yace suje nan da kwanaki biyu su dawo...
A ɓangaren su Ummi kuwa kowa ya tsurawa TV ido in da ake kan cigaba da gudanar da biki,
yayin da su Ummi Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Ya Masa'ud Fauzan Nusai ba, duk kanin su hawayen farin ciki ne ke zuba kan fuskokin su.
Abba da Abbu kuwa ido suka zubawa TV kawai, har kuma lokacin suna tsaye da ƙafafun su,
duk kanin su kuma sun kasa iya furta komai sai zuciyoyin su dake ta ambaton sunan Allah dayi masa godiya.
a hankali suka rika jin zuciyoyin su tana washewa tamkar ana ɗaga musu wani nannauyar dutse data danne musu zuciya.
Abba Abbu Mamie a tare suka dafe kirjin su da suka ji kamar an fincike wannan abu mai nauyi an cire sa gaba ɗaya,
a tare suka sauke nannauyar numfashi...
a ɓangaren SALEEM da tun fitar sa daga parlour'n ɗakin Masa'ud ya shiga ya kwanta kan gadon sa, dafe da kirjin sa har kuma lokacin yana dafe da kirjin nasa, wacce take yi masa wani irin mugun zafi, a take shima yaji kamar an fige masa wani abu mai nauyi cikin zuciyarsa, sai dai zafi da zugin da zuciyar tasa take masa...
Acan cikin parlour'n kuwa Mamie ne tayi wani irin mike wa tare da furta "Wlh HAMDAH ce tabbas ita ce, Alhaji baka ganta ba?."
tayi maganar tana duban Abbu.
Abbu yashiga gyaɗa kai yana nuna TV da yatsa tare da faɗin
"Tabbas ba shakka ita ce."
wani hawayen farin ciki ne yakuma zubowa kan fuskar Ummi, ganin yan da sukayi firgigit tamkar waɗan da suka farka daga bacci, tasan dole watarana gaskiya zatayi halin ta.
Abba kuwa cikin matukar nadama yake kallon ɗiyar tasa daga cikin TV.....
Abuja
Har wajen magriba ana ta kan gudanar da shagalin bikin, salla ce kaɗai take ɗaga wasu agun.
da misalin karfe 11 na dare aka rufe taron bayan an cike waɗan da suka zo bikin da kayan da Ahmad yasa a tanada domin duk wan da ya ziyarci bikin,
duk wan da yazo bikin idan mamace turamen manyan zani guda biyu da kuɗin ɗiki naira dubu goma acikin jaka mai ɗauke da katon hoton Ahmad karami a jiki.
idan kuma na miji ne tsadadden shadda ne shima guda biyu haɗe da kuɗin ɗin kin sa a cikin jakar.
a gajiye muka fito daga cikin hall ɗin mota ta kwashe mu.
ga mamaki na sai na ganmu a airport,
da fuskar mamaki na dubi Ahmad nace
"Rakiya muka zo ne?." da murmushi kan fuskarsa sa yace "Mu aka zo raka mu."
nace "Ina?." nayi maganar ina waro ido.
kuma tuna yaja kana yace "Lagos zamu, gobe za'ayi bikin buɗe Company ki na can, wan da ɗana ya hanaki samun sukunin buɗe shi."
baki na buɗe zanyi magana sai aka buɗe marfin motar,gefen sa da fege
na, sai nayi shiru na fito kawai.
direct cikin jirge muka shige anan na tadda wasu daga cikin mutanen da suka halar ci bikin mu waɗan da suka zo daga wasu ƙasashe har da wasu ɗaiɗai ku ƴan nan kasar mu,
a can kujerar gaba na hango Bappa yana zaune, acikin jirgin nake faɗa wa Ukhtee in da zamu je, na tausaya mata ganin yana yin ta na san tafaji sosai.
a jere suka zauna da Aunty Rasheedat da Naseem da Nasmah, in da muka zauna ni da Ahmad a kujerar bayan su, yana rungume da Ahmad