Showing 111001 words to 114000 words out of 125808 words
zube a gurin tana rusar kuka mai ban tausayi.
abun mamaki duk hayaniyar da ake ɗinan security suna ta sharar bacci karnukan gadi kuma suna zaune in da suke tun ɗazu basu ko mosa ba bare suyi haushi.
motar ambulance da ta iso yanzu cikin hanzari polisawa suka ɗauki Ahmad suka saka shi cikin motar,
in da wasu daga cikin police ɗin duka shige cikin motar
da mugun gudu motar ta fice a gidan.
sauran gawawwakin ɓarayin dake kwance har da mai gadi suma a ka zuba su cikin wata mota aka tafi da su,
ɓarayi biyu kuma da suke da rai wan da Ahmad ya harbe su a kafafun su a ka zubasu cikin wata mota suma a ka tafi da su...
kan kace me a cikin daren unguwar gaba ɗaya ta gama hargitsewa hankalin kowa ya tashi da jin abun da yafaru, matasa suka fito kowa da makamai nan karamar zanga-zanga ya kaure, sai da hukuma sukayi da gaske.
a take a lokacin labari ya iske mahaifan Rasheedat hankali tashe suka iso gidan a cikin daren,
Alhaji Bashir mahaifi ga Rasheedat kani kuma wa Alhaji Tijjani Sabil,Bappan Ahmad kenan, hankalin sa yayi mummunar tashi a take yabi bayan motar da aka tafi da Ahmad, in da mahaifiyar Rasheedat kuma ke tare da ita agidan....
sai da aka kira sallar asuba kafin security suka farka duk tulin bubbuga su da sojojin da suka zo sukayi domin su farka baisa sun farka ba sai a lokacin,
karnuka ma suka kama haushi da tsalle kamar zasuci babu.
hankalin security'n yayi masifar tashi da jin abun da ya faru wan da suna cikin gidan basu kuma san da faruwar hakan ba.
koda ƴan jaridu suka nimi jin ta bakin su sun shaida musu cewa
su sam basusan da faruwan komai ba sun dai sinci kansu cikin yin bacci mai nauyi, bayan da mai gadin gidan ya rabamusu lemun gora a daren ranar yakuma shaidar musu da cewa ogan su ne ya bashi ya basu wato Ahmad ɗin kenan,
shan su kuma bada jimawa ba bacci mai nauyi ya ɗauke su, wan da basu farka ba kuma sai yanzu.
ɗaya daga cikin security ya bada tabbacin cewa
shi bai sha lemun da wuri ba ya aje nashi sai daga baya yasha, lokacin da bacci ya fara fizgarsa bai kai ga ɗaukar sa ba yaga mai gadin yaje in da karnuka suke yana fesa musu wani abu, sai dai baccin da ya zo mishi babu zato ya hanashi tashi ya bincike mai gadin kan abun da yake yiwa karnukan...
har gari yayi haske sosai sojoji na zagaye da gidan, tuni gidajen TV dana rediyo suka fara sakin labarai kan rahoton da suka samu.....
A parlour mukayi salla dukan mu har da su Bappa, dan Bappa yaki matsawa ko nan da can daga in da nake.
ganin gari yayi haske kuma har zuwa lokacin security basu zo da Ahmad kamar yadda Bappa ya faɗa ba.
gashi duk kiran wayar sa da nake baya ɗagawa,
na saka musu kuka nace ni sam zan tafi zanje da kaina gidan.
wayar Bappa ce tayi kara, ya ɗaga tare da yin sallama.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un."
abun da Bappa ya furta kenan, zumbur na mike tsaye ina kallon Bappa, Bappa ya kawar da kansa tare da sauke wayar a kunnen sa, yayin da laɓɓan sa ke motsawa alamun salati yake.
ɓari jikina ya soma murya na rawa nace
"Bappa mene ne wa yayi maka waya?."
kai ya girgiza yayin da idanunsa suka kawo kwalla, sai ya kawar da kansa daga kallo na yace
"Babu komai je ji sa babban mayafi ki zo sai muje gidan Ahmad ɗin kawai tun da har yanzu basu zo ba."
ya dubi Inna Wuro yace
"Je ki rakata tasa mayafin."
sai ya sauya harshen sa izuwa fulatanci yayi mata magana cukin harshen fulatanci,
Inna Wuro ta saki salati tana dafe kirji, sai kuma tayi saurin sauke hannunta a kirjin sabo da maganar da Bappa ya kuma mata da fulatan ci, ta ruko hannuna yayin da hannunta ke ɓari ta janyo ni muka haura sama.
muna shiga muka tadda su Naseem duk sun farka, tace na cire hijabi da kayan baccin da ke jiki na na sa wani kayan.
jiki a sanyaye yayin da hawaye ke bin fuskata nayi kamar yanda tace, nasaka babban hijabi, kana ta ruko hannun su Nasmah ni kuma na ɗau Ahmad karami muka sauko kasa.
tun kan mu karaso parlour'n kasa su Mama suna ganin mu kowa ya shiga sun kuyar da kai suna share hawayen su cikin dabara sai kowa ya mike da sauri akayi waje gaba ɗaya.
da sauri na ɗaga murya nace
"Kukan me kuke yi?."
da sauri Bappa yace
"Kuka kuma sam ba wan da yayi kuka a cikin mu."
cikin rawar murya da kuka ke son kwace min nace
"Na ganku da idona na, ganku kuna kuka ku faɗa min kukan me kuke yi?."
Mama tayi murmushi wan da yafi kuka ciwo tace
"A ina kuma HAMDAH mu sam bamuyi kuka ba muje direba yana jiran mu."
ta ruko hannuna muka karasa fita waje...
koda muka iso parking lot Bappa yace su Zulai su zauna da su Naseem a gida.
a tsakiya suka sani Mama da Inna Wuro, Ahmad karami na rike a hannu na, Bappa kuma ya zauna a gefen mai zaman banza, direba yaja muka fita.
ina zaune shiru hawaye na zuba a idona na, ido na kurawa titi ganin mun ɗau wata hanyar daban ba hanyar gidan Ahmad ba.
a bakin wani katon asibiti direba yayi hon, aka buɗe masa ya sakai ciki ya faka motar muka fito, asibitin zagaye yake da sojoji da ƴan sanda, can na hango Abba Bashir yana sunkuye da alamar kuka yake, wasu mutane na tsaye a kansa. Inna Wuro ta karɓi Ahmad karami dake hannuna, Mama kuma ta ruko hannuna gam ta janyo ni muka nufi cikin asibitin.
da kyar nake iya ɗaga kafafu na da sukayi min mugun nauyi,
maganar Mama na jiyo tana faɗin
"Ba a ja da ikon Allah duk abun da kaga ya sami bawa da sanin ubangiji, Allah kuma baya barin wani dan wani yakan kuma jarabci mutum ta ko wace hanya domin ya gwada imanin sa,
yana da kyau mu kasan ce masu karɓar kaddara mai kyau ko mara kyau aduk san da tazo mana,
Allah yafi mu son bayin sa duk son da muke musu, hakuri kuma shine magani nasan ki da hakuri da iya karɓar kaddara ina fata yau ma ki kasan ce a haka, kice Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kici gaba da nanata shi cikin ranki."
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un³."
nafaɗa da karfi har sau uku dai-dai lokacin da muke sakai cikin parlour'n asibitin, Mama ta daɗa rike hannuna gam jin yan da ilahirin jikina yaɗau ki ɓari tace
"A hankali zaki faɗa ko a cikin ranki ki nusu HAMDAH."
muna shiga jami'an tsaro suka dakatar da mu suka ce mu tsaya anan, wani soja ne ya fito daga cikin wani room yakaraso in da muke yace "Zata iya shiga yanzu."
Bappa ya dube ni cikin rauni yace
"Kullu nafsin za'ikatulmaut duk mai rai mamuci ni, muma bamu da tabbacin zamu iya kaiwa nan da dakika ɗaya, Allah yayi wa Ahmad rasuwa ki daure kiyi masa addu'a."
wani irin dimm haka naji kunnuwa na sunyi min mugun nauyi jiri haɗe da bakin duhuwa ya gilma min,
kallon bakin Bappa nake domin tabbatar da abun da yake faɗa dan ni dai a yanayin da nake jin kaina ciki da yan da maganar tazo min a sama sai ji da gani nake kamar ba gaskiya bane, bakina kuma yayi min mugun nauyi na kasa iya furta komai.
sojan yace
"Madam bismilla sai hakuri fa."
yayi maganar yana nuna min hanya Inna Wuro ta mika min Ahmad karami, kana sojan yayi gaba na bisa a baya ina jan kafata da kyar.
muna isa jikin kofar room ɗin ya murɗa handle ɗin ya shiga, kana yaɗan ja gefe ya bani hanya na sako kai na ciki.
kana ya mai da kofar ya rufe, sojoji ne tsaitsaye cikin room ɗin haɗe da likitoci,
ido na kurawa kan gadon da nake hango mutum kwance an lulluɓe shi daga sama har kasa, jikin a bun da aka lulluɓe sa da shi da ɗigo ɗigon jini tagurin kirjin sa da gefe da gefen cikin sa.
wani dake tsaye ta gurin kansa ga dukkan alama babbane dan da zaran yayi magana sai sauran jami'an tsaron su sara masa.
ya ɗaga hannu tare da yi min alama dana karaso, a hankali naja kafafu na zuwa bakin gadon, ya dube ni tare da faɗin
"Allah ya baki hakuri mun kira ki ne abisa cika masa burin sa na karshe, kiyi hakuri bamusan rai zaiyi halinsa ba tun a daren jiya yanemi da a kira ki sai dai ganin halin da yake ciki yasa muka kasa iya ai watar da hakan burin mu kawai likitoci su samu nasarar kuɓutar da shi daga halin da yake,ga wannan a hannunsa muka samu bayan cikawar sa, ko da muka duba sai muka ga a kanki yake maganar shine muka neme ki kafin mu ɗaga shi a nan mu damka miki sakon sa a hannun ki."
ya mika min takarda wan da gefe da gefen takar dan duk da ɗigon jini,
hannu na na ɓari na karɓi takardan na dunkule shi cikin hannuna.
mutumin ya dubi nakusa da shi yace
"Ku buɗe mata shi ta gansa." ya yaye abun da aka rufe shi da shi daga kansa zuwa wuyan sa.
da gaske Ahmad ne a kwance wan da tun ɗazu ban gaskata abun da suke faɗa min ba sai gani nake kamar ba gaskiya bane.
wani irin tsalle zuciya ta yayi tamkar zai faso kirji na yafito,yayin da ilahirin jiki na ya ɗauki ɓari.
a hankali nashiga jan kafata ina daɗa matsowa bakin gadon yayin da idanuna ke kan fuskarsa, yana kwance idanunsa a rufe yayin da fuskarsa ke bayyane da kayataccen murmushin sa, tam kar akirasa ya amsa.
kai na shiga girgizawa nashiga kokarin motsa laɓɓa na, na mika hannu izuwa jikin sa, nashiga girgiza shi tare da sakin kuka mai taɓa zuciya cikin muryar kuka sosai tamkar numfashi na zai fita nashiga faɗin
"My bana son irin wannan wasan!, My kafarka dan Allah kadai da min irin wannan wasan,ka tashi mana nice fa gimbiyar ka kyakkyawar ka, ka tashi ka gani gani ga Ahmad ɗan ka ɗan da ka fara samu a duniya, shin ka mance alkawarin da ka min da bakin ka kace min bazaka taɓa bari nakara yin kuka ba, kar kayi min haka kar ka tafi ka barmu dan Allah My dan Allah ka tashi so kake Ahmad ya zamo maraya, ka buɗe idanun ka ka faɗa min kalmar da kake faɗa min kullum kana sona nima ina son ka My ina sonka ina sonka My, My ka tashiiiiiiiii kar ka mutu dan Allahhhhhhhhh!!!."
kuka yaci karfi na sai kawai na kife kansa tare da ɗaura Ahmad karami a kansa na saka fuskata kan nashi nashiga goga fuskata cikin nashi ina wani irin kukan danake jin ina ma ace yanzu nima na mutu na bishi, Ahmad karami ya saki kuka yana cakumar sa...
mutumin da ya sa aka buɗe min shi ya girgiza kai tare da share kwalla, kana yace
"I'm so sorry Madam hakika muma munji ɗacin rasa gwarzon jami'in sirri kamar Ahmad, sai dai abun farin ciki duk da bulet har uku da suka same sa a gurare daban-daban wan da ko da ace harbi ɗaya ne bazai iya taɓuka komai ba, amma da bulet ɗin a jikin sa ya kashe mutane biyar yayi wa biyu mummunar raunin da bazasu iya morar raruwar su ba, hakika wannan abun alfahari ne, Allah ya baki hakuri."
sukace na tashi a ɗaga shi fir naki sai ma daɗa kankame shi da nayi.
da kyar babban sun ya iya janye ni a jikin sa,ina mike wa a jikin sa sai ji nayi tamkar an fisgo ni sai kawai na yanki jiki na zube a gurin nan take hankali na yabar jiki na ban kuma sanin abun da ake ciki ba....
After 5 hr.
Sai a lokacin na farka daga doguwar sumar dana tafi,
a hankali nashiga buɗe idananuna dasuka yi min mugun nauyi, maganar Ummi na najiyo a kusa da ni, da sauri na yunkura zan mike, Ummi tayi saurin rike ni tana faɗin
"Yi a hankali HAMDAH."
nace "Ummi ni tashi zanyi." Mamie dake zaune a gefe da waya a kunnen ta tana faɗin
"Mun iso sai dai har yanzu bata farfaɗo ba."
sai kuma tayi saurin kashe wayar ta mike tazo ta rike ni tana faɗin "Zaki iya tashi?."
kai na gyaɗa, tace "To tashi." suka taimaka min na mike zaune,
kokarin durowa a gadon nake Ummi tace
"Da kata HAMDAH ina zaki ko fisari kike ji?."
kuka na fashe da shi nace
"Ni gun Ahmad zan je." hawaye Ummi ta share Mamie tace "Kiyi hakuri HAMDAH, ki tsaya ki daɗa samin sauki tukun."
kai na shiga girgiza wa ina faɗin "A'a ni gurin sa zanje ni dai zanje."
duk yan da suka kai da lallaɓi na fir naji nace nidai gurin sa zani, haka suka hakura suka kyale ni.
na sauko a gadon da gudu nafita a room ɗin, nashiga waige-waige room ɗin da aka kwantar da Ahmad na nufa a guje na tura kofar na shiga, turus nayi cikin ɗakin ganin babu kowa ciki. sai kuma na juya a guje tare da kuka sakin kuka nayi,
su Ummi da suka biyo baya na suka ruko ni.
Mamie ta rike ni gam tana faɗin
"Ki nutsu HAMDAH." nace "Ni gida zan tafi an mai da Ahmad gida nidai gida zanje."
Su Mama Inna Wuro Ummi Mamie duk kanin su hawaye suke cike da matukar tausaya min, Ahmad karami na goye a bayan Mama yana bacci sai sauke ajiyar zuciya yake.
Mamie tace "To muje gidan...
ko da muka iso gida direba na dai-dai ta parking na fito da gudu nayo cikin side ɗi na,tun daga parlour'n kasa nake faɗin
"My kana ina My kadawo gida ko."
har na haura sama ban fasa kiran sa ba, na shige bedroom ina ta waige-waige.
Ummi data biyo baya na da sauri ta ruko ni tana faɗin
"HAMDAH kidawo cikin hayyacin ki, ki nutsu kiji ni, Ahmad ya rasu mutuwa kuma ba karya bace, yanzu addu'a kaɗai yake bukata shi da ma yayi kyakkyawar tafiya ki nutsu ki sawa zuciyar ki salama ki fauwalawa Allah komai, hakika akwai ciwo amma ki daure, ki daure jin ƴata ƴar albarka Allah ya baki ikon cin jarabawar ki."
"Ummi yanzu shima ya tafi kenan bazan sake ganin sa ba kenan Kamar Inna."
kwai Ummi ta shiga girgiza wa tana kwalla.
rungume Ummi nayi tare da sakin wani irin kuka, bata hanani yin kukan ba sai bubbuga bayana da take itama tana kwalla.
su Mama suka janye ni a jikin ta suka zaunar dani bakin gado na zube a gadon ina mai ci gaba da rusar kukan..
Basu hanani kukan ba sai da nayi sosai kafin suka fara rarrashi na, da ban baki har nayi shiru,sukayi ta bani baki haɗe da nasihohi nidai ina nan zaune amma hankali na baya gurin, nan Ummi suke shaida min tare suka zo da su Abbu suna gidan Ahmad can in da ake zaman makoki...
Bayan kwana uku..........!
Mommyn Twin ce
8/19/22, 11:01 - Ummi Tandama😇: 37
Haka zan rungume Ahmad karami nata kuka cike da tausayin sa da kuma tausayin kaina,sai Mamie ko Ummi sun karɓe sa, tun ranar da Ahmad ya rasu Ahmad karami yaki shan nono,
Ummi tace a ɗaga shi kawai a nonon tun da ya makai na yaye...
A ko da yaushe su Ummi suna tare da ni basa taɓa barina na zauna ni kaɗai,yau su Aunty Rafee'ta suka zo ita da Aunty Jaleela da Ya Masa'ud da Goggo Hauwa,
da yamma suka ɗunguma suka je gidan Ahmad domin yi wa ƴan uwan sa da Aunty Rasheedat ta'aziyya har da su Mamie.
kamar yadda suma ƴan uwan nasa suke zuwa har dama ƴan uwan Aunty Rasheedat domin yimin ta'aziyya.
Abba Bashir da mahaifiyar Aunty Rasheedat su tun ranar rasuwar ma suka zo nan..
tare da su Abbu su Ummi suka dawo dan yau an gama zaman makoki...
ranar bakwai da safe Alhaji Bashir da mahaifiyar Aunty Rasheedat da ita Aunty Rasheedat ɗin da wasu daga cijin dangin su, da shaidu da kuma laiyoyi, da manyan malamai suka zo.
duk kanin mu muka hallara a parlour'n kasa.
Aunty Rasheedat na rungume da Ahmad karami a jikin ta, ta kura masa ido sai kawai ta fashe da kuka, ni ma kukan na fashe da shi dan nasan abun da nake ji a raina itama shi take ji.
rarrashin mu akatayi tare da yi mana nasiha har sai da zuciyoyin mu suka sami salama, kana a ka soma gudanar da abin da ya taramu wato rabon gado.
duk kanin dukiyar Ahmad da kaddarorin sa na nan gida Nigeria da kuma na kasashen waje da wan da aka kashe shi domin sa wan da ya damkawa manajan banki, duk aka haɗo kansu.
batare da ɓata lokaci ba malamai suka fara gudanar da rabon gado kamar yadda shariya ya shar'anta, duk kannnin mu uku a ka dan kawa kowa abin da ya gada ni Aunty Rasheedat da kuma Ahmad karami, nayi mamakin tulin dukiya da kandarorin da Ahmad karami ya gada,
daga mahaifinsa nakuma yi mamakin tulin taren dukiya irin na Ahmad.
Washegari su Abba Abbu Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Ya Masa'ud suka koma Bauchi, yarage saura Ummi na,
Ummi tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta gusar min da damuwa ta dan ko nan da can bata matsawa koda yaushe tana tare da ni.
yanzu Mama ma ta dawo side ɗina ita ma muna tare..
lokacin da mukayi arba'in Ummi tace zata koma gida,
washegari bayan ta gama shiri ta je sashin su Bappa bayan sun gaisa take sanar masa yau insha Allah zata koma sannan ta ɗaura da faɗin
"Bappa ina so na tafi da HAMDAH tadanje tayi kwana biyu."
Bappa yace
"Kwarai kuwa kinyi tunani me kyau tafiya da ita ɗin shiyafi saboda acan zata zauna cikin yan'uwanta da iyayenta tunaninta zai ragu akan zamanta anan ɗin, Allah yatsare yakiyaye hanya."
Ummi ta amsa da Amin...
ina zaune dasu Naseem da Nasmah suna gefena sai rikici suke min kaman kullum Naseem daya ware baki zaiyi kuka yace "
Mommy ina Daddy kince zai dawo."
kwalla nashare nace "Naseem nace muku daddy zai dawo daddy yayi tafiya zai dawo." Nasmah tace "Mommy nikam kikaini gun Daddy kinji Mommy."
kaina girgiza yayin da hawaye yake zuba a idona inajin yadda yaran suke bori Naseem yasaya yana fadin nikam ki kiramin Daddy, yami kamin