Showing 93001 words to 96000 words out of 171805 words
Chapter 32 - Inso Cuta Ne Book One Complete Hausa Novel
addabarmin ke kou..don wlhy duk yadda aka kaiga son aurennan inhar zainab na takura miki aurennan baki zamanshi sede ayi yadda za ayi.."
Sahura tace "Insha allahu bazama ayi hknba.."
Jannarht de batace komiba..nan hira ta kacame tsaninsu hirar yaushe rabo jannarht kam se sangartarta takeyi yadda taso..
Hammad Kam yanacan zaune duk byn yan minyoci seya duba wayrshi ya wosa suje gida shide nonon nan na tsole masa ido ynason ya tabasu yji sanyi sanyi....
Har wajajen after magrib suna nan suna hirarsu se sallah ke tadasu,. Duk sunma mnce da wani hammad...har akayi isha I. Ummih tayi feeding jannarht da tuwon semovita miyar yauki. Byn sun Gama sun dawo falon suncigabada hirar shap kowa ya mance da wani hammad. "Wai Anty a nan zaki kwana ne.." cewar sahura
Ummih tace "innalillahi...kngani nama manta shap wallahi..ashe mijinki na motar yana jirnk..
Tashi ki tafi.."
Jannarht tace "Ni a nan zan kwana.."
"Kin tambayeshi.."
Girgiza Kai jannarht tayi ummih tace "saboda a garin gaba gaba muke kawai byn mun dauki alhakinshi tin dazu ynacan yna jirnki kuma seki kwana...sahura jeki hada abinci ki kawo mata takai masa.."
Jannarht ta turo baki tace "habade Ummih takai masa ita.."
Ummih tace "okay haka kikeyi masa a gidan ko..tou kideyi ladabi da biyayya shi aure ba ruwanshi da mgnr shekaru..ni tin farko ba yaron bane bnaso mahaidiyrshice bana kauna a duniyarnan..tinda Allah ya hada knga se hkri...na miqama Allah lamarina.." ummih tamrshe mgnr cikeda sarewa. Jannarht de najinta ita ta rasa abinda yasa Ummih tayi sanyi hk.lallai da walakn goro cikin miya.
Sahura ta hado komi a trea din ta kawo falon. Ummih tace "amsa ki kai masa.."
Lamgwabewa jannarht tayi tace "Ummih Dan Allah ta kai masa kafana ciwo.."
Ummih tace "aishekenan..tafi da key din stting room ki kaishi can yadda zeji dadihn cin abincin."
Tou sahura tace ta juya tabar falon. Direct gun motarshi ta nufa taga murfin a bude tin tini yna zaune sallah ne ke tayrdashi dayaje masallaci yadawo ze koma ya zauna yna jiran fitowarta sam beji haushintana saboda yasan ta jima bata gantaba. "Sannu uncul.." cewar sahura.
"Yauwa...anty jannarht din bata shirya bane.."
Sahura tace "eh...ance kaci abinci tukunna.."
Hammad yace "okay.." dabadan ynason abincin Ummih ba da bazeciba don ya kagu yagansu a gida. Sitting room din ta kaishi ta zuba masa abincin kana ta fice. Tindaya shigo idanuwanshi na kn pictures dinsu dake manne a falon sunyi kyau. Ita da ummih. Se kuma daya ita kadai tana sanye da doguwar rigar dubai me ado a kirji da hannaye. Kyn ya amsheta ta yane knta da gyale setayi kmr yan shuwa arab gashi tayi dariya wushiryarta sama da qasa ta fito radau.. "wow..!Allah yy halittarh.." hammad yace idanuwanshi kyam a kn picture din ji ykeyi kmr itadin yake gani gabanshi gaskia rigarnan ta amshi jikinta ta burgeshi dukdade rigar kyaun ta taras. "Kai daban auretaba danayi asarar mace.." hammad ya furta Hadi da mikewa ya krsa fun hoton ya zuba masa ido. "Farar mace alkyabbar Mata.." gbki dya ya shagaltu da kallon picture dinnata dukya daburce kmr rnr ya fara ganinta. Seda ya dauki minyoci yna tsaye yana kallon picture din kna ya Ciro wayrshi aljihu ya dauki hoton a wayrshi. Cikin farin ciki ya koma ya zauna ya faracin tuwon yanaci yna kallon hotonnata. Allah sarki rai da abinda yakeso se Allah.
"Sahura tashi ki hada mata kynta dazata bukata..tinda gata tazo seta tafi da kynta dmn inaso in Aiko sahura ta kawo Miki.",cewar
Ummih. Sahura tace tou ta nufa upstairs dinyin abinda akasata
Jannarht tace "Ummih kina korana kou..nifa bazan jeba ko inaba..inaso in kwana pls.."
Ummih tace "rufamin asiri mama dan Allah kiyi hkri de kibi mijinki."
Jannarht ace "Ummih banaso in tafi kuma in brki kewarki nyimin yawa..",
Ummih tce "Mee 2 mamana..Amma kinga bata yuwwa baki tambaya mijinkiba ki kwana nan..aikinga bata yuwwa hakannan.."
Jannarht tace "nafa jima bangankiba hba Ummih.."
Ummih tace "dukda hakan mama.." shagwabewa jannarht tayi ita a dole bazata tafiba... Sahura kuwa ta hada mata komi nata ta fara fitar dasu gun motar tashi.
Hammad bayan ya gama cin abincin ya juma, a zaune yagade har dare na nemanyi gimbiyar bata fitoba..mikewa yy ya nufo falon tana kwance kn cinyar Ummih yashigo,. Ya tsugunna yace "Ummih zamu tafi.."
Jannarht tayi charab tace "Ni a nan zan kwana.."
Wani irin kallo ya jefeta dashi batareda Ummih ta luraba. Amma ita tsaf tagani..
"Maza tashi ku tafi ..bari gaddamarnan jannarht tashi ku tafi...inde hk zata rinkayi kadena kawota.." cewar Ummih.
Zumbur tyi ta tashi zaune tace "haba Ummih..."
"Eh mana .." cewar Ummih. Hammad de na kallonta tanata shagwaba ji yakeyi daman shine take yimawa dayafi kowa jin dadih. Shifa kwata kwata be ganin shekarunta ganinta yakeyi kmr yar 12yrs.
Da kyar Ummih ta lallabata tasamu tayarda zata bishi badan hkn tasoba. Suna tafe Ummih da sahura na biyu dasu har bakin motar. Kmr ta tuna wani abu tajawo hannun sahura zasu dawo falon Ummih tace "Wai menene hakane kikeyi mama.."
"Ummih zan dakko abunane.." cewar jannarht
",Maza kiyi sauri don Allah.." cewar Ummih.
A tare da sahura suka shigo falon upstairs suka haye tashiga dakinta ta fara duba drowers dinta taga babu abinda take nema. Cikin lokaci qanqani ta rikita dakin. "Me kike nema anty.." cewar sahura.
"Tablets din da nakesha dinnan.. Naga bngnshiba.."
"Kilan rannan da mukayi kwalima mun zubar a bola..."
"Innalillahi..nashiga uku..." Jannarht ta fada.
Sahura tace "mezakiyi dashi kuma anty bayan kinada aurenki yanzu.."
Harara ta ballah mata "se akace miki muna wani abun ko..."
Zaro ido sahura tayi tace "kina nufin be taba kusantarkiba.."
"Ke kam wani lokacin kmr bakida hnkli..
Ke ynzu nabari wannan ya kusanceni ai kyayimin fada.."cewar Jannarht.
"Fadan me mijinkinefa ba kwartoba...tab gaskia anty bakaramin sonki mutuminnan yakeyiba...wlhy a zamanin Nan bahu namijin daze zauna dake na tsawon wadanna watannin Kuma be kusancekiba, babushi gaskia..."
Jannarht tace "dallah rufamin Baki...aini kin cuceni ynzu yazanyi..."
Sahura tace "kawai ki bada kai bori ya hau.."
Jannarht ta ballara mata harara tace "ba boriba sede kakan bori.." tyi mgnr tana amsar janan dake hannun sahuran ganin kyn hannun nata sunyi mata yawa. Hk suka sakko kasan kicibus sukayi da ummih zatazo kiransu. "Kai mama kinada abun haushi..tin dazu daukko abu kmr knje daukko dakin gabaki daya.." cewar Ummih. "Sorry..." Cewar jannarht. "Ba wani sorry.." ta tasata gama har bakin car din tini ya gama kwashe kayan da sahura ta ajiye bakin car din yasa a but harda manyan akwatinan da nahnah tase Mata.. "shiga Allah ya tsare Allah ya bada haqurin zama.." cewar Ummih.
Hammad ya amsa da "Ameen..." Ummih ta amsa janan daga hannunta janan din na kuka. Bude mata gaban motar ummih tayi .
ta shiga tana hawaye... Ummih tace "tinda kuka kikeyi zance kada ya kara kawoki gaskia...maza share hawayenki." Share hawayen tayi still wasu na bin wasu. Sahura ta zagayo ta mika mata jakar system dinta. Hammad ya ciro kudi kimanin 2000k ya mikawa ummih kn amsa tayi seda ya rinka rokonta kna ta amsa tayi masa godiya Hadi dayi musu adduarh, yashiga motar yajata sukabar gidan. seda Suka fice daga gidan kana Ummih da sahura suka koma cikin hidan. Cikeda kewar jannarht din.
Suna tafe tana Hawaye wani na bin wani. Tsayawa yy ya faka motar yace "kiyi shiru pls in kina kukannan bazan iya driving dinba..."
",Ni ka maidani gidan Ummih to.." cewar jannarht tana hawaye.
"Wasa kikeyi..ke da ace baki biyoneba sede mu kwana nidake a gidan...dubeki kmr wata bby a Haka kuma kikedason girman..."
Goge hawayenta tayi wai gudun kada ya rainata ta tsagaita da kukan.. murmushi yy yace "anty sarkin son girma.." tayrda motar yy sukahau titi sukaci gabada tafiya Yana driving yna satar kallonta, ita Kam knta kasa tana wasa da yatsun hannunta. ''in kaje pharmacy inaso inse magani ..." Ta fada cikin sexy voice dinta.
"Wani irin magani..." Hammadu ya tambayeta..
"Maganin ciwon kafa da ciwon Kai.." jannarht tace hadi da daurewa.
"Okay..kafarne ke ciwo flower...sowie inmunje zanyi miki tausa.."
"Banaso..."
Juyowa yy ya kalleta yace "Wasa kikeyi...ina alwawarinmu .."
Cikin rashin fahimta tace "Alqawarin me.."
"Nonon dakikace zaki barni in taba.."
"Wai meyasa bakajin kunya ne..yanzu aka barka seka taba bayan ina antynka..nifa ba saarhka bace....aah gaskia Ni wasa nakeyi..damande danka barni ne inshiga gidan mu.."
Dan satar kallonta yy wato shi zata renawa hnkli. "Antyna kou matata... Wata rana sekinyi nadamar kalamannan naki anty..kin raina ni ko bakisan namiji ko wanda be kainiba seya saki kuka..abu daya zeyi miki sekin raina kanki....."
Wani kallo ta jefa masa na rainin hnkli. "Ga pharmacy dinnanfa karka wuce.." tayi mgnr tana nuna masa wani katon pharmacy dake kusa..lacking yy yace "gayamin sunan magungunan in amso miki.."
"Ni dakaina zanje.."cewar jannarht.
"akwaifa maza ..Haka kawai wani yazo yayita kallonki knsan wasu mazan ba hnkline dasuba.."
"Nide gaskia kayi zamanka insiyo in dawo .."
"Keda kike ciwon kafa Kuma..zaki iya tafiya."
"Zan iya ai ta cikine yakemin ciwon." Cewar jannarht.
"Okay sowie love.."
"Budemin in fita.."
"Sedefa muje tare madam..."
Ba hkn tasoba...fita yayi ya bude mata motar ta fito a tare suka jero hannunshi na cikinnata.. katon pharmacy ne an rubuta sunanshi a sama yana haske yayinda hadkenshi ya haske wajen *DIALOGUE PHARMACY.* ... Tunanin yadda zatayi takeyi gashi tana fadar sunan maganin a gabanshi zegane ko na mene ne..dai dai sunzo shiga pharmacy din wani dayazo fita tsayawa yy yce yaganshi ..."wa nake gani kmr a.a. waziri family."
Murmushi hammad yy yace "shegen kaya..nine ...oh Ashe rai knga rai..Yaushe kadawo kasarnan hussein. A muhammad.." jannarht kan tana ganin hkn ta sabule hannunta ta shige pharmacy din. Tana godewa allah.
"Kaide bari sati biyu kenan da dawowatar...Kai Ina kasamo me zafinnan.." Cewar Hussein. Hussein abokin krtun hammad ne a china.
Hammad yace "Dan iska ba kayan titi bace ai..wannan kayanace mallakina..me zafinace."
Hussein ya kwasheda dariya yace "ai wannan tafi karfin kayan titi..itace wadda ka aura naga lbrin aurenka a jaridu da social media. allah ya bada zaman lafia ammafa ta hadu..me zafice..Kai kaga mace alhaji kmr ita tayi knta.."
Kishi da haushine ya turniqe hammad Amma ya daure yh murmushi yace "malam ya isa haka kasanfa kanayin Haram ko.."
Hussein yace "am Sorry...kasanmu in muka gani bama shiru.."
Hammadu yace "wannan Kam dole ayi shiru...ya bayan rabuwa kasan rabon da mu hadufa tin a china.."
Hussein yace "Baride frnd..ya yammatrh.."
Hammad yace "shege Hussein...Ni ai tini na ajiyesu a gefe ga iyalina mezanyi da wasu yammatrh.."
Hussein' yace "gaskia ne aboki...aimu muna nan muna tabawa.."
Hammad yace "shege aida wuya ka dena...kwarani denawar zeyimin sauki but ban taba sex ba romancen nede adan huta kawai.."
Hussein yace "aikai karamin Dan iska ne...ai Ina gya mka alhaji in babu gunnan babu rayuwa ..ynzu hk condom's nazo na siya .."
Hammad yace "kade natsu kayi aure kabarcin yammatan mutane.."
Hussein ya kwasheda dariya yace "ina anwar..."
"Anwar yana nan ..aiznbashi lbrin naganka.."
Dai dai jannarht ta fito da pharmacy din. Kwalin maganin ta cire ta yardar ta rike maganin surarshi searched hudu ne a kwalin. Krsowa tayi tasamesh suna hira. Hussein yace "ina wuni madam.." yy gaisuwar yna kureta da ido.
"Lafia lau.." ta amsa cikedajin haushi Dan tasan hammad ne zece ita matarshice salon yaja mata raini.
"Allah ya bada zaman Lafia.."
"Ameen.." ta amsa a takaice.
"Jeki motarh..." Hammad yy directing dinta Hadi da mika mata car key. Daman ko beceba amsa tayi ta nufa car din ta zauna.
Hussein ya bita da kallo...
"Kallon na meye karamin dan iska.."
Hussein yace "kai abokina kana kwasar kaya a gunnan..kaga mace har mace ..dazan samu irinta aida tuni nayi aure nabar harkar banzannan..pls tanada kanwa ina riko.."
Hammad yace "Aiko bazaka samuba sede kasamu wadda bata kaitaba..inma tanada knwa semu baka maciyin mata.."
Hussein ya kwashe da dariya yace "ai zan dena hba nawan.."
Hammad yadan Kai masa dukan wasa yace "Ni zan wuce nabar iyalina a motar.." Nan sukayi sallahma hammad ya bashi card dinshi yace sayi waya. "Okay..mu karasa inyiwa gimbiya sallahmarh..."
Hammad yace "no need..kayi mata sallahmarh ko kaje kayita kallemin iyali...ai danasan zamuci karo da irinku da bata fito bama.."
Hussein yace "daga gani...Allah ya baka hkri gani aiba ci bane..."
"Mtwsss...dankainefa da tini na dura maka asha riya.."
Dariya Hussein yy shi bemasan dariyar kara bashi haushi tajeyiba. Sallahmarh sukayi kowa ya nufa motarshi. "Am sorry flower na barki me kadai.." hammad yace dai dai Yana gama shiga motar yajawo murfin ya rufe. Batare datayi mgnaba yaja motar sukabar gun. A wani babban ostrich yy packing fitowa yy ya shiga bajimawa ya dawo hannunshi niki niki da ledoji.bude baya yy ya ajiye kna yashiga yaja motar sukabar gun.
Suna Isa gida yy packing fitowa sukayi.. ya bude but din Getman yazo ya fara kwasar kayan Yana shiga dashi cikin gidan dasu a falon ya ajiye shi kuma hammad yana kwasa yana shiga dasu bedroom dinta dashi. Ta fara tayashi yace A'arh tabarshi byaso tasha whla. Bedroom din ta nufa ta ajiye magungunan drower din gadon. Seda ya gama kwaso kyn tsat ya samar musu gun zama duk tana zaune tana kallonshi. Ya fita ya kwaso ledojin siyayyar kyn makulashen da yy musu ya dawo dakin tana qoqarin cire hijjb din jikinta ya shigo ajiye ledojin yy a kn dining. Ya zauna a kujerar dining din. Ya zuba mata ido.. "anty ya mgnr nonon dakikace zaki bani.."
Harara ta gallah masa, "Dan Allah bakajin kunya ne kai.."
"Kunyar me..dannace nono..aiba duri naceba.."
Dafe kai tayi tace "pls go out..znyi wanka.."
"Bayan nasha nonon ko...sekiyi wanknki gabaki daya.." ya kashe mata ido daya.
Buga kafafuwan tayi a kasa cikin shagwabar da batamasan tayiba tace "Dan Allah ka fita ...kaina na ciwo..."
Mikewa yy danjin tace knta na ciwo bkaramin burgeshi tayiba.."Muje inyi miki wankan to..tinda knki na ciwon.."
"Dan Allah ka fita..znyi wanka inajin baccine.."
"Tou nanda minti nawa zan dawo.."
"Karka dawo.."
"Kemade kinsan wasa kikeyi..ki gama zandawo." Ya juya yabar dakin. Wankan tashiga tayi a gaggauce ta shirya cikin gown red na bacci tayi mata kyau rigar tanada gidan nono se shading nononta ya kwanta ta sama. Maganin ta daukko tasha Dan har lokacin fllng din be bartaba duka..yna shigowa dakin tayi sauri cusa mgnin saqon gadon. Tinda ya shigo yake kallon nononta kmr maye ji yakeyi kmr ya karasa ya tabosu. Hade rai tayi ganin ya zubowa brsts dinta ido. dan tasan ze iya zuwa ya tabata. Krsowa yy yazauna kusa da ita ta mike tsaye ta Dan ta dakko hijjab...hkn ya bashi Daman zubawa duwawukanta ido...Allah ya wadatata da hips abinda yake matukar kauna kenan jikin mace hips. Da gani zasuyi dadihn tabawa musammanma inya zura mata jiniyrshi ynayi yana Dan shashafasu..wani iri yaji a jikinshi a hnkli ya sauke ajiyar zuciyarh still idonshi na kn kugunta...
Hijjb ta dauko tasaka..ta Kona kn kujera tazauna.
"Meyasa kikasa hijjb.." hammad ya tambayeta.
"Saboda kai..."tace idonta na knshi.
"Ki cire.."
"Inna qifa.."
"Zanzo in cire in miki abinda bakiso inyi..Dan babu abinda ze hanani shan duwawunki inkika bari nazo na cire hijjb dinnan.." ya krshe mgnr Yana miqewa tsaye.
Tasan tsaf ze aikata da sauri ta cire hijjb din ta ajiyrshi a gefe. ,Komawa yy ya zauna yna sauke ajiyar zuciyarh. "ko kefa..an hanani tabawa sannan ana nema a hana Ni kallon kayana..kwara a bari in kalla in rage xafin dake damuna.. " ya krshe mgnr yana lasar laffanshi dasuka bushe. Idonshi kyam a kan nononta farare sol dasu.
"Mal kaje ka kwanta.."
"Ai banajin bacci..",
"Ni inajin baccin ai..kaje dakinka mna sekayita zamnka.."
"Nanma ai dakin iyalinane.." yy mgnr Hadi da mikewa ya fita tashama ya tafine ta hau gadon ta kwanta abinta...
Dawowa yy hannunshi rikeda plets.. arba yy da cinyoyinta rigar ta kware hknne ya bashi dmr kallon cin yoyinta Yan luwuit luwuit dasu,..saura kuris plts din dake hannunshi su subuce su fadi ..da sauri ya shiga ambato sunan Allah ki yakeyi kmr yaje ya tirmusheta yashiga gunnan ko ze samu sassauci.
Zumbur tayi ta tashi zaune ganin ya shigo ya zubo mata ido ita a tunanintama wawiyar kwanciya tayi Allah yasota da pant da ya ganta ya cuceta a banta..ta fada a rnta.
Qoqarin controlling knshi yayi Amma seda abarshi ta amsa..krsawa yy on dining chair ya zauna.. ya bude leda daya ya juyu a pleat din farfesun naman ragone se kamshin yakeyi da Dan romo romo..."flower ki taso..ko in kawo miki nan.."
Kamshine ya cikata tace btre data bashi amsaba ta Taso ta nufa dining din dan ganin meke kamshi hk. Xaunawa tayi idonshi na kn nononta. Nan yashiga qoqarin bata a baki Taki yarda ta amsa spoon din tanaci a hnkli..yy Mata dadih sosai..Shikam gogan da nashi spoon din a hannu juyashi kawai yakeyi amma ya kasa kai ko lomar daya bakinshi.. duk tana ankare dashi "dan iska.." tace a zuciyrta. "Ina na matarka.." ta fada Hadi da mikewa ta bude frij ta daukko peach kna ta dawo ta zauna..."ammm..wacce matar.." ya fada muryarshi so cool.
"wacce mata gareka.." ta fada a takaice.
"Me mna...au Wai Jawaheer.."ya fada yna qoqarin saita knshi danyasan baze samuba sede tashin hnklin kawai.
"Yeah..bazaka kai mata nataba..ya kamata komi ka siyo ka rinka Kai mata gaskia banason cin haqqin wata..Kaji tsoron Allah gaskia nide ba ruwanarh..."
"Tou mah.."
"Ka dauka ka kai mata mna.."
Okay yace Hadi da mikewa ya dauki leda daya yana qoqarin ficewa daga dakin tace "ka koshi ne .."
"Yeah..." yace Hadi da ficewa daga dakin ya nufa upstairs. Yana fita ta kwashe komi ta nufa kiching dasu.wannan shine first time data tafa fitowa falon gidan harta isa kiching tsarin komi na kiching din yy Mata. Taganshi tsaf tsaf dukda hammad ne ke amfani dashi already Daman tasan Hammad yanada tsafta, . Sede kayan a hargitse Nan ta shiga gyara komi da komi tana maidashi mazauninshi..
Tana zaune a falon duk abin duniya ya isheta fitarsu a kn idonta hkma dawowarsu a kn idonta kishi kmr ze kasheta, gashi taje ta duba taji duk dakunan a rufe babu yadda za ayi tasa layarnan..se abun ya zamar mata biyu..
Krsowa yy yasameta tayi tagumi, tana ganinshi ta mike tsaye cikeda murna. "Sannu yah Hammad.."
Hk kawai se yaji tausayinta a rmshi dukdade ba sonta yakeyiba sede kunsan jini.. krsawa yy ya Mika mata ledar dake hannunshi. Amsa tayi cikeda farin ciki. "Bakida wani problem ko..'' ya fada batare daya kalletaba.
Tab farin ciki kmr zata mutu this is the first time daya taba mata mgna cikin sanyin murya.
"Yeah. But sede kewarka.."
"Okay yy kyau.." yace a takaice. Juyawa yy da niyar barin falon tace "yah hammad har zaka tafi bazaka xaunaba Dan Allah.."
"Nop..ina