Showing 96001 words to 99000 words out of 185083 words

Chapter 33 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5504

zama daya tamkar ahali kaman yanda muke so kuwa??

Dagowa yayi ya kalleta da murmushi akan fuskansa yace

"Mun hade already ai baby meya rage tinda munxama business partners hakama familynmu sun hadu an kulla zumunci"

Gama shafa turarukanta na bacci da goge gogen fuskanta tayi tana tasowa ta nufo lafiyayyan gadonsu ta zagayo inda yake ta zauna gefensa tana miqa hannunta akan kirjinsa tana shafawa zuwa wuyansa da kunnensa ya lumshe idanuwansa yana saukesu akanta tareda bata dukkanin nutsuwansa sbd Shafan kunnuwansa zuwa wuyansa datake dole hankalinsa kaf ya tattaru akanta.

Tace

"Partnership na business da wasu huldodin sunada lokacin qarewa da yankewa komai daren dadewa amma zamowa family har abada ne,koda an samu matsala to anriga an zama familyn,
AZIZ LIMBA ba wanda zaadens zasu bari su rasa bane har abada,
Yanada dukkanin abinda kuke buqatan wanda zaku hada komai dashi ya sakance,
He's very very powerful,
a billionaire,he has d biggest connections,he's talented,sharp,genius
Almost perfect in komai da komai,
i dont see any reason da zai saka kuyi wasa da kasa maidasa family,
Haduwan arzikinsa da power dinsa da namu shine zai saka Zaadens su zama unbeatable,untouchable,more and more power zamu sake tsayuwar da babu abinda zai taba shaking namu sbd duk wanda ya sakomu gaba ko waye yanada saa babba sbd a strike daya yayiwa Zaadens girgizan daya tin kakanni baa taba samun wannan zubewan ba"

Shiru maheer yayi yana shiga tinanin maganganunta da tabbas shi kansa jin yake AZIZ din bai shiga hannunsu yanda ya kamata ba sbd kaman yanda Dad yakeson LIMBA da baida mutane a Nigeria su zama sune wainda sukafi kowa kusanci dashi,
Sunason su kasance sune kadai family na biyu dayake da,
Suna son ya zamana komai nasa sunsamu kusancin da sukeda kusan access da komai na tarin businesses nasa.

Anny fuskan Maheer din take kalla tana ganin yanda yake shiga tinani da nazarin maganarta tace

"Yanxu da ace akwai wata princess din a familyn nan da Aure kawai zamu hada dashi ta yanda komai dadewa dai dukiyarsa kaf zata zama ta ita da yayanta ne kuma tinda zaadens zasu zana sirikansa Biyayyan da binku zaiyi sosai Amma babu damar hakan yanzu sbd babu wata 'yar sai Jannah wadda Ammar ne wanda zaa aura mata ita kuma ta kasa tantance ba son aure take masa ba na yayanta dayake tsananin sonta ne kawai take masa,
Tausayima take bani sbd ta rasa gane me zuciyarta ke so kada azo ayi auren ma daga baya ta gane ba son aure take masa ba ta shiga damuwar da zai saka ciwonta dawowa"

Dagowa Maheer yayi ya kalli Anny din cikeda mamakin maganarta data kasa zama abar dauka ta wani bangaren.

Cikin mamakinsa dayake sake bayyana yace

"Jannah na Ammar Soyayyan da sukewaΒ  junansu a bayyane yake,
Tayaya ma zakiyi tinanin Jannah ba son Ammar takeba,
Tin tana yarinyarta da soyayyarsa ta taso ta girma,babu wani dan adamn dai da jannah zata iya so a duniyar nan so na aure idan ba Ammar ba,
Shi kansa kina sane da idan yaji maganar nan ta bakinki zai iya zarewa so kibar maganar nan iya nan ta jannah ba aurensa takesoba kadama na sake jin kin fada"

Kwantar da kirjinta tayi ahankali kan nasa tana zagaya hannuwanta ta rungumesa tana cewa

"Bazan sake fada ba amma kuma ka saka ido sosai akan jannah din ka fahimci abinda nakeson ka fahimta da kanka idan ka karanci komai zabinka ne ka bari ayi auren ta shiga damuwa kokuma a bari ta samu wanda takeso"

Shiru yayi mata sbd baima son jin maganar kawai dai kaman yanda ta fada a farko da ace akwai wata yar a familyn tabbas zasu basa aurenta dan kawai su zama familyn gaske ba wai iya business partners ba duk da hakan zai tattauna da Dad suji yanda zasu sake shigar dashi jikinsu sosai amma bazai iya fadawa dad din maganar da Anny ta fada ba akan Ammar da jannah.

Washe gari breakfast familyn sukai gaba daya a dining,
Idon Maheer akan jannah yake wadda ta zauna gefen Ammar tana kallansa sbd irin kallan dayake mata kaman zai bude zuciyarsa y sakata ciki ya rufe kowama y dena ganinta.

Wani Murmushi me sanyi ta sakar masa wanda baya tattareda asalin farin cikin daya fito daga zuciyar datake cikeda tsananin so.

Anny data lura da yanayin yanda Maheer yake kallan Jannah yana kasa hana zuciyarsa karantar yanayinta sbd Anny ta riga ta jefa masa tinani da wasi wasi.

Murmushi Anny ta sake tana kallan Jannah tace

"Jan yau ne zakije LIMBAs gurin daukan Falaq Aziz?
Inaga zamu tafi tare inason fitan yau nima na yi hayaniya"

Dagowa Jannah tayi ta kalli Anny din wadda taci gaba da cin abincinta kaman ba ita tai maganarba hankali kwance.

Dad cikin kulawa da tsananin kauna yace

"Jan,yau din zakije?
Falaq bata sakaki hayaniya sosai kada kiyi stressing kanki fa kinsan condition naki duk da komai lafiya kalau ne amma dai karki biye mata yarinya ce ita kuma lafiyayya kada kije kiyita tsalle kina wahalanda kanki"

Cikin sakewa ta dago tace

"No dad,banajin sauyin yanayin komai,
Zan kula sosai insha Allah"

Ammar ne ya kalleta yana ajiye fork din hannunsa yace

"Are you sure love"

Gyada masa kai tai tana murmushi tace

"Kaunar yarinyar nakeji sosai kaman nice na haifeta,inason kasancewa da ita sbd ina samun wani farin ciki mai sanyi dayake bani nitsuwa akan kuruciyata dana rasa"

Tsit gaba daya gurin sukai suna zuba mata idanuwa sbd maganar daga zuciyarta take fitowa sbd yanayinta da idanuwanta suna nuna abinda yake zuciyarta ne ta furta ba wasa.

Mimi cikin jin farin ciki tace

"Falaq din nata shiga rai amma ban dauka sosai ta shiga zuciyanki hakaba"

Dad da bai taba jin abinda jannah din ta bude baki kai tsaye ta furta tana kauna da tsananin nutsuwa hakaba kallanta ya sake yi yana karantar da gaske abinda ta fada tsananin kaunar yarinyar take dan haka take yaji shima yana kaunarta sbd duk abinda zai saka yarsa farin ciki da samun nutsuwa irin wannan yana sonsa da kaunarsa babu shakka ko tinanin komai.

Maheer ma jin yayi wani sanyi ya sake shigar zuciyarsa sbd wannan ma wata hanyar sake samun kusanci da kauna ne me karfi tsakaninsu da LIMBA sbd shima a nasa bangaren duk wanda yake so da kaunar 'yarsa babu abinda bazai iya masaba dan haka zasu taya jannah kaunar 'yarsa sosai.

Ammar shiru yayi yana kasa cewa komai tareda zubawa jannah idanuwansa tana sake murmushin da wannan karan tin daga zuciyarta yake fitowa sbd ta bayyana kaunar datakewa Falaq kuma familyn sun nuna farin cikinsu da hakan dan haka take murmushint me kyau tana cigaba da cin abincinta hankali kwance.

Ammar jin yayi kaman cikinsa ya toshe haka kawai dan haka ya dauki cup din warm drink ya kai bakinsa yasha ahankali tareda ajiyewa ya dauki tissue ya goge bakinsa yana cewa ya gama.

Kallansa Jannah tayi tana son nasa magana sai kuma ta fasa tana masa magana da ido dole ya fasa tashi ya zauna yana kallanta tana qarasa cin abincinta cikin jin dadi da kwanciyar hankali harma da farin ciki dan haka kawai taji tama matsu taje gidansu Falaq din.

Suna gama breakfast din ta wuce bedroom dinta ta zauna tana dan wayoyi da dube dube a wayar tana kaida kawo har abincin dataji yana dan zaunu a cikinta kafin ta zare komai ta fada toilet wanka.

Wanka tayi ta fito daure da towel blue ta zauna tana goge jikinta ahankali kafin tafara shafa tana duk abubuwan data saba na shiryawa.

Doguwar riga ta saka maroon sai guraren 2 ta fito riqe da handbag ta Louis Vuitton sai wedges shoes na versace,

Qamshinta ne yake tashi ahankali mai sanyi da dadi,
Key din motarta ne a hannunta da wayarta datake texting falaq din saying she is on her way.

Anny data shirya itama fitowan tayi sanye da boubou din wata tsadaddiyar black lace mara nauyi da hayaniya ko kadan da handbag din chanel sai heels da ita ta saba su take sakawa suka fito suna ficewa gidan.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
51
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC (kayan mata)
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah πŸ₯°πŸ‘ŒπŸ»
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1kπŸ₯­ Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4200
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
πŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ—£οΈ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALAπŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ˜πŸ˜πŸ˜ da 6k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ˜ƒπŸ™ƒKazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadΔ±πŸ˜‹800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Na Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 6k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki



************
Jannah ce take jan motar a nitse zuwa gidan wanda suna sake kusantar isa gidan bugun zuciyarta sauyawa yakeyi ahankali sbd hakanan batason ta hadu da Daddyn Falaq din dan haka koda Anny ke mata maganar Aurenta da Ammar daya kamata a bari sai komai ya sake daidaita batama jinta sosai sbd hankalinta da tinaninta nakan tinanin wanda a ko yaushe yake guri take samun kanta da jin zuciyarta na sauya bugu.

Suna isowa gidan Securities dayake sun san da zuwan na Ms Jannah Zad wadda Falaq ta sanar musu dan haka babu bata lokaci aka bude musu suka shigo cikin tsananin girmamawa.

Parking tayi gabanta na dan faduwa sbd ganin motocin datake da tabbacin yana gidan dan haka ta kasa fitowa motan saida ta daidaita bugun zuciyarta ta bude ta fito.

Anny dake kallan mahaukatan motocin dake harabar gidan da tsarin gidan jin tayi komai ya burgeta sbd Allah bai bata godiyansaba dan a nasu gidan babu kalar jin dadi da duniyar da aka rasa a zadeens hakama gidan LIMBAs din ba fin nasu yayi ba kusan gogawa akeyi kawai dai dan nasa tsarin yana sabo ne kuma daban da nasu amma suma nasu gidan kaman Aljannar duniyarne to amma ganin takeyi duk kaman nan din yafi sbd tsatsar zuciya.

Falaq datake jiran zuwan jannah din tin safe ta hana kowa zama anata shirin zuwan jannah
Me aikin data saka tsaron harabar gidan dan ta sanar mata idan sun iso tana ganin shogowan motarsu juya da sauri taje ta sanarw Fiddausi sbd ita kadai keda ikon zuwa hanyar bangarensa a cikin masu aikin gidan kuma gashi falaq din na gefensa ta hanasa fita tace se baquwanta tazo sbd a rayuwarta wannan shine karo na farko da zatai baquwan kanta shiyasa takejin kaman zata taka jariri sbd murna ta hana kowa sukuni.

Fiddausi data iso kofar palonsa karamar doorspeaker dake gurin mara qara ta taba tareda kai bakinta cikin nutsuwa tace

"Baquwan Falaq Aziz ta iso"

Daga ciki akwai qaramar speaker da ake jin zancen wanda yayi daga wajen kofar ba tareda hayaniyaba dan haka Falaq dake gefen Daddynta tana nuna masa dukkanin firanta da Jan a ipad dinta tana jin hakan miqewa tayi daga jikinsa tana murmushi me tsananin kyau tace

"BestDaddy special guest dina tazo"

Miqewa tana nufar kofa ta fice da sauri tana barin ipad dinta a jikinsa.

Kallan ipad din yayi hotonta ne dana jannah din dayake cikin chats nasu yake bayyane.

Hannunsa ya saka ya danna lock ta rufe kafin hoton lockscreen dinta ya bayyana wanda yake hotonsa ne shida ita tana jikinsa tana dariya sosai cikeda tsananin kaunarsa da bata hada da komaiba.

Harabar gidan ta nufa da gudu Fiddausi na biye da ita cikeda farin ciki tayi kan jannah din ta rungumeta tana dariya.

Itama jannah din dariyar takeyi tana kama hannunta sbd jin numfashinta na sauyawa sbd gudun datai ta janyota gabanta tana cewa

"Ki dena irin wannan gudun okay."

Gyada kai jannah din ke yi tana dan hadiye yawu sbd numfashinta dayake fita da karfi tana jin kaman kirjinta bazai dauka.

Ciki suka nufo Fiddausi na musu sannu da zuwa tana wucewa kitchen da sauri ta daukowa Falaq din da numfashinta yake sauyawa sosai ruwa.

Mama data fito su gaisa ganin yanayin falaq din cewa tayi

"Yaya dai take wannan numfashin?

Fiddausi data bude mata robar ruwa tana zubawa a glass cup miqa mata tai bakinta tana cewa

"Gudu tai sosai"

Jannah ce ta karba cup din tana cewa

"Sha ruwan and calm your self tukuna kinji"

Bude baki tayi tasha ruwa kadan tana kokarin cewa she's ok amma ta kasa ta riqe hannun jannah tana kallanta.

Anny ce ta gaida mama suka gaisa cikin sakewa tana musu barka da zuwa.

Jannah ma gaisawa sukai da maman mama na tambayarsi Mimi cikin sakewa da farin ciki sosai da zuwansu.

Fiddauci ganin yanayin Falaq din ya sakata kasa sakewa tace

"Falaq muje dakinki ki dan kwanta ko some minutes ki nutsu ki samu ki dawo daidai kinji"

Girgiza kai tayi tana rufe idanuwanta har lokacin hannunta na cikin na Jannah wadda take shiga damuwa ganin Falaq din kaman ba lafiya ba.

Miqewa sukai bayan mama ta yadda da hakan itama
tana riqe da hannun jannah suka isa bedroom dinta suka shiga jannah dince ta taimaka mata t kwanta ahankali zuciyarta na sake tsananta bugawa.

Shafa fuskanta zuwa kanta jannah keyi cikin nutsuwa ahankali tana kokarin tayata daidaita numfashinta.

Lumshe idanuwanta da suka dan sauya falaq tayi tana samun sassauci da daidaituwan bugun zuciyar ahankali.

Mama da Fiddausi dake tsaye juyaw sukai sun ficewa mama na jin kwanciyar hankalin ganin yanda Jannah takewa falaq din tamkar uwa,
Hakama falaq dinta na riqe da hannun jannah daya har lokacin.

Mama ce ta nufi palon AZIZ din da kanta ta samesa yana waya a natse,

Ganin yana waya sai bata ce komaiba ta juya zata fice yai sallama da wayar ya kashe yana cewa

"Mama akwai wani abu ne??

Juyowa tai ta kallesa batareda ta dawo ba tace

"Babu komai kawai naso magana dakai ne akan lokacin da yayi na aurenka ko dan samawar 'yarka cikakkiyar kulawa sbd bazaka so ace ta taso ba uwana ta qare a karkashin kulawan masu aiki da nannys batareda ta samu kulawa daga uwa ba har girmanta,
Ga yanayi na ciwonta sai gaba yakeyi sbd yanzu daga gudu kawai tana neman rasa bugun zuciyarta..

Ajiye wayar hannunsa yayi yana miqewa ya nufo kofar yana cewa

"Tayi gudu?
Meyasa tayi gudun?
Ina taje ne??

Mama bata samu amsasa duka ba tayi gaba tana cewa

"Sbd murnan Zuwan jannah ta fita da gudun tarbanta....

Ko qarasa ji baiyiba ya fito yana nufar bedroom din jannah din wanda Fiddausi data kawo zata koma dakin kai wasu ruwan da drinks tana ganinsa tayi saurin dakatawa tana sauke kai qasa harya wuce ya nufi dakin ya bude kai tsaye ya shige.

Budewa idanuwa falaq tayi tana ganinsa ta daga hannunta daya ta miqa masa tana narke fuska.

Qarasowa yayi yana zaunawa bakin gadon tareda dagota gabaki dayanta kafin yayi magana ta kwanta jikinsa tana riqe hannunsa daya sosai.

Cikin wani irin sauti dayake son nuna bacin ransa amma kuma bayason dagawa yarsa harshe dan haka tsananin kulawansa yana danne bacin ran yace

"Meyasa kikai gudu?
Akwai abinda yakai lafiyanki mahimmanci ne da zaki komai kiyi gudu,
Meyene yakeda mahimmancin dazai sakaki irin wannan guje gujen?
Don't you try that again kinaji na??

Gyada kanta tayi ahankali tareda dagowa tana kallansa zuwa lokacin bugun kirjinta ya dawo mata daidai sbd yanda jannah ta kula da ita.

Bude bakinta tayi cikin kaunarsa tace

"Ina murnan zuwan Jan ne,
Amma bazan sake ba BestDaddy"

Sai a lokacin datai maganar ma ya lura sa akwai wani a kusada su din dan haka ya juya idanuwansa akan jannah din wadda tinda ya shigo gurin kamo falaq da hannunt dayake cikin n falaq ya hada ya kamo zuwa jikinsa tai mutuwan zaune a gurin komai na jikinta na dena aiki sai zuciyarta dake harbawa kaman t falaq din.

Kallo daya tai masa ta kasa sake dago idanuwanta ta sake kallansa qamshinsa kuwa dayake shigarta direct ba nisa komai na cikin kanta dena aiki yayi zuciyarta ce kadai take aiki wanda babu komai a cikinta bayan asalin zazzafar soyayyar dake neman fasa kirjinta wadda batasan ta ina,daga ina,ta yaya take shigartaba tana bin jininta....


Hawayen tashin hankali da tsoron abinda take ji a tsakiya da koina na zuciyar ne suka ciko mata idanuwa sbd jin take kaman ta fasa kuka ta bude zuciyarta ta fidda son me tsananin gaske take ji.

Kallan asalin tsana da rashin kaunar duk jinin dayake yawo a duniya yake mata yana jin zafi na cike kirjinsa me karfin gaske zaiyi magana sai kuma ya fasa sbd maganan da ita is like wasting his energy and disrespectin his time a banza dan haka ya miqe yana juyawa yana cewa

"Useless people everywhere"

Ficewa yayi daga dakin yabar Jannah din na bin kofar daya fice da idanuwanta da sukai tsananin sanyi sbd a kunnenta kalmansa ta sauka duk da ba sauti sosai amma kuma ba kalman ce ta kashe jikintaba irin tsananin tsana da qin data hango cikeda fararen idanuwansa da suke qara kashe zuciyarta tako ina da azababbiyar soyayyar datake jin kaman kirjinta bazai iya riqewaba.

Falaq cikin kulawa ta kama hannun jannah tana cewa

"Na dawo daidai ki dena damuwa kaman Bestyn falaq koyaushe yana damuwa abu kadan idan ya sameni"

Sunkuyar da kai jannah tayi tana sauke boyayyar numfashi me tsananin sanyi tana kunya da takaicin kanta.

Fiddausi ce ta shigo da babban trey tana farin cikin dawowan falaq din daidai tana cewa

"Duk murnan zuwan Ms jannah yana neman komawa ciki kina neman daga mana hankali da rana tsaka"

Dariya tayi tana fita da sauri taje palonsa ta dauko ipad dinta tadawo tana zaunawa gefen jannah data dan sake tana magana da Fiddausi dake bata labarin kuruciyan Falaq din tana jin kaunar falaq din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login