Showing 132001 words to 135000 words out of 185083 words
neman zubewa a gurin ya sake riqeta ajikinsa ruwan wankan jikinta na shigewa jikinsa.
Qwacewa tafara kokarin yi wanda ya sakasa bude idanuwansa da sukai jajir suka sauka akan fuskanta yana mata kallo tsanarta na gauraya zuciyarsa sbd Jin bugun zuciyar 'yar uwarsa a kirjinta ya dawo masa da radadin rashinta sabo a zuciyarsa.
Sakinta yayi batareda y dauke idanuwansa akantaba ta fadi qasan toilet hannunta na buguwa sosai amma bata dagoba ta kallesa duk da radadin datake ji hannun.
Rigar jikinsa ya zare ya jefa mata ya juya yabar toilet.
Sayd da baisan yana ciki ba yana ganinsa ko kofar toilet din bai sake kalla ba ya juya yabi bayansa batareda ya sake cewa komaiba akan maganar dayake yi da dr Sameera akan ciwon falaq dayake gabatar mata da record dinta na komai.
Dr Sameera itama kasa cewa komai tayi tabi bayansa da kallo Bugun tata zuciyar itama yana qaruwa sbd ganin lafiyayyar farar fatarsa dake daukan ido da kakkarfan jikinsa daya gama budewa sbd geamin.
Falaq kuwa kofar toilet ta xubawa ido tana jiran fitowan Jannah wadda hannunta ke mata tsananin azaba.
Hawaye ta fara sharewa kafin ta miqe ta iya saka rigar da kyar ta fito.
Juyowa dr Sameera tai tana kallanta da sauri sedai ta boye mamakinta har Jannah din taje ta dauki wani abu a cikin kayan falaq ta daura a jikinta ta fice ta nufi dakinta hannunta na mata wani irin ciwo.
Tana isa dakinta kayan jikinta ta cire daqyar ta iya saka wasu kayan sai kawai ta zauna ta fasa kukan azaba da damuwan datake ranta.
Sai datai sallan azahar ta fito jiki a mace taje ta sake duba falaq ta gaida mama ta koma daki.
Bata fito cin abincin rana ba sedai Fiddausi takai mata daki.
Bata iya cin komaiba kwance taje tana fama da wani irin azababben ciwon hannu da zazzabi.
Sai yamma ta fito taje gurin falaq data warware ba laifi.
A gurinta ta zauna duk da tana jin jikinta bata nuna ba ta jin dadi ba ta ringa kulawa da Falaq din har dare ta lallaba ta koma daki ta kwanta.
Washe gari falaq ta tashi lafiya kalau kaman batai ciwoba sedai fushi take da daddynta tace saiya shirya da Jannah.
Jannah ahankali ciwon yafara cin karfinta har lokacin ita kadaice take wahalanta a daki bata iya bacci kwana takeyi tana kukan azaba da damuwa batareda sanin kowaba.
A haka su anty maryam suka taho gidan duba falaq itada babbar yarta Fadilah wadda ta gama service dinta aiki mamanta keso tayi a karkashin AZIZ wanda baa riga anfadawa ba amma dai ta saka Alh saad ya masa magana.
Wuni sikai a gidan har suka tafi jannah bata fito ba bayan gaisawan da sukai kafin ta shige.
Bata san anan fadilah zatai kwana biyuba saida ta fito da daddare ta ganta a dakin Falaq suna fira.
Falaq na ganin jannah ta taso tana kallan cikeda kulawa tace
"Jan kanki ya dena ciwon?
Gyada mata kai tana zaunawa dan fitowa tai ta ragewa kanta azaba dan haka kallan Fadilah din tai tace
"Ashe kina nan??
"Eh zan dan kwana biyu ne na huta kafin na fara aiki a LIMBAs"
Gyada kai jannah tai kawai tana miqewa dan komawa dakinta kwata kwata ta rasa meyake mata dadi.
Tana komawa daki wayarta ta dauka ta saka kiran Dad yana dauka hawayen datake riqewa suka ringa tsiyayo mata amm bata bari ya gane hakanba sukai yar fira ta aje ta kira mimi itama haka amma sam bataji sassauci abinda take jiba dan haka ta kwanta hawaye na bin gefen idanuwanta har bacci ya dauketa a hakan.
Washe gari Mama ta sake tafiyar kwana biyu hakama falaq ta koma school dan haka ta koma tashin safe da wahalar aikin falaq din wadda take cewa bataso tanayi.
Fadilah kuwa babu abinda take a gidan bayan zuba iko da zuba ado tana nunawa falaq kulawa da sakarwa masu aikim gidan jiki amma duk da hakan jannah ce kadai a zuciyar falaq wadda tafara shiga damuwar ganin halinda jannah take ciki na wahala da damuwa da rashin walwala,
Ta bangare daya hannunta sai gaba yake sosai batareda sanin kowa ba dan harta fara kaiwa bata iya komai dashi.
Wata irin rama takeyi wadda ta saka falaq shiga tsananin damuwa ta dagawa daddynta hankali ya dawo a tafiyar da yayi.
A ranar daya dawo basu saniba falaq na islamiyya jannah tana daki kwance ko tashi bata iyayi da kanta saida.
Fadilah ce kadai tasan dawowansa dan haka da daddare dukansu suka fito cin abinci banda jannah data dena fitowa sbd mama bata nan Fadilah itace kaman me ikon gidan yanzu tin daga lokacinda yayi mata wani irin fada da cin fuska a gaban Fadilah din da masu aiki ta dena rabar Fadilah sbd yanda take mata kallan kaman matar cushe.
Falaq ce take kai mata abinci daki da kanta suna ci tare sbd yanda take cikin rashin lafiyar.
Da daddaren wanka tai daqyar ta fito daga toilet ta saka rigar bacci kawai batareda ta saka komaiba ko shafawa tana kokarin kwantawa taji qarar fashewan glasses da ihun falaq me karfin gaske.
Mummunan faduwa gabanta yayi ta tashi daqyar da sauri ta nufi kofa ta fito idanuwanta suka sauka aka qaton trey din abincin data dauko zata kawo mata ya subuce ya fadi gabaki daya komai ya zube glasses na cup da plate sun zube koina abincin da zafinsa ya zuba a qafar falaq din wanda ya sakata ihun daya fiddo da kowa cikin tashin hankali.
Fadilah data riga kowa isowa cikin daga murya take cewa
"Meyasa ita bazata fito taci abinci ba kullum kece me wahalar kai mata kaman baiwa"
Jannah dataji hakan tashi hankalinta yayi sbd tasan ba qaramin baqin ciki da dacin zuciya zata kunsa ba a gurinsa dan haka jikinta ya dauki rawa ga rashin karfin jikinta zuciyarta na wani irin bugawan daya saka kirjinta mata ciwo.
Basu san dashiba sai ganinsa sukai ya fito yana kallan falaq dake hawayen azaba kuma duk abinda fadilah ta fada a kunnensa....
Jannah data gansa tsananta bugu kirjinta yayi bata ko gani sosai tayi kan falaq batareda ankara da glasses din dake zubeba tayi cikinsu kai tsaye kirjinta na wani irin ciwo.
Kafarta ta daga zatai ciki kirjinta ya gaza idanuwanta taji suna rufewa ta yanke jiki a gurin...
Taku daya yayi ya tareta jikinsa yana hanata zubewa cikin glasses din tareda dauketa gaba daya sbd komai na jikinta ya saki alaman ta suma ko wani abin daban.
Sayd ya kalla da sauri yace
"Kira Doctors yanxun nan"
Falaq na ganin hakan take taji ta dena jin zafin nata ciwon tafara kiran sunan jannah cikin tashin hankali tana bin bayan Daddynta daya nufi bangarensa da Jannah din wadda yake tsananin fatan babu abinda zai sameta sbd zuciyarta datake kirjinta.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
71
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
***********
Sakin baki fadilah tayi tana bin bayansu da kallo zuciyarta na nauyi,
Fiddausi kuwa da daman take cikin damuwa da tsananin tausayin halinda jannah take ciki duk tsawon lokacin jin tai jikinta yayi sanyi.
Falaq dai tini tabi bayansu kusan a tare suka isa tana jin nata ciwon ma kaman ta dena jinsa.
A palonsa ya kwantar da ita kan kujera kafin ya dago kanta falaq tai saurin saka mata pillow tana kallan fuskanta datai fayau.
Shi kansa fuskan tata ya zubawa idanuwansa yana kalla a natse,
Duk da baya mata kallan tsaf sosai bai wani riqe yaya komai nata yake ba yasan tana cikin wani hali sbd yanda tai wani irin pale da rama sosai tareda sauyawa sosai.
Dauke idanuwansa yayi Ahankali daga kanta yana maidawa kan falaq datake kallanta cikeda damuwa da tsoron kada komai ya samu jannah din.
Hannu ya miqawa Falaq din yana hana yanayinsa bayyana ta gurinsa tana fasa kuka ahankali tana cewa
"Daddy Jannah batada lafiya sosai,.ta dade batada lafiya,
Ko abinci bata iya fitowa taci,
Hannunta ya karye sosai take fama dashi nayita cewa muje asibiti or a kira dr sai tana cewa aa kaman tana gudun abinda zakace ne,
Tana cikin damuwa sosai kwata kwata bata cikin farin ciki,
Daddy pls ka kula da ita ka bata farin ciki,
I really love as my mum,bazan iya rabuwa ita ba dan haka daddy dan Allah ka sota sosai ko dan sbd yanda nake kaunarta itama take kaunata pls Daddy na rokeka"
Qarasa zancen tayi hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata wanda ya sakasa maida idanuwansa ahankali akan jannah din wadda bata motsi har lokacin.
Kallon tsafta yayiwa fuskanta tsawon mintina kafin ahankali ya gangaro da idanuwansa akan kirjinta setin zuciyarta ya tsayar dasu agurin yana radadin a zuciyarsa dayake tattare da yanayi biyu,
Jin yake kaman ya kasa,
Jin yayi yana neman tsanar kansa sbd zuciyarsa na kokarin failing Ummitansa.
Hannunsa ba zato a natse falaq ta dora akan hannun Jannah din ta dora nata akan nasa tana cewa
"Daddy pls for my sake ka karbeta a matsayin matarka,wlh tana tsananin sonka Daddy,
Tana enduring da hadiye komai ne sbd son datake mana ni da kai,
Daddy zakaso wasu familyn suyi treating dina kaman yanda mukaiwa Jannah wadda tanada gata da power ta family irin wadda nake dashi??????
Dago idanuwansa da sukai ja yayi ya kalli falaq din yana shigar da ita jikinsa ya rungume yana kokarin dedeta bugun da zuciyarsa takeyi akan zancen da falaq din ta fada kawai akan ayi masa treating dinta kaman hakan zai iya aikata abinda hankali bazai daukaba.
Hawayene suka sake zubowa falaq tana jin kwata kwata basuwa tsananin so da kaunar da jannah take musu ba bayan ta zabi juyawa wanda ya taso da kaunarta shekaru masu yawa baya akan tsananin son datake musu itada Daddynta,
Su kansu iyayenta sun zabi juyawa nasu baya suka zabi basu ita sbd farin cikinta amma gata ta qare a hannunsu masu aikinsu ma sunfita jin dadi.
Dr Sameera ce ta iso gidan cikin gaggawa sbd yanda sayd ya daga mata hankali da kira da buqatanta a cikin tsananin gaggawa.
Knocking kofar palon yayi wanda ya saka Falaq miqewa da sauri ta nufi kofar da fatan Dr ne ya iso.
Ahankali ya dawo da idanuwansa akan Jannah din ya zare tsadaddiyar D&G jacket dinsa ya rufe cinyoyinta farare tas dasuke bayyane sbd rigar jikinta batada tsayi sosai.
Dr Sameera ce ta shigo palon Sayd kuwa baima shigoba ya koma yana tinanin Allah yasa ha matsalar zuciyarta bane sbd irin silent pain din dayake hangowa a idanuwan AZIZ ya tabbatarda jin yake kaman kaman Ummitah ce a gabansa wani abu zai sake samunta sbd dena bugawan zuciyarta kaman sauran abinda ya rage musu na Ummitah ne yabarsu dan haka zuciyoyinsu sukai nauyi da wata damuwar da basusan ta ina take cikesuba.
Dr Sameera kuwa duk taimakon da zata bawa Jannah din ta bata babu alaman suma ne kawai dan haka dole ta buqaci suyi asibiti da ita cikin gaggawa sbd bugun zuciyarta gaba daya ba daidai yake ba.
Hakan da dr Sameera ta fada ya saka AZIZ din zubawa Jannah din idanuwansa yana jin kaman ya hana a kaita asibitin a hakan sedai kuma bazai bari zuciyarta ta dena bugawaba.
Falaq da jikinta har rawa yake sbd tsoron rasa Jannah da sauri ta kallesa zata kira sunansa bai tsaya jiran komaiba ya shiga bedroom dinsa ya dauko daguwar rigarsa jallabiya me shegiyar kyau da qamshi ya zirawa Jannah din ya dauketa gaba dayanta ya nufi kofa suka biyo bayansa.
Sayd na hangosa ya nufi waje da sauri kafin su iso ya tada mota tareda zuwa daf da kofar fitowa main palo ya tsaya Latif ne ya bude motar da sauri shima jikinsa na rawa.
Da mugun speed Sayd yabar harabar gidan da mota bayan securities sun bude musu gate tini.
Dr Sameera falaq tabi sbd yanda ta daga hankalinta ko anbarta kuka zataita yi.
Suna barin gidan Mama na isowa da sabon driver dinta yaje ya daukota Airport.
Cikin mamaki take tambayar Su jannah din da falaq Fiddausi ce ta sanar mata komai cikin mutuwar jiki.
Itama maman damuwa ta shiga tana fidda waya kiran AZIZ sedai harta yanke bai daga ba.
A asibiti suna isa da gaggawa akai emergency da jannah din wadda aka fara kokarin dawo da numfashinta da baya fita sukeyi.
Zaune yake a gurinda aka tanadar masa na jira Sayd na tsaye a bayansa yana kokarin neman hanyar da zasu samu history record na ciwonta sbd dole sai dashi zaa samu damar sanin yanda zaa bi da yanayinta.
Falaq na gefen Daddyn nata idanuwanta sunyi zuru na jiran tsammani.
Zaman awa kusan biyu zuwa uku sukai kowa da abinda yake zuciyarsa kafin Dr Sameera ta fito tareda wani dr Ashir
Ya kallesu yana jiran abinda zasu fada.
Numfashi sauke suna kallansa kafin cikin girmamawa da bayyanarda yanayin da ake ciki Dr Ashir dinne yace
"Numfashinta ya dawo hakama bugun zuciyar ya dan samu sedai ga dukkanin alamun da muka gani shine bugun zuciyarta is very weak wanda hakan na nuna Alamar heart patient ce so for now saita farfado munsan komai akan yanayinta zamu iya dubata dakyau,
Sai kuma hannunta da shima anriga an dubasa anji dashi insha Allah dan haka yanzu muyi fatan farfadowanta a lokaci"
Numfashi mara sauti sosai Sayd da Falaq suka sauke a lokaci daya yana kasa cewa komai.
Shi kuwa dago idanuwansa kadai yayi ya kalli Dr Ashir din a tsanake ya furta
"Thanks Doc"
Shiru sukai dukkaninsu kowannensu da tinanin dayake zuciyarsa sedai babu wanda yace komai sai falaq data lafe gefen jikinsa idanuwanta da jikinta sunyi sanyi.
Har dare bata farka ba dan haka ya buqaci su koma da ita gida a hakan aci gaba da bata kulawan a gida sbd babu yanda zaayi abarta asibiti ita kadai gashi har lokacin Zaadens basu saniba.
Ambulance ce ta dawo da ita gida a daren.
A dakinta aka kwatar da ita ya dauki nurses kwararri guda biyu dan kulawa da ita duk da ga mama ga Fiddausi amma dai nurses din sune zasufi sanin abinda ya kamata.
Saida aka gama mata komai aka falaq ce ta rufeta ta abin rufa me taushi ta zagaya ta kwanta gefenta sbd bazata taba iya kwana daban tabar Jannah a wannan halinba.
Shi kansa saida Falaq din tai bacci a gefen Jannah din kafin ya same sauke numfashi me dumi da gaba daya ayau din sai yanxu ya samu daman sauke numfashi.
Jannah ya saukarwa idanuwansa ya xubawa idanuwanta dake rufe ido yana kallan yanda sukai zurfi....
A bakinta daya bushe ya gangaro da idanuwansa ya zuba musu suma kafin ya dauke su ya maidasu akan hoton dayake bedside dinta a qaramin flame guda uku ajiye.
Hoton Daddynta ne na farkon shi kadai cikin Kamala da cika ido kaman asalin mutumin kirji..
Dauke idanuwansa yayi yana saukarwa akan dayan frame din hoton Mimi da Maheer da saleem ne da Ammar Dukansu da fararen shirts da blue jeans sai Ammar daya saka fcap.
Zubawa hoton karshe ido yayi wanda shine hoton Ammar Zad shi kadai sanye da Black Armanis.....
Tsayar da idanuwansa yayi akansa yana masa kallo biyu masu qarfin gaske na farkon shine kallansa a matsayin wanda ya kashe masa tasa yar uwar da hannuwansa ya zare zuciyarta daga kirjinta ya sakawa tasa macen wadda take matsayin Matarsa a yanzu amma hotonsa ne a gefen gadonta tana kwana dashi tana tashi dashi.
Miqewa yayi tareda ficewa a dakin yana bawa nurses daman su shiga su sake dubata kafin su wuce dakin da aka saukesu.
Kai tsaye hanyar palonsa y nufa yana sako kai ciki Fiddausi na ajiye tray din tea da zuman data kawo masa ta juyo ta fice cikeda girmamawa.
Kai tsaye Bedroom dinsa ya shige yana zare rigar jikinsa ya nufi hanyar toilet yana zare wandon yaja towel ya qarasa cikin toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi yana rufe idanuwansa hannuwansa na dan yin rawa alaman yanayinsa zai motsa amma yana kokarin hana hakan.
Ya dade sosai a ciki yana fama kafin ya fito ya shirya cikin kayan bacci masu santsi da tsada ya haye gadonsa ya kwanta batareda yasha tea din da aka kawo masa ba sbd kansa dayayi nauyi.
Washe gari har 10 bai fito ba sbd ciwon kan daya tashi dashi dan haka sai guraren 11 ya fito kuma kai tsaye dining ya nufa.
Mama dake palo tareda fadilah kallo daya tai masa ta fahimci yanayinsa dan haka cikin kulawa ta amsa gaisuwansa batareda wani dogon zancen ba da zai iya kara masa ciwon kai.
Fadilah kuwa itace ta miqe tabisa har Dining tayi serving dinsa abinci cikin kulawa sosai da kokarin nuna kamun kanta.
Bai cika kallo ba dan haka bai wani yi mata kallan Arzikiba yafara breakfast dinsa a natse.
Falaq na dakin Jannah data farfado sedai kwata kwata ba karfi ko kadan a tareda ita hakama ga hannunta daya a daure bata iya komai dashi sedai da dayan.
A karo na kusan biyar falaq ta fito tana kokarin nufar palonsa sake dubosa Mama tace mata
"Ya fito yana dining room,yaya jikin jannah din??
Juyawa zuwa dining tayi cikin farin cikin son sanar dashi jan din ta farka tacewa mama
"Taji sauki wanka ma zatayi"
Hamdala mama ta sake yi sbd tin safe itama take yawon dakin har bayan farfadowan jannah din,
Dining room din take kokarin nufa sai gashi ya fito a natse kwarjinsa na sake cike idanuwan Fadilah da Fiddausi harma sa maman.
Kama hannunsa tayi cikeda murna tace
"Goodmorning Besty,
Albishirinka,My Jan ta farka tin dazu fa"
Kallanta yayi a natse batareda nuna mahimmancin zancen garesaba ya bude baki yace
"Hakanne ya sakaki farin ciki sosai haka???
Gyada kai tai