Showing 123001 words to 126000 words out of 185083 words
tana sake fuska ta dan shiga firarsu kafin suka je shirin fita.
Driver suka fita dashi su hudu zuwa Saloon din,
Jannah din da falaq sai Anny da Fiddausi jakar hannun Falaq.
Vip card ne dasu a tsadaddiyar Palour din dan haka suna isa suka wuce sama ana musu barka da zuwa gurin tsit a tsare kaman baa Nigeria ba.
Dayake daga falaq din har Fiddausi ma datake matsayin me aiki har inda yafi nan din suna zuwa a kasashe dan haka basu wani damu ba.
Gyaran kai da qafa da fata da duk sauran gyara hankali kwance,
Anan sukai lunch na lafiyayyan tsadaddan abinci sbd akwai komai a cikin gurin kome kakeso zakai order ne a kawo maka.
Farin ciki falaq take cikinsa sosai suma kusan duka a cikin farin ciki da walwala sukai wunin guri.
Daga can wani Mall suka biya suka siya wasu abubuwan hadda Sabbin Nighties suka siya na matching kala jannah da falaq din.
Siyayyar masu abin duniya sukai ba yawa sosai se kudi hakama wani abin kaman baida amfanin siya.
Sai yamma sosai suka dawo gida lokacin ana ma kokarin shiga sallan magrib.
Wanka sukai tareda sallah tukuna suka fito jannah na gaba sanyeda doguwar riga mara nauyi datake rawa ta dan lafe a jikinta ba dankwali akanta tana duba chat a wayarta yunwa take ji ta nufo palo
Mimi da Saleem zaune yana nuna mata wani sako a wayarsa Ammar na kan one sitter yana duba abu a ipad dinsa kamar ma Meeting yakeyi sbd yanda ya nutsu ya maida hankalinsa sosai.
Anny ce ta fito itama tana waya hannunta riqesa robar ruwan datasha ta rage ta zauna gefen Mimi.
Falaq ce a bayan jannah tana duba wayarta data bari gida.
Misscall din Uncle sayd ta gani da numbernsa ta Nigeria da sauri ta sake dubawa farin ciki na mamayeta kafin tai magana qamshin daya shiga hancinta ne ya sakata kallan kofa da sauri tana cewa
"BestDaddy"
Dad ne a gaba da maheer suka shigo palon sai gasa ya shigo a natse kwarjinsa kwarjinsa aura dinsa na cike palon tareda qamshinsa me tsananin sanyi da aji.
Sanye yake cikin black Alexander Mcqueen ya qara wani irin haske da fresh....
Cikin tsananin farin cikin da batasan iyakarsaba falaq tayi kansa da saurin gaske tana ambatar sunansa.
Tin bata qarasoba ya ware mata hannayensa ta fada da karfi tana rungumesa.
Cikeda kaunarta dayake maya me sanyi ya zagayeta da hannuwansa duka biyu yana cewa
"Heyy my angel"
Murmushin karfin hali kowa keyi suna bayyanarda farin cikin ganinsa banda jannah data kasa motsawa daga inda take.
Ammar kuwa ko dagowa baiyiba yaci gaba da abinda yake yana jin nauyi na danne kirjinsa.
Sakinsa tai tana cewa
"Daddy ka dawo baka fada mana ba"
Sake rungumesa tai tana jin kaman zata fashe da farin ciki.
Sakinsa ta sake da sauri ta juya taje gurin jannah ta kamo hannunta ta janyo da karfi ta turata gabansa ba tsammani ta hade kirjinsu tana rungume jannah din ta baya sika fada kansa dukansu kirjinta na qarasa mannuwa da nashi batareda zatonsu ba su dukan dan haka saura kadan numfashin jannah yabar kirjinta har batasan lokacinda ta qanqame gefen rigarsaba a tinaninta rigarta ce tana rintse idanuwanta da karfi sbd fargaba.
A lokacin ne Ammar yaji gabaki daya ya rikice baya gane komai na abinda yakeyi ya dago idanuwansa da sukai jajir ya sauke akan AZIZ din wanda ko inda yake bai kallaba ya saka hannu ya zare jannah din daga jikinsa.
Falaq saurin ture hannunsa tai tana cewa
"Daddy nida Jan munyi missing dinka sosai,
Ka dena turemu" sake qanqamesu duka tai tana sake jin farin cikinta na yawa tace
"We love you Daddy"
Sayd dayake bayansa fuskokin zaadens din ya kalla daya bayan daya yaga yaqe kawai sukeyi babu alamar har zuciyarsu farin cikin yake.
Hannuwansa ya saka duba biyun ya zagayosu jikinsa dakyau yana sauke idanuwansa akan Ammar dayake jiqewa da zufa.
Ita kuwa dagowa tai ta kallesa cikin fargaba da bugawan zuciya jin irin rungumar da yayi musu.
Shima ita ya dawo da kallansa akanta cikin tsananin bugawan da tasa zuciyar tayi sbd jin tsananin bugun zuciyar datake kirjinsa a nasa kirjinsa yana sauka.
Jin yayi zafi da sanyi masu tsananin kargi suna rufesa lokaci daya idanuwansa suka kasa daukewa daga kanta a karan farko yana jin bugun zuciyar Ummitah a kirjinsa.
Janyeta yayi da sauri daga jikinsa yana hana kowa ganin idanuwansa ya kalli jannah din da itama da sauri taja baya tana komawa gefen Dad dinta ta riqe hanunsa zuciyarta na bugawa sosai ta kasa dagowa ta kallesa.
Saleem ne yayi saurin tasowa yana masa barka da dawowa sai a lokacin ya dago ya kallesa yana amsawa a natse kafin ya gaisa da Anny ya kalli Mimi suka gaisa a gajarce sbd ba sabo a tsakaninsu.
Ammar da yake kokarin hana yanayinsa bayyana a gaban AZIZ LIMBA miqewa yayi yana barin palon batareda kowa ya luraba sai shi limba din.
Dad da daman sun gaisa tare sukai magrib ma yace su qarasa palonsa.
Wucewa sukai har lokacin falaq na riqe da hannunsa bakinta yaqi rufuwa.
Jannah ma tana riqe da nata hannun Dad din.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
66
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
***********
Ko zama basuyiba Anny ta shigo tace angama shirya dining suka juya zuwa dining din duk da babu abinda zaici amma sbd Dad din daya sake cewa yaje din da falaq data takura akan sai yana gurin zataci suka nufi dining din.
Maheer ne yaja masa kujera ya zauna cikin basa yar girmamawa matsayin baqonsu kuma sirikinsu.
Zama falaq tayi kusa da daddynta jannah kuma na gefenta shikuma Ammar yana gefen jannah din.
Fiddausi ce tai serving nasu abinci gabaki dayansu sbd kwana biyu ta shiga cikin masu aikin gidan kuma sosai sukejin dadin komai nata akan nasu masu aikin da ake biya da tsada.
Jannah data kasa sakewa taci abinci Ammar ne ya kalleta yana daukan serving spoon zai zuba mata chicken soup akan abincinta dayasan tana so maganar AZIZ LIMBA ta ratsa shirun gurin a natse hankali kwance da cewa
"In the next 40 min zan tafi tareda falaq Aziz da......kallan Ammar yayi kafin ya kalli jannah da bata dagoba yace
"Da Matar da aka bani......"
Serving spoon din hannun Ammar kubucewa yayi daga hannunsa ya fada cikin soup din tayi baltsin daya sakasa saurin dora hannunsa akan fuskan falaq dake gurin daidai tareda hannun jannah din hannunsa ya sauka nata a qasa nasa a sama.
Maheer da Dad kuwa a tare suka sarke da abincin da suke ji suna dagowa kallansa.
Anny tai saurin bawa Maheer ruwa
Mimi ma Dad din ta bawa hannuwanta na dan rawa tana kokarin boye nata tashin hankalin.
Jannah ma ahankali ta dago ta kallesa idanuwanta na cikowa da hawaye.
Shi kuwa kaman bashine yayi maganarba ya kalli falaq da wani irin farin ciki ya sake ciketa ta riqe hannunsa dana jannah tana cewa
"Thank you BestDaddy"
Dad ne daya gama tari ya kallesa yana boye damuwarsa yace
"Da sauri haka babu shirin komai?
Ko zaka bari zuwa nan da kwana biyu ta shirya a natse"
Zubawa dad din idanuwansa yayi baida niyar basa amsa saida Ammar ya kasa hakuri yace
"Daman ai hakan ya kamata abari komai ya tafi a natse"
Batareda AZIZ ya kallesaba ya kalli Dad yace
'idan tana buqatan qarin kwana biyu zan qara mata sati daya Amma Dr Ammar Zad ne zai kaita da kansa,
Idan ya yadda zai kaita har cikin LIMBAs to shikenan ta qara sati daya"
Kallan Ammar kowa yayi ana jiran amsarsa shikuwa AZIZ din ya zubawa ido zuciyarsa kaman zata fashe da tsananin baqin cikin jin shi yakeso yakai Jannah da kansa gidan wani.
Dad ne ya dauke kallansa daga Ammar din yana cewa
"To ai wannan ba damuwa bane tinda daman qanwarsa ce yanada haqqin kaita gidan mijinta dan haka ba damuwa hakan yayi"
Abincin dayake bakin jannah dinne ya wuce mata da karfi tana daukan ruwa a cup tasha ahankali ya wuce.
Ammar ma jin yayi abincin dayake cikin bakinsa ya koma masa kaman madaci ya hadiye daqyar tareda shan ruwa.
Anny kuwa cikin farin ciki itama take dan haka itada saleem ne kadai da falaq sukaci abincinsu hankali kwance akan dining din.
Falaq na gamawa ya tashi tareda ita suka bar dining din dan shima kadan yaci yabar musu kayansu.
A palon Dad suka zauna shida Dad din da daddy mahmoud da maheer sunata firar business da wasu abubuwan.
Ita kuma falaq tana daki Jannah da Fiddausi na hada kayanta dan Daddynta zatabi yau kam sai gida batajin zata iya bacci bayan tasan Daddynta na gari.
9 suka fito tana riqe da hannun jannah tanajin kewanta tin bata tafi ba.
Har mota suka rakata tana kallan uncle dinta datai missing shima cikin tsananin farin ciki.
A motarsa shi da ita ne a baya sai Sayd yana taqi Fiddausi na gaba suka bar zaadens zuwa gida.
Suna zuwa masu aiki sukaita mata barka da dawowa Fiddausi ma jin tayi ta samu sukuni ta dawo gida.
Palonsa suka wuce ita dashi Fiddausi kuma ta wuce da kayanta duka ta kai mata daki.
Firar zamanta a zadeens din taketa basa da yanda kullum suke waya da mama da yanda jan dinta ke tsananin sonta.
Sauraronta kawai yake yana kallanta sbd batason tana basa labari yana qin bata hankalinsa shiyasa idan taba basa labari koda wanda baya sone saiya bata hankalinsa ya saurara.
Sai datai sututunta ta gaji tafara jin bacci ta tafi daki tai shirin bacci ta kwanta.
Shima shirin baccin yayi bayan ya gama waya da mama akan dawowanta gobe tukuna ya kwanta.
Washe gari suna gama breakfast ta kira jannah ta fada mata daura 6 days ta dawo gidansu gaba daya.
Sai yamma sosai mama suka iso itada Baba alhassan wanda yake nan shima yanxu sbd matansa daya ta rasu tin shekaru biyar yanxu dan haka baida mata yanxu hakama yaransa kowace tana gidan aure daman Sayd ne kawai namiji.
Murna sosai su falaq sukai da Fiddausi daga kuma akaita bawa mama labari itama tareda fada mata saura kwana 6 jannah ta taho.
Jin hakan mama tai magana da AZIZ din akan inda jannah zata xauna yace zata zauna dakin dayake kusa dana Falaq sai xuwa gaba zaa ware mata bangarenta idan zaayi gyara.
Hakan baiwa mama ba amma sbd ya fada dalilinsa saita yadda da hakan tasa aka cire komai na dakin duk da sabbi ne matsu tsananin tsada tasa aka saka mata wasu kayan.
Lafiyayyan lefen da aka kashewa kudin gaske da mama ta hada da manyan kudin da sarkokin gwal da English gold din daya kwashe kudade masu yawan gaske mama ta saka su anty maryam da iyalan gidan Alh Ahmed suka kai zaadens wanda ya bawa zaadens mamaki sosai sbd basu dauka AZIZ din zai iya kashe wannan maqudan millions din akan auren da suke tinanin baya so yanxu batareda sun san baimasan da lefen ba shi.
Jikin Mimi da jannah sanyi yayi sosai sbd saura kwana uku tafiyan tata,
Dad duk yanda yaso magana da AZIZ din yaqi barin su gansa,
Sunqi maganar dukiyar aurenta da zasu bada a zuba mata a gidan sbd basason auren ya zama cikakken aure dan haka sukai shiru suma ta wannan bangaren.
Anny ce ta dage da shirye shirye sosai tana ragewa jannah damuwar data shiga.
Ana gobe tarewan sakonsa ya shigo wayar Dad akan cewa goben by 7 Ammar ya iso da Jannah din limbas.
Dad bai taba haduwa da dan adam dayake kallan tsaban idonsaba yayi masa rashin mutunci na kai tsaye ba ba shakkar komai sai LIMBA
Amma dai koma menene zai daure ya hadiye sbd yarsa tana hannunsa yanxu tinda aurensa ne akanta.
Washe gari kaman ba 'yar datafi kowace mace gata da iko ba a zaadens haka akai shirin tafiyarta.
Ammar dayake jin kaman zai mutu ayau din dan zuciyarsa tsananin ciwo take masa hakama kirjinsa kaman zai qone sbd tafasa,
Daddy mahmoud ne ya lallaba ya ringa binsa da zantikan da suka sakasa fitowa kaita din da kansa zuciyarsa na neman bugawa.
Suna kokarin fitowa Jannah tayi kuka har batada karfi saiga Anty maryam da uwargidan Alh Saad din sunzo da mota biyu lafiyayyu na daukanta mama ta aikosu.
Sai alokacin Mimi taji dan sanyi ya dan ratsata sbd ita dai ma bata taba ganin irin wannna kaddararren auren mulkin mallakaba
Su kuma su Dad sbd shine kaman yake riqe dasu ya hanasu qarasa zubewa ya sakasu kasa cewa komai wanda ta wani bangaren ba hakan bane su yanxu hanyar da zasu dawo da komai nasu suke nema su nuna masa Jannah tafi karfin duk wani namijin dayake ji da kansa kamarsa dan kuwa akanta zasu iya batar dashi duniyar ma gabaki daya.
Su anty maryam ne suka karbo Amarya jannah cikin mutuncin da mutuntawa da girmamawa aka basu ita cikin bada amanar suka tafi da ita tareda Anny da mommy matar daddy mahmoud har Limbas.
Baya nan dan haka mama ce ta tarbesu cikeda girmamawa da farin ciki har taiwa Anny da mommy kyautar data dake girgizasu sai guraren 10 suka koma gida.
Su Anty maryam ma sunbar gidan guraren 11 aka bar jannah a taredasu mama da falaq da Fiddausi dasuke jin kaman zasu hadiyeta sbd kauna.
Karfe goma sha daya da mintina kadan motarsa ta dawo gidan.
Sayd ne ya kalli motar Jannah da aka taho da ita aka pake harabar gidan ya juyo kadan ya kalli AY din dake duba sako yace
"Ms jannah ta riga ta shigo LIMBAs"
Dagowa yayi ya kallesa yace
"A goben a kama Dr Abraham din sbd yanxu tana hannuna ko case din batan Dr Abraham ya bayyana zaadens bazasu iya boyeta ba sbd zargin kada akan case dinta su hana asan Gaskiyan tinda batanan"
Ajiyar zuciya Sayd yayi sbd finally dai zai fara farautan makasan Ummitah dan kama dr Abraham shine zai bayyanar musu da duk inda Dr ken yake.
Parking motar akai suka fito ya nufo ciki kai tsaye yana kashe wayoyinsa sbd hutawa yake buqata a yau daya tabbatarda abinda zaadens sukafi so da kauna a rayuwarsu y shigo hannunsa,
Su suna jiran damar da zasu juya rayuwarsa da duk abinda ya mallaka yanda sukaga dama shi kuwa tasa damar akansu har ta shigo hannunsa sai yanda yaga daman juyasu dukansu.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
67
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
********
Bedroom din da aka ware akaiwa gyaran Aljannar duniya akanta su anty maryam suka rakata bayan tin zuwansu suna palon mama suna fira ana sake rarrashinta ganin yanda tai shiru idanuwanta jajir tayi kalan tausayi sosai sbd ta rabu da familynta ba acikin dadin rai ba sbd kaf familyn babu wanda yake cikin farin cikin tarewan tata bayan saleem da Anny wadda ita sbd Son rai take komai.
Ammar zuciyarsa bugawa tai a bayan barin jannah mansion din dan haka a cikin daren aka nema likitoci cikin gaggawa dan kaman zai mutu yanayin yaxo masa dan haka gabaki daya hankalin familyn ya tashi suka aje maganar tarewan jannah din gefe suna kokarin ganin an ceto ran Ammar.
Falaq ce a dakin nata da Fiddausi dake jera mata kayanta a cikin wardrobe duk da sunada tsananin yawa dan kusan setin akwati biyar ne wanda in total zasuyi kusan akwati 30 babu kuma wanda ba designer set bane kudin akwatinan kadai banda kayan cikinsu zasu ciyar da wasu gidajen na watanni masu yawa.
Falaq duk da jan din na cikin damuwa da sanyi sosai kokarin sakawa walwala takeyi amma hakan ya kasa samuwa dan haka ta qyaleta ta zauna kusa da ita tareda riqe hannunta tana kokarin kwantar mata da hankali ta hanyar nuna mata suna tareda ita bata buqatan damuwa tako wane bangare sbd suna tsananin sonta zasu kula da ita kaman a zadeens.
Fiddausi kayan lefenta gaba daya da babu abinda aka taba haka ta kaisu closet ta jeresu tareda sauran akwatinan a gefen da aka ware me kyau na jere akwatina kawai.
Sake gyara dakin tai ta shiga toilet duk a cikin daren ta jere komai na buqatan jannah din a toilet tareda towels da sukafi guda goma sha biyu ta jere mata su sai rigar wanka bathrobe kusan guda goma itama ta jere ta sake gyara toilet din shima ta fito ta daidaita mata ac ta fice tana kallan time,Karfe goma sha biyu saura.
Kitchen taje ta hado ruwa da drink da