Showing 102001 words to 105000 words out of 185083 words

Chapter 35 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5476



"Jannah kinason auren Ammar kokuwa kina buqatan a baki time ki sake tinani??
Kina sonsa ne kawai as brother bakya masa soyayyar aure??"

Wani irin nauyin gaske dayake danne da kirjinta tsawon lokaci taji yana warwarewa ahankali idanuwanta na cikowa da hawaye sbd kunyar Dad din data kanta akan Zamowant kaman butulu ga soyayyar Ammar data taso a cikinta.

Gangarowa hawayenta sukai tana rufe idanuwanta tana jin soyayyar wanda baimasan tanayi ba mai karfi da ciwon gaske,
Ta laluba,ta shiga tinani,tayi kukan tayi binciken inda soyayyar Ammar ta bace bat a zuciyarta ta rasa ya akai...

Sanyi jikin dad yayi sbd kenan dai ta tabbata da gaske ne ba son auren Ammar din takeba.

Wani sarawa yaji kansa yayi sbd wannan wata sabuwar qaramar masifa ce zata qullu dan tabbas Ammar zai tabu,hakama shi bazai iya barinta aure wani gurinba sedai zaman gidan kenan dan bazai bari taje auren wani guri ba tinda ba lafiyayya bace a kashe masa ita a banza dan haka yaya kenan.


Maheer ne ya shiga tareda rufe kofar palon yana kallan Jannah din dake kuka mai tsima zuciya sosai kan qasa ta kasa kallan dad din sbd kunyar itace take tsananin son wanda ko a jerin mutane bai gama ajiyetaba take ganin.

Zaunawa Maheer yayi gefenta yana tausasa murya yace

"Da gasken kenan bakyason auren??
Meyasa Jan?
Ammar tin kina fadowa duniya yake miki tsananin so,
Meyasa duk wannan shekarun baki bawa zuciyanki daman sonsa ba sai yanzu da komai yazo qarshe zaa muku aure??


Girgiza kai tayi cikin tsananin takaicin kanta da sanyin jikin da batasan itama ya zataiba tace

"Bansaniba,wlh inasonsa ina sonsa sosai inason aurensa bansan meya sameniba yanzu,
Bansan meyasa ba,
Zan auresa bazan iya kasa aurensaba sbd inason nasosa kaman yanda yakeso na amma zuciyana ta kasa hakan,

Kallan dad tayi wanda jikinsa ya qarasa mutuwa tace

"Dad zan auresa,
Shi zan aura bazan taba iya fasa aurensa ba dan Allah kada abari yasan laifin da zuciyana tai masa na kasa saka sonsa a cikinta duk da a baya nasan shine yake cikin zuciyata shi kadai.....


Katse Maheer yayi da cewa

"Idan a baya kina sonsa meya faru da yanzu din Jan??
AZIZ LIMBA ne????

Rintse idanuwanta tayi da karfi hawayen cikinsu na sake gangarowa ta zame qasa tana cusa kanta cikin qafafunta tana kasa cewa komai sbd abin daman ya isheta ita kadai take neman bugawa batareda fidda maganar ciki da zuciyarta ba.


Dad kuwa da sauri ya kalli Maheer lafin ya kalli jannah din wadda ta sakasa sake shiga tsananin shock yace

"LIMBA kuma?
Shi takeso?
Are they inlove with each other ko me?


Numfashi me zafin gaske Maheer ya sauke yana cewa

"I dont know Dad amma shine wanda take tsananin so a yanzu"

Wani dan tari dad yayi yana jin tension da kuma sassaucin komai duk a lokaci daya sbd Indai har bata son auren Ammar to baida baqin cikin bawa AZIZ LIMBA jannah dinsa sbd zata cigab da samun rayuwar data taso a cikinta hankali kwance cikin kulawa me tsanani to amma AZIZ din yanason Jannah dinne shima kokuwa.


Maheer ma tinanin ya shiga hakama jannah din wadda takejin nauyin zuciyarta n raguwa sbd kaman ta rage zancen zuciyanta ne ta samu sassauci.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
54
Kasa cewa komai dad yayi sbd bayason ya zafafawa Jannah kuka da damuwanta sedai kuma tinda tariga ta furta da gaske zuciyarta ba son aure takewa Ammar ba tabbas bazai mata dole ba,
AZIZ LIMBA kuma datake so tamkar abu ne me sauki tinda sun zama daya zai basa aurenta dan farin cikinta da kuma sake samun damar zamowa cikakken family.

Maheer kuwa jin yayi kaman kuskure ne babba a cikin abinda duk yake shirin biyowa baya sedai kuma shima indai Jannah batason abu bazai iya bari a mata dolenba dan haka shima yanajin bawa AZIZ LIMBA auren Jannah Zad shine abu mafi nutsuwa a cikin lamarin.


Jannah na fitowa daga gurin dad dinta falaq suna shigowa gidan.

Jannah na ganin falaq din tai kokarin daidaita kanta tana sake murmushi me kyau tana cewa

"Meya sameki?
Meyasa take kuka Fiddausi?

Shigewa jikinta falaq din tayi tana cewa

"Daddy ne"

Jannah na jin hakan ta kama hannunta suna nufar dakinta ta zaunar da ita ta zaro tissue tana goge mata hawayenta cikin kulawa tana cewa

"Kuka bai kamaci wannan beautiful eyes din na falaq Aziz ba"

Dago idanuwa falaq din tai ta zubawa jannah din wadda nata idanuwan itama suka nuna kuka tayi sosai.

Hannu takai ta taba idon jannah din daya tana cewa

"Jan kinyi kuka kema??
Bakyason Auren kowa sai Daddyna da gaske??

Dagowa jannah tayi ta kalleta cikin mamaki da kunyar kanta batareda ta iya cewa komaiba.

"Jan nima banason ki auri kowa sai Daddy na,
Inason ki zama mamana ba matar babana ba,
Inason Daddyna ya aureki kada ki aura kowa kinji"

Girgiza kai jannah tayi tana cewa

"No falaq, i can't" cikin sanyi da mutuwar jiki.

"No jan tinda kinason Daddyna kuma kina sona nai miki alkawarin sai Daddy na ya aureki insha Allah indai yanason farin cikina zai aureki a date din aurenki da Ammar Zad"

Fiddausi dake zaune saurin kallan falaq din tayi dan kuwa indai ta dage da gaske to tabbas auren zai iya tabbata.

Jannah kuwa Girgiza kai ta ringi yi tana cewa falaq din ta dena fadan komai na maganar manya.

Falaq ce ta koma tana rarrashi da kwantarwa da jannah hankali sbd duk da tana yarinya ta fahimci wani irin so ne me karfin gaske jannah kewa Daddynta dan haka tabbas jannah zata zama matar daddynta insha Allah.


Jannah din bayan ta samu ta dawo daidai itama lallaba falaq din tai taci abinci wanda tare sukaci Mimi nata tarairayansu su duka biyun sbd falaq tace ta bata na daddynta amma na iya yau ne.

Anny ma sai lallaba falaq din take tana sake shige mata sbd ta gama sanin sbd falaq zata iya samun abinda yafi wanda take samu daga limbas.

Sai dare suka dawo gida lokacin AZIZ na zaune palonsa har lokacin yana jiran dawowansu.

Yana jin shigowansu ya sauke numfashi me sanyi yana miqewa ya shige bedroom dinsa yana nufar toilet dan wanka da shirin bacci.


Hankali kwance falaq tayi bacci sbd kaman ba itace me kuka ba ta fita.

Da sassafe ta tashi yau tai wanka ta shirya ta nufi bangaren Daddynta cikeda kewansa.

Tana shiga shima yana palo ya gamo geam kenan ya zauna yana amsa wayar maheer dake sanar dashi family dinner da zasuyi a zadeens suna gayyatansa da familyn duka.

Falaq na shigowa da gudu tayo kansa tana cewa

"Daddy Goodmorning"

Kashe wayarsa yayi ya Jiye yana kallan yanda take farin ciki take yaji sanyi da nutsuwan zuciyarsa sun dawo da suka dauke tin jiya.

"Morning Besty, kin dena kukan??

Murmushi tayi tana cewa

"Na dena,Jan tace my eyes are too cute and beautiful da basa kyau da kuka"

Kallanta yayi yana sauya zancen da cewa

"Zaki koma Greece da karatun ki ko kaman zaifi nan"

Tashi tayi daga jikinsa da sauri tana cewa

"Nooooo,bazan je koina ba,
Inda kake zan zauna bazan taba zuwa koina ba dakaiba"

Bai kalleta ba yace

"Anan ba karatun zaki maida hankali kiyiba zakita yawone kina biyewa dumb mutane"

Dariya tayi sbd tasan da jannah yake tace

"No dad my jan is very brave and calm inason zama da ita itama so inason dukanku na zauna tareda ku dan haka am not going anywhere"

Jin ta sako zancen da bayason yace taje gashinan fitowa breakfast.

Miqewa yayi ya nufi bedroom dins ya shige toilet.

Ita kuma fitowa tayi ta nufi dakin mama ta zauna tana fadawa mama ita fa dai daddynta ya auro mata Jan ta dawo gidan nan.

Mama da zancen yake sake mata dadi sbd fatanta dayake neman zama gaskia na ganin aurensa.

Karfe 9 ya fito a shirye cikin Sky blue tsadaddiyar yadin data kwana jikinsa da hula sai qamshinsa ke tashi yana gauraya hanyar dayake wucewa.

Dining ya nufa suna zaune suna jiransa.

Zaunawa yayi yana gaida mama.

Suna fara cin abinci Falaq ta sake jeho masa maganar auren Jannah wanda ya sake gurbata yanayinsa amma baice komaiba yaci gaba da cin abincinsa cikin nutsuwa harya gama ya miqe ya fice.

Office suka fice yana fita falaq jikinta yayi sanyi ta wuce daki tai kwanciyarta.

Bata sake fitowa ba saida lokacin tafiyanta islamiyya yayi ta fito tareda Fiddausi suka shiga mota aka kaita daman da Fiddausi take zuwa sbd bai yadda koina tana zuwa ita kadaiba.

Da driver da Fiddausi a mota suke jirant har tashi su dawo gida.

Gabaki daya ta sauya ta bata ranta taqiwa kowa magana sbd ganin da gaske Daddynta ko maganar yaki taba cewa komai dik tai magana baya cewa komai gashi kwanakin auren sai qara matsowa suke dan haka duk tabi ta shiga damuwa me tsananin gaske sbd yanayin jannah duk da tana kokarin boyewa ta nuna komai lafiya ne sbd tana cusawa kanta son Ammar din karfi da yaji sbd ganin yanda farin cikinsa yake a bayyane jin yake kaf rayuwarsa wannan lokacin ne best lokaci na rayuwarsa sbd mallakar jannah shine hasken rayuwarsa.

Mimi da batasan meyake faruwa ba da gaske take hidiman bikin wanda tini iv masu tsadar gaske wanda Anny ce ta bada aikinsi dan haka bata saka Sunan Ammar ba kawai anyisa ne a matsayin bikin Auren Jannah Zad.

Mimi bata damu ba haka shima Ammar din sbd bana daurin aure bane na daurin auren tini akayosu daga Germany suna aje.


Dad da maheer sosai sukeson ganin AZIZ wanda yana sane da abinda zasu fada mada dan haka yaqi basu daman haduwa dashi koyaushe baya zama sbd har cikin rantsa jin sunanta kadai qona jininsa yake bare aurenta wanda falaq ke kokarin tayar da ciwonta sbd hakan,
Hakama suma sosai sike son ganinsa akan hakan...

Tako wace hanya zaibi dan ganin ya hanawa Ammar samun abinda yakeso indai harya tabbata shine likitan daya cire zuciyar Ummitah da hannunsa ya saka a kirjin Jannah to amma bai taba kawowa kansa wannan hukuncin zai sakasa hada sunansa dana Zaadens ba a matsayin ahali.


Falaq ta dena walwala gaba daya ta dena cin abinci sosai ta daga hankalinta wanda duk yana sane amma abinda takeso tamkar cutatarwane gareta tasowa a hannun wadda aka dauke ran mahifiyar data haifeta sbd ita.

Mama ma sosai ta bude masa wutar fada da nuna bacin ranta tinda dai sun riga sun rada jannah wadda aka saka lalle dole ya nemo mata yayi aure ta basa nan da wata daya idan har ita uwarsa.

Daurewa kansa yayi da damuwa kashi kashi akan lamarin musamman kalaman mama da bata taba furta masa ba hakama falaq ciwo take kokarin kwantawa sbd dumuwan data saka a ranta yana barazana ga ciwonta dan haka ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda kallan Sayd d komai ya gama shirywa na zuwansu Zaadens yau.

Biki akeyi sosai a zadeens wanda duk Mimi ce take hidimar kowa ya lafe yaqi shiga hidimar sosai daga Mimi sai Saleem da Ammar din da amaryan kanta data dage ta sakawa kanta karfin hali bikinta takeyi sosai ko hakan zai mantar da ita komai,

A yanzu tafi Ammar tsananin matsuwa da a daura musu auren sbd aure kadai zaa daura mata ta iya cire AZIZ LIMBA a zuciyarta.


*****koda suka iso gidan bayan magrib ne dan haka cikin farin ciki aka tarbesu.

Mimi farin cikin ganinsu tayi sbd tinda aka fara hidimar bikin basu tahoba sai yau da ake maganar daura aure washe gari.

Falaq da batada lafiya sosai lafewa tayi jikin jannah tana jin tsananin kewanta da jin kaman ta dauketa su gudu d ita zuwa gidansu.

Ita kanta Jannah tai kewanta sosai dan haka ta ringa tarairayanta.

Falaq zuba mata idanuwa kawai takeyi tana kallan wani irin kyau da gyaran datasha ta sauya komai nata daukan ido yakeyi,
Fatarta sheqi takeyi tana fidda wani irin qamshim oud da bata taba jinsa ba take taji tana tsananin kishin Ammar da tsanarsa me karfi sbd Jannah matar da zata kawo farin ciki da walwalwa a rayuwan daddynta ne sbd bayada walwala da sakewa da cikakkiyar farin ciki a Rayuwarsa tinda ya rasa mamanta dan haka jannah matar mahaifinta ce.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
55
Acan palo kuwa AZIZ dinne da dad d maheer Ammar baya nan.

Kallansa dad yayi yana kasa riqe abinda yake ransa,
A matsayinsa na mahaifin da zai iya zubar da mutuncinsa akan yarsa indai zata samu farin ciki baya duba komai da kowa dan haka ya ajiye maganar auren da zaa daura a goben nata yace

"LIMBA a matsayina na uba ina maka tayin auren 'yata sbd son da kukewa junanku.....

Kallansa AZIZ ya juyo yayi yana bayyanar da mamakinsa kadan yace

"Kanada wata 'yar ne?
Ban taba son kowace mace ba a duniya bayan mahaifiyata d mahaifiyar Falaq sai mama da falaq,
Su kadaine matan da AZIZ LIMBA ya taba so yake kuma so,
So bansan wace 'yar kake magana ba coz i thought you only had one daughter wadda zaa daurawa aure gobe."

Kallan Maheer yayi lokacin dayake qarasa maganarsa alaman ko akwai wata yar?

Wani rikitaccen numfashi dad ya sauke hakama maheer rasa abin fada yayi sbd basu taba sanin akwai wanda zai iya fadar magana kai tsaye haka ba akan fuskansu.

Rikicewa maheer yayi zuciyarsa na tsananin zafi da baqin cikin cin fuskan da maganar AZIZ din dan haka ya bude baki zaiyi magana Dad da jininsa yake dan hawa ya dakatar dashi sbd basuda zabin daya wuce daidaitawa dashi ya karbi auren rinda jannah na tsananin sonsa kafin gobe farin cikinta ya lalace idan ta rasashi gaba daya.

Daidaita kai dad yayi cikin nutsuwa da nuna mahimmancin zancen yace

"Duk da hakan ni a matsayina na ubanta na baka aurenta idan har zaka amsa sbd kaunar datake tsakaninmu"

Dan gajeran murmushi me kyau da nutsuwa ya sake kai tsaye cikin steez yace

"No,thank you"

Wani irin zufa ne ya tsinkowa dad din yana kallan AZIZ din wanda kai tsaye yake maganarsa hankali kwance ba kawaici ko daya.

Maheer kuwa kirjinsa yaji ya toshe y kasa furta komai.

Qamshin jannah dinne me shegen dadi da nutsuwa yafara shigowa palon kafin ta sako kai palon cikin riga da skirt na wani plain lace mara nauyi d tsada ya zauna daidai jikinta komai nata ya fito d kyau.

Batasan yana palon ba dan haka ko dankwali babu a kanta dayake daure amma y dan yamutse kadin sbd falaq dake shafa mata shi tin dazu.

Magana zatai idanuwanta suka sauka akansa daidai lokacin shima ya dago amma sam idanuwansa basu sauka akanta ba wayarsa ya daga.

Cak maganarta ta dauke kirjinta ya buga da karfi ta kasa cewa komai saidata hadiye wani nauyin kirji kafin ta bude baki tace

"Dinner Dad"

Gyada mata kai yayi sbd shima ya kasa iya maganar.

Miqewa dad din yayi yayi gaba jikinsa duk a mace sbd sedai a daga daurin auren nan zuwa gaba amma bazaa iya daurasa ba tausayin yarsa yakeji sbd ko yanzu shi kadai yasan meya gani a idanuwanta lokacinda taga AZIZ din.

Maheer dayake jin yan suffocating da sauri ya wuce dad ya fice dad na bayansa.

Itace a bayansu tana kokarin bin bayansu ba tsammani abinda bata taba jib taji an riqo hannunta ta baya.

Cak zuciyarta da dena bugawa numfashinta na kokarin daukewa sbd tsananin shock da mamaki.

Kasa juyowa tayi sbd gap take da samun attack sbd qamshinsa dayake shiga hancinta direct daga jikinsa.

Attack yakeson bata sbd bayason barin gidan ayau sai yasan waye asalin likitan dasuke son sani sbd idan ba sauri yayiba aikinsa zai dade akansu gashi plans na sauyawa aurenta yana neman shigowa ciki bayan babu wannan banzan tsarin ko kadan a cikin plans nasa dan haka samun attack dinta a yanzu shine daidai lokacinda ya kamata ya san abinda yakeson sani.

Juyowa yayi da ita suna fuskantar juna a zuba mata idanuwansa tareda yiwa hannunta wani irin riqon daya saka zuciyarta kasa riqe bugawan ta dago idanuwanta ta zuba masa take taji tana samun attack ta zube a gurin.

Tsallaketa yayi ya fice daga palon daidai nan falaq tazo kiranta kafin tace masa komai ta hango jannah a qasa zube tana neman numfashinta dayake kakarin barin jikinta d qarfi ta kira sunant wanda ya saka kowa dawowa da sauri anayi kan Jannah din cikin matsanancin tashin hankali.

Dad da maheer ne alokacin daya sukacewa Mimi

"Ina Ammar ayi sauri a kirasa da gaggawa...."


Mimi ma cikin tashin hankalin ta saka kiran wayarsa tana cewa

"Ammar kayi sauri jannah is having an attack "

AZIZ da Sayd da sukai mutuwar tsaye suna jiran zuwan Ammar din wanda yazo da mugun sauri daman yana cikin gidan dawowansa kenan yana harabar gidan.

Yana shigowa da sauri ya dauketa cak ya kwantar a kujeran palon ya miqa hannuwansa biyu duka zai bude rigarta dan fara duba bugun zuciyarta aka riqe hannuwan nasa duka biyu cak.

Da wani irin tsananin mamaki da tashin hankali ya juyo.

Sayd ne y riqe hannuwansa yana kallansa.

Kusan kowa dauke wuta yayi a gurin sbd mamaki da tashin hankalin halinda jannah din ke ciki.

AZIZ ne ya tako a hankali cikin isa ya tsaya gaban dad ya kallesa yace

"Idan nace na karba auren daka bani nata kana ganin ya dace shi wannan din ya bude jikinta anan ya tabata?
Dan haka bazai tabataba a nemo likita,
Yana dora hannunsa akanta bazan taba aurentaba har abada."


Cikin wani irin mummunan tashin hankali da shock Ammar ya kalli AZIZ din mimi ma shock din t shiga da tashin hankalin tana kallansa hankali kwance yayi maganar babu damuwar komai aransa dan badan zuciyar dake bugawa a kirjinta ba bazaiqi ta buga a yanzu ta mutu a gurinba.

Sayd sakin hannuwan Ammar yayi yana matsawa baya.

Cikin tsananin fushi da kansa dayake neman juyewa Ammar ya miqa hannunsa zau bude rigar Maheer ya riqe hannunsa da sauri yana Girgiza masai.

Dad kuwa cikin jininsa dayake neman hayewa cikin damuwa me tsanani ya kalli AZIZ yace

"Likatane shi kansa din Dr Ammar Zad
Shine likitanta tin b yanzu ba zai dubata ne a matsayin likita ba wani abinba daban........

Dago idanuwansa yayi ya zubawa dad din sbd daga karshe dai sun fada abinda yakeson tabbatarwa.

Ammar din ya yiwa wani kallan daya saka Mimi zubewa zaune sbd jirim dayake dibanta.

Irin kallan da yayiwa Ammar shi ya yiwa dad da maheer kafin ya hadiye wutar dake cin zuciyarsa ya bude baki yace

"Na karba sadakarka a goben zan aureta a matsayin uwar da Falaq takeso"

Juyawa yayi yabar palon sayd ya kama hannun falaq dake riqe dana jannah din suka bi bayansa daman mama na can palon take Fiddausi na ganin fitowarsu ta kirata suka bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login