Showing 159001 words to 162000 words out of 185083 words

Chapter 54 - Kalbim Book 1 Complete Hausa Novel

Mamuhgee   

23 Sep 2025

5481

kallan Mimi kafin ta maida kallanta kan fuskan Ammar da sai a lokacin ta lura nade take da bandage mummunan duka ne a fuskan ba kyan gani.

Waya Ammar ya fidda ya nuna mata hotinan da yayiwa AZIZ a lokacin daya shaqo Dad ya zubar.

Mummunan faduwa gabanta yayi ta dago cikin slow ta kalli Maheer wanda idanuwansa suke jajir ya kasa kallanta.

Kan Saleem ta maida kallanta wanda ya saukar da idanuwansa da sukai jajir shima a hankali yana jin ciwo da radadin abun har qasan zuciyarsa.

Wani irin nauyi me girman gaske taji yana danne kirjinta ta juya ta kalli mahaifinta hawayen baqin ciki na gangaro mata tareda da jin soyayyar AZIZ LIMBA na sauka daga zuciyarta ahankali tana zubewa.

Ammar kuwa bude bakinsa dayake rawa sosai kamar me koyan magana sbd kansa dayake a juye tin dazu da azabar duka ta tayar da ciwonsa yana bubbuga kansa da hannunsa idanuwansa na sake rinewa da ja yace

"AZIZ LIMBA makashi ne,
Shine ya kashe Daddy mahmoud,
Shine yake kashe kowa,
Shine ya kama su Abraham,
Shine yakeson kashe dad,
Idan ya kashe dad zai kashe kowa,
Kema jannah yace saiya kashe ki,
Zai kashe kowa,
Bazai dena ba saiya kashe kowa dayake zaadens sbd Qanwarsa,
Qanwarsa ce a kirjin jannah,
Qanwarsa ta mutu,
Yace saiya kashe kowa,
Ya fada da bakinsa.......

Shiru sukai dakin ya sake daukan shiru maganganun Ammar na futa hayyaci ne kawai suke tashi ahankali kuka na zuwar masa.

Maheer zuciyarsa ta gama saddakar da komai vazan iya hana ammar maganar data saka su mimi shiga tinani ba sbd komai dai yazo karshe da alama.

Mimi gabaki daya hawaye take tsiyayarwa na baqin cikin jin Ammar na magana a zare basuda abinda zasu iya yi,

Saleem ma baqin ciki da ciwon zarewan Ammar din ne ya hanasa fahimtar abinda Ammar din yake fada.

Falaq dake tsaye kofa isowanta kenan taji dukkanin maganar da Ammar yake fada akan Daddynta wata irin mummunan bugawa kirjinta yayi kafafunta suka dauki rawa zuciyarta na kasa dauka ta shigo idanuwanta na cikowa da hawaye masu zafi tace

"Daddyna ba makashi bane bazai kuma taba zama makashinb insh......."

Ammar da dukkanin jikinsa ke rawa kanta yayi idanuwansa na rufewa ya shaqota yana bugata da bango da karfi bakinta ya fashe da jini ya saka hannuwansa biyu ya shaqeta yana cewa

"Saina kashe AZIZ LIMBA,
Saina kashesa saina kashesa kaman Ummitah,
Saina kasheki,
Ai kene AZIZ LIMBA......

Mimi,Saleem da maheer da tsananin tashin hankalin dayafi wanda suke ciki sukai kansa suna kokarin kwace Falaq wadda bakinta ke jini sosai tana kokarin riqe numfashinta dake kokarin saka zuciyarta dena bugawa sbd bugun zuciyar ya sauya sosai zuwa yanda baa so gashi sosai aka tabbatarwa limbas takai matikin da baaso ta sake samun matsala.

Jannah zubewa qasa tai tana fasa wani irin kuka me tsananin ciwo da qunci kamar zuciyarta zata fashe.
#MAMUH


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
85
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries




***************
Ahankali Dad idanuwansa suka bude sika sauka akan ahalinsa da suke cikin mummunan yanayi anata kokarin cire falaq a hannun Ammar wanda ya qarasa haukacewa gabaki daya ya koma asalin cikakken mahaukaci,

Kuka sosai Mimi takeyi tana jansa a jikinta amma sam yaqi banbaruwa,

Jannah datake kuka mai tsananin gaske jin take inama ta bude ido taga duka wannan rayuwar da sukai tin farkon dawowansu Nigeria mafarki ce,

Inama ta koma lokacinda take cikin ciwonta tayi jinyarta cikin Aminci ta tafi ta huta,

Maheer cikin tsananin zafi da tashin hankali ya sakarwa Ammar din wani mummunan marin daya sakasa faduwa shi da Mimi datake rugume dashi ta baya.

Saleem ne cikin tsananin sauri ya tare falaq ta zata zube qasa babu numfashi a jikinta ko kadan.

Da sauri jikinsa na tsananin rawa ya fito da ita zai nufi emergency da ita latif dayake mota idanuwansa suka sauka akansu da tsananin firgici ya futo ya nufosu yana cewa

"Meya sameta????

Akan jinin dayake fuskanta da kayan jikinta idanuwansa suka sauka wata mugun firgici ya shigesa baisan lokacinda ya kwatota daga hannun saleem dinba yana nufar mota da ita cikin tashin hankali da tsoro me tsananin gaske.

A rikice ya figi motar ya nufi gida kaman zai tashi sama sbd yasan ganganci ne zaiwa AZIZ LIMBA barin a duba falaq din asibitin zaadens.

Koda ya iso gidan cikin matsanancin tashin hankali yayi ciki ya kira mama da Fiddausi cikin tashin hankali suka fito..

Fiddausi kallo daya taiwa Falaq take jikinta ya dauki rawa tayi kanta tana tallafo ta,

Mama kuwa a rikice ta kallesa tace

"Accident kukai?
Meya sameta?
Innalillahi wainna ilayhi rajiun,
Ku kuramun AZIZ da sauri a waya kar naga baqar rana yau"

Kokarin fiddo da falaq din mota ake aka wangale gate
Dukkaninsu mayar da kallansu kan gate din sukai ganin motar AZIZ ce gaban Latif yayi mummunan faduwa.

Sayd parking yayi yana kallan su maman.

Shi kansa AZIZ ganinsu harabar gidan duka ya sakasa fitowa yana kallansu kafin kowa ya motsawa idaniwansa suka sauka akan Falaq da Fiddausi da fadilah suka fitar kamar wadda tai hadarin mota.

Miqawa Sayd wayoyin hannunsa yayi yana isa gurin kai tsaye ya karbeta gabaki dayanta yana cewa

"Meya sameta???? Cikin wani irin mummunan yanayin daya sake saka jikin kowa sanyi.

Mama a rude tabi bayansa tana cewa

"Accident sukai"

Sayd kuwa wayarsa y fidda cikin tsananin sauri ya kira likitoci yanace maza maza ana buqatansu.

Dukkaninsu ciki suka dungumo hankali tashe.

Babu bata lokaci su dr Ashir suka iso tareda nurses da komai na buqatan taimakon gaggawa..

A wannan lokacin ne Latif ya tako ahankali cikin damuwa me tsanani ya sanar dashi ba ba Accident bane daga dakin zaadens kome ya faru.

Rintse idanuwansa da sukai jajir yayi Ahankali wani irin abu na gangarawa kirjinsa ya danne masa.

Abu dayane yazo kansa Ammar ne ya taba masa 'ya....

Sabuwar tsanar zadeens din yaji tana gaurayesa wadda take kewaya dukkanin jinin dayake yawo jikinsa,

Duk taimakon dasu dr Ashir zasu bata sun bata sedai bugun zuciyarta be dawo yanda akesoba da alama ta riga ta shiga stage din da baa so,

A yanzu akwai hope qalilan idan har bazata sake bugawan zuciya ba sbd tana sake samun attack shikenan komai ya lalace kodai a mata dashen zuciya kokuma ayi hakuri a jira lokacinta kawai.

Wannan zancen da dr Ashir ya koro masa bayan sun mata wasu irin gwaje gwaje har kusan asuba shine ya tarwatsa dukkanin kuzari da zuciyar wanda yake limbas sbd maganace da akai gaban kowa.

AZIZ din kasa riqe kansa yayi ya zube qasa a gaban likitan yana cusa kansa cikin qafafunsa idaniwansa n wani irin radadin daya saka mama fasa kuka mai tsima zuciya sbd bata taba tinanin zasu iya rasa jinin da Ummitah tabar musu a duniya ba,

Rasa falaq shine rasa jinin Fatimanta a duniya kwata kwata sbd AZIZ bazai taba rayuwa ba idan ya rasa Falaq wadda itace abinda ta rikesa da yanzu ya dade da mutuwa a nakasashe mara hankali.

Sayd kuwa gurin mahaifinsa ya tafi ahankali ya silale gabansa ya zauna ahankali baisan lokacinda wani irin kuka me sanyi yazo masa ba,

Kaunar yarsa a jininsa yake wadda rasata rasa AZIZ ne wanda yakewa kallan jininsa da shima zai iya shiga mummunan hali idan ya rasa.

Fiddausi ma kuka takeyi sosai sbd tamkar yar data haifa takejin Falaq kaunace a tsakaninsu me girma da tsafta,

Dik karfin halin fadilah ma sanyi jikinta yayi cikeda tausayin ahalin gidan da falaq din kanta data koma abin tausayi lokaci daya tayi fayau da haske sosai sbd matsalar zuciyar a take take janye albarka jikinta..

Tsit gidan yayi kaman gidan mutuwa sbd kowa na cikin tsananin dacin zuciya da qunci,

Ko securities da masu aiki gabaki daya kowa jikinsa a sanyaye yake.

Daman kwana zaune akai gidan likitoci na kan Falaq din.



***acan asibiti suma kwanan zaune sukai sbd Ammar daya rikice hakama Dad ba sauki ko kadan ga Mimi zuciyarta ta fara kasa dauka,

Maheer na ya zaunar da ita ya sanar da ita qasar zasu bari gabaki dayansu.

Shiru tayi zuciyarta na wani irin sanyi da ciwo duk a lokaci daya wanda a wannan karan batajin soyayya zata hanata bude idaniwanta ta tsaya tareda familynta da sukai sacrificing komai akanta,

Numfashi me zafi ta sauke ahankali tana hadiye wani irin daci da ciwo ta kalli Maheer tace

"Na Amince zan biku mu tafi bazan sake waiwayan baya ba"

Dad ne ya sauke numfashi ahankali cikin ciwo na jin dadin abinda ta fada,

Maheer ma numfashin ya sauke yana jin samun sanyi da saukin nauyin kirjinsa.

Hudu na yamma likitoci da nurses din mahaukatan daya gayyato daga lagos jirginsu ya sauka daga airport kai tsaye motocin asibitin Mahaukatan nan abuja ce tazo ta daukesu tareda motar jamian Drugs da babu me alamar yasan imani a acikinsu suka isa asibitin Zaadens.

Suna isa dakin da Ammar yake kwance an dauresa a gado abi na farko wani mahaukacin mari Wani Dan drug ya fara kashesa dashi wanda ya saka haukarsa daukewa ta wucen gadi.

Motocin police ne kusan guda biyar suka iso asibitin take guri ya cika aka hargitse.

Wani mummunan daurin azaba akaiwa Ammar kamar goro yana ihun tsananin azabar da bai taba ji ba aka fito dashi tareda takardar asibitin mahaukata zaa kaisa ta lagos.

Duk tsananin ciwon dad saida ya tashi daqyar suka fito dukkanin familyn suna roko da neman taimako cikin mummunan tashin hankali da fita hayyaci.

Maheer ayau kuka yakeyi kaman mace a gaban tarin mutane amma wani ball da akai dashi saida ya fasa goshi.

Dad ma kuka yakeyi sosai kirjinsa na tsananta ciwo.

Mimi kuwa yanke jiki tai ta fadi saleem yayi kanta.

Jannah kan maheer tayi tana goge masa goshinsa daya fashe da hannun rigarta idanuwanta jajir.

A dakin da dad yake aka kwantar Mimi dan haka dukkaninsu sunyi shiri zuciyoyinsa na ciwo da tarin baqin cikin daya rufesu,

A rayuwarta soyayyar AZIZ LIMBA itace mummunan kaddarar data afkowa rayuwarta harta tarwatsa mata family ayau sike cikin mummunan halin dasuke buqatan dauki.

Tayi danasani da baqin Kamuwa da soyayyar wanda bai taba sonta ba qarshen iyayenta kawai yakeso batareda laifin komaiba,

A yau tayiwa kanta alkawarin ta hakura da rabuwa da aurensa,
Idan ita yar halak ce zata cire soyayyarsa har abada bata buqatansa...

Miqewa tayi ahankali ta fice daga dakin taba jan kafafunta daqyar.

Gate ta nufa idanuwanta jajir ko gani sosai batayi ta tari mota ta shiga ahankali tana rufe idanuwanta bayan ta sanar dashi idan zai kaita.

Ahankali ta miqa hannunta ta dora akan zuciyarta dake bugawa da tsananin ciwo da quncin datake jin yana sake ciketa tako ina.

ko data iso gidan security da sauri suka bude mata gate ta shigo tana tafiya cikin quncin daya rufe idanuwanta.

Ciki ta shigo babu kowa a main palo sai Fiddausi data ganta ta qaraso cikin tsananin sanyi tana mata sannu da zuwa amma sam Jannah batajinta sbd nisan datai a cikik matsanancin qunci da tinani me ciwo.

Kai tsaye dakin Falaq ta isa ta taddata kwance kamar wadda tai shekaru a kwance.

Silalewa tai ahankali bakin gadonta tana fasa wani irin me tsuma zuciya da tsananin ciwo da radadin rabuwar da zatai da ita har abada batason su sake haduwa sbd haduwansu ba alkhairi bane garesu su dukan gwara kowa yayi rayuwarsa.

Kukane tayi sosai wanda baida sauti ko kadan zuciyarta na tsananin ciwo tsawon lokaci kafin ta miqe ko gani batayi sosai ta fice daga dakin sedai batasaniba Falaq din ta bude idanuwanta itama Hawaye takeyi sosai batareda ta motsa ba sbd tsananin qunci da azabar ciwo take ji itama wanda yake sakata jin tsoron kamar mutuwa zatai.


Tana fitowa kai tsaye palonsa ta nufa ta bude kofar ta shiga daidai fitowansa idaniwansa sun fada sosai a lokaci daya sbd tsananin damuwa da tsoron dayake bayyane a yanayinsa na tsoron rasa 'yarsa da itace rayuwarsa.

Tsayawa sukai suna kallan juna ahankali tsana na tasowa ahankali tana rufe zazzzafar soyayyar dake qasan zuciyoyinsu,

Ahankali ta tako ta tsaya gabansa ta bude baki tana kallan cikin idaniwansa tace

"Meyasa?
Why?
Mun cancanta hakan daga gareka ne?
Sbd zuciyana ta mutu akan soyayyarka ne ka zabi hukunta iyayena da yan uwana akan laifin daba nasu ba?
Duka soyayyar danake maka ne ta jawo wannan?

Wasu hawayen tsananin radadin zuciya ta hadiye ahankali tana cewa

"AZIZ LIMBA kaje nayi freeing dinka daga Soyayyar da kake cutatar da ahalina akanta,
Na cireka daga zuciyata bazan qara sonka har abada,
Sadakata aka baka ayau ina rokonka ka jefar da sadakar da bakaso ka bani yancina na maka alkawarin har abada bazaka sake sakani a idaniwanka ba zan tabbatarda hakan sbd ni kaina bazan taba son sake saka ka idaniwanaba.......


Jajir idaniwansa sukai tiririn dayake cin zuciyarsa na tafasowa ya jefa mata mummunan kallo tana ficewa daga rayuwarsa gabaki daya ya dago file din dayake hannunsa nata wanda zai bawa Sayd ayau a saki duniya tasan su waye zaadens ya jefa mata a fuskanta takardun duka watse gabaki daya a qasa.

Cikin tsananin tsanar familynta datake juyewa harda ita yace

"Yaushe kika samu bakin tambayar why?
A zaadens babu me darajar da zai tambayeni na amsa harke din,
Ki dena tambayar auren dayake kanki sbd tin farko ban daukeki mata ba kuma bazaki taba zama matar dani AZIZ LIMBA zan ambata da matataba,

Amsa kikeso na abinda familynki sukai?
Kije ki tambayesu zuciyar waye a kirjinki take harbawa?

Ki duba ga takardu nan rai nawa suka kashe kisan gilla kafin su kashe mace me tsohon cikin da zuciyarta take bugawa yanzu haka a kirjinki,

UMMITAH ABDULAZIZ LIMBA shine sunan,
Shine sunan mahaifiyar data haifi Falaq,
Shine sunan Qanwa kuma jinin AZIZ LIMBA daya dayake da ita a duniya da bustards dincan suka kashe sbd a raya waye?????

Ke sarauniyar Zaadens da ranta yafi na kowa,

Ummitah data raye da yarta da mijinta Sayd a cikin Aminci badan ke ba,
Badan keba da yanzu Falaq tana raye tareda mahaifiyarta,
Da yanzu yaya na yana tareda qanwarsa daya taso baida kowa sai ita,

Itace rayuwata,itace gabaki dayan AZIZ LIMBA amma suka farka kirjinta suka rabata da zuciyarta sbd son zuciya and kin samu daman tambayar me sukai?

Sarewa kafafun Jannah sukai cikin matsanancin tashin hankalin daya saka zuciyarta bugawa ta durqushe tana dafe kirjinta sbd tsananin azabar gaske takeji idanuwanta na neman rage gani.


Falaq datake tsaye bakin kofar cikin rashin karfin jiki kunnuwanta suka ji mata kalaman da suka juya duniyarta lokaci daya jini ya fara biyowa ta hancinta ahankali kafin tausayi wani motsin harta bakinta yafara fitowa....


Mama ma data biyi bayan falaq din dataga wutowarta mutuwar tsaye tayi da abinda kunnuwanta suka ji mata amma ganin yanda jini yake fita baki da hancin Falaq tana yanke jiki ta fadi ya sakata ambatar sunan Falaq din cikin amon daya saka AZIZ kallan kofar yana yi kan falaq cikin mummunan halin dabai taba samun kansa a ciki ba.
#MAMUH
#THE STORY BEGINS
#BEST HATE LOVE STORY
#BESTROMANCE
#AZIZ AY LIMBA
#JANNAH ZAD
#AYSH.......
#CRAZY LOVE
#LOVE TRIANGLE


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
86
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries




************
FALAQQ" shine abinda bakinsa ya furta da wani sauti me fasa zuciyar datake neman rasa kanta yana yin kanta idaniwansa na sauyawa dukkanin hannuwansa na wata irin rawa.

Kafin ya isa ta zube a jikin mama data tareta itama koina jikinta na wata irin rawa sbd jinin daya zubowa daga bakinta wanda ya sakata jin tana rasa kanta itama sbd tinanin zuciyar Falaq din ta riga ta fashe.

Yanda ya furta sunanta da karfin gaske gidan ya amsa gabaki daya ya saka dukkanin dan adam dayake gidan tsayawa cak daga inda yake suka jin zuciyoyinsu na tsinkewa.

Sayd ne ya fito yana qarasowa palon da tsananin sauri da tsoron idan ba collapsing din da akace kada taiba na karshe ta samu.

Tsananin rawan da hannuwansa basu taba yiba hannuwan AZIZ din sukeyi ya ringa goge mata mata bakin da hancin batareda yasan me yakeba yana kiranta bakinsa da hannuwansa suna tsananin rawa jinin na sake fitowa.

Mama ma fita hayyacin nata tai tana kokarin riqesa ganin yanda komai nasa yake rawa yana fita hayyacinsa zarewansa na bayyana tuburan yana kiran sunan Falaq din yana jijjigata gabaki daya jikinsa da nata ya lalace da jini.

Sayd na shigowa hankali a tsananin tashe wani mummunan burki yaci wanda ya sakasa kusan faduwa yana kallansu zuciyarsa na wata irin tsagawa da karfin gaske.

Bude baki yayi da wani irin karfin hali yace

"Asibiti,asibiti"

Kamar jiran afada AZIZ yake ya miqe da sauri da ita a jikinsa ya nufi kofa Sayd na gaba da tsananin sauri ya fiddo mota hannuwansa na rawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login