Showing 126001 words to 129000 words out of 185083 words
snacks a tray me shegen kyau da girma ta kawo dakin ta ajiye a table sbd yunwar dare incase ta fice daga dakin tana mata saida safe.
Batai wani wankan ba sbd tayi na daren kafin zuwanta nan dan haka kayan jikinta kawai ta sauya sbd suma bazata iya kwana dasu bane ta cire ta saka riga da wando masu kauyi da girma da hula akanta ta kwanta tana rufe idanuwanta tareda sauke numfashi me zafi tana tinanin halinda Dad dinta da Ammar suke ciki sbd sune wainda zasufi kowa shiga damuwar kewanta.
Falaq dataso jiran dawowan Daddynta bacci dauketa yayi a palon ba yanda Fiddausi bataiba akan taje daki taqi dan haka dole itama a palon ta tsaya tayata jiran.
Lokacinda ya shigo palon akanta idanuwansa suka fara sauka ya kalli Fiddausi datake tsananin jin bacci amma bazata iya yiba sbd tsaron falaq din.
Tana ganinsa miqewa tayi ahankali cikeda girmamawa tana masa barka da dawowa.
Bai kalletaba Falaq din yake kalla yana ganin farin cikin dayake bayyane a fuskanta duk da tana bacci.
Tausayinta yaji ya cike zuciyarsa sbd tana tsananin kaunar macen da zuciyar mahaifiyarta take kirjinta batareda tasan bugun zuciyar mamanta ne take jiba wanda kila hakan ne ya sakata tsananin so da kaunar Jannah din haka sosai,
A rayuwarta shi kadaine wanda sonsa yafi mata komai na duniya sai yanxu dayake ganin tanawa jannah wannan son wanda yake sakata farin ciki da walwala sosai.
Qarasawa yayi gurinta ya durqusa ahankali ya shafa fuskanta ahankali kafin ya dauketa gaba dayanta ya nufi dakinta Fiddausi na biye dashi, Sayd kuwa juyawa yayi ya nufi hanyar palonsa da bedroom dinsa yana kashe wayoyinsa duk da yakamata yayi aiki yau da dare amma zai bari zuwa da safe.
Kwantar da ita yayi ya rufeta yana mata addua a natse yana gamawa ya sake gyara mata rufa ya rage mata ac.
Fiddausi ce ta kashe komai suka fice daga dakin ya wuce ta kofar dakin da jannah take ciki kwance idanuwanta rufe damuwa da sanyin jiki cike fal da kirjinta.
Fiddausi ma dakinta ta wuce tanajin gajiya sosai ta sauya kayanta zuwa na bacci ta goge fuskanta da wipes ta kwanta tana addua take bacci ya dauketa sbd a tsananin gajiye take.
Washe gari tinda falaq ta gama asuba take son zuwa dakin jannah amma tana fasawa sbd tina fadan mama dataita maimaita mata karta ringa zuwar mata da asuba koda daddare sosai sbd kada ta takura musu itada Daddynta.
Har gari ya fara haske tana son zuwa amma jin ba motsin kowa dole ta koma gadonta ta kwanta ta koma bacci.
Jannah dayake bata samu baccin daren ba saida tai sallar asuba baccin yazo mata bayan tayi waya da Mimi da Dad dinta yace mata komai lafiya tukuna ta kwanta bacci me karfi ya dauketa.
Dayake kowa hutu yakeson samu a gidan sbd yar hayaniyar da akai jiyan ta tarewan baquwansu shiyasa babu wanda ya fito da wuri tsit sai masu aiki dake kaida kawon aikinsu cikin rashin hayaniya suka gyare koina fes koina sai kamshin luxuries yake da Sanyin Ac ba hayaniya.
Ita kanta Fiddausi bata fito da wuri ba sbd ita kaman ta zama family duk da mai aikince amma aikinta na musamman ne kuma duka masu aikin gidan a karkashinta suke dan haka bata fitoba sai kusan karfe goma tana isa kitchen aikin breakfast din mutan gidan ta fara cikin tsari da yanda tasan kowa na son komai nasa ya kasance.
Tana gamawa tafara jere komai a dining din sai alokacin suka fara fitowa.
Mama ce tafara fitowa tana waya cikin riga da zani na wani lallausan lace mara nauyi da hayaniya sai tsada kunnuwanta kuwa daman gwal ne a jikinsu tintini tasaka normal gwal ta saka English duk wanda taga dama sakwa takeyi sbd bata son masu nauyi dan haka idan kagani ma bazaka dauka gwal bane sbd yanda suke simple da rashin ado sosai.
Zaunawa take kokarin yi falaq ta fito daga dakin jannah tareda jannah din datake sanye da Riga da skirt na lace mara nauyi ko kadan itama se tsada navy blue kala daya kwanta a jikinta ya fidda lafiyayyan shape dinta.
Qaramar veil ce akanta wanda iya kacinta wuyanta dan bata iya saka babbar gyaleba batama taba sakasa ba rayuwarta dan haka qaramar veil din data tsaya wuyanta duka sauran jikinta a bayyane yake duk da bawai kamata kayanta yayiba amma daidai jikinta ne.
Falaq ma dakinta ta koma ta sauyo kayanta zuwa irin na jannah din sbd kusan duka kayansu sunada iri dayane sbd duk abinda zata dinka guda biyu take dinka musu itada falaq sbd falaq na son kayan hausa sosai tinda bata taso tana sakasu ba shiyasa take kaunarsu sosai.
Gurin mama jannah din ta qaraso cikin nutsuwa da girmamawa ta gaidata tana dan kokarin korar da damuwan datake fuskanta wadda ta kwana a cikinta.
Cikeda kauna da kulawa batareda damuwa da qaramin mayafin dayake wuyan jannah dinba mama ta miqa hannu ta kama na jannah din ta zaunar da ita gefenta tana amsawa da cewa
"Jannah yaya baqunta?
Karki saka damuwa sosai a ranki nan din gidanki ne,
Kece matar gida ki sakewanki zakiji dadi zama damu sosai sbd muna muna kaunarki kamansu Mimi,
Banason ki takura kanki ko kadan kinji,
Shi kansa AZIZ din rayuwa dashi itace best rayuwar da zakiyi alfahari da ita,
Badan ina mahaifiyarsa ba nake yabansa tabbas Zakiji dadin rayuwar aurenki a Limbas,
Allah yayi muku albarka ya sakawa aurenku albarka da kwanciyar hankali har tsufa da jikoki insha Allah kuna tare."
Amin" falaq take cewa tana qarasowa gurin kafin ta zauna ta juya tayi hanyar palon Daddynta.
Sake juyowa tayi zatai magana Mama tace
"Zo ku tafi da Jannah ku gaida Bestyn naku tinda kince yanzu keda ita kuke dashi,ni danake uwarsa na tashi a banza kenan bana cikin lissafi"
Dawowa tayi da sauri tana kama hannun jannah din wadda gabanta ya fadi jin abinda mama ta fada ta dago fararen idanuwanta ta kalli hannun falaq dayake kama nata ta kasa kallan mama datake jin kunyar tace mata aa batason zuwa.
Fiddausi kuwa dariya tayi tana cewa
"Mama ke ai tini 'yarsa ta rabaki da naki dan tinda tintini tace ita kadai take dashi sai yanzu da akai arziki ta yadda itada Anty Jannah take dashi"
Cikin sakewa mama tace
"Iyi ai kibar yar Albarkar yarinya dan bazance jaira ba duk ta gama zama jairar dan haka gwara mu koma cewa yar albarka din tayita samun albarkar"
Kallan jannah data kasa motsawa maman tai tana cewa
"Kuje ku gaidasa kun fito tare cin abinci"
Rikitaccen numfashi ta sauke a boye me zafi tana miqewa kafafunta na sanyi falaq na sake riqeta suka nufi inda falaq din ke dosa dasu bugun zuciyarta na tsananta.
Suna barin gurin mama tabi bayanta da kallo tana jin kaunarta ta sake shigarta Allah ya cika mata burinta na shekaru yau ta wayi gari a gida daya da matar AZIZ saura jikokinta suma tana fatan Allah ya nuna mata ta wayi gari hayaniyarsu ta cika mata gidan.
Sanyi jikinta yayi sbd Allah beyi fatima ce zata ga hakan ba itace take ganar mata duk da kaman yanda AZIZ bai cire rai daga mahaifiyarsa ba koyaushe bincikensa akan inda take bai taba tsayawaba tinda ya tsayu da kafafunsa yana fatan wata rana ace an samo masa inda take itama hakane bata taba cire rai da sake ganin fatima wadda suke fatan duk inda take ta kasance tana cikin Aminci da kariyar ubangiji.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
68
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?
Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,
Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;
Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
******************
Duk taku daya da suke qarawa na zuwa palon nasa tsananta bugun zuciyarta yake dan haka kafafunta suka qara sanyi kaman bazata iya qarasawa ba takeji sedai kuka mama na palo tana jiran zuwan nasu hakama falaq na maqale da hannunta tana jin kaman suyi gudu su isa da wuri.
Rikitaccen numfashi me zafi mara sauti ko kadan ta sauke a lokacinda falaq ta bude kofar palon kai tsaye wani irin sanyi dayake cikeda qamshinsa tako ina ya bigo a fuskanta yana shiga hancinta tareda qarasa yamutsa bugun zuciyarta gabaki daya.
Bude idanuwanta tayi ahankali cikin nutsuwa tana kallan cikin palon da babu kowa ta sake sauke boyayyar ajiyan zuciyan farin cikin baya nan.
Zaunar da ita falaq tai tana juyawa da sauri zata tinkari bedroom dinsa jannah din tai saurin riqe hannunta tana kallanta sbd ta fahimci ina zata ta bude baki a natse tace
"Ina zakije?
"Zanje na dubosa ne a bedroom dinsa"
Sake kallanta jannah din tai dakyau tana mamakin rashin wayonta sam,
A hakan yake iya bude baki yace tarbiyan gidansa tafi ta wasu.
Dawo da falaq din tai gefenta ta zaunar cikin nutsuwa ta kalleta tace
"Bakisan kinyi girman da bai kamata kina shiga dakin Daddynki kai tsaye ba?
Kin girma kin zama yan mata ke kina buqatan privacy a daidai wannan shekarun naki dan haka shima daddyn yana buqatan privacy...."
Katseta falaq tai da cewa
"Ai babu me shiga duniya idan bani ba ni kadaice nake shiga bedroom dinsa nima sbd ina yarsa ne"
Girgiza mata kai jannah tai tana kama hannunta cikin kulawa tace
"No kema kinyi girman daya kamata ki dena shiga kwata kwata idan ba shine ya kira ba,
Ba daddynki kadai ba bedroom din kowane namiji a duniya karki sake shiga saina mijinki kadai idan anmiki aure,
Baa shiga Addininmu ya hana hakan kwata kwata baayi ki kiyaye sosai karki sake saina mijinki,kinji???
Shiru falaq tai tana nazarin zancenta sbd Daddynta daman yana fada mata kowane namiji a duniya karta yadda ko hannunta ya kama koda da sunan gaisuwa,
Yasha fada mata hakan tin tana yarinya sosai haryanxu bai dena fada mata shiyasa iya shi kadaine take iya hada jikinta da nasa sbd shi mahaifinta ne batama iya zama idan baa kusa dashiba ta maqalqalesa indai yana kusa.
Kallan jannah tai cikin dan tinanin daya rikitar mata da tinani tace
"Kikace harda dakin Daddyna na dena shiga sai nayi aure?
To idan nayi aure saina ringa shiga dakin Daddyn kome??
Shafa fuskanta tayi tace
"No idan kinyi aure dakin mijinki kawai zaki ringa shiga banda na daddynki,
Kwata kwata dakin kowane namijin daga yanxu kin dena shiga saina mijinki har tsufa,
Idan kika shiga dakin wani zai iya cutatar dake kaman irin yanda kika ringa jin tsoro a school lokacin"
Kallanta falaq tai da sauri tana fahimtar abinda take nufi dan haka ta sauke ajiyan zuciya tana gane abinda yasaka kenan Daddynta yana rufe bedroom dinsa wasu lokutan da safe saitayita bugawa yazo ya bude mata.
Kallan jannah ta sakeyi tace
"To ke zaki iya shiga kenan tinda ke mijinkine nima idan nayi aure nima ni kadai zan shiga na nawa mijin ko??
Faduwa gaban Jannah yayi ta kalli falaq din da sauri tace
"Aa ni yanzu nima bazan iya shigaba sai matarsa"
"To ai kece matarsa Jan"
Mantawa jannah tai da fada hakan sbd rikicewan datai ta sake kallan falaq tace
"Yanxu bai tashiba inaga and ba buqatan tadashi mu tafi kawai idan ya tashi ya fito saimu gaidasa acan."
Sam falaq bata yadda da hakanba sbd bata taba zuwa ta fita ziqau batareda taga daddynta ba dan haka miqewa tai tana kama hannun jannah din tana ja zuwa hanyar master bedroom dinsa tana cewa
"To muje tare da matarsa da yarsa tinda ni kince na dena shiga ni daya"
Da sauri jannah take kokarin janye hannunta zata juya aka bude kofar Bedroom din wanda ya sakasu tsayawa cak dukansu itada falaq din suna kallan kofar.
Qamshinsa da koina yakeyi tin daga palon har koina ne ya bugo mata daga cikin kofar datake buden ta dago idanuwanta masu kyau ta kallesa.
Sanye yake da Ash balmains na wata crazy shirt me shegiyar tsada da straight wando sai tsadaddun shoes din dake kafarsa na ballies.
Fuskansa wani irin sabon sirrin kyau ne na safe wanda idan ka fito kafin ka fara hayaniya ko fita a cikin haske kake kasancewa fresh dinka wasu na kiran hakan da morning beauty ko morning freshness.
Fin karfinta zuciyarta tai ta kasa dauke fararen idanuwanta akansa tana masa wani irin kallan dayake bayyanarda gabaki daya sirrin dayake boye a zuciyarta,
Tsananin azabtuwan da zuciyarta take akan tsananin sonsa dayake maqale a cikinta ne idanuwanta ke loosing control gurin bayyanawa har idanuwan na cikowa da hawayen da batasan dasuba.
Falaq tsayawa tayi kallanta cikeda tausayawa sbd duk da ba komai take ganewa ba tasan Jannah na tsananin son Daddynta hakama a yanxu din kallo ne na ganin abinda zuciya take tsananin so amma ta kasa samu.
Ahankali ya qaro taku biyu ya tsaya a gabanta ya dan rankwafo kadan batareda ya kalli cikin idanuwanta ba ya kai bakinsa gefen fuskanta daga nesa kadan sbd kada falaq taji abinda zai fada da wata muryan data sakata qanqame hannuwanta a jikinta sbd kauri da tsananin nutsuwa da taushin muryan yace
"Me kikeson koyawa yarinyana?
Learn to control your feelings Ms,
Sbd kada ko koyar da ita irin hakan bata isa sanin kallan meye wannan ba"
Skipping bugawa zuciyar Jannah tai sbd tsananin kunya da baqin cikin maganarsa tareda wani irin qamshin dataji yana shiga hancinta wanda ta tabbatarda daga bakinsa yake fitowa kaman na lemon da mint sun hadu.
Dagowa yayi yai mata kallo daya yaga yanda idanuwanta ke cikowa da hawayen kunya da baqin ciki yayi gaba yana amsa maganar falaq a natse.
Rawa jannah taji kaman kafafuwanta sunayi
kasa riqe hawayenta tai saida suka sauko ta saka hannunta ta share tana juyowa da kyar ta biyu bayansu.
Mama na ganin fitowansu taji farin ciki ya sake cikata cikin farin cikin ganinsu tace
"Falaq meyasa ke wai bazaki girma bane kinbi kin kanainayesa bazaki bari itama jannah din ta samu damartaba."
Gaida maman yayi yana hanasu cigaba da zancen ta hanyar janyowa mama wani zancen daya san zai dauke hankalinta gaba daya.
Dining suka nufa banda jannah dataji ta kasa sakewa kwata kwata hakama taqi yadda ta sake kallansa sbd kada ya kuma tozartata.
Mama ce ta jata da kanta har Dining din ta zauna a kusa da maman saiga Sayd shima yazo ya zauna yana gaida mama itama kallanta yayi da kulawa suka gaisa kafin ya maida hankalinsa kan falaq datake gaidasa tanason basa labarai amma ba dama dole sai angama.
Suna fara breakfast din babu wanda ya sake magana hakama ita dai bata dagoba ta kallesa.
A natse taci Fried potatoes da liver sauce sai ketchup da kuma tea mara zafi sbd bata wani son zafi sosai a abinci.
Shi kansa abinda yaci kenan sai falaq da sayd da sukaci Da kwai da plantain mama kuwa kunin gyada ta hada dashi wanda yaji madara sosai yayi kauri da haske sosai.
Jannah dince ta fara gamawa amma bata bar table din ba sbd girmama su maman.
Shine ya fara miqewa yabar dining din sayd yabi bayansa sai a lokacin falaq ta dawo gurinta.
Saida mama ta gama tabar dining din itama ta miqe tareda falaq suna kokarin barin dining din Fiddausi tazo tafara tattara gurin.
Bedroom dinta ta koma ta zauna tana janyo wayarta ta sake saka kiran Dad dinta wanda basuyi magana ba da safen.
Waya ta fara yi da familynta da suka boye mata halinda Ammar yake ciki ta debewa kanta kewa sosai da wayan.
Lokacin sallah nayi tayi sallah ta sauya kayanta zuwa marasa nauyi sosau sbd ta saba bata iya wuni da kaya masu nauyi a jikinta.
Fitowa tai ta nufi kitchen dan taya Fiddausi aiki sbd zaman shirun ya isheta.
Falaq ma binsu tai kitchen din duka masu aiki suka fice daga kitchen din aka barsu sbd girmamawa.
Abincin rana din suka kammala a tare Fiddausi ta jera a dining ita kuma ta nufi dakinta ta sake wanka tanajin yar gajiya ta kwanta dan ta dan huta.
Sai yamma sosai ta fito lokacin su mama already sunci abincinsu dan haka ita kadai ta nufi dining din ta zauna falaq na islamiyya.
Gidan tsit ba hayaniya sbd Fiddausi na kitchen mama kuma tana can palonta.
Abincin ta zuba brown spaghetti ce dataji kidney da liver dasu vegetables sai kazan da aka gasa da vegetables.
Daidai cikinta ta zuba abincin ta zuba orange juice a cup tana fara ci kenan Fiddausi tazo dining din ta saks jera wasu abincin tana barin gurin qamshinsa ya doso gurin ta dago ahankali ta kalli hanyar shigowa dining room din daidai yana sako kai sanye da kayan shan iska alaman ya dade da dawowa daga aiki haryayi wanka.
Fararen qafafunsa da gashi me kyau ya kwantawa taiwa kallo daya ta juyo da kanta sbd three quarter Fendis ne a jikinsa farare da suka maidasa wani lafiyayyan Kyakkyawan matashi me ji da hutu da aji.
Shi kansa baiyi tinanin ganinta a dining dinba a daidai wannan lokacin dan haka ko kallanta bai sake yiba saida ya zauna ya kalleta itama shi ta dan dago zata kalla ta gaida zancensa ya katsata da cewa
"Akwai dabiun na rashin tarbiya da kikaxo dasu da kike buqatan sauyawa sbd tarbiyan tawa yar,
Na koyawa yata girmamawa da gaida na gabanta gashi ke da alama baki samu hakan ba"
Qarasawa yayi yana bayyanarda takaicinsa da mamakin rashin hankali da tinani irin na zaadens da babu abinda suka iya sai son zuciya da haryanzu suke a cikinsa.
Dagowa tayi idanuwanta na sauyawa sosai da tsananin ciwon zancensa ta bude baki jiki a mace zata gaidasa din ya daga mata hannu yana nuna mata abincin dayake kan table din da hannu fiskansa a daure sosai baya ko kaunar kallanta a gabansa.
Dan sunkuyar da kanta tayi ta hadiye hawayen